Join Our WhatsApp Group

SAI NA GA RAHMA SADAU Complete Hausa Novel Document by SAI NA GA RAHMA SADAU


SAI NA GA RAHMA SADAU

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 4737



SAI NA GA RAHMA SADAU

Reading Time: 0 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Imam Abdullahi Usman Bandirawo ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 26.64 kb

File Type: txt

Views: 878+

Download: 127+

Last download: 5 days ago

Description/Story: SAI NA GA RAHMA SADAU
Marubuci
Imam abdullahi usman
Publish by:-http://fb.com/hausaebOoks

SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Sulaiman Ibrahim Azlan
Posts by SHURAIH 99%
Part 1
FARKON LABARIN
.
zaune nake a kofar gida, bisa kan benchi. Yammaci ne
misalin karfe 4 da 'yan mintuna.
Nazari nake gami da tunanin lbrn da zan soma wallafa.
"assalamu alaikum" muryar wani matashi ta katseni,
"wa'alai kassalam" nace gami da dagowa na kalleshi.
"yauwa wlh dama ni bakon kane, nasha wahala kafin in
samu gidanku, wuni nai ina yawo.
Yace dani

na sake dubansa, tabbas duk inda aka je, aka zo
bakauyene, kuma ba bafulatani bane.
"gashi kuma bangane kaba, anya kuwa ni imam din kake
nema ? Na ce dashi.
Ya gyara tsayuwa gami da cewa "tabbas kaidin dai,
wannan me rubuta lbr a yanar gizo, koba nan ne
unguwar matsango ba ?
Ya fada gami da jefamin tambaya.
"maraba da zuwa, tabbas nine, na fada gami da mikewa,
nace muje daga ciki.
Daki na na kaishi, gami da dauko masa ruwa da guntun
abincin rana. Na bashi waje, sai da ya gama sannan na
dawo.
"da farko ina maka barka da zuwa, sannan zanso sanin
kai waye da dalilin zuwanka" nace dashi, dai dai lokacin
da zauna bakin katifa.
Bakon yai ajiyar zuciya gami da cewa " sunana rabi'u
amma anfi sani na da rabe, nazo ne daga kauyen dalli nan
karamar hukumar shira, akwai wani abokina dan
makaranta, da muke kwana daki guda da shi, shi ke
karanta mana lbrn ka, gaskiya muna jin dadi. Yanzu haka
takaici nake da ban iya karatu da rubutu ba, tabbas da
ace na iya, da saina kwace maka dukkan magoya
bayanka, da zarar na rubuta lbr daya.
Nai murmushin rainin wayo gami da cewa "ina maka
barka da zuwa, kuma nayi farin ciki, ashe kaima kana da
ra'ayin rubu2 ?
Ya gyara zama "ai kai dai kawai ka bari, allah ne ya ragewa
aya zaki, yanzu dai ka karkada kunnuwanka, kasha lbrn
soyayyata da rahama sadau.
"comedy kenan, na fada araina, yanzu wannan ba kauyen
har ya isa ya tsara wani lbr ? Jifa tsabar shirme wai shi da
rahama sadau. Amma a zahiri sai nace "inajinka" {ko ba
komai ai zansha nishadi dan lokacin completly ali
artwork na dauke shi}
rabe ko ince rabi'u ya soma da cewa....
¤¤
malam barau da gwoggo tani sune mahaifana, babana
bai da wata sana'a face noma, ita kuwa gwoggo tani
dinkin tabarmar kaba take. Ni ka daine dansu, dagani ba
kowa, hakan yasa suka shagwa6ani, bana kallon kowa da
mutumci duk girmanka yanzu zan maka tijara, in
takaicema lbr ko su iyayen nawa ma ban ganinsu da
daraja. Na dago idanuna na kalle shi cikin mamaki.
"karkai mamaki na bawan allah, su suka raine ni da
hakan, kuma na dau course.
Ya cigaba "shekara ta 18, amma bansan ko bihim ba,
abarma maganar boko kam, dan ko A ban saniba. Wayar
da babana ya siyamin ban cika ta da komai ba, face fina
finai da wakoki gami da fotunan rahama sadau. Dan haka
na taso mai kaunar wannan baiwar allah, awancan
lokacin inason rahama sadau fiye da kowa a duniya....!

