Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

AMATULLAH ƳAR UNCLE Book 1 Complete Hausa Novel Document by AMATULLAH ƳAR UNCLE Book 1


AMATULLAH ƳAR UNCLE Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 16493



AMATULLAH ƳAR UNCLE Book 1

Reading Time: 1 Hours

Added On: 13, Nov 2024

Author: Ummu Aisha ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08107640933

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 90.27 kb

File Type: txt

Views: 632+

Download: 331+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: [8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 1&2*

Yanayin garin na Kano yau cike yake da ni'ima, sai iskace mai sanyi take kad'awa a ko ina sakamakon hadarin da ya wuce, kowa ka gani yana harkokinsa cikin farin ciki da walwala.

A cikin unguwar ta Hausawa wata farar mota 'kirar........... ta tsaya 'kofar wani kyakkyawan gida, sau biyu matu'kin motar ya matsa horn mai gadi ya bud'e masu get sai matu'kin motar ya shiga ciki.

Bayan ya samu guri yayi parking wasu matasa ne guda biyu masu kama da juna suka fito, sai dai daga dukkan yanayi d'ayan zai girmi d'aya, babban ri'ke yake da yaro d'an kimanin shekaru biyu a hannunsa.

Daga bayan motar kuma wata mace ce ta fito sai wata 'yar budurwa da ba zata wuce shekaru sha biyar zuwa sha shida ba, sai wasu yara mace da namiji da suka fito duk daga bayan motar.

Cikin d'oki wannan 'yar budurwa tayi hanyar cikin gidan da sauri, d'aya a cikin mazan nan yana mata magana "ke Amatullah wa zaki bari da d'iban kayan" amma ina ko sauraronsa bata yi ba ta shigewarya cikin ginin gidan ta barsu a wurin.

Bayan shigewarta ne babban ya dube shi tare da cewa "ai kaima kasan Amatullah da Hajiya, yadda take d'okin ganin tan nan ban ce ta ji abinda kake cewa bama."

Murmushi kawai ya yi yace "barni da ita kawai Yaya, ai zan shiga gidan na same ta ne."

Daga haka ya zagaya ya bud'e booth ya fito da babban trolly da kuma 'karama, dole shine ya d'auki babban matar kuma ta d'auki 'karamin suka shiga cikin gidan gaba d'aya.

Ita kam Amatullah tana shiga cikin gidan da gudu ta nufi dattijuwar matar da ke zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka 'kawata parlour'n da su ta fad'a jikinta tana cewa "nayi kewarki Hajiyanmu."

Cikin fara'a dattijuwar tasa hannu tana 'ko'karinta ture ta daga jikinta tare da cewa "shiyasa kike 'ko'karinta karyani ki sa 'ya'yana garari, tashi min daga jiki ke da bakya girma."

Gyara kwanciya Amatullah tayi tana cewa "wata nawa ban hau cinyarki ba, kawai ki barni na more."

Sallamar da akayi a ba'kin 'kofar parlour'n ne yasa Hajiya ba ta ce komai ba ta mayar da hankalinta ga masu shigowa fuskarta d'auke da fara'a tana yi musu sannu da zuwa.

Haidar da ya shigo daga ''karshe ya hango yadda Amatullah tayi d'are-d'are a cinyar Hajiya, ai kuwa ya zabga mata harara tare da cewa tashi daga jikinta kafin ranki ya 6aci, uwar 'yan son jiki baki da aiki sai na zama a jikin mutane."

Zum6aro baki tayi yayin da Hajiya tace "to kai ina ruwanka? Jikinka ta hau ko nawa?

Ai kuwa nan Uncle Bashir da ke zaune shida Aunty Habiba suka sa dariya "Uncle yace kai matsalarka kenan Haidar baka gani ka 'kyale sai ka tanka, ka san dai ba'a shiga tsakanin Hajiya da Amatullah, duk wanda ya shiga kuwa shi zai ji kunya."

'Kara had'e fuska yayi yace "ai dama kai da Hajiya ba kwa son laifin Amatullah duk abinda tayi bakwa so a kwa6e ta, shiyasa takewa mutane sangartar da ta ga dama.

Gaba d'ayansu dariya su kai, ganin yadda yayi da fuska kamar 'karamin yaro.

Suna cikin gaisawa ne me aikin Hajiya ta fara shigo da abinci, abinda zai baka tabbacin dama an san da zuwansu.

Zuruf Amatullah tayi ta mi'ke ta isa gaban warmers d'in ta fara bubbud'ewa don ganin abinda ke ciki, ai kuwa tana ganin alkubus fuskarta ta cika da farin ciki da fara'a, tace "yauwa Hajiyata shiyasa nake yinki."

Nan take ta d'auki plate ta fara serving d'in Uncle Bash, ta kai gabansa ta ajje sannan ta zubawa Aunty nata, sai ta zubawa sauran yaran.

Ta mayar da kallonta gurin Haidar tare da cewa "Uncle Haidar a zuba maka?"

Harara ya zabga mata tare da cewa "a'a karki zuba, tunda kinyo guzirin abincin ne kin taho da shi."

