Join Our WhatsApp Group

AWA 48 A ZIRIN GAZA Complete Hausa Novel Document by AWA 48 A ZIRIN GAZA


AWA 48 A ZIRIN GAZA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 14434



AWA 48 A ZIRIN GAZA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 01, Sep 2023

Author: Ahmad Akhatibi Ibrahim Daurawa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 80.45 kb

File Type: txt

Views: 859+

Download: 219+

Last download: 2 days ago

Description/Story: AWA 48 A ZIRIN GAZA
Ibrahim Ahmad Daurawa
Made:- Shuraih Usman

Domin download na wasu kayatattun hausaebooks namu sai ku ziyarcemu a shafin yanar gizo gizon
mu akan wannan adireshi http://shuraih.waphall.com

Kuna iya ziyartarmu a shafinmu na facebook kuyi like http://fb.com/hausaebooks

AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 1
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
JAFFA
.
Allah daya gari ban ban nace a zuciyata bayan da iska mai zafi ta bugi fuskata a lokacin dana leko
waje. Na tsaya karewa wajen kallo , tutar kasar izra'ila na fara hangowa tana filfilawa akan
husumiyar filin jirgin saman , inda nan ake gudawar da zirga zirgar jiragen sama
.
Jama'a suna kaiwa da komowa a filin sannan na fara tako matakalar sauka daga jirgin , wani abu da
bana mantawa da shi ne duk san da na dubi tutar izra'ila sai naji gabana ya yanke ya fadi ras
.
Da haka jakata a rataye a kafada ta muka yi dan tattaki zuwa falon karbar baki , wasu yan uwan su
ko abokan harkansu sun zo tarar su cikin murna da annushwa .
.
Na kuma lura dda wasu ba taryar kowa suka zo ba babu wata walwala ko fara'a tare da su, idanunsu
na kan kowa, kamar yadda kyanwa ke tare nutstuwa idan taji motsin bera. Ko ban fada ba kasan ko
su waye su JAMI'AN TSARO NE
.
Wajen karban baki nan ne kuma ake duba fasgo da sauran takardun tafiye tafiye , gurin a tsare yake
akwai kayan binciken muhimman takardu na zamani kamarsu inji mai kwalkwalwa da fitilun
siddabaru wanda suke bayyana rubutun boye sirri
.
Kaman misali irin na takardar kudi, na bude baki ina kallon abubuwa har layi yazo kaina wani
bayahude ya kalleni sama da kasa alokacin dana mika masa fasgodina a lokaci guda kuma gabana
yaba da ras. Daga nan ya fara jeho tambayoyi barkatai iri iri kamar ruwa, kai ka cebai karanta
fasgodina ba.
.