Bari in takaita haka, in soma fada maka, musabbabin
lamarin.
Karfe 8 da 'yan mintuna, na fito daga dakina rike da wata
tsohuwar jakata, ba komai ciki face 'yan tsummo kara na.
Mahaifiyata dake fama da wutar dumame ta dago ta
dubeni, "dan baba ina zaka da tarin kaya haka ?
Sai da na gama garkame dakin, na dubeta nace "neman
rahama sadau" a zabure ta dubeni, tuni idanun ta sun
kawo ruwa, "dan baba ka rufa mana asiri, dan allah karka
fada uwa duniya.
"wannan kuma ya rage naki gwoggo, amma yau kwana
sai kano. Nace gami da rarumar 'yar jakata na aza a ka.
"wayyo allah malam na shiga uku. Tafada da karfi
babana ya fito daga daki. a rikice taimar bayani, ya ruga
da gudu da nufin ya taroni.
"kai dan baba" naji yana kwadamin kira a sa'ilin har nayi
nisa, na kusa cimma tasha, na tsaya gami da jiransa.
"wlh baba saina tafi nemanta, ai yanzu da hankali na niba
yaro bane. Nace dashi ina huci.
Mahaifina yana kuka, yana roko na, gami da rikemin
jakata. Akan na hakura da tafiyar nan, amma haka na
fizge jakata har sai da ya fadi, naje tasha na hau motar
azare, daganan na shiga ta zuwa kano, da zumar haduwa
da rahama sadau.
Direban motarmu, ya kure totir, gami da jan motar
aguje.......!
¤¤
port 2 na loading
¤
www.facebook.com/hausaebooks
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Kingboy Isa
Posts by SHURAIH 99%
Part 2
.
motarmu ta shalla kan titi, zakai mutukar razana idan
kaga yadda direban mu yake, jan motar da gudu, kai kace
ba rayukan al'uma bane aciki.
An saukemu a wata tasha, da na mance sunanta,
passingers kowa ya soma sanin inda dare yai masa.
Nima jakata na dauka, gami da mikewa nai gabas, sai da
dai 'yar ubansun tafiya sannan na yanke shawarar yin
tambaya, tunda hausawa sunce matambayi bashi 6ata.
Wani mutumi na hango, akallah zaikai shekaru 28 yazo
gilmawa ta gabana.
"malam dan allah tambaya nake" nace dashi
yaimin kallon banza , gami da cewa "ina jinka" na gyara
tsayuwa na ce "dan allah inane gidan "yan film din
hausa ? Ya dubeni a wulakance gami da cewa "ka gamu

