Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

MR BELLO Complete Hausa Novel Document by MR BELLO


MR BELLO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 131172



MR BELLO

Reading Time: 10 Hours

Added On: 10, Jun 2024

Author: Janafty ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : intelligent writer's asso

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 712.15 kb

File Type: txt

Views: 1236+

Download: 3584+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story:
: *MR BELLO..!*
_(The young Teacher)_

*NA*

*JANAFTY*💕
*Wattpad:Janafnancy13*


_*Bismillahir Rahamanir Rahim in the Name of ALLAH the most  Beneficient the most mercerfull praise be to Allah lord of the words.....*_

_Assalamu Alaikum my Follow fans,am starting my new Book i ask ALLAH subhanahu wata"ala to guide me throught and make me it sussufull till End Ameen ya Allah_

*Copycats are not allowed to transform this book by any means without the prior written permission of the writer.Immediate action will be taken if caught?*

? _DEDICATED TO: *Bashir Sufyan Sardauna* and *Nazifi yarima*❤️ Sakallahu fil jannah Dudes..For ur all Support,care and Concern..Allah yabar zumunci Ameen_

*....SHIMFIDA....*

        *🅿?1*

*GGUSS KWATAR-KWASHI*

A haraban Babbar Makarantar ta GGUSS, Goverment Girls Unity Secondry School Kwatar-kwashi Dake Tsakanin Dajin kwatar-kwashi Zuwa Gusau, Da Misalin ƙarfe 10:30am na Safe.

Daga Cikin Babban Filin Haraban Makarantan Na Hangi ɗalibai Birjit ba Adadi mata ne Zallah Ta Ko"ina Suna Yawo Wasu Suna Tsaye da Tarin Akwatunsu da Jakunkunansu Wasu kuma Suna ta Tururuwan Shiga Doguwar Mota Fara mai Ɗauke da Tambarin GGUSS KWATAR-KWASHI, gefe ɗaya kuma Kowaccensu Tana Sanye da Uniform ne Ajikinta wasu Nasu Wando light green ne Both Riga da Wando da Ɗan kwali sai Farin Hijabi A yayinda Wasu kuma ke Sanye da Dark green d'in Wando sai Both Farin Riga da Da'n kwali da Hijabi.

A yadda Haraban Makarantan ta Rikice da Hayaniya da Murna da Iface ifacen Ɗalibai zaka Fahimci Hutu ne Ɗaliban Suka Samu Tun ma Ba Daga yadda Wasu Iyayen Ɗaliban keta Zuwa Ɗaukan yaransu Wanda basu yi Register da Motar Makaranta ba, Ayayinda Wasu ke Ta Fitowa Bakin Get d'in Mkrantar ga masu Mashi nan suna ta Ɗaukansa Zuwa inda zasu Hau Mota Zuwa Gida.

Daga chan ɓangaren Na Hangi Wasu 'Yan mata su Uku Tsaye A bakin Wata Bishiyar Dalbejiya Dukkansu Gabansu Akwai Tarin jakunkuna, da Sauran Tarkacensu masu yawa, sakamakon Wannan Hutun Third term ne ƙarshen Zangon karatunsu na Jss 3 sai Shiga SS1 Kenan, Suna Sanye da Uniform ɗinsu na Junior, light green both Riga da Wando da Ɗankwali sai Hijabi Fari, Dukkansu Ukun Tsawonsu Ɗaya Sai dai kuma Biyu Daga Ciki Farare ne Tas, Sai Ta Ukun Wacce ke Tsakiyansu Ɓaka ce Sulub ammh Bak'inta bamai Duhu bane mai haske ne, Wanda Ke Shining, Doguwa ce Mai K'arancin Girman Jiki, Fuskarta tana da Faɗi Ammh ba Sosai ba, Tana da Manyan Idanuwa Masu Ɗauke da Gashin Ido Zarara sai Ƙaramin bakinta Wanda Yake Baƙi baki, A shekaru Dukkansu bazasu gaza Shekaru goma Sha Shidda ba Daga Kallon Farko Zaka Fahimci Zallar Ƙuruciyarsu A lokacin.

Daga bayansu sukaji Ance " *ANEESA...*" atare Suka Waiga dukkansu suna Kallon Ɗaya Daga Cikin Senoirs ɗinsu Jidda Madaki Waɗanda Suke Kan Zana Jarabawarsu ta Fita Ma'ana WAEC, Saboda Haka Su Suna Makaranta basu Azuwa Hutu sai Sun kammallah Neco wanda kuma bazai yi ba Sai ya Tattara ya koma gida.

