Join Our WhatsApp Group

RABUWA CE SANADI Complete Hausa Novel Document by RABUWA CE SANADI


RABUWA CE SANADI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 77794



RABUWA CE SANADI

Reading Time: 6 Hours

Added On: 28, Jul 2023

Author: Queen Meemi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 502.36 kb

File Type: txt

Views: 603+

Download: 603+

Last download: 23 hours ago

Description/Story: . . . . . ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣1❣



*©Mymounerh Basheer*

*®NWA*

*littattafan marubuciyar*

*soyayya gamon Jini*
*Raheena*
*kishiyoyina*
*habibullah*
*noor ala noor*
*Na Aminta dake*
*gimbiya maimunatu*
*Akan kaskon suya*
*Zeenatu*
*Ashe haka so yake*


*Queenmeemi.WordPress.com*


***************

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM


*_k'aramar hukumar bunkure,dake jihar kano_*


Babban titin dake garin bunkure wanda ya cika da d'aukacin jama'a kowanne ka kalli fuskar sa arazane yake wasu kuma gudu suke ci,ga wasu a kwance dai-dai kusa da wata Babbar mota na gano yarinya
Yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniyaba a zaune kusa da wata mota sai ihu take,Jikinta sai karkarwa yake kukan natan Sam baya fitowa sabili da taci kukan harta k'oshi.


Daamm!!! k'ara ce ta kuma tashi, take mutane suka hau guje-guje yarinyar da Bacci ya fara d'ibanta ta tashi firgigit ta k'wala k'ara ba wanda yasan tanayi gudu ta hauyi irin Na yara bawanda ke Kula taa kowa ta kansa yake ,ke sai kiran momy take da dady ,wata mota ta gano gurin tayi aguje
taje aguje tana bubbugawa dady! dady! neman iyayenta take Amma ko alamarsu Babu ga wajen ya hargitse kowa takansa yake Saboda tashin bomb din da akaji wanda yazamo tamkar wata jaraba gun wani mutumi ta yi ta baya da gudu tayi wajensa tana dady.
juyowa yayi a tsorace yayi arba da ita , yana shirin magana k'arar bindiga ce tafara tashi tas! tas! tas! tas! kakeji nan da nan waje ya kuma hark'ewa hayak'i ko ta ina.
yarinyar da duk Jikinta yajike da fitsari ga bakinta Na jini ,mutumin nan ya falfala yafara gudu ,yarinyar tabiyoshi dady! dady! sojojine suka tawo aguje suna harbi nan da nan mutumin yai wata kwana yarinyar tabishi tana ihu inda ya b'uya taje ta tsaya ta dafa shi "dady momma" hankad'eta yayi yace "Yau naga jaraba ke ina iyayenki? ana wann nan tashin hankalin don sakaci", tureta yayi yace ta bar wajen, tafiya tayi da gudu tayi wani waje tai kwana tana sangal-tangal saboda ciwo dataji a k'afa wani yaro ne ya arto yana haki yai ciki da ita ta fad'i k'asa d'agowar da Zatai akai harbi Allah ya taimaketa ba aharbeta ba Amma tsoro yasa ta suma ganin hakan tausayi yakama mutumin ya fito Daga mab'uyar sa ,yazo ya d'auketa ya
runtuma aguje yana gudu seda yayi nisa yaje motar sa dake ajiye ya ajiye ta agaban mortar dayake motar d'aukan kayace yara su hud'u ya ganni a bayan motar sai ihu suke ya kallesu yace " ina iyayenku"? D'aya ne mai wayo yace "nan mukazo muka b'uya",Sauran kwa ba wanda yayi magana sai kuka duk jikinsu k'ura da d'an Jini-jini ajikin su,jin- jina kai yayi kawai ya shiga motar.



************
*K'auyen mangalu*

Jan motar yayi ya fafara aguje nan yiyi hanyar k'auyensu tafiyar awa d'aya da rabi ya kaishi k'auyen mangalu wanda yake a k'ark'ashin k'aramar hukumar bunkuren, Bayan yaje k'auyen nasu su, take bai zarce ko ina ba sai tasha,ya bud'e motar ya fita yaran yad'ebo, ya sauke su gaban motar yaje don d'auko yarinyar wayam ya nemi yarinyar ya rasa neman duniya yayi bega yarinyar ba mamaki k'arara afuskarsa "kode aljana ce tsuka yaja inajin Aljana ce
sede ko sauka tayi",nan yayi ta dubawa bai ganta ba
Sarkin kasuwa ne yazo aguje "Malam lado me nakeji ne agari wai cikin gari bomb ya tashi da Gaske ne kuwa"?

"Tabbas! hakane Sarkin kasuwa Ni kaina wallahi abun yaban tsoro, lodi fa nake zan kai kaya kasuwa kawai mukaji k'arar tashin bomb ai Wallahi munga tashin hankali don an mutu agun ,dak'yar Na sha,kaga kuwa abin tausayi harda wata yarinya dana gani
agun sai karakaina take tana neman iyayenta kawai sai yarinya ta dinga bina tausayinta yasa Na d'auketa abin mamaki munzo nan Daga sauka din na sauke yaran can na duba bangan taba".

"Allahu Akbar Allah ya k'ara kiyayewa" sarkin kasuwa yafad'a Yaran nan su hud'u malan lado ya mik'awa Sarkin kasuwa da bashi dubu d'aya kan akaisu Police station da ke cikin garin bunkuren ko za asamu iyayensu , sarkin kasuwa yace wa wani d'ahiru ya rik'e yaran ya basu abinci shida MLM lado suka hau dube-duben neman yarinyar nan ,Amma basu ganta ba ,nan suka dawo lokacin yaran Sunci Sun sha MLM lado ya deb'e su sarkin kasuwama ya shiga motar .

