Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

RIJIYA GABA DUBU Book 6 Complete Hausa Novel Document by RIJIYA GABA DUBU Book 6


RIJIYA GABA DUBU Book 6

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 10907



RIJIYA GABA DUBU Book 6

Reading Time: 0 Hours

Added On: 13, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Al'amin Ahmed Misau

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 58.56 kb

File Type: txt

Views: 930+

Download: 386+

Last download: 2 days ago

Description/Story: RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Shida (6)
Part A.
Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Labari Ya Isowa Shagala Cewa
Marubucin Yaci gaba da cewa.....

Badakaren ya kawo
gwauron numfadhi ya ajiye sannan yace ai
muna rabuwa da kai na taho iZuwa nan
dakina domin na yi shiri na tafi izuwa
cikin gari don cika umarninka. Na juya
baya ina sa tufafina sai na ji an turo
kofar dakin nan an shigo. Katin na
waigo naga mai shigowa sai ji nayi an
gabza mini naushi a kan kunnena na
hagu. Daga nan ban san abin da ya faru
ba sai farkawa nayi na ganni a kwance
da rub da ciki kuma a daure.
Kafin badakare ya gama rufe
bakinsa tuni Zamaru ya nike tsaye ya
ruga waje da gudu. Wannan shi ne abin
da ya faru a cikin gidani sarautar sarki
Taryan bayan dare ya raba a ranar da
jaruni imhal ya lashe gasar lambun
jarumta a zagaye na hudu,
Al'amarin jarumi Imhal kuwa sa
da ya shafe kwana biyu a kwance yana
cikin natsananciyar rashin lafiya da
jinya ba tare da ya ma san wanda ke
kansa ba.
A tsawon wadannan kwanaki babu
mai shiga cikin dakin da aka ajiyeshi
face sarki Taryan da likitansa. Ita kanta
gimbiya Shumaira babu yadda bata yi ba
akan sarki Taryan ya amince mata ta
shiga taje ta ga lafiyar Imhal amma ya ki.
Babban abin da ya dada dugunzuna
hankalinta shi ne gaba daya ta daina
ganin Muzaira a tsawon kwanakin biyu
bare ta toketa ta shigar da ita inda aka
6oye jarumi Imhal kuma bata san dalilin
bacewar Muzaira ba.
A wannan dare na biyu ne kafin
daren ya raba jarumi Imhal ya dawo
cikin haiyacinsa har ya bude idanunsa.
Yana bude idanun nasa ya yi arba da
sarkí Taryan da likitansa zaune a
gabansa kawai sai ya yunkura ya mike
Zaune, yana shirin mikewa tsaye kenan
sarki Taryan ya ce, kada kayi
Kwakkwaran motsi domin dinkin da na
yiwa raunikan jikinka zai iya farkewa kuma
kaga raunikan basu gama
warkewa ba.
Ko da jin
wannan batu sai kwallar
takaici ta zubowa jarumi Imhal ya du
ikitan sannan ya dubi sarki Taryan ya
ce, na gaji da wannan gasa haka kuma
na gaji da irin bakar wahalar da nake sha
don baka lallai gobe da safe nake son na
yi wasan karshe da sarki Gurzalu domi
na kawo karshen komai, ko ni ko shi
Ina son na sami'yancin kaina haka na
gaji da ganin jinina na zuba.
Ko da gama fadin haka sai jarumi
Imhal ya yunkura cikin zafin nama va
hankade sarki Taryan da likitansa daga
gabansa suka zube kasa sannan
takarkare ya kwarara uban ihu wanda ya
sannan ya
Cika gidan sarautar gaba daya da amsa
kuwa. Hatta sarki Gurzalu dake tsaye a
Can cikin turakarsa sai da zucivarsa ta
buga da karfi sakamakon jiyo wannan
sautin ihu domin ya gane muryar mai
ihun ba ta wani bace face ta jarumi
Imhal. nan take ya cika da tsananin
mamaki bisa yadda akayi jarumi Imhal
ya
Sami lafiyar da har zai iya yin
