Join Our WhatsApp Group

KUDI DA MACIJI Complete Hausa Novel Document by KUDI DA MACIJI


KUDI DA MACIJI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 30267



KUDI DA MACIJI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 168.39 kb

File Type: txt

Views: 795+

Download: 220+

Last download: 12 hours ago

Description/Story: KUDI DA MACIJI
NAZIR ADAM SALIH 2005
Ebook creator Shuraih usman 2018

Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya
saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com
Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download
it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at
www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading

Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga
wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group
a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan
wannan nombar 08170707521
Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan
adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah
muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu

Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a
whattsap asha karatu lafiya

Hakkin mallaka (m) Nazir Adam Salih

KUDI DA MACIJI l-01
NAZIR ADAM SALIH (Nas 2005)
KASHI NA FARKO 1884
DAYA
Abakin Wata katuwar fadama da misalin karfe hudu da rabin wata ranar Juma'a ta karshen karni na
goma sha takwas wasu jinsin tsuntsaye sukayi sahu sahu abakin fadamar suna ta shakatawa abinsu
domin kuwa babu abunda ya dame su don basa fargabar a fada musu da yaki ko kuma a kawo musu
hari kamar yadda sauran jama'ar gari keta kwanan zullumin kasancewar wadannan abubuwa guda
biyu akansu.
Da yawa daga cikin tsuntsayen dake bakin fadamar neman abincinsu sukeyi yayinda wasunsu kuma
keta wanka abinsu wasu ko sai shawagi sukeyi a gefen fadamar suna kaiwa yan kananan kifaye hari
ko Allah zaisa su dace su sami Abinci.
Acan gefe fadamar daga yamma wani manomi ya jefar da fatanyarsa gefe guda ya mike tsaye ya
share gumi kana ya juya ya dubi matarsa wacce ke ta faman aiki babu ko sassautawa kaikace itace
Mijin.
Matar ta dago kai ta dube shi a yatsine tace
To Uban malalata yanzu fa saikace harga gaji ko? Na dauka tun duku dukun nazo gonar nan bance
nagaji ba saikai dakazo da tsakar Rana.
Manomin ya dubi matar cikin murmushi haba Tagogori ke kinsan Ai nayi kokari ma da na kawo
haryanzu ina noma nifa na rigaya na fada miki bazan iya noma ba gara ki kyale ni akan sana'ata
Tagogori ta dubi mijinta a fusace domin tasan abinda yake nufi Oh Amma dai zangeru wallahi kaji
kunya yanzu ace mutum ya fifita SATA akan sana'armu ta Gado Noma?
Zangeru ya dubi tagogori ya fashe da dariya sautin dariyarsa ya watsu aduk fadin fadamar harda
dama daga cikin tsuntsayen dake garin suka tashi a tsorace.
Haba Tagogori kin manta da cewa abindana gada kenan tun kaka da kakanni? Ta gogori ta jefar da
fatanyar dake hannunta ta mike tsaye sosai ta dube shi kai kasan da tun farko nasan kai BARAWO
ne na rantse da Allah bazan fara ma aurenka ba.
Zangeru ya sakato datti daga kogon kunnensa cikin murmushi yace kinga kuwa ni a ganina wallahi
duk cikin sa'anninki babu wacce tayi dace da miji kamar ke domin ke kadaice kikayi dacen auren
Jarumi.

