Join Our WhatsApp Group

SADAUKI UBAN SADAUKAI BOOK 1 AND 2 Complete Hausa Novel Document by SADAUKI UBAN SADAUKAI BOOK 1 AND 2


SADAUKI UBAN SADAUKAI BOOK 1 AND 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13825



SADAUKI UBAN SADAUKAI BOOK 1 AND 2

Reading Time: 1 Hours

Added On: 18, Jul 2023

Author: Shuraihu Usman ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08140419490

Book License : Free

Category: Adventure novels

File Size: 78.38 kb

File Type: txt

Views: 1712+

Download: 247+

Last download: 5 hours ago

Description/Story: SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafina daya 1
Marubuci Shuraih Usman 99%
Ebook created by Shuraih Usman
Sold @ www.hausaebooks.com.ng


SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@hausaebooks.cf
Part A
.
.
Kimanin shekaru dubu daya da suka gabata a nahiyar sudan anyi wata birnin mai suna yemen birnin yemen babban birni ne don duk nahiyar babu wata birni data kaita girma, tattalin arziki da yawan dakarun yaki,
.
Birnin yemen na karkashin mulkin wani adalin sarkine ma'abocin addinin musulunci, sannan daukkan jama'an wannan birni Addini daya suke bi, itace kuwa Addinin Islama
.
Sarki ayyub ya kasance yana da matan aure hudu sannan kuma yana da ilmin Addini daidai gwargwardo kuma ya kasance yana kamanta adalci a tsakanin matayensa bil haqqi
.
Wayannan matayen nasa kyawawane na gaban kwatance dukkansu sun fito ne daga manyan gida in ka dauke amaryarsa mai suna Taufidatu, itace kawai ta kasance ya ga wani talakan masinci
.
Mahaifinta sunansa Imran kuma talaka ne don kuwa tun yana karami ya ke bin mahaifinsa a rafi, kuma da wannan sana'ar suke ci sannan susha har takai ga ma sun biya wasu bukatunsu
.
Ahaka imran ya taso har mahaifinsa ya rasu shi kuma ya riqi wannan sana'a da kima ya kuma jajirce ba'a dade ba ya auri wata kyakkywar mace wacce saboda saban kyawunta sai da akayi gasa kafin ya samu aureta
.
Al'adar wannan garine a duk lokacin da aka samu wasu suna son mace daya toh gasa akeyi don a fidda gwani, wannan gasar bata komi bane face gasar jarumta, shi dai imran da farko ba jarumi bane amma saboda tsananin kaunarsa ga Halimatu hakan yasa ya dage lallai sai ya shiga wannan gasa
.
Da ranar gasa tayi, mutane da yawa sun taru don kashe kwarkwatar idanuwansu, yayin da aka zagaye filin da wani yanki na jan kyalle, a dokar wannan gasa duk wanda ya fita daga cikin filin ko ya kama jan kyallen nan, ko kuma ya bari ta taba jikinsa toh ya fadi take zai fito daga cikin filin
.
Yadda akeyin gasar dai shine dukkanku za'ataru ku a cikin wannan fili duk wanda ya samu nasarar fitar da dan uwansa daga filin har ya rage babu kowa a filin sai shi kadai toh shine zakara
.
Zaratan Jarumai ne da sadaukai masu kirar sadaukan taka sannan sai kirba kirban katti sun kai su hamsin sai kuma masunci Imran wanda duk cikinsu shine san karami kuma baya da kirar jarumtaka a jikinsa,
.
Hakanne yasa mutane sukai tai masa dariya , koda aka buga gangar fara gasa sai filin ya haustine karajin mazaje ya yawaita kura ta turnuke, don kuwa sai dai kaga kato ya daka kato sama ya yi jifa dashi wajen filin , take wannan da'akayi jifa dashin zai karkade jikinsa yaje gefe don kuwa ya riga daya fadi
.
Shi kuwa imran cikin ikon Allah sai ba'a samu wani wanda ya dumfare shi ba, har dai jaruman da suke filin suka rage basufi su goma ba, can sai wani jarumi ya dumfari imran, take sai imran ya fara addu'a tun kafin jarumin kariso
.
Ai koda jarumin ya kariso sai ya kaiwa imran sura nan kuwa yayi nasarar kama mai wuya ya daga shi sama ya rungi tafiya da shi har yazo daidai wajen jan kyallen nan, shi kuwa imran sai wutsil wutsil yake da nufin ya kwace kansa amma katon yafi karfinsa , abisa dole yayi lamo tamkar ya suma
.
