Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

TSAKANINMU BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by TSAKANINMU BOOK 1


TSAKANINMU BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30573



TSAKANINMU BOOK 1

Reading Time: 2 Hours

Added On: 25, Jul 2024

Author: Nanameera ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 09086030007

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 167.71 kb

File Type: txt

Views: 556+

Download: 330+

Last download: 4 days ago

Description/Story: [1/31, 10:21] Nanameera writer: https://chat.whatsapp.com/BRBJgmCve2uEO7OzFYz8Sj


💖💖TSAKANINMU💖💖




Story and written by:
*Nanameera*



.....Tauraruwar royal star✨


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*Haɗaka palace*
*kungiyar masu posting ce ba marubuta ba*




*Bismillahi rahmani raheem*





🅿️. ONE..




*KANO STATE*




Gama shirya warta kenan ta buɗe ƙofa ta shigo, kallonta ta yi ta ce " haba samha wannan wane irin wulaƙanci ne ace tun ɗazu common wanka da saka kaya amma kinfi awa guda kuma kinsan driver na jiranmu awaje wannan bai kamata ba " wacce aka kira da Samha ta juyo sai a sannan na ƙare mata kallo fara ce tas kuma asalin kyakyawa dan tafi kamada half-case ɗin nan cikin ƙasa da murya na rashin son hayaniya ta ce " meyasa kika fiye ƙorafi Saima?, kina gani fa banda wankan babu abinda nayi amma kinzo kina mana shouting aka " tsayawa Saima ta yi tana kallon zallar rainin hankalin biyunin tata, tsabar baƙinciki yasa tayi waje ba tareda ta ce mata komai ba. Ganin ta fita yasa ta ɗauko veil ɗin abayar jikinta ta yafa, tayi kyau sosai musamman yanda black abayar ta karɓi white skin ɗinta ta ɗauka hand bag sannan ta ɗauki wayarta ƙirar iphone 13pro max tayi waje, tsaye ta samesu ta tsuguna ƙasa ta ce " good morning Dad, good morning Mom " murmushi Wanda aka kira da Daddyn ya yi sannan ya ce " Samha meyasa kuke makara makaranta kuma ke ce kike jawowa " cikeda ladabi ta ce " wallahi Daddy ina iya bakin ƙoƙarina wajen ganin na shirya da wuri kawai saboda ita Saima ta nada gaggawa yasa ake ganin bana saurin " miƙewa ya yi ya ce " adinga ƙoƙari ana tafi da wuri kinji, tashi ku tafi " sai a sannan ta miƙe ta ce " Mom sai mun dawo" murmushi Mom ɗin ta yi ta ce " Allah ya tsare my Twins please ku kiyaye mutuncinku kunji " toh suka ce duka sanann sukai waje don tafiya makarantar.........






*Su wanene Saima da Samha?*


Alhaji Ahmad wanda ya kasance shine mahaifinsu sai kuma mahaifiyarsu wato Doctor Maryam ta kasance professer kuma likita dan tana da asibiti mai zaman kansa, mijinta Alhaji Ahmad ya kasance ɗan ƙasar Etopia ne wanda kasuwanci ne ya dawo dashi ƙasar Nigeria kuma cikakken ɗan boko ne a gefe guda, sunɗauki shekaru a ƙalla goma da aure kafin Allah yasa su sami ƴaƴansu wato Fatima wacce suke kira da Samha sai kuma Zainab wacce suke cewa Saima kasancewar su kaɗai iyayensu suka mallaka kuma ga tarin dukiya yasa duk abinda suke so arayuwa suke samu sai dai idan ya saɓawa Addinin musulunci, bazasu wuce shekaru sha bakwai ba suna level one a jami'ar bayero inda Samha take karantar pharmacy ita kuma Saima computer science. Kasan cewar sun ban-banta a fanni karatu yasa dasun shiga makaranta suke rabuwa sai kuma antashi kamarsu ɗaya dan irin identical Twins ɗin nanne abu ɗaya ne ya rabasu ita Samha fara ce ita kuma Saima chocolate colour ce wannan shine abinda ya rabasu dan hatta sutura iri ɗaya suke sawa, akwai shaƙuwa sosai Tsakaninsu wani lokacin idan suna abu Mommy takance"
wannan abun naku wata rana baza kuyi ba saboda aure dole sai ya rabaku " dariya suke suce atare " ai Mommy babu wanda zai shiga *TSAKANINMU* sai mutuwa dan ko aure zamuyi to Twins irinmu zamu aura " sai tayi murmushi ta ce " Allah yasa".......


