Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

ZUCIYA DA KWANJI 2 Complete Hausa Novel Document by ZUCIYA DA KWANJI 2


ZUCIYA DA KWANJI 2

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36985



ZUCIYA DA KWANJI 2

Reading Time: 3 Hours

Added On: 01, Oct 2023

Author: Amierah S man ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 186.38 kb

File Type: txt

Views: 1057+

Download: 491+

Last download: 1 day ago

Description/Story: ZUCIYA DA KWANJI 2
.1)Abdullahi ya mike ya fara ja da baya ba tare
da fuskarsa ta bayyana tsoro ko shakka ba, sai
da ya dangane da bango sannan ya daga mata
hannu alamar sallamawa, yana kuma dariya ya
ce. "Wai dukana zaki yi ne? Kawai sai ta ci
kwalarsa cikin yanayi na fita hayyacin ta,fara
magana da sarkewar murya. "Ai wallahi ba ka
isa
ba... Na rantse ka yi kadan ka tozarta
rayuwata.... In aure ka in ci me da kai....? Ni ba
na sonka.... Na rantse yau sai ka sallame ni na
bar gidan nan, in ba haka ba sai dai mu kashe
juna ni da kai". Sun fi minti biyar a haka tana
sakin maganar da ranta ya raya mata tana
kuka,
sannan tana faman jijjiga shi har da duka. Ya
tsaya kawai ya zuba mata ido,tun yana dariya
har dariyar ta gagara..... Sai da ya. Tabbatar ba
ta da niyyar ta hakura ,sannan ya yi
maganinta.
Ya riko gashinta da karfi,wanda. Ya karya.
Lagonta ta fara kara,ya dago kanta tana
surutai
na cin fuska gare shi,kawai sai ya rufe bakinta
da
nasa. Ya kuma nuna mata shi jarumi namiji
ne,inda ya saki gashinta ya matse ta sosai cikin
gwaninta ya fara juya harshenta da nasa Ya
rufe
bakin masifa duk kokarinta ta kasa kwatar
kanta
ita da kanta sai da ta ji a ranta akwai inda
mazan suke. Numfashinsu ya sarke da na
juna,ya
daga aikawa kwakwalwarsu wani sako mai wuyar
fasara. Ya dai yi nasarar motsa duk wata
halittar
soyayyarta da ke zuciyarsa,ya gadar masa da
doki da fatan kasancewar su tare matsawar
numfashi.shaukin da ke shake numfashinsa bai
taba jin rabinsa daga wata ba....... Akwai
bambanci tsakaninta da shi,ita halin da ta sami
kanta bai wuce kwakwarewar komai a
kwakwalwarta ba. Ma'ana ya sauke farashin
masifarta da cushe mata zuciya kuma ya
sassauta mata zafinsa da kiyayyarsa da ta ke ji
a
makogwaronta,sai ya sanya mata raunin jiki da
na zuciya,yayin da kwakwalwarta ta dauki wani
aikin daban. Sai da Abdullahi ya fahimci hakan
sannan ya kyaleta,ya rungume ta tsan tsan a
jikinta,ta saki runane kukanta mai tsuma
rai,sai
ra bar shi da hawayen zafin kauna. Ya dago
kanta da rikitacciyar murya ya kira.
Sunanta,ya
fara girgiza mata kai... Bai jira ta ce wani abu
na
ya fara dauke hawayenta da halshensa,sai ya
....
Ashe bakinta,ya ja ta kujera ya zaunar sannan
ya
zauna gabanta a kasa da nasa kwallar ya fara
magana a tausashe. "Fatima kar ki wahalar da
numfashinmu,ba zamu iya rabuwa ba. Ban aure
ki don na saki ba tun kafin na dora idona a
kanki.... Ya ya kike tsammanin zan iya sakinki
bayan na ganki soyayyarki ta shige ni da zafi?
Ban taba dandanar so mai zakin naki ba fatima
ban taba jin a raina zan iya mutuwa a kan
mace
ba,sao akanki. Na kuma ji a raina ni ne zan da
ce
da mijinki ni dai ana aure domin bauta.....