Wannsn uban ihu a vanzu
Saboda ihun da jarumi Imhal ke yi
sai dinkin raunikan jikinsa suka rinka
farkewa amma kuma sai gashi raunikan
sun warke babu inda jini ya tsattsafo.
Al'amarin da ya yi matukar baivwa
sarki Taryan da ikitansa mamaki kenan
Imhal ya ci gaba da kwarara ihu
yana zarya. a cikin dakin tankar
mahaukacin tsohon rikakken zalki
wanda ya fusata ainun a cikin daji.
Sai da sarki Taryan ya taso da
sauri ya kama jarumi Imhal da karfin
tsiya ya zaunar da shi kasa sannan ya
shiga rarrashinsa yana bashi baki amma
Imhal bai nutsu ba sai da sarki
Taryan ya amince da batun cewar
gaba da gasar kambun jarumta gobe da
safe.
A cikin wannan dare kuwa aka
yada labarin ci gaba da gasar kamnbun
jarumta gobe da safe.
Ai kuwa nan da nan labari ya bazu
a ko ina birni da kauye, mutane suka
rinka cewa lallai jarumi Imhal ba mutum
ba ne, aljani ne shi don babu yadda za a
yi ace mutum ya warke daga iin
mugayen raunikan da ke jikinsa guda
shida.
Al'amarin gimbiya Lamrita kuwa
tun daga lokacin da ta sami nasara
kufcewa daga hanun su sarkin yalki acan
birnin Kisra ta fada cikin daji. bata
saurara ba da gudu akan doki don gudun
kada su sarkin yaki su biyo bayanta su
cimmata saboda ta san cewa sarkin yawa
yafi sarkin karfi. idan suka yi mata
rubdugu zasu iya cafketa su je su jefataa
cikin kurkukun da ba za ta iya guduwa
ba.
Lamrita bata yada zango ba sai da
ta ga dokinta ya gaji likis kuma itama ta
gajin kuma yunwa da kishirwa sun fara
galabaitar da ita sannan ta tsaya a bakin
wata korama ta sauko daga kan dokin
suka kama shan wannan ruwa ita da
dokin nata.
Da yake tana tsoron kada cikinta
ya kulle sakamakon yunwar da take ji
sai ta sha ruwan dan kadan.
Ita dai wannan korama tana da
zurfi amma bata da fadi sosai kuma
mahada ce ta ruwan wani katon kogi da
ke can gaba a cikin daji.
Kash rashin sani yafi dare duhu.a
she dai dai wurin da gimbiya Lamrita ta
tsuguna tana shan ruwa akwai wata
murtukekiyar macijiya mai kauri da
tsawon gaske wacce ta yi lambo a
AA Misau ke Magana
Karkashin ruwan, kawai jira take Allah
ya kawvo wata dabbar mai tsautsayi
shan ruwa ta yi kalaci da ita saboda
tana cikin matsananciyar yunwa. Ko do
Lamrita ta gama shan ruwa ta mike zata
kama dokinta su bar wajen sai kawai taji
an fincikota izuwa cikin ruwan da Karfin
tsiya, kafin tayi wani yunkuri macijiyar
ta fara kanannade kafafunta ta kasa
zuwa kugunta ne ta sa hannayenta ta
tokare macijiyar.
Nan fa suka kama kokowa suna
nutsewa izuwa kasan ruwan Suna
dagowa sama Suna ta birgima,
Sakamakon nutsewar da suke yi izuwa
kasan ruwan sai Lamrita ta fara
galabaita saboda daukewar numfashinta,
gashi dai suna ta fafatawa ita macijiyar
ta kasa karasa kanannadeta ita kuma ta
kasa samun damar zare wuka ko
takobinta ta cutar da ita.
A daidai wannan lokaci hankalin
gimbiya Lamrita ya dugunzuma ainun
domin karfinta ya fara karewa ta san
cewa da zarar macijiyar ta karasa
kanannadeta zata karya gaba dayan
kasasuwan jikinta ta hadiye ta.
Nan take Lamrita ta cire kai ga
samun tsira ta saddakar da cewa lokacin
mutuwarta ya yi.
Kwatsam sai ga wani matafiyi bisa
wani dogon rakumi sanye da fararen
tufafi ya zo giftawa. Matafiyin ya rufe
fuskarsa, idnaunsa ne kadai ake gani.
Ko da ya ga abin da ke faruwa sai
ya dako tsalle sama daga kan rakumin,
