Join Our WhatsApp Group

MATA IYAYEN GIJI Complete Hausa Novel Document by MATA IYAYEN GIJI


MATA IYAYEN GIJI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 22015



MATA IYAYEN GIJI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Sep 2023

Author: Mrs Bukhari ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gawurtattu Biyar

Author Phone : 08104334144, 08179523215, 07068606171

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 125.26 kb

File Type: txt

Views: 551+

Download: 165+

Last download: 1 day ago

Description/Story: MATA..
IYAYEN..
GIJI

DAGA ALƘALAMIN
BADI'AT IBRAHIM
(MRS BUKHARI)

(GAWURTATTU UKU)

( WANNAN LITTAFIN BA ƘIRƘIRARREN LABARI BANE. LABARINE DAYA FARU A ZAHIRI. LABARINE MAI CIKE DA ƊUMBIN DARASI. DUK WATA MACE DA TACI KARO DA LABARINNAN, TAYI ƘOƘARI TA BIBIYESHI HAR ƘARSHE. ZATA AMFANA DA ABUBBUWA DA DAMA.)



LAMBA TA ƊAYA

SAMFOTI

SADAUKARWA:
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN KACOKAM ZUWA GA JAM'IYYAR MATAN AREWA. ALLAH YA ƘARA ƊAUKAKA WANNAN ƘUNGIYA.


GAISUWA: Gaisuwar ban girma a gareki, shugaba uwa jagorar mata. ( Hajiya Rabi Saulawa. President ta jam'iyyar matan Arewa) Ina miƙa saƙon gaisuwata a gareki da ahalin gidanki baki ɗaya.

JINJINA:
ina miƙa jinjinata ga dukkan wata uwa ta faɗin duniya baki ɗaya. Mata iyayen giji.

ƘAWAYENA:
Maman Khairat. ( Ke alkhairi ce a rayuwata)
Maman Yaseer ( ƙawar arziki)
Ummu maheer miss Green ( Mai farar zuchiya)
Ummu Affan Fatima Sunusu Rabi'u. ( Ke ta musamman ce)
Hajjon Bakori ( Ƙawar amana)
Anty Laila Ali Othman ( matsayinki da banne)
Ummu Affan

Da sauran ƙawayena da ban kira sunanku ba. Kuna da yawa ne.


GAISUWA ZUWA GAREKI UWAR ƊAKINA:
ANTY HADIZA BARA'U GIDAN IKO. SARAUNIYAR MARUBUTA, INA JINJINA BAIWARKI, KUMA INA AMFANA DA RUBUTUNKI"



KATSINA
ƘARAMAR HUKUMAR BAKORI:

LAILA:

Wasu shekaru da suka shuɗe a baya can_can:

So! So!! So!!! Itace igiyar da take zarge da ko wanne ruhi. Wannan igiyar ita ta jefani a cikin gadar da taima rayuwata mugun bugun da saida ta haddasa ma rayuwata karayar da babu maɗorin da zai iya kawo mun ɗauki. Ashe na shiga ban ɗauka ba baya fidda ɓarawo, tunda so ba goriba bane balle kace zarenta iyakar haƙori zai zarge ma, in ka gaji kayi fatali da'ita. Dama ace ina da ƙafafun da zan iya shure so, ko kuma sandar da zanbi so da mugun gudun da saina halakashi kowa ya ma ya huta. Akace so Zuma ne, ni dana sha sai ya zame mun farar guba mai ruguza gangar jiki, so ya maisheni nakashashshiyar ƙarfi da yaji. Kallon mai lalura akeyi mini, har wasu na danganta hakan da shafar junnu, ba su son so bane yabi dare ya durƙusar dani ba. Na tattare kaya na daga majalisar so, ni da wannan majalisar haihata_haihata.






