Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

DAN DABA Complete Hausa Novel Document by DAN DABA


DAN DABA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 51072



DAN DABA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 03, Oct 2024

Author: Mrs Sadauki ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +22795045822

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 252.23 kb

File Type: txt

Views: 1093+

Download: 2030+

Last download: 3 days ago

Description/Story: *ƊAN DABA*💞
```love and romantic story```


` ~``MRS SADAUKI~ ``` 💫

*Dedicated* to My Babbar Yaya Nafissa Laouali Rabo🥰

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*☀️

____________________
BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

*FREE BOOK NE in kun yi comments shi zai sa na gane kun karɓe shi labarin ya maku kenan,ban buƙatar stickers ko tnx ban son su yadda na ɓata lokaci nayi maku typing ku bada time ɗinku kuma ku yi comments miye duniyar yi min in yi maka ne*🤷🏻‍♀️

Page 1-2


Yaf-yaf-yaf haka ruwan saman ke sauka a hankali yayinda mutane suka fara guduwa,wasu na tsayar da abun hawa wasu kuma na ɗaukar motocin su.
Ganin mutane na watsewa ne ya jawo hankalin Leemat ta waro ido lokacin da idonta yayi tozali da baƙin hadarin da ke wuluniya tare da gangamuwa,da ƙarfi ta furta "hadariii"zumbur Siya ta miƙe tana lalubar ƴar sandarta ta ƙarfe tare da fiddo ido waje cikin muryarta mai kama da ta yara tace "Leemat ki tsayar mana da abun hawa please kafin ruwan ya fara sauka"Leemat wacce ke bakin shagon ta ƙaraso ta kama sandar ƴar uwarta ta tace "ina wani abun hawa a nan tuni ƴan adaidaitu suka tsaya zo mu tafi ko Allah ya datar da mu a hanya"tana faɗin haka ne tare ɗaukar ledar kayan da suka saya.
Leemat na gaba Siya na biye da ita a baya yayinda ƙarfin ruwan ya ke ƙaruwa ahankali,sun yi nisa sosai amman shiru babu abun hawar da ke wucewa kasancewar dare ya tsala sosai ga kuma ga hadari shiyasa mutane suka yi zafin shigewa gida.
Kwalta suke bi suna yin direction ɗin da za ta sada su da gidan su har suka kawo rond-point gouvernorat tsit titin ya ke,kamar waƙiya haka Leemat ta ga giftawar mutum a gaban su cak ta ja ta tsaya har sai da Siya ta kawo mata karo.
"Miye kuma kika tsaya"Siya ta tambaya kafin ta kai ga bata amsa sai jin kukan kare suka "huhuhu🦮"yadda ya ke kukan ya ke tunkaro su shi ya fi komi ɗaga masu hankali,Siya wacce ba gani ta ke ba ta ƙanƙame Leemat tana mai jin wasu hawaye suna shirin zubo mata.Ba ta ida jingina da jikinta ba taji Leemat ta zuba da gudu a waje,ta ɗaga ƙafa da niyyar guduwa ta ji ta kaiwa wani ƙaton mutum karo ko kafin ta kai da tambayar wanene taji ya sungumeta yayinda kukan karen ke take masu baya alamun mai karen ne.
"Wayyo Leemat ki zo ki cece ni zai kashe ni"Siya ta faɗa kanta na ƙasa dan bisa kafaɗar shi ya ɗora ta, Leemat wacce tayi ɗan nisa ta tsinkayo murya Siya abun ka da ƴan uwantaka ta jini sai ta dawo baya tana kiran sunanta "Siya? Siya?Siya?"ko kafin ta ƙaraso ya hahe ƙaton babur ɗin shi routier 🏍️ ya danna mashi huta baƙin karen shi kuma na take mashi baya a guje.
Zaman ƴan bori Leemat tayi tana mai ɗora hannu a kai,daidai nan kuma wata adaidaita sahu ta hasketa shi ya taimake ta ya kaita gida.


Da isar su ya buɗe ƙofar gida ya shiga cikin ɗaki can tsakiyar gado ya cilla Siya,hasken ɗakin ya kunna tare da AC.Zumbur ta miƙe tace "wanene kai?mi nayi maka da za ka raba ni da ƴar uwata?"ko kallonta bai yi ba sai ƙarasawa ma yayi bakin mirror ya fara ɓalle buton ɗin rigar shi wacce ta jiƙe sharkaf da ruwa,faɗaɗen ƙirjin shi wanda ya ke da kwantacen gashi ya shafa kafin ya ɗaga duk hannuwan shi biyu sama hakan ya baiwa murɗaɗin muscules ɗin shi damar ƙara haɓaka.
Sai da ya ɗan jinjina su sannan ya riƙe ƙugu ya na kallon kyakkyawar fuskar shi mai ɗauke da saje da manyan ido,sai jajayen laɓan shi masu sheƙi murmurshi ya saki wanda ya baiwa dimple ɗin shi lotsawa.