da aiki ai shasha, anan zakai ta gararamba" yana gama
fadin hakan yai tafiyarsa.
Na bishi da idanu gami da jijjiga kai, lokaci guda naji
hajijiya na damuna, sakamakon cikina dake min korafin
yunwa.
Sannu ahankali na bude baki gami da kiran wata yarinya
mai sai da gurasa da ruwansha.
Haka na ci gura sar nan, tana shakata ina korawa da
ruwa.
Nakoma jikin wata inuwa na dan huta. Daga bisani na
kuma daukan jakata, lokacin rana ta take.
"malam dan allah ni bakone, tambaya nake. Na ce da
wani mutumi da nake kyautata zaton zai kai 30.
Ya dubeni cikin sakin fuska " yauwa inajin ka" cikin
kwarin gwiywa nace "wlh ni bako ne, daga jihar bauchi
nazo wajen "yan film ne, ina son ganin RAHAMA SADAU.
Mutumin yazaro idanu gami da yin murmushi cikin farin
ciki yace "alhamdullah, ka godewa allah, tazo gidan sauki,
allah ya takai tama, sunana YASEEN AUWAL". Cikin
zumudi na dubeshi, kana nufin daraktan film din
RARIYA..? Ya jinjina kai gami da yin murmushi, yace
tabbas kuwa "yanzu haka na kai mota ta gareji ne.
"dan allah malam ka taimakeni, dan allah kaimin hanyar
ganinta, wlh dan ita nazo. Nace dashi cikin sigar rarrashi.
Ya dubeni gami da dafa kafadata yace "zan tai ma keka,
kasa aranka kaga PRIANKHA, ni dai kawai bukatata kayar
da dani.
"malam na yarda dakai wlh, nace dashi cikin zumudi.
Nan ya tara mana adai dai ta.
muka shiga, aka kaimu wata unguwa.
Kasan me yaban mamaki imam ? Na jijjiga kaina. yace "
gidan da ya kaini amatsayin gidansa, bawani gd ne na
kuzo, mu gani ba, dan gidan kansilan kauyenmu ma ya
fishi.
Daki dayane ciki da falo, balaifi akwai tv da "yan kujeru a
falon, dakin kuma katifa dayane.
Bandaki ya soma nunamin yace naje nai wanka, yana
zuwa. Na dade ina wankan, daga bisani na fito. Na tarar
da shi zaune, a bakin katifar ga wata kodaddiyar kula a
gabansa.
Da kyar na iya sanya kaya, duk ya kureni da wasu
idanuwansa, niko ba sabawa nai ba. Ya sani agaba sai da
naci abincin.
Daga nan hira muka dingayi, yana bani lbrn wuyar da
suka sha a shooting din RARIYA, nayi mamaki da wani
abokinsa ya kawo masa ziyara, naji yana kiransa NURA
AJI DADI, amma banda halin tambaya.
Da daddare an kawo wuta, tun kusan 8 ya kunna mana
kallo, anan yake sanar dani cewa RAHAMA SADAU taje
daukar wani film za suy kwana 6 su dawo.
Ni kuma na yarda.
Da daddare muna kwance....!

Rabe yana zuwa nan ya fashe da kuka, na dago gami da
kallonsa cikin kaduwa nace meya faru? Ya jijjiga kai gami
da share kwalla yace..... Ashe....!
¤¤¤
page na loarding
¤
¤
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Dedicated to Jidda Abdullahi Usman
Posts by SHURAIH 99%
Part 3
.
rabe ya tsai da hawayen dake gudana a idanuwan sa, yace
ashe..! Mutumin nan yaudarata yai, mutumin banza ne,
fasiki, macuci, ji nai ya sanya hannun sa a al'aurata...!
"Innalillahi shine abinda na fada cikin tashin hankali, nace
ya aka kare ?
Rabe ya jijjiga kayi gami da share wasu hawaye, lokaci
guda wasu suka biyo baya.
Muryarsa adashe yaci gaba, "haka inaji, ina gani, ba barci
nake ba, ya karishi wasan sa dani...!
Rabe na zuwa nan ya kuma fashewa da kuka, na matso
kusa dashi gami da dafashi, ina mai bashi hakuri.
Ya cigaba da bani lbr, "imam bani da mafita a wannan
lokaci, sabida a wannan lokaci idan nai wani yunkuri,
komai zai iya faruwa. Da gari yawaye har kusan 7 bai
tashi daga bacci ba, cikin sanda na hada na dau jakata,
gami da ficewa daga gidan, wani kuka ne, ya su6ucemin
lokacin da na tuna abinda wannan tsinannen bawan allah
yaimin.
Na dubi rabe gami da cewa "ba yaseen auwal din bane ba
kenan?
Ya dubeni cikin takaici, "haba imam yakake tambayar
abinda ka sani ? Kaima kasan kawai ya yaudareni ne ya
cuceni.
Nai tsam, dani dama tunda ya soma bani lbrn na gano
wannan mutumin 6atagari ne, baida nasaba da'yan
wasan hausa.
Inajin ka malam rabi'u nace dashi.
Ya cigaba "jiki na yana rawa, na gaggauta barin layin, sai
da na danyi nisa, na sami waje na zauna gami da soma
risgar kuka, hawaye nata kwarara a idanuwa na.
"malam tun dazu nazo wucewa, na tarar da kai kana ta
kuka lafiya ? Wani matashi da nake zaton zai kai 20
yaimin wannan tambaya.
Na dago da jajayen idanuwana, na kalleshi, koba komai
ina bukatar taima ko.
"dan allah ka fadamin damuwarka, musulmi dan uwan
musulmi ne, kuma daga gani kai bakone" yace dani cikin
sigar lallashi.