Aurenmu ne zai samar da riba biyu, wato rayuwa
mai dadi, wadda kuma zata samar da lada,ki ba
ni dama mu gwada wannan sa'ar fatima,sai kin
sami kanki a aljannar da ta zarce ta gidan
Alh,don ba kudin ne kawai jin dadin rayuwa
ba,sannan ki sami Allah kin mai biyayya ga
umarnisa,amma me kika tanadar tsayawa
gaban
Allah idan kin yi zaman haramci da Alh?
Like · React · Report · May 15, 2015
Xaeenab Umar Yaqub
tnx
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
2) Da tana ta shesshekar kuka,sai a wannan
gabar ta tare shi. "Ina ruwanka? Ko kana da
kaso
a cikin hisabina? Idan haka ne ka fada min?"
Ya
kara zagewa da rarrashi. "Wannan hisabin mu
uku,ya shafa,da. Alama kuma zan fi kowa
tabewa
tunda ban mori komai ba a duniyar..... Koda
yake
ku ma din ba zaku mora ba, shaidan ne kawai
yake rudinku,ko ba ki tuna yadda kike kin Alh a
da? Sai bayan ya sake ki shaidan ya kawata miki
shi, shi ma shaidan ya kara haska masa ke har
kuka sami damar ture komai kuka halatta
haram.
Hawaye ya bushe a idonta ta fara magana a
sanyaye,sai dai klaman nata da zafi. "Ko ina
son
Alh,ko bana sonsa binciko wannan ba zai amfane
ka da komai ba, don kai dai bana sonka,kuma ba
zan taba iya zama da kai da kai ba.... Kuma
dole
ne ka sake ni idan ba haka ba sai dai cikinmu
wani ya bar wa wani duniyar. "Ko a jikinsa,ya
ce
mata. "Ai na shirya,ina fatan ke ma haka....
Na yi
mutuwar so ke ki yi taki,zan yi farin ciki idan za
mu bar duniyar tare sai mu tashi da juna".
"Allah
ya kiyaye". Ta fada da karaji. Ya tashi da sauri
tare da dora yatsa a lebe,sannan ya fara yi
mata
inkiya da window da kofa alamar kar makota su
jiyo ta ya ce. "Na riga ki a wajen Allah, ga shi
kuma alhairin na je masa da shi ba sharri ba,
fatima kar ki batawa kanki lokaci na fada miki
ban aure ki don na saki ba..." Sai ta yi zuru
tana
kallonsa lokacin da zuciyarta ta kai matukar
kuntata. Ya rabu da ita ya sa kai ya shige dakin
baccinta ya yi kwanciyarsa. Ta yi kukan,ta yi
rurin har ta hakurkuratar da kanta ta nufi
bandaki
ta dinga wankin bakinta, sannan ta zo ta dau
hijabinta ta nufi kofa.yana jinta. Ta bude
kofar
dakin ta fita tana faman kukan,ya yi dif yana
sauraronta don yasan babu inda zata iya
zuwa.illa kuwa sai gata a guje ta dawo ta shigo
falon ta rufe. Ya koma ya kwanta yana dariya.
Ta
fice karfe biyu da rabi a falo tana kuka,ta rasa
ta
inda zata fara wannan rayuwar bakin cikin da
kuma tunanin makomar lafiyar Alh da ya
kwallafa
ransa a kanta,to ga jarrabar da Allah ya aiko
musu. Babu dabara ta kwashi kafa ta tafi gidan
su wanda tafiyar ce zata to asirin abin da suka
binne idan Abdullahi ya bara.gara ma ta zauna
su
gurji juna duk wanda ya ji jiki sai ya sallama.
Sai
da karfe uku ta gota ya daina jin shesshekar
kukunta.da ya lallaba ya leko sai ya ganta kife
kan kujera bacci ya kwashe ta. Ya fito da bargo
a
hannunsa neman yadda zai gyara mata
kwanciyar ya zama jidali,dole sai bargon ya
rufe
mata ya wuce bandaki ya dauro alwala ya zo ya
gurfana gaban mai share hawaye. Sai hudu da
rabi ya dan kwanta ya runtsabaccin rabin
awa,sannan ya farka domin sallatar sallar
asuba.
Bayan ya dauro alwala ya zo ya bude fuskarta
