Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

BUSA A MUTU Book 7 Complete Hausa Novel Document by BUSA A MUTU Book 7


BUSA A MUTU Book 7

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 17063



BUSA A MUTU Book 7

Reading Time: 1 Hours

Added On: 29, Feb 2024

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini ,

Ebook Compiler : Al'amin ahmed Misau, Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 90.58 kb

File Type: txt

Views: 973+

Download: 574+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: BUSA A MUTU 💕
Littafi Na Bakwai (7)🩸
Part A💎
Na Abdulaziz Sani M Gini 🤴
Typing by AA Misau ke Magana
✍️⭐⭐⭐
(ALKAWARIN MU NA NAN DANI DAKU IN KUN LATSA MANA LIKES & COMMENTS KUNA ZUCIYATA 🎧🎤🎷🤓🤓🤓)
Labari Ya Isowa Shagala Cewa...
DA JARUMI IMRAN DA JARUMI MURAISU DA
SU MAHAIFIYARSA HUSNAILA SUKA SHAFE SAMA DA
SA'A UKU SUNA FAFATA YAKI, AMMA DAYANSU BAI
SAMI NASARAR KODA KWARAZANAR JIKIN DAYA BA.
Al'amarin da ya fusata kOwanncnsu ke nan. Da kansu
suka ja da baya, suka yi cirko-cirko suna haki da kallon
juna.
Kawai sai jarumi Imran ya mai da takobinsa cikin
kufe yai jifa da ita, sannan ya dubi Muraisu da Husnaila ya
ce, "Tun da dai iya yakinmu ya zo daya me zai hana mu
jarraba amfani da tsagwaron karfin dantsen mu amma bisa
sharadi guda,"
Cikin alamun fishi da mamnaki jarumi Muraisu ya ce,
"Wanne irin sharadi ke nan kake nufi?"
Jarumi Imran ya ce, "Sharadin shi ne, idan na sami
sarar kaiku kas za ku janye dukkan nufinku ku kar6i
addinina. Idan kuma ku ka sami nasara a kaina zan kyaleku
ku ci gaba da yin abinda kuka sa a gabanku. Na yi haka ne
domin na kawo karshen gardamar da ke tsakaninmu".
Koda jin wannan batu sai jarumi Muraisu da
mahaifiyarsa Husnaila suka dubi junansu sannan suka
koma gefe daya domin su yi shawara.
Muraisu ya dubi Husnaila ya ce, "Ya ke Ummina
yanzu ke a ganinki mene ne abinda ya kamata mu yi?"
Koda jin wannan tambaya sai Husnaila ta sunkui da
janta kas tana tunanı har 1zuwa tsaWon 'yan
dakiku, daga can sai ta dago kai ta dubi Muraisu cikin
alamun tsananin damuwa ta ce, "Ya kai dana, ka yi sani
cewa da dadewa tun ina yarinya Karama na taba ji daga
bakin mahaifina cewar ma'abota addinin Musulunci suna
da matukar sa'a da nasara bisa duk abinda suka sa a
gabansu.
Tabbas Biri ya yi kama da Mutum, tunda gashi mun
gani a zahiri, ta yadda mu biyu muka kasa samun nasara
akan wannan bakon jarumi duk da mun hada KARFI DA
KARFE ni da kai.
Ni ina ganin cewar zamanmu a cikin wannan daji na
Kirzufa yanzu ya kare, domin na fuskanci cewa sihirin da
ke cikinsa ya daina aiki tunda gashi KAHONKA na BUSA
A MUTU ya daina BUSUWA.
Kuma ga dukkan alamu wannan jarumi da ya z0 sai
ya fita daga cikin dajin nan lafiya kuma a raye, ka ga ke
sihirin dajin ya karye tunda a ka'ida duk mahalukin da
ya shigo bai isa ya fita a raye ba.
Yanzu idan har muna son wannan KAHO na BUSA
A MUTU ya sake BUSUWA, dole ne mu nemo wannan
Gashin SIHIRI wanda dan uwana Sarki Imras ya Boye
domin bisa binciken da na yi, na gano cevwa da wannan
gashi ne kadai zamu iya dawo da karfin sihirin kahon