Ƙunshin kayana dana ƙunso a ɗankwali mai ɗawusu na yar a filin tsakar ɗakin mahaifiyata. Idanuna caɓe_caɓe da hawayen daya haɗu ya dame da farin kwallin dake idanuna. Hakan ya saka fuskata ta ƙara yin baƙi. Mahaifiyata ta dubeni tace.
"Karfa kice mun yaji kikayo da yamma sakaliya haka Laila, baki da hankaline, ko so kike ki zubar mana da mutunci a gari, ince dai surukanki, da facalolinki basu san yaji kika yo ba ko?" Cikin in_da_in_da nace."
Ba yaji nayo ba Inna, Auren Shehu ne na dena. So yake ya kashe ni Wallahi".
Bub, ta bige mun bakina da bayan hannunta, take bakina ya fashe ya soma zubar jini. Ga tsohon ciki a jikina haihuwa ko yanzu ko anjima.
"Kul kika ce zaki toni asirin mijinki, babu kyau yin hakan sam, labule ai asirin ɗakine. Ki ɗauki ƙunshin kayanki, tunda duhu ya soma rufawa, ki yi komawarki ɗakinki tun kafin mahaifinki yazo ya tadda ki, wallahi bazaki ji da daɗi ba. Ba tsohon ciki gareki ba, wallahi ko haihuwa zaki yi yanzu, saiya saɓa miki. Kuma kinsan baki da wajan zama a gidannan ai. Shashashar kawai, yara basu san darajar aure da miji ba, sai shirme, da bankaura kaɗai suka iya a gidan mutane." Ni dai ina tsaye, sai shirɓine hawaye nake yi da bayan hannuna. Muryar mahaifina muka jiyo yana kwaɗama Innata kira.
"Ke Ta Asibi, Ta Asibi ke" Mahaifiyata sabida kaɗuwa kasa amsa kiran tayi. Labulen ɗakin ya yaye, ya doge a baƙin ƙofar, yana kallona.
"Dan ubanki ashe da gaske ne ke aka gani ɗin kenan?" Ƙunshin kaya na dake ƙasa ya duba, ya ɗago ya zuba ma mahaifiyata idanu. Dani da'ita duk kawunanmu a sauke suke.
"Ta Asibi, yaji Lailan tayo shine kika bata wajan tsaiwa, kin tsaya sauraronta kenan ko, sabida zaki bata mafita?".
"A'a Malam Haram giya a gidan liman. Ban tsaya naji komai ba, kuma yanzu zata koma dama. Laila ɗauki ƙunshin kayanki ki koma ɗakin mijinki, aljannarki tana ƙarƙashin tafin ƙafarshi, kiyi mishi biyayya. Duk macen duniya da kika ga tayi lib a gidan mijinta, haƙuri take yi, kuma tana duba makomar rayuwar yaranta. Aure wata tara, baki taɓa zuwa ganin gida ba sai yaji? Wallahi in kika sake yin wannan kuskuren ni da ke ne, tunda ko saɓani baki taɓa ganin mun samu da mahaifinki ba, ballantana harta kaini ga yin yaji." Cewar mahaifiyata kenan. Da jin muryarta cike take da tsantsar tausayina.
"Au jawabi ma kike yi mata? Bari kiga."
Shigowa mahaifina yayi, banyi auneba ya rufeni da duka takota ina. Ko tausayin abunda ke ƙunshe a cikina baya ji. Wai me yasa maza suka ɗauki mace tamkar baiwar da su ka siyo a kasuwa da silalla danta bauta musu ne?" A guje na fita da ƙunshin kayana, nama mance cikine a jikina, tsabaragen kaɗuwar da nayi. Da Kishiyar mahaifiyata naci karo a tsakar gida. Ina wuce ta nayi da mugun gudu. Mahaifina ya biyoni da mugun gudu shima har waje. Gudu nake yi sosai yana bina, ina kukan fitar rai, sai da mu kai nisa, sai naga mahaifina ya dakata., Yana nuna ni da karar dake hannunshi"
Tsaiwa nayi nima na dinga sauke numfashi, ga wani irin haki da yake ta taso mun, irinna masu tsohon ciki. Haka naita dawowa baya cikin jan ƙafa, har zuwa tashar (Bodi) Keken shanu.
Malam zaka ƙarasa Ƙauyan unguwar Alƙali?"



