Join Our WhatsApp Group

TSANTSAR BUTULCI Complete Hausa Novel Document by TSANTSAR BUTULCI


TSANTSAR BUTULCI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 19079



TSANTSAR BUTULCI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 27, Dec 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

Author Phone : 08089965176, 07084653262

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 111.5 kb

File Type: txt

Views: 668+

Download: 239+

Last download: 5 days ago

Description/Story: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
*TSANTSAR BUTULCI*
⚱⚱⚱⚱


*NA*
*BINTA UMAR ABBALE*
*®BINTUBATULA👄*


```Marubuciyar```

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING....```

_*TSANTSAR BUTULCI*_



*NA FARA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI*



_*Arashi*_

*WANNAN LITTAFIN K'AGAGGE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BANYI DOMIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE*



*BAN YARDA WANI KO WATA BA YAYI AMFANI DA WANI B'ANGARE NA RUBUTU NA BA,BA TARE DA IZINA NA BA, AYI HATTARA*




*WANNAN LITTAFIN NA KUD'I NE, NAIRA D'ARI BIYU IN MUTUM NA BUK'ATA SAI YA BI WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA*
08089965176
07084653262



*UP*
*UP*
*UP*
*KUNA RAINA, BINTA UMAR FAN'S HAK'IK'A BANI DA ABUNDA ZANCE DA KU SAI FATAN ALKAIRI*

*GAISUWAR KU DABAN TAKE, DOMIN BAKWA GAJIYA DA YI MIN COMMENT*

*UMMAHANI "YAR MUTAN BAUCI*

*NANA AISHATU " YAR MUTAN KATSINAWA*

*PREETY "YAR MUTAN BARNO*

*ZAINAB " YAR MUTAN KATSINAWA*

*MAMAN SUDAIS SAKWATTO*

*HAJIYA INDO AMADU*

*FAUZIYA MA'AWIYYA*

*RAHAMA ALIYU*

*MAHILLA UMAR*

HAK'IKA BAZAN TAB'A MANCE KARAMCIN KU GAMI DA FATAN ALKAIRIN KU A GARE NI, NAGODE SOSAI DA ADDU'AR KU.

KUYI HAKURI WANDA BAN FAD'A BA KUMA KUNA RAINA SOSAI ANA MUGUN TARE🤝🏻



_ZAMANI WRITERS ASSOCIATION_
_________________________
*KUN CANCANCI YABO DA GODIYA A GARE NI*

*1 HUSAINI ATK 80k*

*2 ZAINAB ABDULLAHI,SHAXXI*

*3 NASMATU "YAR MUTAN ARKILLAH*


HAK'IKA BANI DA BAKIN GODIYA A GARE KU SAI DAI IN CE ALLAH YA K'ARA MUKU LAFIYA DA NISAN KWANA, MUNA TARE IYA WUYA🤝🏻




_ALHAMDULILLAHI INAI WA D'AUKACIN AL'UMAR MUSULMI MURNAR BABBAR SALLAH UBANGIJI ALLAH YA MAIMAITA MANA YASA MUGA NA SHEKARU MASU YAWA, ALLAH KA SHAFE MANA ZUNUBAN MU, AMEEN_



_*WANNAN PEGE D'IN NAKI NE*_


*HAUWA S ZARI'A*
(Maman Usuwan)

*ALLAH YA K'ARA HIKIMA DA AZANCI*





*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM*






*🅿1&2*







Wani babban gida ne me d'auke da d'akuna masu ciki da rumfa-rumfa za su kai bakwai, kana ganin gidan kasan gidan yawa ne kuma da ka gani me gidan me tsohuwar dukiya ne, a zamanin sa, bene uku ne a gidan d'aya a soro biyu a babban tsakar gidan, tsakar gida babban gaske ne ga wasu manyan bishiyu na dirimi a gidan har guda biyu, band'aki na futsari uku ne haka kuma na bayan gida uku ne,bayan na tsakar gidan a kwai wasu a bene guda bibbiyu. Kana ganin benen kasan na samari ne saboda yadda suka barbaza takalmansu da gajerun wandunansu, fulas din abuncin su, da kwalaben lemo gami da robobin ruwa da ledar pure watar duk ga sunan a watse a barandar benan me d'auke da d'akuna biyar.

Kicin d'in na kalla naga wata k'atuwar tukunya a kan murhu ana ta da huwar abunci "yan matan gidan ne suke ta kai kawo tsakanin kcin d'in da d'akunansu, ko wacce da aikin da take banda mutum d'aya, Rabi'a kenan,tana kwance can k'arshen rumfar su tana karatun wani k'aton novel na turanci sai mutsu-mustu take tana lumshe ido ita kad'ai, k'anwarta ce tazo ta tsaya a kanta tana zumbura baki tace" Ke Rabi'a Mama tace"Kizo ki daka mata citta da kanin fari ki d'ora mata shayi kin San yau littinin tana azimi"