BUSAA MUTU da kuma sihirin wannan daji na
KIRZUFA.
Ka ga ke nan yanzu zamanmu anan cikin dajin
Kirzufa bashi da wani amfani, dole ne mu fice daga cikinsa
mu tafi neman GASHIN SIHIRIN.
Sabo da haka, yanzu dole ne mu janye yaki da
Wannan bakon jarumi tunda ba shi bane
abokin gabarmu ba, ko addininsa gaskiya ne ko karya ne ba
ta tashi mu ke yi ba.
Dole ne mu san hanyar da zamu bi yanzu mu gujewa
wannan bakon saurayi da abokan tafiyarsa".
Cikin alamun tsananin damuwa Muraisu ya dubi
mahaifiyarsa Husnaila ya ce, "To yanzu wacce dabara
zamu yi mu gujewa wannan bakon jarumi?"
Husnaila ta yi murmushi ta ce, "Kar ka damu, zo mu
je mu yi magana da shi".
Nan take Muraisu da Husnaila suka koma inda jarumi
Imran da su jaruma Suzaila ke tsaye suna saurarensu.
Da zuwansu sai Husnaila ta dubi Imran ta ce, "Ya kai
wannan GWARZON MAYAKI, ka yi sani cewa mu yanzu
amince zamu bayar da gaskiya ga addininka, amma
sai idan mun zauna tare da kai mun yi maka wadansu 'yan
jarrabobi da za su tabbatar mana da gaskiyarka da
addininka.
Yanzu za mu je mu debo 'yan kayayyakinmu mu biku
mu tafi mu bar dajin nan gaba daya har abada ba zamu
dawo ba.
Amma ka sani cewa Sarki Imras da Sarki Huraisu su
ne manyan abokan gabarmu wadanda in dai zamu hadu da
su babu abinda zai rabamu da su face KAIFIN TAKOBI!
Don haka, kada ka kaimu izuwa garuruwansu".
Koda jin wannan batu sai jarumi Imran ya dubi
Husnaila cikin alamun damuwa ya ce, "Ya ke wannan 'yar
Sarki, ki yi sani cewa koda zamu hadu da su Sarki Imras ba
Zan bari su cutar da ku ba, wannan alkawari ne tsakanina
da ku.
AA Misau ke Magana
Ku sani cewa ni ina s0 ne na yi sulhu a tsakaninku
domin an riga an yi kuskure tun a baya, tunda dai akwai
nasaba ta jini a tsakaninku, ya kamata a yafi juna".
Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jarumi Muraisu
ya ce, "Ta ya ya kake tsammanin zan iya yafewa Sarki
Huraisu wanda ya kashe mahaifina, ya jefa mahaifiyata a
cikin rayuwar kunci da wahala, rayuwar daji inda babu
abinci da abin sha mai dadi, kuma babu makwanci mai
kyau, alhalin ada ta saba da rayuwa mai dadi?
Kamar yadda nima ba zan iya yafewa Sarki Huraisu
ba, haka ma mahaifiyata ba za ta iya yafewa Sarki Imras
ba, tunda ya so ya lalata rayuwarta ya hanata yin aure da
haihuwa, kuma gashi da shi aka hada kai aka kashe mijinta.
Ka yi sani cewa tun dazu mahailiyata ta yi bincike ta
gano cewa Sarki Imras da Sarki Huraisu sun yi gagarumin
shiri sun taho izuwa nan dajin Kirzufa bisa kan wani aljani
domin su hallakamu. Yanzu mene ne abin yi?"
Koda jin wannan tambaya sai jarumi Imran ya sunkui
da kansa Kas ya yi dan guntun tunani sannan ya dago kai
va ce, "Yanzu abinda za a yi, akwai wani Kauye wanda
muka ci su da yaki muka kafa addinina a cikinsa, zamu je
can mu zauna tare da ku a can. Amma ina son ka gaya mini
iva tsawon kwanakin da za ku yi ku gama jarrabani don
tabbatar da gaskiyata da adalcina".
Koda jin haka sai jarumi Huraisu da mahaifiyarsa
Husnaila suka dubi juna, sannan Husnaila ta ce, "Muna son
ka barnu kwana ashirin da daya kawai."
Koda jin haka sai jarumi Imran ya gyada kai ya ce,