Nan take na juye masa lbr na, da duk wani abu da yafaru
dani.
Ya tausayamin sosai, sannan ya dora da cewar " wancan
gidan ba gidan mutanen arziki bane, an dade dama ana
zarginsu da naiman juna, allah ya kyauta. Idan bazaka
damu ba, kabiyoni muje wajen uwargijiyata, wata
matace mai saida abinci, nasan bazaka samu matsala ba,
inyaso kadan zauna na wani lokaci kafin ka ta samma
komawa gida, tunda kaga ga yanayin da ake ciki.
Nan nabi wannan bawan allah, ya tara mana adaidaita
muka nufi kasuwa, domin dama siyayya zaiyowa ogarsa.
Nikam duk da wannan bala'i da nagani, ina nan da kudiri
na na SAI NAGA RAHAMA SADAU.
A hanyarmu ta zuwa wurin abincin nasu, yake shaidamin
sunansa ali, asali shi almajiri ne, tun yana yaro ya 6ige da
yiwa wannan mata aiki. Acewarsa yunwa ce tasa shi
guduwa da makaranta, kuma an kawo shi tun yana
kankani ne, zuwa yanzu malamin nasu ya mace, shekaru
12 da suka gabata, kuma bai san garinsu ba, dan haka
uwani mai abinci itace uwarsa da ubansa, dan tai masa
abinda iyayen nasa basu masa ba. Acewar sa kenan.
"rabe zakaji dadin gurin mu, dan akwai wata kawata a
wajen, itama mayyar rahama sadauce, zuwa yanzu
sunanta ya tashi daga hanne ya koma SADAU, dan haka
zaka samu bayanai da dama awajenta. Alin keta koromin
wannan bayani, dai dai lokacin da adai daitan keta tsala
gudu, gaskiya wajen nasu da nisa na fada araina.
" alokuta da dama nakanji haushin, HANNE SADAU idan
naji ta fiye maganar wannan fitsararrar yarinya rahama.
Nai murmushi cikin zolaya nace, "ba'a zagin sadau a
wajena" yaduben cikin raha yace "SAI KAGA RAHAMA
SADAU"
murmushi kawai nayi.
Wurin abincin nasu wajen garine, rumface sai dakuna
langa langa, guda uku. Mai adai dai ta ya sauke mu, gami
da dire kayan har harabar wajen, gayyar doyace da
shinkafa gami da sauran tarkace.
Wata siririyar matashiya na gani, wanda ko kadan bata
more mayin bilicin ba, domin ita da taima 6ata mata
fuska yai, ta zama 2 kala. Tana zaune tana tsintar wake.
Ga iyayen tukwane guda uku a murhu.
Wata gajeriya mummuna, mai mici mici idanu, tafi to
daga cikin rumfar ta nufomu.
"shegen sama ka dawo ne? take fada dai lokacin da ta
karaso garemu.
"Eh wlh hajiya" aliyu ya bata amsa
"ina ka samo wannan dan shilan kuma ? Ko shima ya fito
ne ? Matar ta kuma tambayarsa.
wannan siririyar matashiyar dubo yadda muke aka ron
farko gami da watsamin harara....!
¤¤
page 4 is loading