Hajiya tace "wai me yasa kai ba'a yi maka gwaninta ne? Yanzu daga tambaya sai ya zama laifi? Ai sanin tsurfarka tayi, yanzu idan ta zuba ma in baka ga dama ba cewa zakai baka saka ta ba.

Ita dai Amatullah bata 'kara magana ba ta zuba masa abincin ta kai gabansa ta ajje, sannan ta d'ebi dai-dai wanda ta san zata iya ci ta zauna a gefe ta fara ci.

Bayan kowa ya gama cin abincin ta tattare kwanukan da su kai amfani da su, ta mayar kitchen, tana dawowa parlour'n ana kiran sallar la'asar wannan yasa mazan mi'kewa suka fita don yin alwala su tafi masallaci, su kuma matan kowacce ta nemi inda zatai alwala don gabatar da tata sallar.


*Ummu Aisha*
[8/29, 2:26 PM] Oum Ai'sha: *AMATULLAH*
*('Yar Uncle)*

*By*
*Ummu Aisha*



*💦AREWA WRITER'S ASSOCIATIONS💦*


*Wannan littafin na kud'i ne, idan kina so zaki iya turo N200 ta wannan account d'in 0019792794, sannan sai ki turo shaidar biya ta wannan layin 08107640933, ko kuma katin waya MTN ta wannan layin dake sama.*

*Free page 3&4*

Tun bayan da suka fita babu wanda ya dawo cikin gidan sai dai jin 'karar motarsu su kai, alamun dai dake nuna sun bar gidan, su kuwa su Amatullah kowacce parlour ta dawo har Hajiya, nan suka zauna ana ta hirar yaushe gamo, sai labari suke bawa Hajiya.

Wajen biyar da rabi na yamma Hajiya ta d'auko mukullai ta bawa Amatullah tace su je ita da Baba Mairo (wato mai aikin Hajiya) su share gidansu, ba sai an jima sun koma a tsaya sharewa ba.

Babu musu Amatullah ta kar6i mukullin, ta jira Baba Mairo suka fita, Muhammad 'karamin yaron Aunty Habiba sai rigima yake zai bi ta, ita kuma tace "babu in da zanje da kai, haka kawai ka hana ni aiki da 'kiriniyarka.

Gidan da suka shiga a Jere suke da gidan Hajiya, sai dai shi a rufe yake saboda babu kowa a gidan.

Duk da ba wani dad'ewa sosai sukai da barin garin ba, amma sun sami gidan yayi 'Kura sosai, kasancewar babu kowa a gidan, sun sha aiki sosai don sai da sukai sallar magriba sannan suka gama komai, suka rufe gidan suka koma gidan Hajiya.

Bayan sallar isha Alhaji Babba suka shigo gidan yana kan gaba, yayinda matsan 'ya'yan nasa ke biye da shi a baya.

Kai tsaye parlour'nsa ya wuce, ai kuwa da sauri Amatullah ta mi'ke zata bishi, sai Haidar ya kama harararta tare da cewa " Allah yasa naga 'kafarki a parlour'n Alhaji ki ga yadda zamu yi da ke, daga dawowarsa ba zaki bari ya huta ba zaki je ki takura masa."

Hajiya da ke fitowa daga d'aki tace "wai Haidar ina ruwanka da takwarata ne? Ka d'aurawa yarinyar nan zani da tsanani a gidan nan fa, wallahi za mu sa 'kafar wando d'aya da kai."

Aunty Habiba da ke zaune tana sauraronsa tace "ina ganin kishi yake ta zo zata tare masa fada tunda shine auta, yanzu kuma zata 'kwace duk kulawar da kuke bashi ku mayar kan......."

Kafin ta 'karasa ya katseta tare ta da cewa ashe kin gane inda matsalar take, idan yarinyar nan ta zo daga Hajiya har Alhaji mantawa suke da ni, komai sai dai kiji sun ce ita."

Bashir da har ya kai hannunsa jikin 'kofa zai bud'e yana son zuwa parlour'n Alhaji don su gaisa ya juyo ya ce "amma dai kai anyi babban banza mai kishi da 'yarsa."

Hajiya ce ta cewa Amatullah "kinga takwarata tashi ki je ku gaisa da Alhaji tun kafin ya fara cigiyarki."

Ai kuwa da sauri ta mi'ke don dama kad'an take jira.

Tana shiga bata zauna ko ina ba sai gefensa, sannan ta gaida shi, shima cikin sakin fuska ya amsa mata, abinda ke nuna akwai 'kauna da sha'kuwa tsakaninta da shi, nan yake tambayarta karatunta, ta bashi amsa da "Alhamdulillah."

Can ta d'anyi 'kasa da murya yadda Uncle Bash dake zaune a parlour'n ba zai ji abinda take cewa ba tana magana, dattijon ya d'ago kai yana kallonta sai kuma yasa hannu ya dungure mata kai, "ai dama nasan aikin kenan, tun da Kura ta zo, wai Sa'adatu yaushe ne zaki daina kwad'ayi?"

'Bata fuska tayi kamar mai son yin kuka, cikin
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download AMATULLAH ƳAR UNCLE Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album