"Shi ke nan, kamar yadda kuka yi shawara kai da
mahaifiyarka nima akwai bukatar na je na yi
shawara da Lushaira, saboda ta zama tamkar 'yar uwata ta
jini yanzu tunda ta karbi addinina".
Gama fadin hakan ke da wuya sai jarumi Imran ya
juya ya koma inda su Husnaila ke tsaye , wato in da ya
shata musu layi ya ce kada su kuskura su ketara.
Da zuwansa sai ya dubi Lushaira ya ce, "Ya ke 'yar
uwata matso kusa da ni donin mu yi shawara a matsayinki
na 'yar uwata musulma".
Koda jin wannan batu sai jaruma Suzaila taji ta kamu
da tsananin kishi, ta jìi kamar ta hana Lushaira zuwa wajen
Imran, amma sai ta kanne.
Ba tare da 6ata wani lokaci ba Lushaira ta tako
Kafafunta ta gota wannan layi wanda jarumi Imran ya shata
musu, ta z0 daf da shi ta tsaya yadda har suna iya jin
numfashin juna.
Al'amarin da ya kara tunzura Suzaila ke nan, jikinta
ya kama tsuma. Ita kanta sai taji tana mamakin kanta, na
vadda take jin tsananin kishi akan mutumin da bai san ma
tana sOnsa ba.
Nan take Imran ya kwashe labarin duk abinda suka
tattauna shi da su jarumi Muraisu ya zaiyanewa Lushaira.
Kuma ya nemi shawararta bisa abinda take ganin zai
fishshesu".
Koda jin haka sai Lushaira tayi dan shiru tana nazari.
Daga can sai ta fago kai ta dubi Imran ta ce, "Ka amince
da wannan sharadi da suka zo da shi.
Amma fa dole ne mu zuba ido sOsai akansu domin
alkawarin duk mutunin da bai addinin Musulunci ba,
alkawari ne mara tabbas.
Ka sani cewa wadannan mutanc za su iya yaudararmu
su gudu su karya alkawarin da ke tsakaninmu.
Abu na biyu kuma, dole ne mu kula da alakarsu da su
jaruma Suzaila da tamu ni da dan uwana Husnalu, saboda
za su iya huce haushinsu akanmu.
Ma'ana za su iya kokarin hallaka Suzaila a matsayinta
na 'yar Sarki Huraisu ko kuma su yi yunkurin hallakamu ni
da Husnalu a matsayinmu na 'ya'yan Sarki Imras, domin su
đauki fansa."
Sa'adda jarumi Imran yaji wannan batu sai ya jinjina
kai ya ce, "Kada ki damu za mnu sa ido sosai akansu ni dai
kawai fatana shi ne Allah Ya sa su gane gaskiya kuma su
karbcta.
Koda gama fadin hakan sai ya koma wajen su jarumi
Muraisu ya ce, "Na gama shawara da 'yar uwata kuma na
amincc da sharadin da ku ka zo mini da su. Don haka sai
ku je ku dcbo kayanku ku zo mu tafi".
Cikin farin ciki jarumi Muraisu da Husnaila suka juya
da sauri suka nausa izuwa cikin dajin Kirzufa.
A kan hanyarsu ne Muraisu ya dubi Husnaila cikin
alanun tsananin damuwa ya cc, "Haba ya ke Ummina ya
ya ke da muka gama magana akan cewa guduwa zammu yi
amma kuma yanzu kı ka sauya magana kika ce zama za mu
yi tare da su? Ta ya ya ke nan za mu sami nasarar ganin
bay an wadannan abokan gaba namu idan jarumi Imran ya
sami nasarar yin sulhu tsakaninmu da su?"
Koda jin wannan tambaya sai Husnaila te yi
murmushi ta ce, "Ya kai dana kai yaro ne har yanzu baka
san cewa yaki dan zamba banc.
Tunani na yi na ga cewa ...


Read / Download BUSA A MUTU Book 7

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On BUSA A MUTU Book 7
avatar
walid

4 months ago

Reply

Is so sweet

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album