Join Our WhatsApp Group

MATSALARMU A YAU Book 1 Complete Hausa Novel Document by MATSALARMU A YAU Book 1


MATSALARMU A YAU Book 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 28783



MATSALARMU A YAU Book 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 01, Dec 2023

Author: Binta Umar Abbale ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION

Author Phone : *07084653262* *08089965176* *22790899076*

Book License : Paid

Category: Love Novels

File Size: 161.62 kb

File Type: txt

Views: 528+

Download: 195+

Last download: 2 days ago

Description/Story: [9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

*FreePege1&2*
Cikin nutsuwa take tura keken guragun da yake zaune. a hankali ta fito dashi kofar gida ta tsaya tana kallonsa da idanuwanta da suke cika da ruwan hawaye. Cikin kulawa da tausayawa yake kallonta ya sauke ajiyar zuciya cike da jarumta yace."Surayya nace ki daina kuka duk da yanzu yamma ce idan na fita Allah ba zai hana ni abinda zan siya miki littatafan makaranta ba saboda naga kin damu yasa na yanke shawarar fita ko Allah zai sa a dace."

Hannu tasa ta share hawayen idonta tace."Baba Tausayin ka nake ji wallahi baka da koshin lafiya kawai ka koma gida ka zauna na hakura."

Girgiza kansa yayi da murmushi a fuskarsa yace."Surayya ai tunda na fito ba zan koma ba sai na fita dama can ala dole nake zama a gida tunda yanzu naji kwarin jikina sai na fita watakila Allah yasa a dace."

A sanyaye tace."To shikkenan Baba bari na tura ka bakin titin." Girgiza kansa yayi yace."Aa kin san bana so kina bina bakin titin nan wasu mutanan basu da uziri."

A shagwabe tace."Na sani Baba yau d'aya ka bari na tura ka." Murmushi yayi yana girgiza kansa yanzu duk wanda zai ganshi da yarinyar tana turashi sai ya dauka bara sukeyi yasan bai wuce a bashi sadaka ba amma tunda Allah yasa yana iya sarrafa hannayensa to babu abinda zai gagareshi a yanda Allah ya halliceshi a haka yake so ya cigaba da bashi kwarin gwiwar sauke nauyin iyalinsa zuciyarsa a tsaye take sam bashi da kasala da nuna cewa shi din nakasashshe ne dole jama'a su taimaka masa.

Idan yaga 'yan uwansa nakasassu suna yawo kan titi na suna bara da maula ransa yana baci mutuka shiyasa shi ya d'aura d'amarar neman halalinsa tunda Allah ya bashi rai da lafiya to nakasarsa ba zata hanashi aiwatar da komai na rayuwarsa ba.

Cikin nutsuwa take turashi suna hira sai murmushi yake yana amsa mata. Wani matashin saurayi ya tare musu hanya.

Surayya ta 'bata rai ta kallashi da fadin." Bawan Allah menene haka zaka tare mana hanya."

Shahid murmushi yayi yasa hannu ya sosa sumar kanshi ya d'an risinar da kai da fadin."Baba barka da yamma." Malam Habu ya amsa kadaran kadahan sam irin wad'annan samarin basa burgeshi yafi san nagartattun mutane su nemi auran 'yarshi.

Shahid ya jefe ta da kallon kauna yace."Surayya ya kwana biyu."? Gabanta ne ya fadi da sauri taja tsaki ta yi saurin tura keken suka barshi a tsaye a gurin. bayansu yabi da kallo yana murmushi shi dai Allah ya sanya masa kaunar yarinyar a cikin ransa.


Suna kokarin karya kwana ta hango maigadin gidan yana gyara masa kujerar da ya saba zama a irin wannan lokacin. kafin ta dauke idonta ya fito daga gidan yana sanye da farar t-shirt tas had'e da jins blue black idanuwansa sakaye da farin gilashi fuskarsa jiya i yau kamar ko da yaushe dai zama yayi kan kafin ya kar'bi dictionary din dake hannun Haruna Maigadi dake tsaye a kusa dashi. Hannu ya daga masa alamun ya bashi guri. da sauri ya shige cikin gidan tare da sakayo karamar kofar.

