Join Our WhatsApp Group

MARUBUCI Complete Hausa Novel Document by MARUBUCI


MARUBUCI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

DOWNLOAD

Uploaded by @Taskar

Total Words: 11357



MARUBUCI

Reading Time: 0 Hours

Added On: 21, May 2023

Author: Ahmed Bello Sardauna ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08169047840

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 64.03 kb

File Type: txt

Views: 621+

Download: 198+

Last download: 2 hours ago

DOWNLOAD
Description/Story:  AHMED B. SARDAUNA
.
FACEBOOK ACCOUNT👇👇
(Ahmed bello sardauna)
WHATSAPP NUMBER👇👇
(08169047840)
.
NOTE: bana tura littafai a private, amma inada group na whatsapp da facebbok.

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen lAn dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
LABARIN ALJANI YA TAKA WUTAabari.


*
Page *1*


_Bismillahir rahamanir raheem._

Da sunan Allah mai rahma mai jinkai. Alhamdulillah dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Wanda ya bani dama da ikon fara rubuta wannan takaitaccen labari mai ɗauke da rikicin soyayya. Labarin MARUBUCI labari ne da zai wayar wa masoya kan su domin gane yadda daraja da kuma kimar soyayyar gaskiya take. Da kuma yadda ake sadaukarwa kan soyayya da sallama rayuwa ga biyan bukatar masoyi. Jigon wannan labari shine soyayya darajarta da kimar ta. Da fatan masoya zasu biyo ni sannu a hankali domin kwasar romon dake cikinsa.


Bazan iya kirga ku ba masoyana ko kuma groups da litattafai na suke zuwa, sai dai ina so ku sani sakonnin ku na zuwa gare ni bisa kari kuma ina godiya da kulawa. Sannan ina so ku sani ina kaunar ku ina kuma jin daɗin shawarwarinku gare ni Allah ya bar zumunci 🤝
__________
_______
____
__
_ farkon labari...



Zaune yake bisa wani dutse wanda da yayi sama kaɗan da kasa, karkashin wata bishiya mai yawan ni'ima da yalwar sanyi ga wata ni'mtacciyar iska dake kaɗawa. Wannan bishiyar a bayan gari take gurin da Muhsin ya mayar tamkar fadar sa ko wata majalisa ta zama musamman idan yana so ya jarraba fasaharsa. Yau ma kamar kowane lokaci yana jingine da jikin bishiyar hannun sa rike da farin littafi da alkalamin rubutu. Ya ɗora alkalamin bisa littafin kamar mai yin rubutun sai dai har yanzu ya kasa rubuta koda harafin 'A' a jikin littafin.

Tun yana yi da sauki har ya dawo yi da dukkanin karfin zuciyarshi amma abokiyar gwagwarmaya kwakwalwa ta ki ta bashi haɗin kai kamar kowane lokaci dai. Idanunsa suka cicciko da kwalla jikinsa ya hau kyarma yayi watsi da littafi har ma da alkalamin, tsananin takaici ya kama shi. Ya shiga kuka da takaicin kasancewarsa dakiki mai kunshe da babban buri.

Allah sarki Muhsin. Ni da nake zaune a gefe ina kallon inda ke faruwa na share kwalla, tsantsan tausayinsa ya kara kama ni. Duk da cewa nasan baya gani na amma hakan baya sanyayyar min guiwa ko dakile zuciyata ga jin tausayinsa da kuma kara nutsawa a tafkin kaunar sa.

Kuka yake sosai yana buga kansa a jikin bishiyar nan kamar yadda ya saba yi idan irin hakan ta kama shi. Da sauri na mike domin dakatar da shi tun bai kai ga illata min kansa ba. Cikin dabaru da hikima da kuma kwarewa irin tamu ta sarrafa bil'adama na dakatar da shi ga abinda yake yi. Sai dai har yanzu bai daina kukan ba. Yana yi ina yi an rasa wanda zai rarrashi wani. Ban san ya zan yi ba, damuwar Muhsin na tada hankalina kamar yadda zubar hawayensa ke haifar da fitar nawa hawayen. Tsananin so da tausayinsa na neman hallaka ni, rashin sanin hanyar da zan bi dan in taimake shi na neman illata zuciyata. Yau kimanin shekaru ashirin kenan ina bautar da rayuwa ta ga soyayyarshi. Duk da cewa bai ma san ina yi ba amma na taimaki rayuwarsa ta hanyoyi masu yawa... Muna haɗuwa da Muhsin har ma na labarta masa irin kaunar da nake masa amma cikin mafarkin shi ni kuma zahiri na. Har yau bai ji a ransa cewa da gaske ni ɗin wata ce ta gaskiya ba, ya ɗauki mafarkin da yake yi dani tamkar irin sauran mafarke-mafaken da ake yi a cikin bacci.