¤
¤
journalist din kune.
SAI NA GA RAHMA SADAU
Na IMAM ABDULLAHI USMAN
Gajeren labari
Posts by SHURAIH 99%
Part 4
.
ali ya dubi uwani mai abinci gami da cewa "hajja rahama
sadau ya fito nema.
Hajja tai wata shu'umar dariya irin tasu, ta gogaggun 'yan
duniya tace "da haka muka soma, wai kuturu yaga mai
kyasbi. Ta dubeni na dan lokaci tace da aliyu "shegen kai
shi da kinka, in mun gama aiki, sai inzo in dora masa
karatu"
ali ya dubeni gami da cewa "muje ciki" na bishi a baya.
Har yanzu wannan siririya mai kama da kilaki tana
watsamin harara.
Wata macacciyar katifa ce a ya she, cikin dakin sai
tabarma guda daya gami da dan tarkace da ba'a rasaba.
"nan ne dakina, anan zamu zauna, har zuwa lokacin da
zakai gaba" shegen sama ko ince ali ke koromin wannan
bayani, bayan mun shige dakin langa langar madaidaici.
Na ajiye jakata gefe gami da tsayuwa ina karewa tsohon
langa langan idanu.
"Ka zauna mana, muryar ali ta katseni, zamanai a kan
tabarmar dake yashe.
Da karfi aka banko kofar cikin fusata, hajja ce tana huci,
ta malmalo ashariya "banason shirme shege, kazo kai
aiki, ka wani kule dakin dan uwarka, musamu mu
kammala, bayan kasan kwanan zancen. tafada tana zare
mici micin idanuwanta, bakinta har kumfa yake tsabar
masifa.
Shikam shegen sama, tun lokacin da ta soma sirfa masifa
jikinsa ke ta rawa. A gaggauce ya fice tabi bayansa.
Nai ajiyar zuciya gami da kwantawa kan katifar, sai
alokacin na tuna mahaifiyata gwoggo tani, alkah sarki
mace mai sanyi maras hayaniya, baki na ta6e gami da
runtse idanuwa, bacci yai awon gaba dani.
Bansan iya lokacin da na dauka ina bacci ba, na dai farka
naga wata madaidaiciyar kula a gabana da ruwan sha a
kofi.
Wata matashi wanda itama nake kyautata zaton
ma'aikaciyar hajjace, ta shiga ba tare da sallama ba. Sai
dai ga dukkan alamu tasan yadda ake bilicin tunda ita
kam yo kodar da ita, kamar yadda take bida, duk da
kasancewar ta kakkaura.
"hajja tace kaci abinci, ga ruwansha, zata zo kuy magana.
Tana gama fadin hakan ta nufi kofar ficewa, "dan allah
ina aliyu ? Na jefe ta da wannan tambayar "wai shegen
sama kake tambaya ? Ai ya tafi naiman arziki" matashiyar

tace dani, dai dai lokacin da ta isa bakin kofa ?
"naiman arziki ? Na tambayeta cikin mamaki
ta kalleni gami da yin wani shu'umin murmushi tace "kar
ka damu, zaka gane da zarar hajja tazo, ta dora maka
karatu" tana gama fadin hakan tai ficewarta.
Zulumi tare da juyayi suka ziyarci kwanyata, daga bisani
na bude abincin domin ina fada da "yar gusau {tofa
katsinawa} shinkafa jalofiya harda namanta tana kamshi.
Banyi wasa da abincin nan ba, haka na ringa sanya shi
acikina, sai da na koshi. Na kora da ruwa.
Na koma na kwanta, inajin hayaniyar mutane a wajen,
daga bisani hayaniyar ta dan ragu wajejen mangariba.
Hajjo ta shigo dakin wannan karon wani leshine ajikinta,
harda "yar kwalliyarta, sai dai abinda na fahimta ga hajjo
shine, ita muninta na musamman ne domin da tai
kwalliyar maimakon tai kyan gani, a'a sai kwalliyar ta fito
mata da asirin siririn kan da ke gareta.
Ta karaso ta zauna gefen katifar da nake daf dani, har
munajin numfashin juna.
Tai ajiyar zuciya gami da cewa, "ka saki jikin ka dan shila,
dama irin ku nake nema, kana da kyau ka godewa allah
tun daga nan ya baka jari. Abinci muke sai dawa kamar
yadda ka gani anan, a kallah munkai mu 13, duk a
karkashina suke, ciki kuwa harda mai mana gadin wajen
nan, sakamakon da daddare mukam fita naiman abin
rufawa juna asiri, kasan dai wannan abincin da muke
bazai kwashe mana duk bukatun mu ba, kasan rai da buri
muna son tara arziki.
Yanzu haka shegen sama {ali} hajiyarsa tazo ta daukeshi,
taimin balance idan ya kare kwanaki biyun zatai masa
nasa balance din, kayar da ka zauna damu, ka tara arziki,
ita da kanta RAHAMA SADAU zata nemeka. Yadda kake da
kyan nan, bazan saka a kasuwa ba, zan barwa kaina kai ni
zannayima ka balance din, a duk lokacin da kaimin...


Read / Download SAI NA GA RAHMA SADAU

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album