Koda katon yaga ya sumar da imran sai ya sake shi ya fadi a kasa sannan ya daga kafa da nufin ya taka shi ya fice daga filin , cikin shammata sai imran ya farka sannan ya matsa wa kafar wannan jarumi ai koda kafar wannan jarumi tabi iska sai yayi tangal tangal saakamakon rinjayi yarshi da kafartayi, shi kuwa imran koda yaga haka sai yazo ya bangeje wannan jarumi da kafarsa take jarumin yafadi ajikin wannan jan kyalle daya zagaye filin ai nan take jama'a suka dau shewa
Cikin jin kunya wannan jarumin ya fice daga filin
.
Haka aka cigaba da wannan gasa har ya rage saura imran da wani narkeken kato kadai a cikin filin, shi dai wannan kato ana kiransa da suna Narkul kuma duk cikin birnin yemen babu wanda yakaishi girman jiki, asalinsa ma zuwa yayi daga wata kasar,
.
Narkul ya dubi imran ya kece da dariyar farinciki don kuwa shi yariga da ya aiyana akan ya gama cinye wannan gasa don har ya fara hango amaryarsa a cikin dakin shi,
.
Narkul ya dumfari imran gadan gadan shi kuwa imran sai zulliya da gociya ya runga yiwa narkul take mutane suka ringa kiran sunan narkul, koda narkul yaga imran na neman ya bata mai lokaci sai yayi kukan kura ya falfalo da gudu don yayiwa imran kwab daya ya fiddashi daga filin ,
.
Alokacinda imran yaga narkul ya falfalo da wannan azababben gudun sai dai hankalinsa yayi matukar tashi, dai dai ya rage baifi saura taku goma b ba narkul ya riski imran sai imran shima falfalo da gudu yana dumfarar narkul, ai nan jama'a suka zuba idanu don suga waye zaa kayar
.
Koda ya rage baifi saura zira'I daya ba su hadu sai imran ya tsuguna akan guiwowinsa cikin wani irin salo na ban mamaki ya bi ta tsakanin kafafuwan narkul ya wuce, shi kuwa narkul saboda karfin gudunsa yama kasa tsaida kanshi don kuwa yayi turjiyar amma sai da ya karisa wajen jen kyallen nan har ya ballata
.
Ai koda da ganin hakan sai jama'a suka dauki shewa kowa yana ma imran jinjina
Toh kunji yadda imran yayi gwagwarmaya akan mahaifiyar Taufidatu,
.
Basufi shekara biyu ba Allah ya arzucesu da kyakkyawar yarinya inda suka saka mata suna taufidatu, tun taufidati tana karama take da matukar kyawu don kuwa saboda kyawunta ne ma masunci imran ya hanata fitowa koda bakin kofar gidanne ahaka har ta girma
.
Wata rana ta tafi icce a jeji ta saba takan rufe fuskarta da mayani ta tafi yin iccenta kuma izan ta tafi tunda safe bata dawowa sai dare hakan yasa take daukar abincinta da abinshata ta tafi dasu wannan jeji,
.
Wata rana ta fita icce kawai sai taga wata barewa tana gudu dakyar a kafar barewan na dama akwai wani kifiya take tausayin wannan barewa ya darsu a zuciyanta
Barewar ta zube kasa sakamakon raunin dake kafarta,
.
Taufidatu ta karisa wajen barewar sannan ta zare wannan kibiya daya ke kafar barewar, har hawaye na zuba a fuskarta ta cire mayanin data rufe fuskarta ta daure daidai wajenda yake zubar dai jinin, motsi taji abayanta ta cikin surkukin daji
.
Hakan yasa ta waiga don taga wanene nan tayi arba da sarki Ayyub koda sarki Ayyub yaganta sai ya dimauce nan danan ya ce " tsarki ya tabbata ga Allah daya halicci wannan kyakkyawa"
.
Sarki ayyub yaji ya kamu da tsananin son taufidatu ya tambayeta gidan da suke da zama ta bashi amsa , ko takan barewar daya biyo bai bi ba yana komawa fada ya shirya yanufi gidan don neman auren taufidatu, babu wata gardama masicni imran yaba shi aurenta
.
Ranar auren anyi shagali kala kala, don kuwa duk cikin matan sarki ayuub babu wacce yake matukar kauna tamkar Taufidatu
.
Wannan ce ta sanya hassada hade da kishi suka darsu a zuciyoyin wayannan kishiyoyin nata
.
Sarki ayyub baya da wata matsala sannan talakawa najin dadin mulkinsa ayayin da attajirai da masu hannu da shuni ke matukar bakin ciki
.
Kunsan ance kowane dan adam adunua bazai rasa wata matsala ba toh hakan take ga sarki ayyub, don dhi matsalar saya ce