*Wane ne Muhsin?*

Tsayayen saurayi kyakkyawa na gaban kwatance ɗan kimanin shekaru ashirin da biyar da haihuwa. Fari sal mai matsakaicin tsayi da faɗi.

Muhsin Al'hussain shine cikakken sunan sa. Ɗa na biyu a gidan sarautar garin gabas wanda yake cikin nahiyar birnin lumai. Garin gabas babban birni ne wanda ya kunshi mutane daban-daban maban-bantan akidu da addinai. Mahaifin Muhsin mai martaba sarki Al'hussain shi ne yake rike da mulkin kasar a yanzu, wanda shima gadon sarautar yayi a gurin yayansa yayan nasa kuma ya gada a gurin iyayensa haka tsarin yake. Mai martaba sarki Al'hussain shi da iyalansa duka ma biya addinin musulunci ne. Yana da mata biyu da ya'ya biyar inda Muhsin ya kasance na biyu a cikin su. Yayansa ɗaya Kabir sai Fatima karamar kanwar su. Su ne yan' ɗaki ɗaya, wato ya'yan uwar gida gimbiya Suhaima. Sai ya'yan ɗakin gimbiya Amrah su biyu Suhaila da Aliyu.

Duk cikin waɗannan ya'yan Muhsin ne kaɗai ya fito daban. Dukkanin su suna da ilmi da kwazon karatu yana shiga kansu sosai, amma shi kam sam kansa baya ɗaukar karatu sau tari a magana ma in yaje wani matakin makalewa yake yi. A wasu lokutan yana magana yana kuka abin tausayi. Akwai kwazon maida hankali da tsare litattafai da ido yana karantawa amma duk abinda ya karanto sai dai ya tsaya iya bakinsa baya kaiwa ga kwakwalwarsa balle ta ajiye masa shi duk kuwa da irin ko'karin da yake na ganin ya saka karatun a kansa.

Hakan ba karamin raini ya ja mishi ga sauran kannensa ba kai har ma da waɗansu ya'yan sarakan idan aka haɗu wawa dolo mai ɗanyen kai babu abinda basa ce masa. Matsalarsa ta gawurta tun iyayen na ɗauka laifinsa ne har suka dawo suka saduda suka fauwala al'amuransu ga Allah.

Sai kuma wani iko na Ubangiji da ya yi a kansa, ya kawo tsananin so da burin zamowa MARUBUCI ya saka mishi a rai, a duniya babu abinda yake burge Muhsin kamar rubuta kirkirarren labari. Kamar yadda babu abinda yafi so kamar ya ga kansa a matsayin MARUBUCI. Lokuta da yawa yakan ji kamar yana tsara labari a zuciyarsa amma idan yaje ya zauna da burin son rubutawa sai kwakwalwarsa ta hargitse ta dagula masa komai. Ya dawo kamar wani zautacce baya kula kowa ba kuma ya shiga kowace irin sabga sai dai ka ganshi yayi lamo yana nazari a kullum Muhsin cikin tunani yake a koda yaushe hawayensa zuba suke yi. Ya rasa abinda yasa ya kasance haka.

* * * * * *
Ni kuwa ikon Allah ne ya haɗa ni da Muhsin, da gani ɗaya naji na kamu da tsananin tausayinsa tun yana yaro ɗan kimanin shekaru biyar a duniya. Tun a lokacin na fara shiga rayuwarsa ina son taimakon sa amma matsalar sa ta sha gaban tunani da sani na.

Alakata da Muhsin tayi girman da duk wani ɗan'uwana na kusa da na nesa yasan ina tare da shi kuma ina matukar kaunarsa. Babu yadda iyayena basu yi ba dan ganin sun raba tsakani na da Muhsin amma abin ya gagara, tun suna jin haushi na har suka dawo suka hakura.

* * * * *

Ni jinsin Alajan ce wadda ta fito daga babban gida mai daraja a can tamu nahiyar. Ni kaɗai Allah ya azurta iyayena da haihuwa kuma mahaifina babban Malamin addinin musulunci ne a can, shi yasa dukkan mu muka zamo mabiya addinin.

Babu irin rokon da ban yiwa mahaifiyata da mahaifina ba kan su taimaka in sunada wani taimako ko masaniya akan lalurar da Muhsin ke ɗauke da ita su taimaka su gaya min amma sun ki. Duk kuwa da cewa inada yakini cewa babana Malam ba zai rasa masaniya akan maganin warakar wannan cutar ba.

Wannan kenan.


Cigaban labari...