tun kan ya fado kan macijiyar ya zaro
wata sharbebiyar wuka kawai sai ya
sokawa macijiyar wuka a idonta guda
Take idon ya fashe, macijiyar ta yi wani
uban ruri saboda tsananin zafi da zogin
da taji a sa'adda iini ya kama shatatowa
kasa, ba ta san sa'adda ta saki Lamrita
ba saboda dimaucewa, ai kuwa sai ta
koma kan wannan bakon matafiyi shima
ta fara kanannadeshi amma sai ya yi wuf
ya kama jelarta da hannu guda kuma ya
wuyanta da daya hannun ya
warware nadewar da tayi masa a hankali
da karfin tsiya.
Nan take kwanjin hannayensa suka
kumburo har hannun rigarsa ya yayyage
saboda tsabar karfin damtse nasa. Tuni a
wannan lokaci gimbiya Lamrita ta fito
daga cikin koramar da kyar tana jan ciki
saboda tsananin galabaitar da tayi.
tana numfarfashi
Ko da ta ga irin tsananin karfin
wannan matafiyi da ya kawo mata dauki
sai ta ci gaba da kura masa idanu tana
kallon gumurzun da yakeyi da wannan
katuwar macijiya a cikin ruwa. Tun da
gimbiya Lamrita ta zo duniya bata taba
ganin mutum mai kirar sadaukai ba da
tsananin karfi kamarsa domin duk
girman macijiyar sai ga ta hannunsa ta
kasa kufcewa.
Ana cikin wannan artabu ne taga
jarumjin ya daga macijiyar sama ya tabe
hannayensa yana mai kwala kabbara.
Nan take ya tsinke macijiyar ta dare gida
biyu ya yi jifa da gawarta a cikin ruwan.
Saboda tsananin mamaki
gimbiya Lamrita ta sandare kamar
gunki, baki a bude, idanu a kafe ta kura
masa idanu ko kiftawa ba ta yi har ya
fito daga cikin koramar ya zo daf da ita
ya tsuguna sannan ya kwaye rawanin da
ya rufe fuskarsa da shi suka yi arba da
juna yana mai yi mata murmushi.
sai
Ko da gimbiya Lamrita ta ga irin
tsananin kyawun fuskar saurayin sai ta
sake dimaucewa har yayi mata kwarjini
ainun ta kasa ci gaba da kallonsa ta dan
sunkui da kanta kas, a sannan ne ya
dubeta ya ce, ina fatan dai babu wani
rauni a jikinki?
Ko da jin wannan tambaya sai
gimbiya Lamrita ta mike tsaye ta duba
ko ina a jikinta ta tabbatar da cewar
babu wani rauni sannan ta dubi saurayin
ta ce, ina godiya a gareka mara adadi
bisa ceton rayuwata da ka yi daga
sharrin wannan katuwar macijiya.
Sunana gimbiya Lamrita 'ya ga sarki
Gurzalu na birnin Kisra kuma ina kan
hanyata ne ta zuwa bimin Misra don
hallarar gasar kambun jarumta, wanene
kai, daga ina ka fito kuma ina ka dosa
yanzu?
Sa'adda kyakkyawan saurayin ya
ji wannan tambaya sai ya cika da
mamaki amma sai ya dubi gimbiya
Lamrita cikin murmushi ya ce, ni sunana
Salman bin Usman kuma na fito daga
wata kasa da ake kira Madinatul Ansar
dake kudancin nahiyarku. Babu inda na
nufa face birnin Misra inda ake wannan
gasa ta kambun jarumta domin nima n
AA Misau Ke Magana
shiga gasar amnma da wata manufa. Na
dade ina jin labarin wannan gasa da
yanayinta irin yadda ake fafatawa da
manyan jarumai na duniya ana yi musu
kisan gilla. Lallai idanuna sun kagu da
su ga yadda ake wannan bakin gumurzu.
Yake yar sarki ki yi sani cewa
kafin anzo nan na sauka a cikin birninku
na Kisra har na kwana biyu kuma na
sami labarin cewa mahaifinki sarki
Gurzalu shi ne zakaran wannan gasa ta
kambun jarumta kuma yanzu haka yana
can birnin Misra yana yin gasar. Menene
dalilin da ya sa baki bishi kun tafi tare
ba izuwa birnin na...


Read / Download RIJIYA GABA DUBU Book 6

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album