Join Our WhatsApp Group

YAR JAMIA Complete Hausa Novel Document by YAR JAMIA


YAR JAMIA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 60954



YAR JAMIA

Reading Time: 5 Hours

Added On: 13, Sep 2023

Author: Hewwerh Jidderh ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 318.79 kb

File Type: txt

Views: 807+

Download: 365+

Last download: 4 days ago

Description/Story: ο»Ώ[1:50pm, 05/05/2016] πŸ““
πŸ““01 *'YAR JAMI'A*πŸ““πŸ““

_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


_In Devotion to yuh my Dearies:

*ANEESAH ABUBAKAR RIMI*
*(ANEELURV)*
&
*UMMIEE ADNAN*



Gabatarwa:

Assalamu alaikum 'yan uwa da masoyana baki daya naga irin sakonnin ku naso da na ci gaba da rubutu akan littafina na 'yar jami'a hakan bai yiyu ba sakamakon rashin samun cikakken labarin daga wanda abun ya shafa!yanxu haka an samu gashi kuma xamu ci gaba!kamar kullum LITTAFINA YAR JAMI'A banyi don xagi ko batanci ga wata/wani ba sai don ya xama darasi garemu!allah ya bamu ikon anfana dashi ameen!!
Wattsapp:comment only 08103439416
Visit me @ herwwerhjidderh92.wordpress.com.


Hi Daddy shigowar tane yasa daddy da umma tsayawa daga hirar da suke da mai da kallon su gareta dariyar da daddy ya sakarmata yasa ta kara langwasar da jikinta ta hanyar fadawa jikin umma tana wani shashsheka kamar mai shirin kuka daddy xan wuce scul na ji ance jiya anyi lecture toh ai kinga irinta dama ai nasan xa'a rina kamar na sani nace jiya karkije airport tarar mahaifinki amma kika ki ji ki sani fa wannan makarantar ba kamar ta baya bace dole sai kin kula cewar umma tana kallonta fuska ba yabo ba fallasa tuni hajara ta mike daga jikinta tana bubbuga kafa a kasa tana daddy ka ganta ko ai bashiri daddy yaja hannunta fuuuu suka haye sama yana mai bata baki shigarsu dakinsa ke da wuya daddy yace beauty rufe idonki ki karbi tsarabarki amma fa bayawa kin san ba shiri kika sa na dawo dan naga murnar xagayowar haihuwarki gobe cikin sauri ta rufe tare da cewa toh na rufe daddy dakko min hannu yasaka cikin aljihun riga yaxaro karamar takarda ya bude hannunta ya saka mata yace gashi babu yawa kya iya bude idonki yanxu;ai kamar jira take ta bude me xata gani takarda(check)da rubutun kudi har naira dubu dari biyar,tace daddy wannan fa bade shine na kayan da xan siya na birthday na ba tana fadi tare da bata rai yace haba beauty kamar ni na baki haka a birthday"kawai na shiga scul ne dan ki farin cikin daddynki ya dawo" woooo" ihun da tasa ke nan tana mai rungumesa da fadin sai daddy na wallahi ko garin ba kowa amma fa ki kula maza kisaka a jakarki kafin......bude kofar da akai ne yasa ta yi saurin saka takardar a jaka da fadin bye daddy kam tayi bakin kofa ita bata wuce ba kuma batai magana ba har sai da daddy yace bata hanya fa kar 'yata tai latti matsawar umma yabata damar fita cikin sigar sauri batayarda tayi magana ba sai da takai bakin kofa da sauti mai karfi tana umma xan siya miki ice-cream rufe kofar tai da xura wa mijin nata ido sanin da abinda ya kawota yasa yayi azamar juyawa da bude kofar bandaki murmushi kawai ta saki tace kashiga kafito ina jiranka don akwai maganar da xamuyi!


Abangaren beauty kuwa kamar jira take ta karasa wajen aje mota tana dariya ta bude jaka ta xaro key ta bude motar tare da rufe ta tadau kusan minti biyar tana kallon kanta a madubin motar kafin tunaninta ya koma kan takardar daddy!yanxu toh yau me xanyi wanda yafi na kullum yanda xai sa na wuce duk wata kaza a scul din nan don allah yau sai an bini ko ba'a so hhhhhhhhh!jin dariya kawai kake na tashi kamar tana hira da wata karar wayarta ya katseta daga kogin tunanin data fada ganin wacceta kirata yasata saurin dauka da karawa a kunne tana fadin duk inda kike yanzu ki fito ki tsaya a bakin gate na scul dan yau akwai harka...





