Join Our WhatsApp Group

MAZA SUN FADI 1 to 4 Complete Hausa Novel Document by MAZA SUN FADI 1 to 4


MAZA SUN FADI 1 to 4

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42395



MAZA SUN FADI 1 to 4

Reading Time: 3 Hours

Added On: 21, Jul 2023

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 233.67 kb

File Type: txt

Views: 1654+

Download: 792+

Last download: 3 hours ago

Description/Story: MAZA SUN FADI Part 1

RANA ta take kuma tayi zafi sossai,
Amma hakan bai hana mutane cigaba
da Harakokinsu ba a cikin birnin kowa
ka gani sha’anin gabansa yakeyi, har a
cikin kasuwa kuwa ana ta kai kawo ana saye da
sayarwa.
Kwatam sai aka hango wani matashin saurayi
wanda ba zaifi shekara goma shabiyar ba,
ya ratso kasuwa yana tafe yana layi sakamakon
jini dake zuba a jikinsa har idanunsa suna
lumshewa,
kai da ganinsa kasan cewa yasha fama gudu sai
haki yake,
Rigar jikinsa kuwa ta jike sharkaf da jini, nan take
ya kife kasa da rub da ciki a tsakiyar kasuwar.
Al'amarin da ya matukar razana mutane kenan
domin ba'a san yadda wannan saurayi ya shiga
wannan hali ba.
Nan da nan mutane suka taru suka kewaye
wannan saurayi amma aka rasa wanda zai
taimakeshi,
Sai wani tsoho ne yayi sauri ya tashe shi zaune
ya daura masa ruwa a baki yasha,
Koda tsohon ya dubi fuskar saurayin sai ya
tsorata ainun ya dubeshi cikin dimauta yace ya
kai SHUBAIRU waye yayi maka Wannnan karen
aiki?''
Cikin matukar karfin hali shubairu ya dubi tsohon
ya bude idanunsa da bakinsa da kyar yace,
''kowa yai sauri yayi gudun ransa
domin wadansu yan harine suka biyoni da gudu
da kyar na guje musu na iso nan,
Ina gaya muku cewa suna da tsananin yawan
gaske Idan suka iso cikin garin nan sai sun
kashe kowa kuma su debe mana dukiyoyinmu ''
Koda jin wannan batu sai gaba daya kasuwar ta
yamutse mutane suka fara guje-guje da iface-
iface masu kokarin kwashe hajojinsu nayi,wasu
na bangaje wasu a lokacin gudun, maza da mata
yara da manya, nan da nan labari yakai har cikin
gari.
Shi kuwa wannan tsohon ko juyawa izuwa cikin
rumfarsa baiyi ba,
sai yai sauri ya tashi shubairu tsaye ya kaishi
inda dokinsa yake ya dorashi akai yace,
dashi ''maxa ka ruga izuwa gida ka sanar da dan
uwanka HUZAIRU halin da ake ciki kuma ka gaya
masa ya hanzarta dinke maka raunin dake
bayanka domin sara da akayi maka mai zurfi ne''
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa shubairu
yace,
''Yakai Abbana Yaza'ayi na tafi na barka anan
yan sumame su kasheka?''
Tsoho KALMARU ya dubi shubairu a lokacin da
shima kwalla ta cika masa idanu yace, ''idan na
bika muka tafi tare, Biyu babu za'a yi sbd dokin
nawa bashida issashiyar lfy ba xai iya daukarmu
mu biyu ba.
Dolene na tsaya na tari 'yan harin nan nayi iya
kokarina na bata musu lokaci don ka isa Gida da
wuri,
ku sami damar guduwa kai da dan uwanka
huzairu,
Na sani cewa dan uwanka huzairu yanada taurin
zuciya zai iya cewa sai ya dawo nan ya ceceni
to ka gaya masa cewa ko!
idan har ya biyo bayana ya karya alkawarin da ya
daukarwa mahaifiyarku. Na cewa komai rintsi zai
rayu domin ya dauki fansar ranta. ''
Gama fadin hakan keda wuya sai hawaye ya
zubowa tsoho kalmaru ya yiwa shubairu kallon
karshe mai nuna bankwana,
dan ya san cewa baxa su sake saduwa ba.
Nan take kalmaru ya doki bayan dokin da tafin
hannunsa nan take dokin ya zaburi shubairu da
gudu izuwa cikin gari.
A Wannnan lokaci tuni kasuwar ta dade da
watsewa,
babu mutum koda guda daya jal a cikinta face
tsoho kalmaru.