Kauyen Unguwar alkali dake qarqashin karamar hukumar Bakori ta jahar katsina. ya kasance kauyene daba makarantar boko, babu ta addini, ba su da wutan lantarki, ba asibiti, ƙauyene dai irin ƙayau ɗinnan zamu iya cewa. tunda ko ilimin addini bai wadacesuba, sannan basuda wadataccen ruwa haka suke rayuwarsu.
A qauyen sau daya ake aurar wa shine lokacin kaka wato hatsi yadawo gida, suna noma sosai da sosai. In aka tashi biki, Abokan ango suke girka abincin daza aci aranar daurin aure wannan al adarsu tun iyaye da kakanni in aka kai amarya da yamma, to adaren ranar akwai wasan da suke yi tsakanin abokan amarya, da abokan ango, Wanda abokan ango zasu zuba kudi, na amarya ma zasu zuba. Wanda nashi yafi yawa to shi ya ciri tuta, za kuma a yi mishi kyauta ta kayan noma, ko buhun masara, ko dawa, ko gero. Wannan kenan.
Dubana matuƙin bodinnan yayi, yace.
"Gaskiya bazan ƙarasaba, iyakacina Rimi nan dandali, anan zan tsaya." Bance mishi komai ba na shiga cikin Bodinnan na zauna. Mata ne su biyu a cikin Bodin, ko wacce da goyo a bayanta. Gaggaisawa mu ka yi da matannan. Sannan mu ka ci gaba da zaman jira, saida muka cika mu goma cib matuƙin Bodin ya ja linzamin bakin shanun suka soma tafiya." Tafiyace mara sauri sam, dan hanyace mai cike da ciyayi, da gonakai, da kauci. Baka jin ƙaran komai a hanya, sai haushin karnuka, da kukan kwaɗi, da kukan gyare. Da duk wata dabba da dare ne yake zama rana a wajanta. Tsoro ne fal raina, dan muna fama da mayu sosai. Munyi tafiya mai ɗan karen nisa kafin muka iso Rimi dandali. Sai lokacin na sauke ajjiyar zuchiya, dan ina jiyo hayaniyar samari da ƴan mata, ga hasken wutar kara ina hangowa. A hankali na sauka, dan jikina yayi mugun laushi, ga ƙafata bata da wani ishashshen lafiya guda ɗaya, ta ɓarayin hannun dama. A bakin dandalin na tsaya, wajan masu sai da ƙwalam da maƙulashe. Dangin Algaragis, carbin malam, hana kwalla, alawar ɗinya, ɗan ta matsitsi, kwaskwaro, kantun riɗi, tsami gaye, ƙurmus, hallaka kwabo. Ga ɓangaren kuma masu, ɗan gauda, bagalaji, tako, rama, dinkim, ɗan malele, wara, da sauransu.
Ke bani Tako na sile biyar."
Hannu nasa a cikin lalitata na kwaso tsaabar dake ciki, na ƙirga tsabobinta sile biyar na bata, ta zuba mun tako a leda, harda ƙara mun mai da albasa mai lawashi." Tako wani abin maƙulashe ne na katsinawa, anayin tako ne da kofaton dabba, saniya, rago, akuya. Katsinawa suna mugun son tako. Duk da gidan da ake sarrafa tako baya ko iya shiguwa ta daɗi tsabar wari. Ina tafe ina cin tako na, na ɗaura ƙunshin kayana a kaina. Wani ruwane, naji yana bin ƙafata dalalala, kuma kamar ruwan yana da ɗan yauki. A haka dai naci gaba da jan ƙafata a hankali. Wata ƙatuwar mage ce tazo ta wuceni. Gabana ya yanke ya faɗi, yaron dake cikin cikina shi kanshi saida ya zabura.
"Laila Uwar maza" wannan magen naji ta faɗa, da wata dattijuwar murya. Nan na ya da ƙunshin kayan nawa na ari na kare. Gudu nayi sosai, ta tsakiyar maza masu kwana a ƙofar gidajensu na ratsa na shige gidan aurena a guje." Tsattsallake mata, da yara, dake kwance a tsakar gida nayi. Dan tsakiyar lokacin zafi muke yanzu, ɗaki baya shiguwa, garin Katsina ƙasace mai zafi, kasancewar tana maƙwabtaka da ƙasar dake da sahara." Garam na tura ƙyauran ɗakina na shiga."
Shehu na gani a kwance a maulidi na, +gado mai rumfa) Babu ko wando a jikinshi, ya shirɓine jikinshi da man shafawa mai gurguwa, sai wasa da jikinshi yake yi, a ƙoƙarinshi na son gamsar da kanshi." Kuka na rushe dashi kawai, ga wani irin kaɗuwa da hantar cikina take yi, marata ma sai tsungulina take yi.
Da sauri Shehu ya diro a gadonnan, ya riƙoni yana ɗan jijjigani.
"Manene Laila, ko Babane ya biyo ki da gudu har nan?
Bai bani zarafin yin magana ba, ya shiga laluben hakkinshi. Tsabar takaici, ban iya cewa dashi komai ba, a halin da nake ciki ya shiga biyan buƙatarshi, wanda hakan ya ɗebemu mintici da dama, marata ce ta shiga ciwo ganga_ganga, bayana da ƙafata mai lalura sai amsawa suke yi. Nayi yunƙurin ture Shehu amman na kasa. Ƙara na saki mai amon da sai da kowa ya jiyo. Da sauri Shehu ya sake ni, ya rarumi wandonshi da ƴar shararshi ya saka.
Wayyo zan mutu, Shehu ka kirawo mun Matar malam, haihuwa zanyi, Shehu zan mutu." A gaggauce Shehu ya fita tsakar gidan, ya barni a kwance a leda ina juyin azaba."