πŸ““πŸ““ 02 *'YAR JAMI'A*πŸ““πŸ““

_By_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Harka kuma?ka ga shegiyar gari waya gina ki haka ?gaskiya beauty ba kyau wajen samu kalaman matashiyar yarinya xee-xee kenan wacce ta amsa sunanta! Shike nan dama ina hanya na tsaya gidan mai ne amma yanxu xaki ganni,ok toh sai mun hade haka ta fada tare da kashe wayar tana maida numfashi! Cikin nutsuwa takunna motar tare da kara sautin wakar (u are my african queen) wanda ya bata damar juya kan motar tai hanyar gate gaisuwa baba me gadi ke kai wa da washe baki yana kokarin bude kofar!jaka ta bude ta zaro dubu hudu ta mika masa tai waje ai godiya da kirari wajen baba me gadi ba kama hannun yaro!!


Kofar shiga jami'a cike take da motoci,mashina,kekuna da kuma dalibai matafiya kasa kowa cikin layi don karbar takardar shedar shiga jami'ar(gate pass)hange take tayi ko ta gano inda aminiyarta ta tsaya amma yawan motoci sun hana dole ta kira ta a waya tasanar da ita inda ta tsaya!can gefen titi kadan da gate ta tsayar da motar!gano lambar motar yasa beauty tai saurin karasawa tare da tsayar da motarta,tsayuwarta ya ba xee-xee damar bude motarta da nufowa wajen beauty;ai kamar jira take ta shigo beauty ta saki wata dariya jikake tana fadin ai mun afuwa na jima ko? sarkin fushi kallon data sakar mata yasa tai ajiyar zuciya tare da fadin mene labari!
Sannin kanki ne xee-xee daga haduwarmu wancan satin xuwa yau mun shaku da yawa kuma tamu tazo daya dan haka ina so na ke ta raini a scul yau fiye da yadda na yi satin daya wuce don so nake na zama 'yar jami'a lamba daya da kowa zai so ni a makarantar nan duk da ana cewa sai ka gama tashenka wani bai san da zamanka ba!amma ni beauty kisani da ban nake kuma dole abi ni don salona daban yake tawan!!hhhhhh dariya xee-xee ta saki tare da kallonta tana fadin kina wuta beauty! Naga wani country mall wajen ya hadu amma fa ban taba lekawa ba kawai xamu shiga ki siya ki canja acan tunda akwai wajen sa kaya sai kuma nima asai min nawa ko kuwa??xee-xee tai furucin tana mai watsa hannayenta!hmmn kema kin san wannan ba matala bace ke dai shiga motarki ki biyo ni kawai!!


πŸ““πŸ““03 *'YAR JAMI'A*πŸ““πŸ““
*BY HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Haj.Halima ce zaune bakin gado"wato umma tana jiran fitowar daddy daga wanka" tunani fal cikinta ta sak'a wan-can ta kunce wan-can" jin da tayi an watsa mata ruwa a fuska ana dariya yasa ta dagowa tana kallonsa"!har ka fito dear ta fada tana kauda kanta" !juyawa kawai yayi yana fadar ai tunda ba taimako ba dole nai saurin fitowa ba" don nasan ko fita ban gama yiba na fito !jin tayi shiru yasa shi juyowa tare da fadin ki tallafa min wajen shafa lotion mana uwar'gidan!mikewa kawai tayi ta dawo kusa dashi batare data bari sun hada ido ba"tahau shafa masa sai da tagama tsaf tana shirin tashi yace yau kuma fuskar laifi me tai miki kika barta?cikin halin ko in kula ta debo lotion din ta kai hannunta fuskar ke nan ya ruku hannun tare da fadin haba farin ciki na ki shafamin mai tare da kallon kwayar idona shine abinda nafi so sama da komai a yanzu dan nasan baki da musu.
Sannin halin matar tasa yasa ya dago fuskarta suna duban juna yace kiyi sauri mana ina so naji damuwarki fa kallon daya bita dashi ne yasa ta murmushi tana fadin dear kasan lagona da yawa duk damuwata ka iya da ita maza tashi kasa kaya muyi maganar!!murmushi ya saki ai kin san mata da miji sai allah tawan!
*******