Kawai sai kalmaru ya ruga izuwa cikin rumfarsa
ya dauko takobi da garkuwa sannan ya fito ya
hau kan wani dogon mumbari dake tsakiyar
kasuwar ya tsaya cak!'' yana kallon hanyar da
yan harin zasu shigo.
Kallo daya mutum zai yiwa tsoho kalmaru ya
tabbatarda cewa ya kasance tsohon Sadaukin
Jarumi,
domin da gani babu tambaya sbd ya kasance
dogo mai murdadden jiki, duk da kasancewar
shekarunsa a yanzu sun haura saba'in (70)
kasancewar akwai sauran kuzari a tare dashi,
kuma komai takamar Jarumi zai yi shakka yayi
masa shiga farat daya, saboda kwarjininsa.
Bayan tsayuwar tsohon kalmaru da kamar tsawon
dakika dari da ashirin sai ya jiyo sukuwar
dawakai babu adadi sun durfafo kasuwar.
Duk da cewa kalmaru yanada dakakkiyar zuciya
irinta manyan maxaje sai da tsoro ya darsu
acikin zuciyarsa,
Ba wai tsoro bane na mutuwa ko irin fafatawar
da xaiyi ba,
tsoro ne na takaicin irin barna da wadannan
dakarun sumame zasu yi idan suka shigo wannan
karamin kauye nasu.
Shi dai wannan kauyen nasu tsoho kalmaru ana
kiransa da suna HIDAIMAT mutanen kauyen gaba
dayansu masu sana'ar kera jirgin ruwa ne,
kasancewar kauyen yana bakin teku
Asalin kauyen tsoho kalmaru ne ya kirkireshe
domin shine ya fara zama a bakin tekun, tun
kafin matarsa ta haife masa ya'yansa guda biyu,
SHUBAIRU DA HUZAIRU
Kafin tsoho kalmaru yayi aure ya kasance
mataimakin sarkin yakin birnin zamar kuma sai
da ya shekara ashirin da biyu yana yiwa sarki
Barham bauta.
Duk sa'adda kalmaru Ya jagoranci yaki sai an
sami nasara ba'a taba samun akasi ba,
Al'amarin da ya janyo kishi kenan tsakaninsa da
sarkin yaki HAMSARU sbd shi kuma duk sa'adda
ya jagoranci yaki anfi yin RAGAS ba'a cika
samun nasara ba,
Wani babban abun takaici shine sarkin yaki
Hamsaru da kalmaru sun kasance 'yan uwan na
jini domin dan wa da dan kane suke,
Mahaifin Hamsaru ne yayan mahaifin kalmaru,
Tun sa'adda kalmaru da Hamsaru suka taso da
kurciya ya xamana Cewa ana basu horon yaki a
gidan sarautar zamar, kasancewar a wannan
lokaci mahaifin kalmaru ne sarkin yaki,
Burin mahaifin kalmaru shine dansa ya gajeshi
amma sai ya zamana cewa Hamsaru yafi
kalmaru tsagwaron karfin damtse da iya yaki,
Shi kuma kalmaru sai yazamana cewa yafi
Hamsaru sa'a gamida taurin zuciya.
Komai hadarin yaki da yawan abokan gaba
kalmaru baya ja da baya.
Lokacin da tsufa ya riski mahaifin kalmaru sossai
har ya zamana cewa baya iya zuwa fada bare
yaje yaki sai kalmaru da Hamsaru ne suke
walkitarsa sai sarki Barham yasa aka kirawoshi
suka kebe inda ya dubeshi yace ,
''ya kai dirkar birnin zamar kasani cewa kai yanzu
tsufa ya riskeka har ta kai cewa ka kasa ruke
mukaminka, sai ya'ya'nka ne suke kula dashi, sbd
haka inason a cikin ya'yan nan naka ka zabi daya
daga cikinsu wanda kake ganin cewa shine mafi
cancanta daya gajeka,
Lokacinda sarkin yaki yaji wannan batu na sarki
Barham, sai hankalinsa ya dugunzuma ainun sbd
shi baxai iya zabar daya daga cikinsu kalmaru
ba.
Duk da cewa a zuciyarsa yafi son dan cikinsa
kalmaru ya gajeshi sbd bayason wani abu da xai
kawo sabani tsakaninsa da dan uwansa wato
mahaifin Hamsaru. Sarkin yaki yai shiru yana
tunani har izuwa tsawon wani dan lokaci
sannnan ya dago kai ya dubi sarki Barham yace,
''ya shugabana kai da kanka ka sani cewa
Hamsaru yafi kalmaru tsagwaron karfin damtse
da iya yaki,
Amma kuma kalmaru yafi Hamsaru sa'a da taurin
zuciya da naci.
Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi
wanda zai gajeni ba daga cikinsu ba. MAZA SUN FADI!!! Part 2