yana yarfa mata ruwan hannunsa. Frigigit ta
bude
idanunta da suka yi jawur,ya ce mata. "To
sarkin
kuka tashi ki yi sallah,in yaso sai ki kai wa
ubangiji kara ta,ki dinga addu'a sai ki ga Allah
ya
warware miki duk wani kulli da ke cikin
zuciyarki,yanzu ina amfanin da kukan da kika
kwana kina yi jiya,ya samar miki? Da kin yi
dabara sai ki yi alwalarki ki kai wa ubangiji kara
ta.idan babu khairi a tare da ni ya canja miki
ni".
Ta yunkura ta tashi tana janye jiki.ya bita da
kallo da yanayi na nuna kulawa. "Me yasa ba ki
shiga wancan dakin kin kwanta ba, idan ba za ki
hada daki da ni ba? Sai ki takura kanki a nan
fatima?". Ta gyara zama tana zabga masa
harara,ta ce. "Ai ni na gama jin dadin
rayuwa,in
dai da kai zan yi ta. Ya yi murmushi,tukunna
tawa tare, tunda ni ba ni da rayuwa mai dadin
da
babu ke, sai kuma ka yi sa'a muka yi haduwar da
babu rabuwa". Cikin girgiza kan girmmar bacin
rai,ta ce "Allah ba zai cikawa maci amana irinka
burin ba Abdullahi...."
Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
3) Ya tare ta yana kallon kwayar idonta. "Da
na ci amanar wa? Ke ba ki san an ce mafi
sharrin
mutane shi ne wanda yake salwantar da
addininsa domin duniyar waninsa ba? Matsayin
na ke nan idan kuka yi tsani da ni kuka kulla
zaman haram...... Kuma da kike maganar Allah
ba zai cika min buri ba, ai ni Allah ya cika min
buri a kanki fatima,ya aura min soyayyarki
wanda
ina cike da fatan hakan. Tunda har Alh da kika
aura bisa kaddara kika yi zaman dole da shi ya
sami gurbin son da kike jin zaki iya zaman
haram
da shi,balle ni da kika zaba a matsayin
jaruminki
fatima.... Karkari ki yi boren ba ni da kudi, to ni
zan tabbatar miki kudi ba su kadai ne nasarar a
rayuwa ba". Ta yi kasake kawai tana kallonsa,
ya
ya aka yi ne yasa tsakaninta da Alh haka?
"Tashi
ki yi sallah" Ya fada lokacin da ya daidaita kan
sallayar,sannan ya tayar da kabbarar
raka'atainil
fijir.bayan ya idar ya sa kai ya fice masallaci.
Cikin sanyin jiki ta tashi wasu abubuwa na yawo
a ranta.dole ta yi taka tsan tsan da Abdullahi
tunda ya san abubuwa da dama a kanta. Ta
dauki shawararsa wajen kai kukanta wajeb mai
duka sannan ta takure akan sallayar har ya
dawo
masallaci ya same ta. Kai tsaye wardrobe ya
wuce ya bude yana nazarin ciki,sannan ya fara
yo
waje da kayan wankin kayan da ta shafe
kwanakin ta a gidan tana sanyawa ba tare da ta
nemi mai wanki ba. Ya ware wadanda suka
kamata akai wanki ya kulle,sannan ya kwashi
kananan kaya irin su vest da underware da su
rigunan bacci zai fita da su. Fatina da ke satar
kallonsa tun dazu sai ga ta tsaye. A kulule ta ce.
"Ina zaka kai min kaya?" Ya tsaya yana
dubanta,ya ce. "Wai gaisuwar ke nan?" A
tsiwace
ta ce masa. "A matsayinka na wa zan gaishe
ka?" Ya yi mata kallo da gefen ido,sannan ya
ajiye kayan a gefe yana cewa. "To ko in zo in
nuna miki matsayina?" Ta yi saurin komawa ta
zauna tana kunkuni. "Abin da ka iya ke nan".
Ya
tuntsure da dariya ya dauki kayan ya fice.
Yana
cewa. "Ashe har kin fahimci ni?" Can baya ya
zagaya ya wanke kayan tsab ya shanya sannan
ya dawo ya...


Read / Download ZUCIYA DA KWANJI 2

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album