A fusace Rabi'a ta aje novel d'in hannunta tace"Wallahi zanci uwarki Sumayya, kin raina ni ko? Ke me ya hana ki d'ora mata shayin da zakice dole sai ni"

Buga cinya Sumayya tayi,tace"Yo ai bani bace Mama ce ta aiko ni, kuma wallahi bani kika zaga ba kanki kika zaga ehe!
Da sauri Rab'ia ta mik'e zata kai mata duka, tayi waje da gudu tana dariya gami da tsalle-tsalle tana murgud'a mata mazaunanta,
Ta kalmi Rabi'a ta d'auka ta jefe mata tace"Shegiya "yar lukuta kawai"

Da gudu ta k'arasa kusa da Mamansu Hajiya Zulai kenan tana zaune kan dadduma tunda ta idar da sallahr la'asar take zaune tana lazimi, tayi saurin yin gyaran murya ganin yadda Rabi'a tayo kan Sumayya tana k'okarin dukanta da takalmi, rike'hannun Rabi'a tayi tana d'an hararata, Rabi'a ta gane hukuncin Mamansu ko da ido ma tana yi, girgiza kai tayi ta bar gurin tana fad'in za ki shigo hannu ne yarinya Allah sai na zane ki"
Gwalo Sumayya tayi mata tana dariya ta d'ora kanta kan cinyar Maman nasu.

Hajiya Gaji ce ta futo daga d'akinta da murmushi a fuskarta ta kalli Sumayya tace"Ke kam kinji kunya, kullum kina nad'e a cinya kin girma baki san kin girma ba wai ke "yar shagwaba'a"
Bubbuga k'afa Sumayya tayi cikin shagwab'a tace" Ni Mama a k'yaleni inci lokacina nice fa duk "yar k'arama a gidanan, a k'yaleni in suburbud'a sha'anina"

Dariya Hajiya Gaji tayi tace"Dube ta don Allah,da baki kamar gidan tsutsa ya iya fad'ar suburbud'a"

Murmushi Hajiya Zulai tayi da carbi a hanunta k'okarinta taga ta kammala laziminta ta shigarwa Sumayya domin yanzu Hajiya Tabawa ma ta futo d'orawa zatayi kan abunda Hajiya Gaji take wa Sumayya suyi mata taron dangi wanda yake sata kuka.
Zumbura baki Sumayya tayi tana kauda kanta.

Hajiya Gaji ta wuce bakin rariya tana dariya.



*TUSHEN LABARI*

ALHAJI MADO GWADABE
Shararran d'an kasuwa ne, me dukiya taban mamaki wanda yasha gwagwar maya a harkar kasuwanci inda ya tsaya da k'afafunsa a wancan lokacin da turawan ingila yake harkar atampah da yadika irin na maza da d'ankwali na mata, mutum ne shi me nasibi shiyasa ko wane gari kayansa suke zagawa idan yaje ya dawo zai rarraba kaya cikin sauk'i da rahusa kafin kace kwabo kaya sun k'are, kamfaninsa biyu a ingila wanda ake atampah d'aya a chana ana d'ankwali, sosai mutane suke ci a karkashinsa, mutum ne shi me k'arfin zuri'a, mutane da dama na cewa gado yayi saboda mahaifinsa Gwadabe ya haihu sosai da sosai wasu sun mutu wasu sunanan a raye shi Mado ya taso bai san ubansa ba domin ya kasance dan amaryasa ne, wanda ya kasance shine k'arami a cikinsu,yana a
Da she kara d'aya a duniya mahaifin nasu ya rasu.



_Tab'a ka lashe_
*ZAN CIGABA INSHA ALLAH SABODA MASU BUK'ATA KAFIN IN DA TURAWA GROUPS SAI WANDA YA BIYA*
*200*
[14/08, 13:13] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿3&4*



A k'alla Gwadabe ya haifi "yaya arb'in da bakwai tare da mataye iri-iri kasancewar shi mutum ne me aure-aure shiyasa ya tara " yaya da yawa mace d'aya sai ka same ta da "yaya goma, ko goma sha biyu cikin mantan nasa guda hud'u harda me " yaya goma sha biyar, Mado ne kawai bashi da d'an uwa saboda da kan babarsa Gwadabe bai k'ara auran wata mata ba, gashi lokacin ya tsufa sosai,kuma mahaifiyarsa ta dad'e bata haihu ba.