Tagogori ta turo baki gaba kamar suda wanene Jarumin?
Zangeru ya bugi kirjinsa da karfi yabada wani sauti Fuss tsuntsaye suka sake watsewa ya dubi
matarsa Tagogori tace Ni Kuwa aganina babu rago kamar malalacin daya zabi sata fiyeda noma
dubi fa ciki ne dani wata biyu amma tun hudowar rana nake aiki haryanzu bangajiya ba.
Zangeru ya kurawa matarsa tagogori idanu na tsawon lokaci sannan saiya danki fatanya ya rataya a
kafada yace shiyasa nake son ki rabu da wahala amma har kullum inata kokarin nuna miki Annabi
kina runtse idanu dubi cikinki ya fara girma amma kullum kina kara cusa kanki cikin wahala ya
danyi shiru yana kallonta.
Ganin tayi shiru batace komai ba sai yaci gaba.
Toni yanzu tagogori in banda abinki ma dan abin nan da zamu samu awannan yar gonar nawa yake?
Sanin kanki ne acikin dare guda ina iya tara miki abinda zamuyi shekara guda muna ci amma duk in
kin bi kin dami kanki.
Tagogori ta sunkuyar dakai tana murmushe kasar dake mammanne ajikin busassun yan yatsunta
wadanda tsabar wahala da noma duk ya busar dasu kamar itace. Akwai alamun gajiyawa a fuskarta
kuma dayake zangeru ya kura mata idanu ya fahimci hakan. Wannan shi ya kara masa kwarin
gwiwar cewa
dauki fatanyarki mu tafi gida kinga rana ta tasamma faduwa.
Tagogori ta dago kai ta dube shi ranta a bace ta bude baki kamar zatayi magana saita fasa ta dauki
fatanya ta saba fatanyarta a kafada.
Zangeru ya dubeta da murmushi yace kwantar da hankalinki Tagogori nan da badi zan zama babban
attajirin da ba'a tabayin kamarsa ba aduk garinmu yana gama fadin haka saiya juya ya fara tafiya.
Tagogori batace dashi kala ba sai kawai ta bishi abaya suka nufi bakin fadamar nan wadda ga
Al'ada aduk lokacin da sukazo noma anan suke dauraye jikinsu su sha ruwa kafin su koma gida.
Sa'ar da suka kai bakin koramar sai suka tsugunna suka fara dauraye jikinsu sassanyar iskar
yammacin dake hurowa daga cikin fadamar ba karamin jefa zangeru cikin nishadi takeyi ba sau da
yawa ya gwammace ya wuni ya kwana gindin fadamar yana shan iska da lofe a hannunsa fiyeda ace
ya noma daidai da kunya biyu.
Adaidai lokacinne to tagogori ta dube shi tace naji dazun kanayin wani mafarki wai kwananan zaka
zama babban Attajiri ko? Tayaya to zaka zama attajirin? Da lalaci ko da me? Tayi shiru tana kallon
mijinta zangeru wanda ke zaune ya tura kafafunsa biyu cikin fadamar idanunsa lumshe yana
sauraren kukan tsuntsaye.
Zangeru ya bude idanunsa ya dubeta.
Kina shakkar zamana Attajirine?
Tagogori tayi dariya a karo na farko.
Attajiri fa kace niko naga mutumin da ko kankani bashida son yasha wahala arayuwarsa tayaya zai
zama Attajiri?
Zangeru ya girgiza kai yace tagogori kenan wato wani lokaci kikan bani mamaki da kike daukata
amatsayin rago ko malalaci kada fa ki manta cewa sana'ata tafi karfin rago ko malalaci yadanyi
shiru ya girgiza kafafunsa akan ruwa
akwai alamar murmushi abakinsa duk kuwa da cewa baifito fili ba to amma tagogori ta lura da
hakan.
Sau da yawa idan taga zangeru yana irin wannan boyayyen murmushi bata magana domin duk sa'ar
da zai fita wata gawurtacciyar sata irin murmushin yake yi.
Sannu ahankali zan tabbatar miki da zamana attajiri tagogori ta sunkuyar dakai tace to Allah ya
sauwaka.
Daga nan basu sake cewa da juna komai ba sai ma'auratan biyu suka cigaba da wanke jikinsu tsahon
lokacin suna cikin wannan hali zangeru na cikin tsananin nishadi domin wani sa'ilin shi kadai sai ya
daki tsakiyar ruwan da kafarsa ya fashe da dariya Tagogori bata tanka masa ba.
Daga inda zangeru yake zaune yana iya hango jerin sahu sahun jinjin tsuntsayen dake kai kawo
suna shawagi a saman fadamar kamar jirage a cikin ne to ya lura da cewa akwai wata BALBELA
ita kada tana tsaye abakin fadamar. Duk cikin jinsin tsuntsayen ita kadaice batada yar uwa balbelar