Yana kokarin bude littafin ya hange su Tana tura shi a keken yana gargada tare da cijewa da alama yafi karfinta kokari kawai take cikin nutsuwa yake kallonsu yana jin wani irin yanayi a tare dashi.......Ita kuwa wani irin sanyi jikinta yayi gabanta in banda fad'uwa babu abinda yake a duk lokacin da za tayi tozali dashi takan rasa kuzari a tare da ita.

Malam Habu tun kafin su 'karasa inda yake ya saki fuskarsa sai fara'a yake. A nutse ya mike da littafin a hannunsa ba tare da ya kalleta ba ya miqa mata littafin hannunta na rawa ta kar'ba shi kuma ya ri'ke keken ya cigaba da tura shi Malam Habu na 'yar dariya yace." Nuraddin anya ban katse maka uziri ba. Murmushi yayi a nutse yace."Babu damuwa Malam ina ka nufa ne da wannan yammacin."?

Malam Habu yayi jim kafin Yace."Zanje bakin titi ne kwana biyu na dan kwanta a gida ban fita ba." Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Me zai hana ka koma gida tunda daf ake da a kira sallar magriba Idan Allah ya kaimu gobe da safe sai ka fita.

Shuru yayi yana nazarin maganar da zai fada masa yanzu idan ya koma gida bai sai abinda zai bawa iyalinsa suci da daddare ba da safe da rana matarsa Habiba tayi fafutuka to yana da kyau yanzu shi kuma ya tabuka nasa kokarin.

Ganin yayi shuru yasa ya gane abinda yake da akwai. a sace ya kalli gefen da take tana tafiya salau-salau tamkar ka bushe ta saboda tsabar rama tausayinsu ya 'kara ratsa shi hakika yunwa da tsananin takura tana damunsu.

Yace."Malam ina neman alfarma a gurinka." Malam Habu yace."Wace irin alfarma kake nema Nura." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Ka koma gida ka kwanta ka huta gobe idan Allah ya kaimu sai ka fita."

Malam Habu yace."Nuraddin nayi maka Alfarma." Murmushi yayi na jin dadi yace."Nagode Malam." Da sauri ya juyar da akalar keken domin komawa gida............Salo-salo take bin bayansu zanin jikinta sai hard'e ta yake gefe guda kuma k'amshin turarensa dake fita daga jikin dictionary dinsa dake hannunta ya bala'in kashe mata jiki tana tafiya tana sansana littafin tana lumshe ido tamkar bugaggiya haka ta zama aikuwa ba tare da tayi aune ba taji ta facal cikin kwata tayi tsumbul ta kamo kifi ka dictionary din sai yawo yake a saman kwatar........Cikin wani irin yanayi ta kira sunan mahaifinta nata hawaye kuwa tuni suka 'kwace mata.






_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
[9/25, 3:47 PM] Jamila Yushau: *MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_

*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________

*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_

FreePege
*3&4*
Kusan a tare suka juyo ganinta tsulum a cikin kwata yasa shi ya mutse fuskarsa kawai sai ya tsaya yana jifanta da wani irin kallo mai kama da harara idonsa akan dictionary dinsa dake jike da ruwan kwata!

Sunkuyar da kanta tayi hawaye na sauka a samam fuskarta. Malam Habu cikin damuwa yace."Surayya garin ya akayi kika fada kwata da girmanki da komai."

Murya na rawa tace."Wallahi Baba ban san lokacin ba." Girgiza kansa kawai yayi yace."Ai sai kiyi dubura ki fito gashinan kin jefa masa littafi cikin ruwan kwata.''

Cikin damuwa da alhini ta dauko littafin wai zata fito dashi. ya girgiza kai yana yamutsa fuskarsa yace."Me kike tsammanin zanyi dashi."?

Kallonsa tayi yace."Kawai ki fito ki barshi tunda kinyi min asara dole na nemi wani."

A sanyaye ta sunkuyar da kanta ta fara kokarin fitowa santsin ruwan kwatar yana mayar da ita gabad'aya k'yamar kanta da kanta take ballantana kuma wani.