To mutane suna cewa Mado ai gado yayi saboda mahaifinsa yayi aure-aure shine shima yake yi saboda yaga yana da kud'i, lokacin da zaiyi auran fari ma da mata biyu ya fara, kuma suna haihuwar fari ya k'aro wani auran inda ya auri mace d'aya itama da tsohon ciki ya cikashe ta hud'un babu abunda ya dame shi.
Yanzu haka yana da "yaya ashirn da bakwai mata da maza, wasu iyayensu ma basa gidan.

Yana da " yaya maza goma sha hud'u inda mata suka kasance su goma sha uku, matayensa uku ne suka rage kasancewar amaryarsa ta futa ta dalilin babban d'ansa me suna Habib, wanda yanzu haka yana can ingila kan harkokin mahaifin nasu shi da k'aninsa Auwal me bi masa kenan,

Fafur!Habib ya hana mahaifinsa k'ara wani auran tunda amaryarsa ta futa yace"Har indai yarinya zai je ya d'auko to gwara kawai ya hak'ura da auran domin yanaji yana gani ba zai yarda yaje ya d'auko musu yarinya k'arama ba tazo tana zagin iyayensu, waccen ma kafin ta futa sai da ya sumar da ita dalili ta zagi Hajiya Tabawa matar mahaifin nasu ta uku, sosai yaran gidan maza da mata suka taso da tarbiya da nutsuwa uwa uba ilimin addini da na boko dai-dai gwargwado kowa najin magana, banda Sumayya ta gagari kowa a gidan maza da mata, mussaman yanzu da ta samu sakewa Yaya Habibu bayanan sai tak'i zuwa makaranta haka duk za'a d'ad'e a gidan babba da yaro duk su tafi banda ita, daga taga lokacin makaranta yayi sai ta shige k'uryan d'akin su tayi kwanciyarta kan gadon k'arfen Mama ta shige loko sosai ta saki labule, haka za'a k'araci nemanta a hak'ura sai taji gidan yayi tsaitt! sai ta futo tana sharb'a gumi tana sosa soshe irin na rashin gaskiya.

Nan Hjy Gaji zata kamata ta murd'e mata kunne tai ta fad'a tana cewa"Wallahi ko don wannan abun naki da kikeyi zan tursasa Yayanku ya dawo domin shine maganin ki,haka zaki zauna babu karatu,shashashar yarinya kawai"
Zumb'ura baki take kawai taje ta d'ane karfen baranda tana sufa tana kyalkyala dariya sai kace wata shashasha, haka take yi ni tana wasa a gidan, babu ruwanta,da zuwa makaranta sai taga dama, har inda kaga tana himmar zuwa makaranta to tabbata Habibu yazo gida,nan ne zaka ga ta nutsu tana abu simi-simi kamar me gaskiya ko tsokanarta akayi a gidan bata ramawa Dan kar ya dake ta, saboda in yazo gurin baya tsayawa ya bi ba'asi zane ta yake ciki da bai yace"Ai itace bata da gaskiya,sai dai tayi kukanta ta gaji, Mama kuwa haushi duk ya isheta duk ranar da Habibu ya dake ta yini take bata kulashi ba,sai dai yazo ya karaci maganarsa ya tafi.
Haka "yan matan zasu dawo gida kowa na bitar karatun da akai masa a makaranta amma banda Sumayya, magariba nayi zasu shirya su tafi makarantar magariba, nan ma sai ta tsiri baccin k'arya, Rabi'a tai ta tashinta tana ji tayi shiru mamansu tace tak'yale ta kawai tayi tafiyarta, haka zasu tafi Rab'ia na jin haushin yadda Sumayya ta maida kanta koma baya cikin " yan uwa, lafin su dawo kuwa ta fakaici idon matan gidan mussaman insun shiga sallah,sai taje ta bud'e miya ta tsamo nama ta tsuguna kchin din tana ci, sai taci me isarta sannan zata gudu gurin Babansu Alh Mado kenan d'akinsa na can benen soro dake d'akuna uku ne sai ya d'au d'aya Habibu ya d'auki d'aya shima Auwalu ya d'auki d'aya, to can gurinsa take guduwa tayi kwanciyarta har sai garin Allah ya waye sannan take sakkowa tana zumb'ure-zumb'uran baki.