Ni ina ganin cewa bani ne ya kamata na zabi
wanda zai gajeni ba daga cikinsu.
Kamata yayi kai da sauran yan majalisa ku zauna
kuyi tunani kuyi zabin da kanku bisa wanda kuke
ganin yafi cancanta,
Kasani cewa idan na zabi dana kalmaru zan sami
matsala da dan uwana mahaifin Hamsaru wato
YUNARU,har zumuncin mu ya raunana ''
Sa'adda sarkin yaki yazo nan a zancensa sai sarki
Barham yai shiru yana nazarin al'amarin.
Daga can sai ya dago kai ya dubeshi yace,
''ya kai dirkar birnin zamar hakika na karbi
uzurinka,
Amma baza mu zabi magajinka ba Nida yan
majalisata kadai ba,
Abinda zamuyi kawai shine, zamu shirya gasa ta
jarumtaka tsakanin kalmaru da Hamsaru, su yaki
juna a tsakiyar fada agaban alkalan gasa, 'yan
majalisa da mutanen gari.
Wanda da duk yasami nasara kai wani kasa daga
cikinsu shine zai gajeka,
Koda jin haka sai mamaki da tsoro ya kama
sarkin yaki ya dubi sarki Barham cikin tsananin
damuwa yace,
'' haba ya shugabana ai bai kamata ayi hakan ba
tunda kowa ya san cewa Hamsaru yafi kalmaru
karfin damtse da iya yaki.
Sarki Barham yai ajiyar zuciya yace,
''ya kai abokina kasani cewa kai aminina ne
kuma tun muna yara muka taso tare,
Bamu taba rabuwa ba,
Ko ayanzu daka tsufa har takai cewa baka iya
zuwa fada, bana shafe kwana 2 bankai maka
ziyara ba har gidanka,
Wannan tsufa naka da rashin kuzari a jikinka
yanada nasaba da asirin da dan uwanka yayi
maka yasa maka rashin lfy sbd bakin cikin
kasami sarautar sarkin yaki shi bai samuba,
Ka sani cewa duk fadin kasar nan ni Kadai ne na
san wannan Sirri kuma bantaba gayawa wani ba.
Ta yaya kake tsammani cewa zanso dansa ya
zama sarkin yakina? ''
A koda yaushe ciwon dake jikinka xai iya zama
ajalinka,
Idan har ka tafi ka barni zanso ace na rinka
ganin danka akusa dani tunda kammaninku iri
daya ne sak tamkar an tsaga kara, tunda idan ina
ganinsa zan samu saukin kewarka.
Lallai zanso ace kalmaru ya gajeka,
Zan iya amfani da karfin kujerata na tabbatarda
cewa kalmaru ya gajeka,
To amma idan nayi hakan jama'a zasu ce nayi
son zuciya sbd ansan kusancina dakai.
Nayarda da sa'ar danka kalmaru gamida da
nacinsa don haka nayi imani cewar zai iya lashe
wannan gasa''
Lokacin da sarki Barham yazo nan a zancensa
sai idanun sarkin yaki suka ciko da kwallah har
hawaye ya zubo masa yace,, ''yakai abokina
nasani cewa kana son ka kasance dani da
zuri'arka har karshen rayuwaka to amma dole mu
rungumi kaddara domin hakan baxai taba yi yuwa
ba.
Na yarda batun wannan gasa da kashirya kuma
ina yiwa mai sa'a fatar samun nasara ''
Koda gama fadin hakan sai sarkin yaki Yayiwa
sarki Barham sallama ya mike tsaye da kyar! Sbd
laulayin rashin lfy da tsufa ya fice daga cikin
dakin dasu ka gana.
Tafiyar sarkin yaki ke da wuya sai sarki Barham
ya kira wani babban hadiminsa wanda ake kira
zilla ya umurceshi da yaje yasa ayi shelar
wannan gasa da za'a yi a fada a gobe kuma ana
gayyatar kowa da kowa birni da kauye.
Nan take kuwa zilla yaje ya cika umurni,
Lokacin da mutanen gari suka ji wannan shela
sai aka cika da tsananin mamaki domin a tarihin
masarautar ba'a taba shirya gasa ba akan zaben
sarkin yaki.
Kawai sarki ne yake duba cancanta ya zabarwa
kansa sarkin yaki,