Abin dayai ba shi muhimmancin shine "me ya kai ka bosniya Hasgobina har tsahon wata biyar "
don ya lura kan sarkin dayake jikin fasgon da kuma sabon da aka buga akwai tsahon kusan wata
biyar a tsakani.
.
Azuciyar tana ce wannan bai shafe ka ba. Ina tunanin amsar da zan bashi yace "me ya kaika
sayarebo" kai tsaye na bashi amsa "neman labari ya kaini" ya dubeni sosai kamar lokacin ya fara
gani na "me ya zaunar da kai har tsahon wannan lokaci " ya bude ta ya kuma dubeni sosai " na so
dawowa amma babu hanya saboda filin jirgin saman sayarebo yasha wata majalisar dinkin duniya
ne ta rufeshi" yayi mini kallon ban gamsu ba
.
Ya gyada kansa cikin dabara hannunsa yanakan tebur ya gusa da shi gefen teburin ya danna wani
dan kulltu wanda aka rufe gefensa da takardu, cikin ya aikata amma na lura da komai, don haka
nasan cewa wani abu zai faru
.
Na kalleshi ido da ido yana shirin sake tambayata a cikin dakin dayake ciki kofa ta bude daga
bayansa wani dogo kakkarfan bayahude ya fito ko'ina jikinsa an rubuce shi da jami'an tsaro ba sai
ka tambaya ba duk da babu wata alama ko ta kayan sarki ,kallo daya kawai zaka yi masa ka tabbata
jami'in tsaro ne ajin farkon babu wata tantama
.
Ya karbi fasgodina ya duba sukayi yaren yahudanci ya danna na'urar mai kwalkwalwa, yayi nazarin
wasu bayanai cikin sauri "daga wacce kasa kazo nan" ya jeho min tambayarsa a lokaci guda kuma
ya kura mini ido "daga Bosniya nake" na maida masa kai tsaye nima na kura masa ido " kai dan
wacce kasa ce" ya sake tambaya ta
.
"Nijeria" na fada ba tare da na dauke idona daga kansa ba
"Me ya kawo ka nan?"
Nayi tunnani cikin sauri kafin na bashi amsa don na fara fahimta makircin da suke shirin kulla min
kuma na san kasar izra'ila basa maraba da yan jarida kasan wanda yake da abin fada kum yason a
afada bazai taba maraba da dan jarida mai kishin ba, sai dai yan abi yarima asha kida
.
Ni HADI sam ba irinsu bane ni dan jarida ne na hakika mai kishi, ina cikin wannan sake sake ne
yace meye sana'arka na amsa "rubuce rubuce da neman labari" ya matso kusa dani "kana da sheda"
na ciro katina daga aljihun rigata na mika masa ya duba ya kalleni ya sake kallona ya dauki kan
talho yayi magana .
.
Ya ajjiye shi a hankali naga kamar yana tuna wani abu "me kazo yi nan" cikin sauri nace "yawon
bude ido" ya tsira mini ido yasa hannunsa daya a aljihun wando ya kuma nuna ni da hannunsa na
dama "bana son yan jarida a kasarmu sam bana maraba da ungulaye"
.
Yana rufe bakinsa wasu majiya karfi suka nufoni sun fito daga kofar kudu da inda nake ,kai tsaye
suka nufo ni kamar kibiya,cikin sauri suka kewayeni daga nan suka ce na bisu inda suka fito na bisu
ban yi wata gardamaba suka kai ni wani dakin bincike kwkkwara duk kayan jikina ba ain da basu
duba ba hatta dunduniyar takalmina sai da aka kusa ballata bayan an gama bincike da wata yar
na'ura mai kwalkwalwa da ake kira metal detector kwalar rigata ma bata tsira ba, babu inda ba'a
bincike ba na share sama da sa'o'I ana yimin tambayoyi kala kala kamar mutumin daya fado daga
duniyar wata
.
Daga karshe aka shige dani wani ofis inda na iske wani bayahude kato zaune akan kujera mai
juyawa yana da kasumba da saje da gemu da kumatu luhu luhu yan idanunsa sun nutse ciki , akan
teburin akwai talho zai kai biyar daya ajjiye wannan sai ya dauki wannan, ban ga sunan sa ba kamar
yadda ake ajiye sunan mutum akan tebur ajikin dan katako ko roba , yana zaune yana busa tabar
hanavana katuwa ahannunsa kamar yankan rake, muna shiga firgigit ya juyo da kujerar ya zuramin

ido tamkar yana kallon wani dan kwaron da yake neman fada masa cikin shanyinsa ya gummtsi
hayaki ya fesa sama, kumatunsa sukayi sama da kasa sai naji wani dan sauti kamar na kuya
"Vulture are not welcome here and we think you have a hidden mission not tourism, even though
we have nothing to incriminate you"
Ma'ana ba a maraba da da ungulaye ,kuma muna tsammanin kana da wani boyayyen shiri ba yawon
bude ido ka zo ba, ya sake busa sigarinsa na dube shi kawai cikin tsana da bacin rai don duk na
gama galabaita da tambayoyi da bincike na wulakanci ga kallon kaskanci iri iri ya kalleni sosai
"you are to deported back to where you come from" bansa dana yi subul da baka ba nace " tafi nono
fari" ya dubi jami'an tsaron dake baya. Nan da nan suka bukaci dana fassara abin da na fada ya nace
"shi kenan na gode"