* * * * *

Dogon numfashi na koma ja a karo na barkatai, ina karewa masoyina Muhsin da bacci ya sace kallo. Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, yana fidda numfashi slowly. Na rufe dara-daran idona na koma buɗe su a kansa. Ga namiji har namiji amma wananan lalurar zata nakasa shi. Wani irin shaukin son sa ne ka kara ninkuwa a raina yana daɗa mamaye duk wata kafa ta sadar da tunanina. Nan da nan na yanke shawarar tafiya na mika ajiyayyun sakonnin soyayyata ta kafar sadarwar da na shirya mana ta haɗuwa da masoyina ba tareda ya san ko ni wacce ba a cikin mafarki. Dama haka na saba a duk lokacin da shaukin kaunarsa ya motsa mini, nakan zama tamkar inuwa na ratsa jikinsa harma da tunaninsa sai ya ganni kamar yana mafarki ta nan muka saba da Muhsin sosai kuma ta nan ne nake sanar mishi irin son da nake masa. Ta wannan hanyar ne nake farantawa Muhsin ina ɗebe masa kewar rayuwar kaɗaicin da yake. Domin daga ni sai mahaifiyarsa gimbiya Suhaima mu kaɗai ne muke shiga rayuwarsa kuma muke ko'karin faranta masa domin mahaifinsa baya da lokaci koda yaushe yana cikin fada yana fama da talakawa da matsalolinsu.

Na lumshe idona cike da shauki sannan na yunkura da nufin aiwatar da nufina, na shiga jikin masoyina domin sada zumuncin kauna. Kamar daga sama naji an yi gaggawar riko kafaɗata ta baya ana faɗin

"dakata Na'eema"










*Nasmat* ✍
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MARUBUCI...*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀


*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________

©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________





📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com



*Page 2*




*Alhamdulillah ina godiya ga Allah (s.w.a) kuma ina godiya gareku bisa yadda kuka kar6i wannan labarin kuma kuke kara karfafa min guiwa a kan sa. Na gode! Na gode! Masoyana Allah ya bar min ku a duk inda kuke. One love 🤝*







Wannan dakatarwar da aka yi min ba karamin 6ata mini rai tayi ba, na juyo a fusace dan ganin wane ne wannan da yayi min irin wannan katsalandan a cikin rayuwata. "Ummy" na faɗa cike da mamakin ganin mahaifiyata a gabana, wadda ban ta6a tsammanin ta a yanzu kuma a nan ba. Ta zuba min fararen idanunta fuskarta cike da damuwa. Wannan ne ya kara sanyayar mini da ga66an jikina.

"Ummy lafiya?" na tambaye ta cikin karfin hali da dakewa. "wai ke wacce irin kafaffiyar yarinya ce Na'eema?, kin kuwa san irin wahalar neman ki da aka sha yau? Duk faɗin nahiyar nan babu inda ba'a watsa Barade neman ki ba, ashe wai kina nan gun wannan bil'adaman kina gadin sa." maganganun Ummy basu bani mamaki sosai ba domin na saba da jin ire-iren su har ma da waɗanda suka fisu daga gareta a kan Muhsin. Abu ɗaya ne ya tsaya min a maganarta inda take cewa 'babu inda ba' a watsa Barade nema na ba'. To yau kuma me na yiwa Sarki da har za'a baza Baradensa nema na?.

Ummy ta kalle ni rai a 6ace "to tunanin me kike kuma? Maza ki zo mu tafi tsawon awanni Sarki da jama'arsa suna zaman jiran ki." tana kaiwa nan ta kama hannuna daga ni har ita muka 6ata 6at!.

Al'amura sun cakuɗe a matashiyar kwakwalwata, ban gama warware sarkakiyar farko ba Ummy ta koma saka ni a wata. To me kuma zai sa sarki da jama'arsa jira na?. Ina cikin wannan tunanin ne nida Ummy muka bayyana a babban ɗakin baki na mahaifina Malam. Inda naci karo da wani sabon abin mamaki wanda ya haɗu da maganganun Ummy ya cure min a kwakwalwa. Duk da cewa waɗanda da naci karo da su ba bakin fuska bane a gurina, amma ina mamakin taruwar su a gidanmu kuma har ake nema na.

Babu yanda na iya haka na adana tambayoyi da mamakina, na zube kasa na kwashi gaisuwa ga sarkin Aljanu na nahiyar baki ɗaya sarki Shadad. Da uwar gidansa Ummu Haiman da kuma shi kansa babban ɗan nasu Haiman. Suka amsa mini gaisuwar cikin sakin fuska da kauna kamar dai yadda suka saba musamman Haiman wanda shi kallon so ne karara yake jifa ta da shi. Ni kuwa na basar nayi kamar ban san abinda yake ba. Sauran kuyangin gimbiya Ummu Haiman da fadawa yan rakiyar sarki suka zube kasa suna gaishe da ni. Na amsa cikin nuna kulawa sannan na mike na matsa can kusa da kujerar da mahaifina yake kai na zauna dab da kafafunshi ina mai sunkui da kaina alamar girmamawa gareshi.

Baba Malam yayi gyaran murya ya 6oye 6acin ransa na nema na da aka yita yi tsawon lokaci, saboda yasan na wuce ayi mini faɗa a gaban sarki. Duk kuwa wanda yayi to zai ga...


Read / Download MARUBUCI

DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

DOWNLOAD
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album