Ganin yara sun fara taruwa a gurin yasa ya matsa inda tare da mika mata hannunsa. kallonsa tayi gabanta sai faduwa yake. babu walwala a tare dashi yace ."Rike hannuna ki fito ."

A sanyaye tasa hannunta cikin nashi kawai taji fittt! ya janyo ta waje dama ba wani kwari ne da ita ba da kyar ta iya tsayuwa da kafafunta sabida razana! duk ta 'bata masa jikinsa.....Hararar gefen ido yayi mata ba tare da yace mata komai ba ya bar gurin.

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka tabi bayansu jikinta duk ya mutu ga yara sai kallonta sukeyi.

Koda tazo shiga gidan bata yarda sun hada ido ba simi-simi ta shige su tana takure jikinta.

A nutse yace."Malam ka zaka iya shiga gidan ko.''? Malam Habu yace."Eh zan iya shiga Nura nagode sosai Allah yayi maka albarka ya baka mace tagari."

Ya amsa da "Ameen ya Allah Malam ni bari naje gida anjima zan dawo insha Allah." Malam Habu yace."To shikkenan Nura a gaishe da mutan gidan." Yana kokarin barin gurin ya amsa da "Insha Allahu za'a fada musu."


Kai tsaye ruwa ta jawo a rijiya ta shiga bandaki ta wanke jikinta......Tun kafin ta fito daga bandakin take jin muryar mahaifiyarta tana fad'a. "Sai kace wata yarinya karama saboda shashanci zata jefa masa littafi a cikin kwata wallahi malam ban san abinda yake damun yarinyar nan ba.


Yace." Nima banji dadi ba na lura shima Yaron ransa ya 'baci kawai ya 'boye ne." Innah Habi ta cigaba da fad'a! wanda ya sanya ta fargabar fitowa daga bandakin tasan halin mahaifiyarta mafadaciyar macace. aikuwa koda ta gama ra'be-ra'ben ta ta fito rufe ta tayi da fad'a wanda ya sanyata kuka tana bata hakuri da fadin."Tsautsayi ne Innah Habi gabadaya taqi kar'bar uzurinta sosai tayi mata fad'a ta shiga daki taci kukanta ta koshi.


To shima koda ya shiga gidansu kai tsaye gurinsa ya nufa a gurguje ya tsaftace jikinsa ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin jallabiya ruwan madara turare yasa a jikinsa ya dauki carbi ya nufi massalaci sai da ya gabatar da isha'i sannan ya shigo gidan.


Nan ya samu 'yan uwanshi dasu da 'ya'yansu sun cika falon sai hayaniya sukeyi suna shewa ga kayan abinci nan baja-baja..........Babu walwala a tare dashi ya tsaya a bakin kofar falon yana kallonsu.

Fadila da Yusura da Shafa sukayi saurin sunkuyar da kansu suna gaisheshi a dakile ya amsa yana bin falon da kallo a rayuwarsa ya tsani rashin nutsuwa da kamun kai wai saboda lalacewar zamani iyaye ne da 'ya'yansu suka zauna suna shashanci a guri daya.


Aunty Jamila ta kalleshi da fadin." To sarkin Masifa da Miskilanci ka shigo." 'Bata rai yayi yace."Yanzu Aunty Jamila wannan wace irin Dabi'a ce kun zauna tare da yara sai shirme kuke yi."

Aunty Nafisa ta watsa masa harara da fadin."To menene a ciki dukkaninsu mata ne idan ba mu zauna dasu ba dawa zamu zauna."

Hannu ya d'aga mata babu sukuni yace."Ba dake nake magana ba sabida haka kada ki kara saka min baki a maganata." Dama can a tsakaninsu basa jituwa yafi shiri da Aunty Jamila.

Tsaki taja ta dauke kanta tasan halinsa baya daukar raini duk da tana gaba dashi yanzu sai yayi mata rashin mutunci kuma ya kwana lafiya shiyasa tayi shuru da bakinta sabida tana jin tsoron ta sake magana ya tsinkata a gaban 'ya'yanta."


Guri ya samu ya zauna yana 'bata rai Fadila ta kalleshi da fadin."Uncle a kawo maka abinci.''?