Toh anan zan dakata Tambayata anan shine
MAI NE NE SUNAN MARUBUCIN LITTAFINNAN
.
AWANI SHEKARA YA WALLAFA WANNAN LITTAFI
Bazan ga masu cika bakin cewa wai su suna karanta tsoffin littatafan hausa
Daga naku shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 2
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Lokacin daya juya na naji yayi tsaki yace "we don't know who give you this pucking visas....."
Na dan tsaya don naji karashen maganar jami'in tsaron ya rike kafada ya hankadani gaba "you are
not welcome here"
Turanci irin na amurka
.
Hankalina ya tashi gaba daya yayin da muka fito muka shiga dakin da akayi min bin cikie na zauna
ina jiransu su tattaro min kayana .
Raina ya gama baci matuka ainun don ba irin wulakancin da ban gani ba wajen binciken nan
tambaya kamar wanda aka kama da laifin kisan kai
.
Aka garomin fasgo din akan tebur ya fado kan cinyata na yunkura na dauki jakata , don haushi ko
budawa banyi ba na saka a ljihu, na figi jakata na saba a kafada nayi waje fuskata a daure rai na
abace
.inajin takun sahun mutun yana biye dan yana kokarin kwantar min da hankali wai ba sun yi min
hakan don wulakanci ko kin bako bane sunyi ne don matakan tsaro
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ni dai ko sauraransa ban yi ba da haka ya rakoni har tsakiyar filin jirgin saman abin dauya dameni
kawai in rabu da wadannan yan wulakancin in dawo sayarebo wajen kausar ko hankalinta ya
kwanta ni kuma inji sanyi a raina saboda ganin masoyiyata
.
Mutumin yayi min rakia zuwa kofar wani jirgin saman "swiss air" ina kokarin mika "boarding pass"
dina na shige jirgin sai naji an rike min hannu ta baya , na juya a hankali na dube shi tsaf, dogo ne
fatar jikinsa jajaja alamar ya zauna a kasa mai zafi ,
.

Idonsa kanana masu launin toka toka , gashin kansa ruwan gitsawa yana da gashin baki ba gemu
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Ya mika mini hannu nine mr Ros ina son ganinka a ofis dina
Wannan kalaman sun bata mini rai kwarai sai naji kamar ya kwaro min ruwan zafi, cikin sauri na
nuna masa bodin pas "bana bukatar ganawa da kowa ba kun koreni ba na jefa masa maganar cikin
gadara
.
Alokaci guda nayi kokarin shigewa ya rikeni gam " haryanzu kana cikin kasar izra'ila don haka dole
ka mutunta dokokin karsa, ka biyoni kada kaji komai"
.
Naso nayi gardama koda na lura jami'an tsaro suna yimin muzurai kuma na san cewa ban shiga
cikin jirgin ba dana shiga to nabar izra'ila kenan, ina cikin inuwar swizland" dole subarni ganin haka
dole na rufawa kaina asiri na bishi duk jama'a suna kallona sun kuma san cewa da walakin goro
amiya wannan shima ba karamin wulakanci bane , ace cikin dubbai an tasa ka gaba kamar barawo
kowa na kallonka
.
mintina biyar a tsakanin ya miko min takardar iznin yawon bude ido a izra'ila amma banda wasu
wurare daya kira "security zone" na duba takardun na ga babu iznin zama a telaviv da kewayanta
sannan kuma an rubuta baro baro kada na shige kwana uku a kasar
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Na nutsu sosai wata tambaya tazo min me yasa yanzu aka bani izini bayan angama wulakantani an
galabaitar dani an koreni kuma meyasa aka bani izni bayan da an mini cikakken bincike an gano ni
hatsari ne ga tsaron izra'ila har an koreni don a huta da kaya sannan kuma a kirayoni a bani iznin ba
wani kace na ce , lai lai da sake wai mai kaza ya tashi da kai, don haka nace dole nayi taka tsantsan
da mutanen nan sai maganar shugaban hizbulla a sarayebo ta fado min "zasu iya binka su halaka
ka"
**************************************
Rana ta raba sama gari ya dauki zafi sosai na duba agogona na ga shabiyu da rabi na rana , na shafe
a sama da awa biyar kenan a filin jirgin saman ana yimin tambayoyi da binciken bin kwakwaf
.
Na fito harabar filin jirgin tare da dan rakiyata inda jama'a suke zirga zirga a wajen akwai wajen
ajiye motoci masu zuwa filin jirgin.
Akwai kuma wajen ajiye motocin haya da bas bas na alfarma sunyi layi , sai ka fadi inda zaka kuyi
tsada da direba
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Kai tsaye ko kuma kaje ofis dinsu idan kana da kudi da yawa ka cashe musu kudinsu su baka direna
ya kai ka duk inda kake son zuwa iya tsahon zaman ka a kasar, idan kuma kai sananne ka iya hayar
motar har iya zamanka.
.
Na dauki hayar mota ajin masu kudi duk kuwa da cewa ba matsala bane a guna amma ina da wani
abu araina
.
Muna shige shigen karge na jami'an tsaron filin jirgin sama na faa fahimtar halin kuncin da
falasdinawa suke ciki.
.
Duk ina da naga ana aikin kaskanci ko aikin wahala idan na tambayi direna sai yace falasdinawa ne.
Ina son tambayar dalilin daya sa falasdinawa ne kawai suke aikin kaskanci sai naji gabana ya fadi
Ras. Don haka na kanne nace na bincika da kaina
.
Yayin da yake shigowa yakin cikin birnin telaviv lokacin na kuma ga wani abu daban wato taruwan
jami'an tsaro da sojoji dauke da makamai kamar ana yaki, motocin yan sandan tarzoma suna zirga