Mrs Bukhari ce


Ku kasance tare dani, dan karanta wannan littafin mai ɗauke da salo irin na rayuwar iyayenmu ta shekarun baya. Labarine mai ɗumbun darasi. Duk macen data karanta littafinnan na tabbatar zata ilmantu da ilimi mai tarin yawa.


Gawurtattu uku,zasu buɗe aji na musamman da azumi,don koyar da girke girke na musamman na azumi don kun san mu mata ƴan adone,wajen yin girki in akace baki iya girki ba to tabbas mijinki fa kullum yana kan hanyar yawon restuarent, sannan idanuwansa suna kan ƴammata saboda ya samu sarauniyar girki, kada ki bari a barki a baya don gwangwaje me gidanki.

Domin nema ƙarin bayani,sai ku tuntuɓi waɗannan numbobin👇🏻👇🏻

07068606171
08104335144
08179523215

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*🤟GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARA TA 2023🤟*
*_Ina kuke masoyan gawurtattu uku ga su ssun dawo muku da wasu sabbin labaransu a wannan sabuwar shekarar, wannan karon salon gawurtacce ne, ku hanzarto kar ku sake ayi babu ku._*
_Sun shirya tsaf a wannan karon don kawo muku labaran da zakuyi fahari da su, tafiyar mai zafi ce sannan ta musamman._

*_Haziƙai kuma gawurtattu ukun sun shirya ne domin kawo muku gwarazan labaran da zaku yi alfahari da su._*

*MATA IYAYEN GIJI*
_Mrs Bukhari_


*INDA BA ƘASA..!*
_Ummu Maheer_


*KARO ƊAYA...!*
_Ummu Affan_


_LITATTAFAN GABAƊAYA AKAN FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA 1K_