To duk me girki a ranar in taga an tab'a tukunya tasan Sumayya ce,haka zata k'araci fad'anta ta hak'ura saboda in tace zata bita saman tayi mata fad'a zasu iya b'atawa da me gidan domin ba'a tab'a masa shalelensa,ko kayan kasuwa ya siyo duk yawansu ita yake bawa yace ta raba musu, in ta sakko k'asa sai tasha na sha taci na ci sannan zata raba musu ragowar Rabi'a tai ta dukanta, ita kuma tana b'are baki tana kuka, babansu najin kukanta,zai lek'o ta taga yayi ta fad'a haka zasu hak'ura su k'yale ta.

Babbar yarsu Zainab tana aure a Kaduna tana da yara bakwai, Ihisan ce babbar "yarta kuma duk itace mace sauran duk maza ne.Ihisan Aminiyar Sumayya ce sosai in tazo Hutu. haka zasuyi ta tsula siyarsu

Sai Khadija ita kuma tana Aure a jibi'a can katsina kenan yaranta uku duk maza

Sai Aisha ita kuma shekararta biyar da aure Allah bai bata haihuwa ba, tana can abuja can take aure






*_Wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu kacal in mutum na buk'atar cigabansa ga numbar ta nan_*
08089965176
07084653262
[15/08, 15:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________


_*Wannan littafin na kud'i ne, naira d'ari biyu in kana buk'atar sa ga numbar nan*_

08089965176
07084653262



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿5&6*



Rabi'a da Suwaiba ne cikin k'uryan d'akin Hajiya Gaji, suna hira k'asa-k'asa Sumayya ta zo ta lab'e bayan labule ta kasa kunne tana jin abunda suke fad'a

Rabi'a tace"Wallahi Suwaiba aure nake so, na gaji da zaman gidan nan gwara ayi min aure kawai in je in mori k'uruciyata,bakiji yadda nake ji ba in ina karanta novels duk sai in dunga jin tsigar jikina na tashi, humm kin san shekaran jiya a gidan k'awata Nusaiba na wuni wallahi baki ga yarda suke soyyaya da mijinta ba,a gabana fa naga yana tsotsar bakinta, wallahi ji nayi ina ma nice"
Hannu Suwaiba tabata suka tafa suna dariya tace"Ba sai ki fad'awa babanmu aure kike so,nasan halin baba aure zai miki da Ansar d'in ki"

"Humm nasan da haka ai,kin san babbar damuwa ta wacce tasa na hana Ansar zuwa gidanan shine, Wallahi ina bal'in jin tsoran masifar yayanmu, kin sam shi babu abunda yake so muyi a yanzu idan ba karatu ba,ni kuma wallahi aure nake so"
Rabi'a ta k'are maganar tana sauke ajiyar zuciya kana kallon yanayin ta kasan da gaske take.

Suwaiba tace"Bake kad'ai ba,Allah nima da zan samu tsayyayen miji aurena zanyi babu ruwana da wani karatu," Tafawa sukayi a karo na biyu suna k'yalkyala dariya.
Motsi sukaji a falo gabansu ya fad'i a hankali Rab'ia tace"Allah yasa babu wanda yaji Suwaiba ce ta d'aga labule a hankali tana lek'owa,kawai sai ta hango k'afar Sumayya bayan labule, tana k'okarin guduwa Suwaiba ta rik'eta tam!tana janta tana turjewa, fad'i take"Wallahi naji abunda kuke fad'a sai na fad'awa yayanmu,ko in fad'awa Babanmu, tabd'ijam,wai aur....da sauri Rabi'a ta rufe mata baki suka jata da k'arfi suka kaita d'aki.
Turje-turje take tana k'okarin kwantar kanta ta gudu sun rik'eta sosai, Rabi'a tace"Haba k'anwata ta kaina, bani ce fa nace ina son aure ba labarin k'awata Nusaiba nake bawa Suwaiba, don Allah kar ki fad'awa kowa kinji"
Kamar zatayi kuka ta k'arashe maganar.

"Oho miki,ni dai sai na fad'a ehe!ai naji sanda kike cewa wai mijin Nusaiba yana tsotsar bakinta, kema kina so,sai na fad'awa yayanmu in ya dawo wai kina so mijin ki ya tsotsi bakin ki"

Cikin rawar murya Rabi'a tace"Ayya Sweet Sistar na, nace miki fa bani nace, labari ne kawai a novel irin...


Read / Download TSANTSAR BUTULCI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album