*Wannan kenan*


Suna shiga makarantar bayan driver ya yi parking suka fito atare daidai lokacin motar ƙawar Saima Aleeya ta shigo bayan tafito ta zo ta rungume ƙawar tata cikeda jindaɗin ganin juna kallo kawai Samha ta bisu dashi sannan tayi gaba cikin rashin jindaɗi Aleeya ta ce " wai Saima meyasa Samha batason kula kowa?, bakiga yanda ake munafurcinta ba" kama hannunta Saima tayi suna tafiya sannan ta ce" wallahi bansani ba ni kai wani lokacin *TSAKANINMU* da juna sai kallo ko agida haka take batada yawan magana " ajiyar zuciya Aleeya ta sauke sannan ta ce "ai kuwa kudinga bata shawara ta daina, gashi ko maza bata kulawa kamar ba maceba wasu cewa suke wai ƴar wulaƙanci ce " ɗaga kafaɗa Saima tayi alamar bai dametaba ta ce " tai tayi ni babu ruwana" dariya Aleeya ta yi ta ce " aikuwa kice da ruwa " shiru sukayi saboda ƙofar class ɗinsu da suka zo.....






Sosai take sauri saboda tasan halin lecturer'n su ai kuwa ilai ta zuwa ta tarar ya shiga, da sallama tashiga ajin a ɗan tsoroce cikin kakkausar murya ya ce " keee! Get out " juyowa ta yi ta kalleshi ta ce " sir please sorry" cikin faɗa ya ce " sorry For your self, get out!!! " da sauri ta yi waje saboda ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba. Haka ta dinga zama har aka fito break sannan wata ƙawarta wacce suke mutunci tazo gurinta ta zauna budurwa mai suna Aysha ta ce " Samha meyasa kike makara wai?, duk randa lecturer'n nan zai shigo bakya zuwa da huri kuma kinsan hakan zai jawo miki matsala " kallonta Samha ta yi kamar bazatai magana ba sai kuma ta ce " isn't my fault kawai ya tsaneni ne yasa yake yimin haka amma ai bakowa yake cewa ya fita ba kina gani bayan ya koreni wata tashiga kuma ya barta " cikin damuwa Aysha ta ce " nasani amma kidinga ƙoƙari duk ran lecture sa kina zuwa da wuri " murmushi ta yi har saida beauty point ɗinta suka loma sannan ta ce " thank for caring In sha Allah zan dunga zuwa before yazo " murmushi itama ta yi ta ce " yawwa ko kefa, tashi muje muci abinci " ok ta ce sannan suka tafi.......






Inda tayi parking motarta suka zo da mamaki Samha ta ce " A'a ba abinci zamuje siyaba ?" murmushi Aysha ta yi ta buɗe motarta ta ɗauko wani kwondo sannan ta ce " banason abincin makaranta shiyasa yau na dafo mana agida kizo muje mu zauna muci " murmushi ta yi ta ce " ok amma sannunki har kikai girki kika tawo kuma kika zo da wuri tab" dariya Aysha tayi ta ce " toh aka ce miki kowa irinki ne rago me zama bacci " kwaɓe fuska tayi ta ce " zan mara ne" dariya ta yi sannan sukai gaba dan samun inda zasu ci abincin........






Ɓangaren Saima kuwa zaune suke sunata hira da ƴan click ɗinta saboda ita friendful ce ba kamar Samha ba wani namiji mai suna Khaleepa ya ce " wai Saima ina yayarki Samha kwana biyu batazo wajenki ba?" harara ta galla mai sannan ta ce " wace yayar tawa?, wallahi sai na maka rashin mutunci ka sake cewa Samha yata banda iskanci yaushe ta zama yar tawa?" sheƙewa sukai da dariya gaba ɗayansu sannan Khaleepa ya ce " ai kowa yasan yarki ce saboda saida ta fito daga ciki sannan kika fito kinga kuwa yayarki ce ni wallahi Saima ina sonta kuma zan aureta please kimin campaing " kallonsa ta yi irin kayi haukan nan sannan ta ce " game fili ga mai doki kaje da kanka wajenta ɗan rainin hankali " murmushi ya yi ya ce " wallahi Saima da gaske nake inason Samha dan Allah " tashi tayi tsam ta ce " lallaima!! To bari kaji idan ba Twins ba babu wanda zamu aura saboda bazamu auri waƴanda zasu rabamu ba " zai ƙara magana ta ɗaga mai hannu ta ce " please karka ɓatamin rai zan maka rashin mutunci wallahi " ganin yanda ta fusata yasa ya ce " Allah ya baki haƙuri sarkin zuciya " bata tsaya saurarenshi ba ta ɗau jakarta ta bar wajen rai ɓace......







Sai kusan magrib sannan suka dawo gida, suna shiga ko wacce tayi ɗakinta kasancewar parlour suka haɗa amma bedroom ɗin kowa daban. Bayan sunyi sallah suka zauna karatun al-qur'ani sakamakon sabon da sukai na duk bayan sallar asuba da magrib sai sun karanta al-qur'ani.....






Banda ƙarar cokula babu abinda ke tashi a dinning area ɗin Daddy ne ya kallasu ya ce " when zakuyi exams? " Next month suka faɗa, a nutse ya ce " ok idan kun gama zamuje Etopia saboda granny ɗinku ta matsamin " murmushi sukai sannan suka cigaba da cin abincinsu kusan two minutes sai kuma Saima ta ce " Dad" uhmm"ya amsa cikin shagwaba ta ce " Dad please abarmu mu dinga zuwa makaranta da kanmu ba sai driver ya kaimu ba wallahi kowa da kanshi yake zuwa "
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download TSAKANINMU BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album