Girgiza kansa yayi da fadin."Hau sama ki kira min Hajia." Da sauri tace.''Uncle." Ya kalli Aunty Jamila da fadin." Ku dubi Time fa takwas da rabi na dare sai yaushe zaku tafi gidajenku."


Saboda tasan halinsa a tsorace ta fadi maganar." Kwana za muyi sai gobe da yamma."


Wani irin kallo yake mata kafin yace."Me akeyi biki ko Suna da zaku kwana."?

Shuru tayi masa yace."Saboda kawai kun samu labarin Abbah baya gari shikkenan sai ku baro gidajen mazajenku daku da 'ya'yanku shin me hakan yake nufi."


Tace."Kaga Nura don Allah ka kyale mu wallahi ni bana san takura da matsala kai ba kai kake auranmu ba amma kazo kana tsara mana yanda za muyi."


Ido ya zuba mata yace."Saboda kawai za'a gyara miki kuskuranki shine kike wannan maganar." Tana kokarin magana Hajia ta karaso gurin tana kallonsa tace."Babangida haka take kiransa saboda sunan kakanta ne dashi. Ya amsa da Na'am Hajia ya gida."? Tace."Lafiya lau Fadila tace kana nema sai nace to Allah yasa kudi zan samu."

Gyara fuska yayi yana kallonta ta zauna a kusa dashi sai washe baki take tana fadin." Hausawa suka ce idan kaji kira ba banza ba Allah yasa samuwa ce."

Girgiza kansa kawai yake yana mamakin halin saon kudi irin na mahaifiyarsa macace mai masifar san kudi da rashin alkairi bata kaunar talaka ya ra'bi inda take kullum tafi bukatar ta zauna ita da 'ya'yanta gabad'aya 'kawayenta masu kudi ne bata yarda tayi mu'amula da talaka ba. Akan wannan halin nata suke rigima da mijinta domin shi Alhaji Sabo mutum ne mai saukin hali da taimakawa talaka.


Ajiyar zuciya ya sauke yace." Idan da akwai abinci inaso a zuba a cikin fulas zan fita dashi."

Tace." Ba'ki kayi ne."? Girgiza kansa yayi." Sai ta 'bata fuska da fadin." To wa zaka bawa abinci kuma da wannan daran."

Bai da munafurci ko kadai komai zaiyi kansa tsaye yake yi shiyasa yake rayuwarsa cikin kwanciyar hankali......."Babangida magana fa nake maka kayi shuru kana kallon guri daya.

Yace."Inaso zan kai gidan Malam Habu ne." Wani matsiyacin tsaki taja ta waiwaya tana kallonsu tace."Nafisa kiji wata magana don Allah."

Ta bude baki za tayi magana ya watsa mata muguwar harara! sai tayi shuru da bakinta tana ya'ke!

Aunty Jamila tace."To kai haka kawai zaka kai musu abinci ko ro'kar ka sukayi."?


Ransa a bace yace." Don Allah bana san surutu wannan abin da kuke sam bai dace ba menene abinci abinda kuka fi karfinsa wannan bawan Allahn yana bukatar taimako ko ya roka ko bai roka ba yana da kyau a taimaka masa."

Hajia Sabuwa ganin yanda ya 'bata rai yasa ta kalli Fadila da fadin." Ki tashi kije ki zuba musu abincin Allah ya kyauta."

Fadila ta tashi ta nufi kicin din ranta a 'bace ita kam ta tsani yanda yake nuna kulawarsa a kan mutanan sam bata kaunarsu saboda talaucinsu.


Tana kawo masa abincin bai jira komai ba ya mike ya fita ya basu guri aikuwa suka dasa gulmarsa sai zagin Malam Habu suke shida Iyalinsa Hajia Sabuwa tace."Gurgu dashi sai muguwar bakar zuciya dole ne na tashi a tsaye akan wannan alakar da take tsakaninsu watakila ma asiri yake masa.......Aunty Nafisa ta dinga tunzurata da fadin." Lallai da akwai alamun gaskiya a cikin maganarta.





_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP...


Read / Download MATSALARMU A YAU Book 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album