Join Our WhatsApp Group

LINZAMIN SHAIDAN Complete Hausa Novel Document by LINZAMIN SHAIDAN


LINZAMIN SHAIDAN

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 26368



LINZAMIN SHAIDAN

Reading Time: 2 Hours

Added On: 27, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 140.86 kb

File Type: txt

Views: 900+

Download: 280+

Last download: 2 days ago

Description/Story: LINZAMIN SHAIDAN
Complet
(M) Nazir Adam Salih
Made by Shuraih Usman
@http://fb.com/hausaebooks

INZAMIN SHAIDAN-01
.
A cikin irin ni'imantattun
ranakun nan ne ma'abota lullumi
da sassanyar iska mai sa ka
manta kofar shiga gidanku ne
na fito daga namu gidan sanye
da 'yar fingila-fingilar riga ta
shan iska zuwa kofar gida. In da
na fito din gindin katangar wani
gida ne in da duk sa'ar da rana
tayi yamma sai inuwar katangar
ta mamaye gurin musamman ma
idan akace karfe biyar na yamma
ta dan gota. Fitowa ke da wuya
sai na hangi benci babu kowa a
kai dan haka sai na nufi inda
bencin yake da niyyar na zauna
domin taren daddadar iskar
dake busowa daga gabas zuwa
yamma. Kai bani kadai ba hatta kananan kwari da kudaje kokarin kai kansu suke ga
inuwar dan hutawa. A dai-dai
lokacin ne to naji anyi min sallama.
'Amin wa'alaikumussalam''
Na amsa game da juyawa
lokaci guda. Wani dan saurayi ne
mai fuskar matsorata ke yi min
sallamar. Saurayin dogo ne mai
dogon baki, sanye da doguwar
riga fara, tashi ka fiye naci sanye
a dogon kansa. Shekarunsa zasu
iya yin dai-dai da nawa, to amma
me yiwuwa na bashi koda
watanni ne.
''Kaine Nas?'' Ya

tambaya kai tsaye ba tare da ya
'bata lokaci ba. ''Na'am, ni ne''.
Nace dashi ina dubansa. ''Zauna
mana'' Nace dashi gami da nuna
masa bencin da hannuna.
Sannan lokaci guda sai na zauna
ina mai sauraron ya zauna, domin tabbas nasan wannan
shima ire-iren abokaina ne
makaranta da suka saba kawo min ziyara lokaci-lokaci. ''Nas ba
zama ne ya kawo ni ba''. Yace da
ni gami da sakin wani
busashshen murmushinsa na
kure adaka. ''Wani kakana ne
yake son magana da kai''. Kusan
dakiku biyar ban amsa ba,
domin kallonsa kawai nake yi ina
mai kokwanto anya kuwa naji
abin da ya fada dai-dai?
''Kakanka fa kace?''. Saurayin ya
gyad'a kai. ''Kwarai kuwa''. Yace
da ni. ''Yanzun nan yake son
ganinka, dan tun jiya nake zuwa
nemanka Allah bai sa na same ka
ba sai yanzu''. Na dubeshi cikin
mamaki. ''A ina kakan naka yake?''. Saurayin yayi murmushi
yace. ''Kada ka damu. Shin baka san
SIDI MAI JAKA bane?''. Na dube shi cikin mamaki a karo na
biyu nace. ''A'a nasan shi mana.
Dama kai jikansa ne? Amma ba'a
unguwar nan kake da zama ba
ko?''. ''Kwarai kuwa, shekaran
jiya na dawo daga Kaduna. Kuma
ni makarancin littattafanka ne, to
shine nazo dasu da yawa, sai shi
kakan nawa ya gani shine yake
tambayata wai me muke ji idan
mun karanta littattafan nan? A take a gurin na ce dashi ya saurara na
karanta masa yaji. To shine shekaran jiya da daddare na
karanta masa littafinka
''NAIRA DA KWABO''
ina gama karantawa
sai na ga ya fara kuka, shine to
ya takura akan wai dole sai na
kirawo masa kai, domin an sha
bashi labarin cewa akwai wani
yaro marubuci a unguwar nan''.
.
''Tashi mu tafi''. Nace da shi. Zaka
yi mamakin dalilin tashi na lokaci
guda. To amma zuwan nawa
gurin dattijon shine tushen duk
wani labari da zaka ji daga baki