Lokacinda kalmaru yaji ansa gasa tsakaninsa da
dan uwansa Hamsaru akan takarar kujerar sarkin
yaki sai hankalinsa ya dugunzuma ainun don
haka sai ya shiga cikin turakar sarkin yaki ya
sameshi kuwa a zaune yayi tagumi yana tunani.
Kalmaru ya xauna daf da sarkin yaki ya dubeshi
cikin alamun tsananin damuwa yace,,
''ya kai Abbana saboda me kana raye da lafiyarka
kuma kanaji kana gani zaka bari a aiwatar da
abinda zai haddasa gaba tsakanina da dan
uwana Hamsaru kuma ya lalata zumuncin dake
tsakanika da dan uwanka?''
Ina mai rokonka daka hanzarta komawa yau
wajen sarki ka nemi alfarma a janye wannan
gasa,
Ni kam na hakura na baiwa dan uwana Hamsaru
wannan kujera.
Shin ka manta ne da halin mahaifin Hamsaru? ''
Akan Hamsaru ya mallaki wannan matsayi babu
abinda baxai iya ba koda kuwa sai ta kai cewa
an hallakani ko kai an hallaka ka''
Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa
sarkin yaki, ya dubi kalmaru yace,,
''ya kai dana kayi sani cewa bakin alkalami ya
bushe.
Domin babu abinda zanyi wanda zai sa sarki ya
janye batun wannan gasa,
Hakika so sone amma son kai yana gaba da
komai ,
Babu yadda za'ayi naso wani ya gajeni face kai,
Kawai kaje ka fara shirye-shiryen wannan gasa
da za'a yi gobe,
Wanda keda rabo a cikin ku shine zai gajeni,,
Daga yanzu zuwa gobe ka tsare kanka domin
za'a iya yunkurin cutar dakai ko kuma a
hallakaka.
Na sallameka kuma banason naji wani korafi
daga bakinka,
Cikin alamun tsananin damuwa kalmaru ya juya
ya fice daga cikin turakar sarkin yaki.
******
AL'AMARIN Hamsaru kuwa lokacin da yaji cewar
sarki ya shirya gasa tsakaninsa da dan uwansa
kalmaru akan zaben sarkin yaki bisa cewar duk
wanda ya kai wani kasa shine zai sami mukami
sai ya kamu da tsananin farinciki sbd yana ganin
cewa tunda yafi kalmaru karfi da iya yaki dole ne
ya sami nasara lashe gasar sarkin yaki.
Kai tsaye Hamsaru ya wuce izuwa cikin gidansu
fuskarsa cike da walwala da annuri,
Yana isa turakar mahaifinsa sai ya iske
mahaifinsa da mahaifiyarsa a zaune sunyi jugum-
jugum kamar anyi mutuwa.
Al'amarin da yai matukar baiwa Hamsaru
mamaki kenan ya dubesu cikin damuwa yace,,
''yaku iyayena menene kuma ya faru haka na
ganku acikin yanayin damuwa?
Dajin wannan tambaya sai mahaifiyarsa ta dago
kai tace,, ''ya kai Hamsaru sbd me ba zamu
kasance a cikin tsananin damuwa ba alhalin mun
kwallafa burin mu gaba daya akan gasar da za
kayi gobe kuma gashi bamuda tabbacin cewa
zaka lashe gasar,
Koda jin haka sai mamaki ya sake turnike
Hamsaru yace,
Me kike nupi da cewar burinku yana kan wannan
gasa da zanyi kuma sbd Me kuke shakkar
nasarata alhalin kunsan cewa nafi kalmaru karfi
da iya yaki,
Dajin haka sai YUNARU mahaifin Hamsaru ya
numfasa ya dubeshi yace,
Kai yanzu kana ganin cewa zaka iya kai kalmaru
kasa ne da karfin damtsenka da iya yakin ka?"
To ka sauya tunani tunda wuri domin kuwa idan
bamuyi amfani da yaudara ko ha'inci babu yadda
za'ayi ka sami nasara akan kalmaru sbd ya fika
naci da juriya,
Ina mai tabbatar maka da cewa zai iya jure duk
irin wani sara da sukan da zaka rinka kai masa
gami da naushi da bugun hannu da kafa har
izuwa lokaci mai dan tsawo sa'adda zaka gaji ya
sami nasara akan ka. MAZA SUN FADI!!! Part 3