Sautin murmurshin shi ne ya sa Siya saurin ɗagowa duk da ba ta gani amman taji inda sautin ya fito,tasowa tayi ta nufi gun tare da haɗe hannuwa waje guda alamun roƙo tace "dan Allah kar ka cutar da ni ka taimaka ka mayar da ni Mami na za ta shiga tashin hankali, please ni Makauniya ce fah"juyowa yayi ya na facing ta ya na kallo kyakkyawar Makauniyar fuskarta,jawota ta yi ya na mai furta "shuuut!ba sai kin gaya min ba na fi ki sanin ke ɗin Makauniya ce sannan ke karan kan ki ma dan haka kar ki yi ɓarnar bakin ki na fi ki sanin ke ɗin wacece"murya na ɗan rawa tace "wanene kai?mi nayi maka to da za ka kidnapping ɗina?"murmurshin da ya zame mashi jiki yayi yace "soyayya ce,I love You SIYAAA son ki ya sa haka"fizgewa tayi tace "ƙarya ce mai son ka ba zai taɓa cutar da kai ba"ya fizgota yace "ki rufe min baki in ba so kike na hukunta ki ba,ni age mate ɗin ki ne da za ki ce ina ƙarya"kwaratsin muryar shi ya firgitata ainun hakan yasa ta lafe a ƙirjin shi ta fashe da kuka,bayanta ya shiga bubugawa "yi shiru babyna nima ban so na tsorata ki ba,laifin ki ne ban son raini ko kaɗan"ya faɗi haka ya na mai ɗago fuskarta ya ɗora bakin shi kan tausasan lips ɗin ta.Har ga Allah ba ta son kissing ɗin ta da ya ke amman tsananin tsoron shi ya hanata yi mashi magana,gefen cikinta ya riƙe tayi saurin ja da baya tana mai ɗora hannuwanta akan ƙirjin shi da zumar ƙwace bakinta sai dai bai bata dama ba.
Sai da ya gaji dan kan shi ya ƙyaleta "ki cire kayan jikinki ki saka wasu kar mura ta kama ki"ya faɗa a wahalce,baki na ɗan rawa tace "ban iya ba"hijab ɗin ya kama zai cire mata tayi saurin riƙe shi gam tare da girgiza kai alamar ba ta so "babu abinda zan yi maki Siya juste canza maki kaya zan yi"yadda yayi maganar cikin taushi ya sa ta bar shi ya sauya mata kaya zuwa wata doguwar rigar barci mai nauyi.
Ac ɗakin ya rage lokacin da ya shimfiɗeta a bed, ya shiga ya watsa ruwa sannan ya shirya tsaf cikin kayan barci.Kamar wata matar shi haka ya haye gadon tare da ja masu blanket,wayar shi da ke bisa didilin gado ya ɗauka yayi ƴan danne-danne tare da karawa a kunne.
Jin ta na ta sonné ba'a ɗaga ba yasa shi sanya Hand free "Weeliam xava cmnt vas tu?"murya wata mata ta faɗa cike da fara'a dan ka na jin sautin murmurshin ta, "je vais bien Maman ya kike ina Miki?"ya faɗa ya na juyawa Siya baya.
Tayi dariya tace "ga ta nan kusa da ni tace na faɗa ma ka kawo mata mijinta tayi kewar shi" dariya Weeliam yayi yace "soon za ta ganin shi nima na samo tawa matar"cike da murna Maman tace "congratulations mn bb"yace "Merci à demain muaaah"ya faɗa ya na kashe wayar tare da juyawa ya jawo Siya wacce ke kwance lamo tana sauraren shi tare da juya sunan WEELIAM a ranta.
A tare suka sauke numfashi ya jaye pilow ɗin da ta aza kanta ya mata remplacer da hannun shi na dama yayinda ya zagaye na hagun kan ruwan cikinta.




Tas-tas haka Mami ta wanketa da mari tace "shirmen banza kenan da ya ɗauke ta miyasa ba ki bi bayan shi ba?to maza ki fice min daga gida duk gidan ubanda kika kaita sai kin fito da ita kuma ki gaggauta kafin labari ya isarwa ga Abban ku"Leemat ta ɗago da jajayen idonta ta kalli Mami tace "ina zan ganin shi Mami?ta yaya ma da hankalina zan bi bayan *ƊAN DABA* in Fab ya kashe ni"
"Da kashe ki ɗin yayi ai da ya fi sauƙi kan azabar da Abba zai jajaga maki"cewar Laila tana kuka,dariya Jasmine tayi tace "wai kuka ne za ki yi?tab ai ba zan ɓarnar hawayena ba dan kuwa duk wanda ya ji wannan zance ya san shiri ne ba gaskiya ba ne tunda sai da aka hanata fita da Siya amman ta nace kan za ta kula da ita sosai.To yanzu ki faɗa min miye sunan wannan shirin Film ɗin da kika tsara?ohoho wai ma in tambaye ki ya aka yi kika san da *ƊAN DABA*
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download DAN DABA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album