zirga ko'ina rike da bindigogi da rediyon walis a kugunsu suna lura da kowa suna muzurai kai kace
jiya jiya ne akaci garin da yaki.
.
Gaba daya yanayin garin ya sauya ya koma irin yanayin filin daga , a gaskiya har yasa tunanin tuzla
ya fado mini arai, naji na kasa jurea har zuciyata ta fara bugawa da karfi, na dubi wanda yake
gefena wanda shine dan rakiyata "tourist guide " na kalleshi sosai "wannan jami'an tsaron haka
lafiya kuwa?" Na tambayeshi tun daya shigo baice komai ba sai a lokacin
"Sune dakarun zaman lafiya" ya dauke kansa yana kallon waje a daidai lokacin wata mota ta gifta
mu na lura da ita ganin yadda ya kalleta, sabuwa ce mutum biyu ne acikinta daya yana magana ta
rediyon walis dake cikin motar babu fallen rubutun lamba, bayanta kuma wata ta shigemu an rubuta
"first class citizen" dan kasa mai daraja ta daya. Ba a jima ba kuma wata ta shige da lambar "third
class" da fari dai banyi niyyar tambaya ba saboda yadda naga na kusa dani yana kallona amma cikin
dabara sai na jeho tambayar"mai daraja ta daya" meye kuma haka ya dubeni zaiyi magana sai
mukayi burki a shigen jami'an tsaro
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
A gabanu jerin gwanon motoci suna tafiya a hankali zuwa kofar shingen sojoji da yan danda wasu
dauke da bindigogi suna muzurai, wasu kuwa suna rike da na'urorin bincike irinsu na'urar sansanar
bomb data binciken bindiga wasu kuma suna takardun mutane sunayensu da kuma gurin da zaus da
lambar motar da matsayin mai motar wato bako ne ko dan gida ne, shi din ma wacce daraja yake da
ita kuma wanne jinsi ne bayahude ne ko balarabe "kai wadannan mutane da rashin yarda suke"
bansan lokacin da wannan furucin ya fito daga bakina ba sai dai nayi sa'a da harshen hausa nayi shi
.
Mutumin dake kusa dani ya kura mini ido ya kalleni sosai, adai dai lokacin kuma motarmu cikin
sanda ta kai ga kofar shingen wani soja rike da bindigarsa kirar amurka m16 ya iso cikin sauri ya
sunkuya tun kafin yayi magana direban ya bashi takardunsa sukayi magana, ga alama dai sun saba
da shi na lura lokacin daya mika takardunsa sinyi musanyar alama ta cikin dabara cikin na lura da
su ta wutsiyar idona
.
Wani ya karaso dauke da wani dogon karfe mai fadi daga karshen sa kamar shebur ya karasashe a
karkashin motar sannan ya umarcemu mu fito ya kara mana na'urar binciken bindiga, ya bukaci
fasgo dina na mika masa ya buda ya dubeni sama da kasa
[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne].
Yayi magana sojoji cikin sauri suka baibayeni kafin kace kwabo har wani ya doramin bindiga a
wuya , sunyi mamaki da suka ga ko gezau banyi ba ni mamaki kawai suke bani ba tsoro ba,
Na dubesu daidai cikin natsuwa "ka keta dokar kasar izra'ila "wata murya ta fada a bayana nayi
kokari na waiwaya don yin tozali da mai maganai suka hanani motsawa "what is the hell with you"
na fada cikin fushi "you are deported" murya ta mayar mini duk jami'an tsaro dake wajen suka juyo
guri na cikin sauri suna jiran cika aiki kamar kare ya hango muzuru
.
Toh anan zan tsaya don na gaji
Sai mun hadu ranar friday
Daga shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 3
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[kar ku manta...


Read / Download AWA 48 A ZIRIN GAZA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album