Matsalar saiki ayyub itace rashin samun haihuwa
Yakan tara manyan malaman kasar yasanya su roka masa Allaj yabashi haihuwa a bangarensa kuwa baya samun isasshen barci sakamakon raba dare dayake yana rokon Allah akan yasa mu magaji
.
Izan kuwa ya zauna a waje guda kuwa babu abinda yake face tunanin irin duk arzikinan daya mallaka da kuma shuhurar dayayi a fadin nahiyar nan yasan cewa yana mutuwa shi kenan za'a dibi arzikinsa wanda shi bai masan yawansu ba , a raba wa matansa saura kuma asaka a baitulmali, daga nan shikenan an manta da shi kenan
.
Wata rana a fada ana ta fadanci sarki ayyun ya kacire bisa wata kujera ta alfarma wacce aka sana'antata da zallar jauhari sannan aka mata cinbaki da duwatsun yakutu a gefensa kuwa waziri ne sannan sai galadima a gefen hauninsa
.
A sannan ne wata mummunan kara mai kama da sautin jaki ta bayyana koda jin wannan kara sai hadimmai da dakaru suka fara zarya a cikin wannan suna neman daga inda karar yake fitowa,
............99%
........
....
..
.
Toj anan zan tsaya kar dai ku manta nidinne Shuraih Usman inkiya shuraih 99%
A littafina na SADAUKI UBAN SADAUKAI
Daga hausaebooks.cf
.
SADAUKI UBAN SADAUKAI
Littafi na daya 1
Marubuci:- Shuraih Usman
Typing:- Shuraih 99%
@hausaebooks.cf
Part B
.
.
Koda wannan kara yayi kamar dakiku ashirin sai ya dauke dif tamkar bai taba wanzuwa ba
Wazirine ya dubi sarki ayyub sai yaga ko gezau ba yayi ba, sannan fuskarsa yana duban gaban fada kai daga ni kasan yayi nisa acikin tunani
.
"Ranka shi dade " waziri yace
Firgigit sarki yayi sannan ya mike tsaye a matukar razane koda ganin hakan sai kowa dake wannan fadar ya mike tsaye
.
Sarki ya dubi jama'ansa a matukar tsorace yace da su
"Yaku Al'ummar birnin yemen shin idanuwanku basu gane muku abin dana gani bane, "
Koda jin haka sai dakaru ,hadimai da yan majalisa duk suka hada baki suka ce
"Ba muga komai ba ranka shi dade"
Nan take sarki ayyub ya dubesu yace da su
"Yaku mutanina kuyi sani cewa dazu da wannan kara mai amo mara dadin sauraro ta bayyana a wannan fada, to kusani a sa'ilin ne wani haske ya bayyana a gabana take wannan hasken ya rikide ya koma izuwa wani kyakkyawan saurayi wanda ko atarihi ban taba jin labarin sa ba
.
Saurayin ya dubeni yace dani "yakai wannan sarki mai tarin iko ina mai yi maka albishir da abubuwa guda biyu, na farko ina mai sanar dakai nan da kwana bakwai daya daga cikin matayenka zata sami cikinka,
Koda naji ya ambata cewa zan sami haihuwa sai na kamu da tsananin farincik, ai bansan lokacin dana tari numfashin wannan kyakkyawan saurayi nace da shi
"Ya kai wannan kyakkyawan saurayi gaggauta sanar dani shin waye kai?" Nan take wannan saurayi yayi murmushi sannan yace " sanin ko waye ni ba shine mai muhimmanci ba, n manzo ne kuma zan isar da sakon da aka aikoni da shi,
Abu na biyu dazan sanar dakai shine
.
Yaron da zaka haifaa zaizo da ababen mamaki da al'ajabi, sannan kuma zai shuhura agaba dayan wannan duniya har sai takai cewa kowa dake fadin wannan duniya ya sansa, kuma ya san sunansa, ammafa zai shiga cikin muggun yanayi don kuwa zaiga masifu da bala'u kala daban daban, akarshe sai ya yada addinin musulunci a gaba dayan wannan duniya"
.$
Koda kyakyawan saurayinnan yazo nan a zancensa sai yayi mani murmushi wanda sai da hakoransa suka fito take wani siririn haske ya daga cikin tsakiyan hakwaransa tun wannan hasken na fitowa kadan kadan har wannan hasken ya cika mani idanuwa har takai bana iyaganin wannan saurayi,
Lokaci guda sai wannan hasken ya bace bat , na nemi saurayin kasa ko sama ban ganshi ba, hakan ya tabbatar mani da cewa ba mutum bane
.
Sarki ayyub ya tada gwauron numfashi sannan ya dubi dukkan yan majalisarsa wayanda suke a matukar tsorace game da jin wannan labari da sarki ayyub ya basu, yace dasu