Katon katafaren kantin nan na country mall beauty ta tsaya tare da fitowa cikin zumudi don taga lokaci na tafiya!besty yi sauri fito mu shiga ba lokaci fa cikin karamin lokaci suka shiga dauki wan-can aje wan-can" har sai da mai kula da wajen kayan mata ta karaso (area sider) lura da yadda suke bincike kayan tana tambayar baku sami abinda kuka zo nema bane?" naga tun daxu sai bin cike kuke? cikin sauri xee-xee ke labarta mata me suke so!murmushi kawai tayi tare da jan hannun beauty xuwa wani daki"daki ne madai-daici amma fal yake da kaya na alfarma"dubanta beauty tai cike da mamaki tace wow fantastic"nan matar ta dafota tana fadin wannan kayan da kika gani anan d'akin sai manyan mata ke sayansu ga k'yau ga kudi in zaki iya nasa ashirya ki a tailoring room dinmu" ya kika gani?baki kawai beauty ta bude tana kallon matar ai auntyn 'yan gayu kudi ba matsala ta bane ke dai ashirya ni kawai!auntyn 'yan gayu kuma kaji sabon suna cewar matar tana dariya"nan suka fito daga d'akin xee-xee de na tsaye tana kare ma wajen kallo auntyn 'yan gayu ce ta waigo tace kawar beauty ki zabi naki bari na kai ta ciki a gyara ta!toh kawai tabita dashi xee-xee tana kare ma wajen kallo lallai gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta!


πŸ““πŸ““04 *"YAR JAMI'A*πŸ““πŸ““

_By_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRUNCESS'QUE~DEE*



Shalele na ya kika ga wannan shigar! dagani ba tambaya wannan shine namijin da baya tsufa!dariya suka saki a tare sannan ya dawo gefen gado kusa da ita ya zauna yana mai mata nuni da ta juyo inda yake!uwar gidana mata daya tal gare ni a duniya har lahira inshaallahu haleematu na gaya min damuwarki!Damuwata sanin kanka ne baza ta wuce taka da ta 'yarka ba wallahi dear ina shiga cikin wani matsanan cin hali idan naga yadda kake tafiyar da rayuwa hajara katuna yanxu ba da bace!ace yarinya tun tana karama sai abinda take so ake mata bata san fada ba!har tana ganin kamar kafi sonta akai na gaskiya dear da sake don haka kasan abinyi akanta!ya kamata muzauna muduba rayuwar yarinyar nan don nan gaba fa aure zatai haka zataje gidan mijin nata kuma har ta iya rike 'ya'yanta da wannan tarbiyyar hab.....ke!ke!ke dakata halima wannan ne daman damuwar naki ashe kuwa zaki jima cikinta ko dan bana miki magana kina gani ina kauda kai shiyasa yau kika biyo ni ta haka"?eeyee"?nayi zaton ma kina missing beauty ne din xata je scul ta barmu da kadai ci"ashe ke ba haka ba!toh idan ban nuna mata so ba wa zai nuna mata?ai wannan shine gata!"gata"?gata fa kace dear?wannan ba gata bane wallahi cutar kaine kuma ya kamata ace kasan da haka" inda nima haka aka kawo maka ni ai da nasan yanzu labari ya canja kafa tsaya ka duba maganar nan dear!"dubawar kenan kuma kisani rai na ya baci dan haka idan bazaki iya taimaka min akan tarbiyyarta ba ni zan iya ni kadai !kuma kar naji kar na gani bacin ranki akanta halimatu!

Mekewar da yayi ne yana neman fita rai a bace wai shi me 'ya yasata durkusawa gabansa tana mai sunkuyar da kai!dear dan Allah ka gafarta min kada fushinka yasa na samu fushin mahaliccina natuba kuma bazan sake ba amma na san da ranar nadama!hmmm tawan kenan tashi na ji ba komai kuma ya wuce amma ba ranar nadama!!cikin yanayin bacin rai ya fice tare da rufo kofar gammm kake ji !!tashi tai ta zauna tana kare ma dakin kallo!hmmn Allah gatan bawa ga dukiyar ga soyayyar ina samu amma tarbiyar 'yar ciki na an hana nabata wannan wace irin rayuwa ce da anyi magana ya hau fushi yana kururuwa kamar wani zaki wai shi me 'ya!"
hmm na biye ma tunani tabbas zan iya kamuwa da wata cutar bari kaga na tashi na leka kitchen naga me ladiyo ta ke yi!