Na fuskanci cewar har yanzu kana shakkar abinda
nake fada maka,
Shin kun taba yin gurmuzun da ya kai na rabin
sa'a kai dashi a yayin da kuke baiwa juna horo? "
Koda jin wannan tambaya sai jikin Hamsaru yayi
sanyi yace,
Ai bamu taba yin gurmuzun da yakai na tsawon
dakika dari biyu ba ni dashi,
YUNARU yayi dan guntun murmushi yace,
Shiyasa ba zaka taba fahimtar bam-bamcinka
dashi ba, ai kallon kitse kake yiwa rogo.
Na rantse da darajar iyayena bazaka iya kai
kalmaru kasa ba domin ya gado kakanmu a
tsananin juriya da naci,
Hatta yanayin jikinsa da sifofin jikinsu duk iri
daya ne,
Har kakanmu ya bar duniya ba'a taba samun
jarumin da ya kai shi kasa ba kuma komai yawan
dakaru shi kadai yana iya tarwatsa su,
Hakika MAZA SUN FADI!!!
Inda ace kakanmu har yanzu yana raye a doron
kasa a wannan zamani kuma yana cikin koshin
lfy da rashin cutar tsufa irin wacce ta kama dan
uwana sarkin yaki a yanzu da zai iya mulkar
duniya Gaba daya,
abu daya nake tsoro.
Wani boka ya tabbar mini da cewa idan har
kalmaru ya yi aure to zai iya haihuwa dan da zai
sami gagarumin karfi irin na kakanmu kuma xai
iya mulkar duniya Gaba daya.
''Ya kai dana kayi sani cewa dole sai idan ka
lashe wannan gasa akan kalmaru sannan zamu
iya hanashi yin aure bare har ya haifi dan da zai
mulki duniya."
Sa'adda YUNARU yazo nan a zancensa sai kan
Hamsaru ya sake daurewa yace,, Ta yaya zaka
iya hana kalmaru yin aure ta hanyar amfani da
karfin kujerata ta sarkin yaki? "
YUNARU ya sake yin murmushi a karo na biyu
yace,, "kada ka damu zaka sani nan gaba idan ka
hau kan kujerarka.
Abinda nake da kai shine , ka kwantar da
hankalinka tuni na gama tunani akan yadda zaka
sami nasara akan kalmaru ka kaishi kasa kuwa a
daren yau zangama shirina,
Kaje kayi kwanciyarka kasha barcinka,
Kada ka wahalarda kanka wajen kokarin baiwa
kanka horon yaki a yau sbd gasar ta gobe,
Dajin haka sai Hamsaru ya mike tsaye ya fice
daga cikin fallon ya tafi izuwa dakinsa yana mai
mamaki zullumi gamida tunanin irin abin da
mahaifin nasa xai shirya don tabbatarda samun
nasararsa a Wannnan gasa,
Har izuwa wannan lokaci Hamsaru bayajin
shakkar komai a cikin zuciyarsa bisa fuskantar
kalmaru,
Abin da Hamsaru baisaniba shine,
Kalmaru baya sakin jikinsa da karfinsa gaba daya
a duk sa'adda zasuyi gurmuzun sbd yana
girmamashi Amatsayinsa na yayansa wanda ya
girmeshi a shekara
*****
LOKACIN da kalmaru ya isa turakarsa sai ya iske
mai kula da abincinsa wata baiwa mai suna
ZULAIMA ta shirya masa abincinsa akan tebur ta
kawo ruwan inibi acikin tulu ta ajiye,
Zulaima tsohuwa ce wadda shekarunta sun haura
saba'in,
Tun kalmaru baifi shekara shidda ba a duniya
Zulaima take rainonsa sakamakon mutuwar
mahaifiyarsa har kalmaru ya girma bai san
uwarsa ba sai Zulaima domin itace take masa
komai kamar yadda kowace uwa keyiwa danta,
Kalmaru da Zulaima sun shaku ainun kuma sun
yarda da juna ainun,
Shi kansa sarkin yaki ya yarda da Zulaima dari
bisa dari domin tun tana budurwa ya siyeta a
matsayin baiwa har yazo ya 'yantata amma wani
abu bai taba shiga tsakaninsu ba domin ya
dauketa tamkar 'yar cikinsa,
Duk da cewa ya yantata sai ta kasa tafiya ta
barshi, tayi alkawarin zata zauna tare dashi har
izuwa karshen rayuwata...


Read / Download MAZA SUN FADI 1 to 4

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On MAZA SUN FADI 1 to 4
avatar
abubakar-abdullahi-6

2 months ago

Reply

yes

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album