Sun fita titi caraf idon sarkin kasuwa ya gano masa yarinyar nan gefen titi da Rabin bread a hannu tana ci tana kuka,yace "hala dai ita ce waccan"? Malam lado yace "ita ce" direct motar ta tsaya suka fita abin tausayi
jikinta zafi zau suka d'auketa,sunje police station suka bada yaran kan b'atansu a dalilin tashin bomb d'in ,sunayensu a ka d'auka da hotuna,da yake gidan sarkin kasuwa anan yake yasa aka bar yaran a gidan nasa,su kuma 'yan sanda suka hau sanarwar neman iyayensu. malam lado ma ya tafi kan duk yanda akai Skasuwa ya Sanar mai.


*by Queen meemi*



. . January 2017 Queen meemi
⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜ ❣ ⚜


❣ ⚜ ⚜❣

*❣RABUWA CE SANADI❣*

*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
❣2❣


*©Mymouner Basheer*


*®NWA*


*Queenmeemi.WordPress.com*


wajen yamma MLM lado ya je gida a gajiye shigar sa gida ya Tarar da gwamma na tsinkar zogale d'agowa tayi tace ''MLM Yau kayi nisa da yawa" ,ruwa ya d'ebo a randa ya sha San nan ya zauna atabar mar da gwamma ke kai,yace "ai Yau munsha da k'yar nan ya labar ta Mata dafe k'irji tayi "kai Amma ka auna arziki' ,dama naji labarin birni bai shiga ta Dad'i, gashi yazo garin nan yanzu" alamar jimami ne fuskar sa,yace "ai kede bari gwamma Allah ya kyau ta dai" kallonta ya kumayi "wai Ni ina jummai ne"? tab'e baki gwamma tayi "ai kasan ayawoma ce Sam bata zama agidan nan muddin kasa k'afa ka fice".murmushi yayi don inda sabo ya Saba da halayen gwamma wajen yiwa jummai sharri,sallamar jummai ce ta katse musu hirar da harara gwamma ta sauki jummai da murmushi d'auke a fuskar jummai ta tsugunna tace "malam Barka da dawowa ,naje gidan kaka ne gaida ita Batada lafiya" nan yace bakomi jummai nasan da dalili ai " gwamma tace "tab! Lalle malam ka sakarwa jummai da yawa ace Mata ta fita bada izininka ba, Amma bazakai Mata fad'a ba,ita ga matar so" tashi jummai tayi ta d'auko kwanon abincin malam ta aje mai da ruwa daya ke itace da girki Yau, nan ya hau ci dama yunwa ce ke cinsa.




*BAYAN SATI D'AYA*


MLM lado na zaune a soro yana jin radio domin tun lokacin da bomb ya tashi bai koma cikin gari lodin kaya ba, don yaji labarin wajen ansa masu tsaro , kuma gashi saboda tsoron karyaje tsautsayi ya afka dashi, sallamar sarkin kasuwa ce ta katse mai jin radio d'in da yake da fara'a ya zauna suka gaisa mudi D'an MLM lado mai kimanin shekara goma ya kawo mai ruwa,sarkin kasuwa yace "wato MLM lado yaran nan cikin ikon Allah duk anga iyayen su biyu a asibiti akaga nasu iyayen sauran kuma duk yan uwan su ne suka karbe su duk ta dalilin faruwan tashin bomb dinne yara suka bata ,kuma duk Daga wani garin suke,wani hanzari ba gudu ba ,yarinyar nan Sam! ko alamar wanda ya Santa ba agani ba balle su zo",gaban MLM lado ne ya fad'i cike da tausayi yace "ikon Allah yanzu ya za ai ke nan sarkin kasuwa yace ai police sunce mu rik'eta agunmu zasu cigaba da dubawa gashi Ni kuma zan tafi garin gabas jibi" ,mlm lado yace "to ai ba matsala ka kawota gurina muga yanda Allah ya yi ,haka sukai sallama ya tafi.



*WASHEGARI*

wajen k'arfe goma sha d'aya saiga sarkin kasuwa nan da yarinyar suna tsaye sai ga Shi ya fito musabaha sukai da Shi nan yace "to MLM lado gata nan godia malam lado yayi mai ya tafi Shi kuma ya d'auketa suka shige ciki.


gwamma na hura ice jummai kuma na tankad'e MLM lado ya shiga kallo suka bishi da shi ,murmushi ne Akan fuskar sa gwamma tace "malam wan nan yarinyar fa"? ,kallonta yayi yace "Dad'i na dake wutar ciki, to 'ya na samu" nan ya kwashe duk yanda abun ya faru ya gaya musu jummai harda kuka saboda tausayin yarinyar gwamma kuwa tace "to rik'eta zakai kenan"! MLM lado yace "to ya zanyi Allah ne ya had'ani da ita" nan ya kalli jummai yace "ga 'ya na kawo miki ki na Kula da ita, kafin Aga iyayenta,da murna ta karb'eta dama bata da yaro tun lokacin da yarta hansai ta mutu har yanzu bata K'ara haihuwa ba,kallon yarinyar tayi tace "ya sunan ki ,batai magana ba sai D'an motsa baki da tayi,malam yace "kinga jummai kisa Mata suna na wucin gadi sai ana kiranta dashi kan Aga iyayenata".


"MLM zan ce Mata hansai sunan marigayiya",gwamma tace "Amma ke kan jummai anyi solob'iyo ayi dai mu gani Daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i" MLM lado yace" kinga gwamma ban San neman magana tunda bake na bawa ba baruwan ki" tab'e baki tayi ay ba tun Yau nasan kafisan jummai dani ba ,me zanyi da tsintacciyar mage, nan ta buga...


Read / Download RABUWA CE SANADI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album