Itama ɗin Sanye Take da Uniform ɗinsu na Senior, Dark green da Farar riga da Hijabi, Kyakkyawar Gaske ce Gata Fara gata Doguwa mai Ɗauke Da Daran Daran Idanuwa masu Haske Cikin Siririyar Muryanta tace "Aneesa Plz D'an zo na ganki..." Ta faɗa Cikin Yanga Wanda ya Zame mata Halitta.

Jin Abunda tace yasa Aneesa Ta ƙara Haɗe Ran Kamar Wacce Aka Aikoma da Saƙon Mutuwa Saɓanin Sauran ƙawayenta da Fuskarsu ke Washe na Farin cikin Zasu koma gida yau, Cikin Sanyi Jiki da Takun Ɓacin Rai Aneesa Ta Nufi Jidda tana Faɗin " *S. JIBIYA, B. KAITA* Ku jirani bari na Dawo.." Jin Haka yasa S. Jibiya tace "Ok *A. BUKAR BULAMA*..." Ta faɗa Tana bin Aneesan Da Kallo kafin Ta Maida Kallonta kan B. Kaita Suka haɗa ido Suna Ƙunshe Dariya.

Aneesa kamar bazata Taka ƙasa ba Haka ta Rinƙa jan ƙafa Zuwa Wajen Jidda Dake Tsaye tana Jiranta Tana ƙarisowa ta Riƙo Duka Hannayeta Cikin Salon Muryanta tace "Aneesa Don Allah karki manta da Alƙawarin mu Kinji.." Ta faɗa Tana Sakar mata Fararen Idanuwanta.

Gyara Tsayuwa Aneesa Tayi Tana Jifan Jiddan Da Wani Banza Kallo A fakaice, kafin tace "Wani Alƙawari kenan...?" Ta faɗa Da Sigar Rainin Wayau Lokaci Ɗaya Itama tana Sakar mata Manyan baƙaƙen Idanuwanta masu Ɗauke da Zara zaran Gashinta baƙaƙe masu ƙara Fito da Salon Kamaninta da *KANURI*, Jidda Ta Saki Ajiyar Zuciya kafin Ta ƙara Riƙe Hannun Aneesa Tana bin Haraban Mkrantan da Kallo Yadda Taga Kowa na Haraman Tafiya sai D'ai d'ai Irinsu ne Suke Hidimar gabansu.

Cikin ƙara Kwantar da Murya Tana faɗin "Haba My Anee, har kin manta da mganarmu na Kiyi ƙoƙarin Saka yayanki Ya Soni koda bai kai Kwatankwacin Irin Son Da Nike mai ba, plz Anee Ki Taimake ni Don Allah Wlh bazan iya Rayuwa ba Matuƙar babu *MR BELLO JIƘAMSHI*...." Ta faɗa idanuwanta Sun ciko da Ƙwallah Suna Ƙoƙarin Zubowa.

Cikin Wani Baƙin ciki da Takaichi, Aneesa ke Bin Jidda da Kallo kafin Tace "Oh..! Na Manta ammh Tunda kin Tuna min zanyi k'ok'ari sosai Anty Jidda.." Ta faɗa tana Zare Hannunta Cikin na Jidda Wace ke Share Ƙaramar Kwallar data Ziraro mata, Murmushi ta sakarma Aneesa kafin tace "Yauwa ko kefa Anee, Ammh zaki Dawo ki Ɗora SS1 Ɗinki Anan ko Aneesa..?"

Ɓata Rai Aneesa Tayi kafin tace "A"a bazan Dawo ba Nifa Na gama Wannan karatun Har Abada Tunda bana Shiga Aljanna bane.." Ta faɗa Cikin Nuna yadda Ta Tsani Karatun Gaba ɗaya, Dariya Jidda Tasaki Cikin Aji da Wayewa Tace "Oh Anee Wai ke bazaki Chanza ba Shiyasa bakwa Shiiri da Mr Bello sam, Kuna gida Ɗaya Ammh Ra"ayinku ya bambanta Shida baya son Zama da Wanda baya son Karatu.." Tura baki Aneesa Tayi kafin Tace "Aiko da Muke gida Ɗaya ba Uwarmu Ɗaya ba Kuma ba Ubanmu Ɗaya ba, Ba Abunda Na Haɗa Dashi Hanyar jirgi Daban na Mota Daban.." Dariya Jidda Ta ƙara Sakawa Tana kallon Aneesa Wacce ke Kallonta Tana ƙara Haɗe Rai Fuskar nan na ƙyalli baki da kuma Uban man Vaseline d'in Da Aneesa ta Shafama Fuskarta.