(WANNAN KENAN)



πŸ““πŸ““

05 *"YAR JAMI'A*πŸ““πŸ““

_By_ *HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS'QUE~DEE*


Bude kofar da akai ne yasa xee-xee saurin juyawa rike da wata hadaddiyar doguwar riga a hannunta da alama ita ta xaba xa ta saka baki bude tabi beauty da kallo!ya kika ganni?cewar beauty tana kara gyara xaman kayan jikinta!wani smiling xee-xee ta saki hade da fadin mace kamar hawainiya lokaci kankani haka kin canja gaskia dole akira ki da *beauty* kyau kamar ba gobe"bari kiga nima nai sauri na gyara sai mu wuce kin san fa wannan tsohon mutumin ne damu!"wanne farin ko bakin?!bakin dai mana nifa naga ko d'an sako wasa cikin karatunsa baya yi balle dariya!ke dai yi sauri shirya mu wuce tun da bai iya wannan ba ai zai iya kallo ko?cewar beauty tana wani karkada boobs nata"cikin sauri xee-xee ta shirya ta fito ta tarar da beauty na karbar receipt daga hannun auntyn 'yan gayu da alama ta biya kudin kayan ne!xamu iya wucewa kawai na gama!hmmn yarinya ga kyau ga diri kin fa fita da yawa cewar beauty tana danna waya!yawwa na shigar da nambar sai kin ji ni auntyna" dariya kawai ta sakar mata hade da sallama suka wuce!

Gudu take sosai da motar kamar mai shirin tashi sama har ta isa babban gate na shiga *Jami'ar* ta karbi takardar shiga(gate pass) ta wuce har takai *A.Bukar twin theatre*ji kake kiiiiiiiiii... ta ja birki! Ido kawai jama'ar wajen suka bita dashi atunanin su motar ta kwace ma ta ne!hankali kwance ta bude motar ta fito rige da karamar jaka a hannu!ta hau duba bayanta ko zataga motar xee-xee can ta hangota ta kusa karasowa ta ja wani karamin tsaki!cikin sauri xee-xee ta karaso ta fito tana nufota tana cewa lokaci ya wuce nasan ma yanxu ya shiga wallahi mu d'aga k'afa!ke dalla mene haka da kin san da haka kike tuki kamar 'yar koyo!wai yanxu karfe nawa ne?10.a.m fa xee-xee ta fada jiki a sanyaye ni naga ko a jikin ki beauty wai ke baki da tsoro ne?hmmm kin san lokacin da aka haifi tsoro ina bacci pls ki biyo ni kawai...
Bin ta kawai take amma hankalinta duk ya gama tashi!daliban dake wajen kuwa tuni kallo da hira ta koma kansu kowa na tofa albarka cin bakinsa!

Kofa ce a rufe da alama an rufo wajen ne!hannu ta saka ta bude tare da shiga sauri-sauri" gudu-gudu take taka matattakalar ta haye sama ta na duba wajen zama! Can ta hango wuri kusa da wani saurayi taje ta zauna tana fadin dan matsa na samar ma xee-xee waje!tuni ya matsa yana binta da kallo na mamaki!daga kan da zatayi ta hango xee-xee tsaye bakin kofa ta kasa shigowa! In ranta yayi dubu toh ya gama baci!cikin tsawa kake jin maganarta tana fadin kishi go malama kar a gama attendance bake....

*Get out of my class*"!!!(fitar min daga aji) Maganar prof.kAS kenan yana cire karamin gilashin dake manne idonsa!binsa tai da kallo kawai ba tare data motsaba!are you not hearing me?(bakya ji na ne?) I said leave...(nace ki fita...)sorry sir i didn't get u(malam ban fahimce kaba)!!tafada tana watsa hannayenta cike da raini"dogon tabur din dake gabansa ya kaiwa duka da hannu"kafin yace"toh dan ubanki zan miki da yaran da zaki gane fice min daga aji kuma kar na kara...


Read / Download YAR JAMIA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album