ta taso ahankali cikin lalaci ta sauka adaidai inda su zangeru suke zaune zangeru ya dubi balbelar
cikin murmushi sannan ya dubi matarsa yace tagogori dubi wata balbela mai kyau ta ziyarce mu
tagogori ta dubi balbelar shekeke tace na ganta sannan ta dauke kai gefe guda.
Yaya naga kin bata rai?
Tagogori ta hade fuska tace haka dai ka iya gashi nan yanzu ka rabo mu da aikinmu ka kawo mu
bakin fadama muna zaman banza kagani in ba yanzu zaka tafi ba ni kabarni in tafi gida ko kuma in
koma gina na karasa sauran aikin dake gabana.
Zangeru ya dubi tagogori cikin murmushi kana iya duba balbelar yace bakisan irin yadda nake
kaunar tsuntsaye ba ne musamman ma balbelar nan fara mai dogon wuya da jan baki kyakkyawa
kai ina ma ace ina iya zama tsuntsaye dana zama Balbela tagogori ta fashe da dariya tace Oh
zangeru al'amuranka sai kai.
Zangeru ya dubi matarsa cikin nishadi yace Allah kuwa tagogori da gaske nakeyi domin bakiji
yadda nake kaunar balbelar nan ba bari mugani yana fadin haka saiya mika hannunsa zai kama
balbelar.
Ga mamakinsa sai kawai yaga balbelar ta taso da kanta ahankali ta sauka akan cinyarsa nan da nan
ya dubi tagogori cikin farin ciki kinga abinda nake fada da miki ko itama balbelar a hannunsa cikin
tarairaya dubi tagogori ungo rike min ita zan tafi gida
tagogori ta mike tsaye ta dube shi tace kaga idan bakada aikinyi ni inada shi agida sai kawai ta juya
zata fara tafiya.
Adaidai lokacinne to sukaji kamar daga sama ance
"Haba baiwar Allah tunda yace dake ki rike masa ni yana kaunata ba saiki daukeni ba."
Tagogori ta tsaya cak kamar an soketa da kibiya ta juyo a razane ko shakka batayi ba zangeru ne ke
mata magana ba.
Zangeru yaji sautin muryar shi kansa saida abin yasa shi mutuwar tsohuwa zaune abakin fadamar
numfashinsa ya dauke ya dubi balbelar cikin tsananin kaduwa ko shakka bayayi balbelar ce ke
magana
tagogori ta dubi zangeru a tsorace tace bakinta na rawa
Wa..ne ne keyi min..magana naji muryar kamar ba... Kai ba?
Zangeru ya dubi balbelar dake kan cinyarsa cikin kaduwa sannan ya dubi tagogori
'Nice nake yi miki magana baiwar Allah gani nayi yadage akan cewa yana kaunata ke kuma sai
kokarin rabamu kikeyi.
Tagogori taja da baya cikin kaduwa tace kiyimin rai baiwar Allah ke kike ganinmu ba mumuke
ganin ki ba..wallahi bansan...tagogori ta kasa karasawa saboda tsabar firgita.
Kada kiji tsorona domin ba zan taba cutar ki ba tun da mijinki ya ambata yana kaunata abinda nake
so dake shine ki daukeni kamar yadda ya umarceki kutafi dani gida domin daga yau har iya
rayuwarku zaku kasance tare dani bazaku taba rabuwa dani ba tunda dai kuna kaunata
zangeru yayi ta yan maza ya tashi tsaye sai balbelar tayi tsalle ta hau kafadarsa tace zo ki daukeni
tagogori
tagogori taji kamar an doke kafafunta da gora nan da nan taji juna biyun dake jikinta ya fara motsi
kamar zatayi bari tun kafin lokacin haihuwarsa ya karaso.
*** *** ******* ****** ****** ****** ********
Adaidai lokacin da duk wannan ke faruwane akayiwa wani tsohon malami gwanin iya bugun kasa
iso agidan sarki SABITU wannan malamin tsohone kwarai da gaske kuma babu wanda yasan
takamaiman shekarunsa aduniya domin duk garin babu koda wanda yakusan sa'a dashi to amma
duk da haka jita jita ne cewa tsohon zaiyi kusan shekaru dari biyu zuwa dari da hamsin aduniya kai
akwai ma wani makaryacin baduku agarin dayayita yada jita jitar cewa wai tsohon yakai shekaru
dari biyar da tamanin wasu ko suna tunanin ma tsohon malamin ba Mutum bane Aljani ne.
To kma dai menene wannan tsohon malami mai suna MALAM DAWAYE shine babban malamin
sarki sabitu kuma shi kansa sarki sabitun ya gaji wannan malami ne agurin mahaifinsa sarki MAI
KWARANGWAMA.
Malam dawaye dogo ne fari siriri sosai ta tankware kamar baka tun daga kansa har zuwa gemunsa
babu alamar bakin gashi sai fari tass kamar an shafa masa garin Alli to amma wani abin mamaki