Haushin Dariyan Jidda yasa ta Juya Zata Tafi Da Hanzari Ta Riƙo Hannunta tana 'yar Dariya tace "Sorry my Anee, na daina Dariyan Kinji ko? Na yarda baku Haɗa komai ba Ammh dai gidanku Ɗaya, zaki min Abunda na Sakaki ko..?" Aneesa Data Waigo Tana Ƙara Tamke Fuska tace "Nifa bana Shiga Harkanshi Sai dai nama Anty Rahila mgana Tayi mishi Tunda Ita Naga Suna Shiri Sosai.."

Da Sauri Jidda Tace "Yauwa Ki Gaya mata Kinji ko, Ga Nombar Wayata In kin koma gida ki kirani ko da wayar Anty Rahilan ne Kinji ko my Anee.." Ta faɗa Da Sigar Lallashi Lokaci Ɗaya Tana Saka mata Takardan Data Rubuta mata Lambarta Karɓa Aneesa Tayi Cikin Ƙosawa Tace "Naji Anty Jidda bari na Tafi Su B. Kaita na Jirana.." Fuskarta Jidda Ta Shafa tana Faɗin "Ok Aneesa nagode sai naji kiranki.." Da Sauri Aneesa Ta Ƙwace Hannunta ta Wuce Tana Sakin Tsaki Acikin Ranta Take Faɗin "Ai sai kiyi Tayi Iska na Wahalar da mai kayan kara Uban Waye zai kiraki kan Wannan Mugun.." Ta faɗa Harda Tsirtar da yawu kafin tace "Allah ya Tsareni da Haɗa Shirgina Da Mara Imani."

Ta faɗa Tana Ƙarisowa Wajen Dasu S. Jibiya Suke Suna Jiranta Tun kafin Ta Ƙariso ta Dunƙule Takardan Da Jidda Ta bata ta Wurgar Da Ita gefe Tana Waigon Jidda Wacce ta Juya ta Nufi Hostels ɗinsu na DAURAMA part 2, Da kallon Mamaki B. Kaita tace mata "A. Bukar me aka baki kika yaga Haka..?" Tsaki Aneesa Taja Tana Gyara Tsayuwa kafin tace "Nombar Wayar yar Wahalar ce wai na Kirata in na Koma gida.."

S. Jibiya tasaki Dariya kafin tace "Ikon Allah Toh kan mene..?" Aneesa Tace "Kan Wannan Mugun mara Imanin Wanda ya baroni da gidanmu ya kawoni Cikin Wannan Dajin yana Cin Zalina mana.." A tare S. Jibiya da B. Kaita Suka Haɗa baki Suka ce "Wai *MR BELLO MUHAMMED JIƘAMSHI*....?" Aneesa Ta Ƙara Jan Tsaki tace "Bello dai kam Don ni bazan ce mai Mr Bello ba Wlh..."

B. Kaita tace "Gaskiya Aneesa bakya kyautama kanki ina Laifin Mr bello Da Kika bi kika Tsaneshi, taimakon ki fa yayi Daya kawoki mkranta kikayi karatu kika zama 'ya kamar Kowa.." Da Mamaki Aneesa Ta kalleta kafin tace "Nace ne ya Taimakeni ko Kinji nace miki ina Buƙatar Taimako ne, King B. Kaita Ki kama bakinki karki gaya min mganar banza nace Baƙin Mugu Wanda ya Kawoni Wannan Dajin Allah Yana Cin Zalina ko Zaki Rama mai Ne Domin Naga Alamar Kema Cikin Layin Su Jidda ne na Son Wanda bai Dace daku ba.." Ta faɗa Cikin Fushi.

B. Kaita ta Harzuƙo ma Aneesa Tana Faɗin "Eh ɗin Faɗi ki ƙara Ina Son Mallam Bello kuma so na Aure Aneesa Zuciyata Kullum Tana Zafi da Takaichi Duk Sanda Naji Kina Aibatan Mr Bello, Haba Shikenan kuma don Jininku bai Haɗu ba, baki Sonshi sai ki Hanamu mu...


Read / Download MR BELLO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album