"Kunji al'amarin daya kasance dani a yayin da wannan karar mai amo da sauti ya bayyana"
.
Koda yan majalisa da sauran fadawa suka saurari wannan zance mai kama da al'mara daga bakin sarkinsu sai wasu daga cikinsu suka kamu da matukar farincikin jin cewa burin adalin sarkinsu zai cika, a sannan ne wasu kuma suka kamu da tsananin bakin ciki
.
****
Babban turaka ne wanda aka kawata shi ainun da ababen kawa
Zaune bisa kujeru na alfarma yan mata ne kyawawa su uku, dukkansu sunci ado ainun
Wayannan yan mata ba wasu bane face matayen sarki ayyub kishiyoyin Taufidatu
Dukkansu suna zzazaune a bisa kujeru na alfarma a yayin da suka yi zagaye da junansu yadda zasu fuskanci juna
.
Babbarsu mai suna zulaikha ta mike tsaye tace "yaku yan uwana, hakika kunsan cewa an sanar da mai martaba cewa daya daga cikin matansa nan da kwanaki bakwai zata samu ciki, shin idan cikin ya kasance ya bayyana ga abokiyar hamayyarmu fa, mene ne mafita
.
Ta biyun wacce ta kasance sunanta shamlika , ta mike tsaye ta fara bayani "hakika zulaikha kinzo da magana mai muhimmanci, ni kuma nan take zan warware wannan matsalar"
Zulaikha ta dubeta tace " tayaya kenan "
Murmushin mugunta shamlika tayi sannan tace "ta hanyar hana sarki ayyub kusantar taufidatu, ta hanyar kissa da kisisina "
.
Ta ukunsu wacce tunda aka fara wannan tadin bata ce uffan ba , sunan ta zarishatu ta dubesu sannan ta kyalkyale da dariya sai da tayi mai isarta sannan tace
" Yanzu akan wannan dan abin ne muke ta wani damun kawunanmu, sannan tayi shiru na dan lokaci kankani
.
Ita dai zarishatu bakaramar hatsabibiya bace don kuwa mahaifinta wani babban Attajirine wanda duk kasar yemen babu mai arzikinsa, ko sarki ayyub bazai nuna masa arziki ba sunansa Sirrinaddalib
.
Alokacin da sirrinaddalib ya cika shekaru ashirin da biyu a duniya sai ya kasance wata rana da daddare yana barci yayi mafarki acikin mafarkin nasa yaga wata kyakkyawar budurwa sai gudu take a cikin dokar daji kafafunta babu takalmi sai sossokewa take da kayoyi koda yai duba izuwa bayan wannan budurwa sai yaga wani murtukeken naman jejine yake biye da ita, koda wannan dabbar ya kusan cimma kyakkyawar budurwan sai sirrinaddalib yasha gabansa take wannan dabbar yayi tsalle da zummar ya fadawa sirrinaddalib
.
Firgigit ya farka daga wannan mafarki washe gari kuwa da sirrinaddalib yayi shiri ya fita farauta don kuwa halaiyarsa ce duk wata ranar alhamis toh wajibine agareshi sai yaje farauta shida hadimansa da dakarunsa kimanin su dari,
Ayayin da suka tsinci kansu acikin dokar daji sun
.
Sai ya kasance cewa sun zagaye wannnan jeji kaf amma ko bera basu kama ba, nan take sirrinaddalib ya harzuka yaba wa hadimansa umarni cewa acigaba da tafiya koda kuwa za'a kwana ne ana wannan farauta ba zamu koma da baya zuwa gari batare da mun kama wani dabba ba,
.
Suna cikin wannan zance ne sukaji alamun motsi a cikin ciyawa take kowannensu yayi shirin fada dakarunsa suka zare takubbansu masu kibbau suka dameta,
Wata kyakkyawar budurwace mai matsakaicin tsayi da matsakaicin jiki ta fito daga cikin wannan ciyayin tana mai falfala masifaffen gudu,
A bayanta kuwa wata murgujejiyar zakanya ce ke biye da ita ,
Koda sirrinaddalib yaga haka sai ya tuna da mafarkinsa nan take yabada umarnin a sakar ma wannan zakin ruwan kibbau
Dakiku kadan sai ga wannan zakanyar ta fadi rikica aa kasa gaba dayan jikinta kibiyoyine
.
Bayan kuran ta lafane attajiri sirranaddalib ya iso gaban kyakkyawan budurwannan sannan yayi mata nuni data hau kan dokinsa , batare da gardama ba kuwa ta hau,
Koda Sirrinaddalib da tawargarsa suka cikin gari sai ya nufi gidansa wacce aka kawata ainun har...


Read / Download SADAUKI UBAN SADAUKAI BOOK 1 AND 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album