girar idonsa guda daya ta bangaren hagu bakace siliq har tana kyalli kodayake wasu shakiyar sunce
wai bakin shuni yake sha mata.
Lokacin da wannan lamai ya karaso gidan sarki la'asar sakaliya ce sarkin dogarai HAMBARA shine
yayi masa iso ya kuma wuce kai tsaye dashi har zuwa inda sarki sabitu yake kwance wanda yau
kusan wata guda kenan..
KUDI DA MACIJI - 02
Sarkin dogarai hambara shine yayi masa iso ya kuma wuce kai tsaye dashi har zuwa inda sarki
sabitu yake kwance wanda yau kusan wata guda kenan yana fama da matsananciyar rashin lafiya.
Malam Dawaye ya durkusa gaban shimfidar sarki yayi gaisuwa sarkin dogarai ya amsa masa sannan
sai sarkin dogaran ya mike tsaye zai fice daga dakin domin yabasu guri su gana.
Sai sarki sabitu ya dago kai daga kwance ya dubi sarkin dogarai sannan yace cikin shakakkiyar
murya idan anyi sallar magariba inason kazo min da SARKIN MAKERA.
An gama Allah ya dada ma lafiya da imani sarkin dogarai ya amsa sannan ya fice azuciyarsa yana
cewa anya kuwa sarkin nan ba mutuwa zaiyi ba domin ya fahimci kusan kullum a yan kwanakin
nan sai sarki sabitu ya gana da akalla aminansa guda uku zuwa hudu kuma duk acikin sirri
ficewar sarkin dogarai keda wuya sai malam dawaye ya sake fadawa gaban sarki ya dada gaisuwa
sannan yace Allah ya kara ma lafiya da nasara gani.
Sarki sabitu ya dubi malam dawaye daga kwance na tsawon lokaci akwai alamun karaya da
sallamawa duniya karara akan fuskarsa.
Malam dawaye ya fuskanci hakan don haka sai ya sunkuyar da kansa kasa ba zai iya hada idanu da
sarkin ba domin sai ya zubar da hawaye tsawon lokaci suna cikin wannan hali daga karshe dai sarki
sabitu yace malam dawaye abinda yasa na kirawo ka shine na fahimci rashin lafiyar nan tawa bata
tashi bace kuma ba tun yau ba ka rigaya kasan irin muguwar kiyayyar da wazirina DANDUNA
Keyimin kasan kuma cewa babu makawa da zarar na mutu shine zai zama sarkinku ya danyi shiru
yana mayar da numfashi.
Dawaye a kullum na tuna da irin kiyayyar dake tsakanina da waziri dandunawa saina shiga cikin
tsananin damuwa domin bansan irin halin da yan kananan ya'yana hassan da hussaina zasu shiga ba
wannan shine dalilin dayasa na kiraka domin ka buga min kasa ka gano min irin yadda zasu kasance
a hannun azzalumai waziri dandunawa bayan mutuwata.
Sarki sabitu yayi shiru yayinda shi kuma malam dawaye ya shafi dogon gemunsa fari tas mai kamar
gashin tunkiya sannan ya janyo allon bugun kasar dayazo dashi agabansa ya baza shida hannunsa
sannan ya dubi sarki sabitu yace
Allah ya baka nasara da lafiya an gama bari mu gani ai wuyar aiki ba'a fara ba.
Fuskar sarki sabitu ta washe kadan domin yasan tsohon malamin bai taba bugun kasa an sami wani
kwakkawaran sabani ba. Domin a tarihi a kuma iya tsawon lokacin da sarki sabitu yayi yana mulki
wannan tsohon malami ya buga masa kasa sau goma sha uku inda duk ya tabbatar masa da samun
nasarar yaki.
Amma sau daya tak aka sami sabani inda sukayi kare jini biri jini su da Kudawa wannan shine yasa
duk wani abu daya shafi kasar tun daga hangen al'amuran da suka shafi yanayin gari zuwa
albarkatun noma tsohon malamin ne ke bugawa ya sanar da sarki.
Malam dawaye ya dubi allon duban dake dauke da lallausan yashi sannan ya fara zana alkaluman
lissafi na duba yana gogewa lokaci lokaci sai ya daga kansa ya girgiza sannan daga karshe sai ya
dago kai ya dubi sarki yace.
Allah yabaka lafiya da nasara dabarar da kake kokarin yi itace kawai mafita kana son aikawa wani
babban amininka dukiya mai yawa domin ya boyewa ya'yanka ko?
Sarki sabitu ya gyada kai a tausashe tabbas wannan shine nufina
malam dawaye yaci gaba da cewa tabbas wannan dabara ce mai girma domin abayanka waziri
dundunawa tabbas shi zai zama sarki kuma abin bakin ciki zai zamo daga cikin manyan azzaluman
sakarunan da ba'a taba yinsu a kasar nan ba inason kuma ka sani cewa da zarar ka mutu sarauta zata
bar hannun yan gidanku za kuma a cusgunawa yan gidanku da ya'yanka guda biyu hassan da
hussaina wanda daga karshe zai zamanto duk sun fice daga gidan sarautar nan baki daya Allah ya
kara ma nasara wannan shine abinda na gani.

Malam dawaye yayi shiru lokaci guda kuma ya sunkuyar da kai domin ya fahimci cewa hawaye ne
ke zuba kamar ruwa daga idanun sarki sabitu
shi kenan malam dawaye allah ya hada fuskokinmu a Darussalam sarki...


Read / Download KUDI DA MACIJI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album