1 500
2 700
3 1000

_Kai tsaye zaku tura kuɗinku ta wannan account number ɗin._
2212328303
RABIATU BASHIR
Zenith bank

_Don Allah wannan karon ba ma buƙatar katin waya, idan baka da account to kaje POS ka bada 50 kob 100 a cikin kuɗin a turo ta account number please._


_Ƴan ƙasar Niger kai tsaye zaku turo ta nan._ 0706 860 6171

*DOMIN NEMAN ƘARIN BAYANI A TUNTUƁI ƊAYA DAGA CIKIN LAMBOBIN NAN.*

0810 433 4144
0817 952 3215
0706 860 6171


*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU UKU A SABUWAR SHEKARAR 2023 SABON SALO SABON TAKU.*


_TEAM GAWURTATTU UKU 2023_

*Mrs Bukhari ce 👉🏾👉🏻*
MATA...
IYAYEN..
GIJI


BADI'AT IBRAHIM ( MRS BUKHARI)
( GAWURTATTU UKU)




LAMBA TA BIYU
SAMFOTI


*_🔥GAWURTATTU UKU🤟2023_*

*_TALLAH TALLAH TALLA🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️_*

_A HAYYEH SAMAH MATAH💃💃💃💃💃🏻💃🏻_
*Ku shiga wannan link ɗin don zaɓar kaya masu rahusa👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻*
https://chat.whatsapp.com/G6BmHCxso0rDZyWVQGgYYj
----------
No
07067964894

*_INA KUKE MATAN KWARAI MATAN DA SUKA AMSA SUNAN SU NA MATA A DUNIYA KU GARZAYO KUZO M A C DON ZABEN NA KWARAI KI DAURA ASAN KIN DAURA SAI ATAMFA DA LACE DA SHADDA, MATERIAL WITH SHOE'S AND BAG WITH JEWELRIES DAGA MAMAN ANNUR COLLECTION._*
*_ANAN KWALIYA ZATA MAIDA KUDINTA GAREKI, KIFITO ASAN KIN FITO KIN FASA TARO SAI M.A.C AKAN FARASHI MAI RAHUSA SAYEN NAGARI MAIDA KUDI GIDA IYA KUDIN KI IYA SHAGALINKI🤝_*
*_TANA KANO TANA AIKAWA KO INA DA IKON ALLAH A CIKIN AMINCIN DA YARDAN UBANGIJI_*
*_YAN UWA INA MASU SON SUYI SANA,A BASU DA JARI TOH GA DAMA TA SAMU, INJI MAMAN ANUR DON ZAKU IYA DAUKAN KAYAN MU KU TALLATA KU DORA NAKU RIBAN SAMA ZAMU AIKA MAKU KAYA GA MAISHI DA SUNAN KU A DUK INDA CUSTOMER DIN KU YAKE BA TARE DA MUYI SAVING NO BASHI BA KUMA BA ZAISAN BA DAGA WURIN KI KAYAN YA FITO BA TAKEN MU GASKIYA DA AMANA, MUM ANNUR COLLECTION DA KARAMAR RIBA MUKA DOGARA SABODA NEMAN ALBARKA SAI KUN ZO 👏👏👏👏👏_*




MATAR MALAM:
Fitowarta kenan daga sakaki ( Bayan gida) ta jiyo ihun Laila. Sai kuma taga Shehu a ruɗe ya fito.
"Shehu lafiya, Laila ta dawo ne, ni naji ihu ko?"
"E matar Malam, naƙuda inaga ta soma, sai juyi take yi aƙasa." Butar hannunta ta ajjiye tace.
"Ka tashi Mai riga, da Iyami maza. Bari ni in soma zuwa." Tana kaiwa nan ta shige ɗakin Laila, shi kuma ya wuce Shiyyar su Baba Mai riga mahaifiyarshi.
"Baba Mai riga, Baba"
"Kaik waye wannan haka nenene?"
...


Read / Download MATA IYAYEN GIJI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album