na. Lokacin da muka 'karasa
zauren gidan dattijon na zaune akan kujerar katako yana jiran
zuwanmu. Tun kafin mu karaso
gareshi ya fara yi min
murmushin marhabun. Kallo
daya nayi masa sai naji ina kaunar dattijon a raina. To saidai kuma bana kaunar irin warin
daudar dake fita daga jikinsa. Ga
dukkan alamu dattijo Sidi Mai Jaka ya dade rabon da suyi
musabaha da sabulu. Dattijon
dogo ne fari, haka nan kansa fari
fat da furfura, gami da dogon
farin gemu, wanda ya dace da
doguwar fuskarsa, gami da
fashin goshin dake fuskarsa.
Kayan da suke jikin dattijon duk
tsummokara ne yagaggu, haka
nan kuma idan kayi nazarin irin
kayan dake jikinsa zaka fara
tunanin lallai ba irin kayan wannan karni da muke ciki
bane. Dattijon sanye yake da
farin tabarau, me yiwuwa na kara gani ne, shekarunsa zasu
kai saba'in da doriya a duniya. Hakan shi ya sani matukar
mamaki sa'ar daya dube ni yana
murmushi, domin duk kusan
hakoransa suna nan ras a bakinsa babu wanda ya fita.
''Sannu da zuwa samari''. Yace
da ni. Sannan sai ya dubi saurayin daya tura kirana. ''Dan
bamu guri zamu gana''. Saurayin
yayi biyayya ya fice daga zauren
kai tsaye.
A dai-dai lokacin ne ni kuma ke
zaune ina ta faman nazarin zauren gidan. Babu wani abin ku
zo ku gani, komai irin na da can ne. Yanayin ginin, rufinsa kai duk
wani abu dake gidan na wancan
'karnin ne.
.
"Naji dadin zuwanka
Nas. Ko da yake na san yanzu
cike kake da mamaki?''
.
''Kwarai kuwa Baba''. Nace dashi cikin
ladabi.
.
"Sunana Sidi mai Jaka, kamar kuma yadda me yiwuwa
zaka sami labari a gurin iyayenka,
ni ba asalin dan garin nan bane, zuwa nayi.... Koda yake sa'ar nan
ba a haifeku ba....'' Na gyada kaina gami da murmushi. ''Jiya wannan jikan nawa dana tura
kiranka ya karanta min wani
labarinka daya tayar mini da hankali
Shine to yanzu na 'kiraka
muyi cinikin wani labarin idan
zaka siya....''. Maganar ta girgiza

ni. To amma sai na dauka wasa
yake, dan haka sai kawai nayi
dariya ban amsa masa ba. Sidi
mai Jaka ya muskuta a hankali
yana dubana, sannan sai ya cire
tabaron dake fuskarsa yana
kallona kamar wanda ke
tsammanin zai sami wani abu a
ciki, dan lokaci sai ya mai da shi
idanunsa yace. ''Kamar yadda
kake gani a yanzu ni talaka ne,
ina bukatar taimako, don haka in kana so to sayi na sayar maka
wani labari da me yiwuwa ya isa
ka maida shi littafi''. Na dago a
hankali na dubeshi a karo na
farko nace. ''Baba da gaske
kake?''. Sidi mai Jaka yayi dariya,
sannan yace. ''Haba dana, zan
'kira ka har nan na fada maka
'karya ne ? Ai kasan dattijo
kamata baya fadan 'karya, domin
ita
KARYA LINZAMIN SHAI'DAN ce.
.
Kai dai in kana so ka saurareni
da kyau mu gani daga nan zuwa
sallar magariba.....kona zo maka
da labarin da me yiwuwa da
kanka zaka ga ya dace ka biyani''.
Na muskuta cikin mamaki da
'kosawa, domin tuni ya fara
gundurata. Dan na sha jin irin
labarin tsofaffun nan rikitattu
wanda gigin tsufa ke sa su
shirme. ''Yanzu in ba haka ba
wannan tsoho wane labari yake
da shi da har ya isa a saya?''.
Nace cikin zuciyata ina kokarin
mikewa tsaye. To amma banyi
hakan ba don gudun kada yace
na raina shi ko kuma na
muzantashi a matsayinsa na dan
adam. ''Kada ka gudu 'dana,
nasan abin da kake tunani, kana
tsammanin bani da hankali ko? To
ba haka bane, saurareni da kyau,
idan kaga labarin da zan baka
duk bata lokaci ne to sai ka tashi
kayi tafiyarka''. Dattijo Sidi mai
Jaka yayi shiru yana dubana. Ga
mamakina sai na ga 'kwalla ta
fara tsartu tsakanin fuskarsa da

gilashinsa. 'Dana da ace na iya
rubutu da bazan taba baka
labarin nan ba, da ni zan rubuta
kayana, don nasan ko nawa zan
sayar maka shi a yanzu to ba riba
sai faduwa''. Na dubi agogon
dake hannuna, a dai-dai sa'ar da dattijon yayi shiru. Ina da
alkawari da wasu samari da
zasu zo nemana da karfe shida
na yammacin, dan haka sai nace
da shi. ''Baba ka bari to da
magari ba sai na dawo ka.....''
Ya katseni sa'ar da ya daga
busassun hannayensa sama.
''Nas kada kayi gajen
hakuri......kada ka raina ni...abin
da nake so da kai shine, bani
mintuna goma kawai na fara
kwararo maka labarin, idan kaji
duk shirme ne bai birgeka ba,
babu kuma ma'ana, to nayi maka
uzuri kana iya tafiya abin ka''.
Banso ba domin nasan kawai
'bata lokaci zan yi.... To amma tun
da yace minti goma.... To minti
goma ba su kasheni....''
''Ina sauraronka to''. Na ce da shi ina
duban farin gemunsa. ''Yauwa
Nas, ko kai fa..... Sai kace ba
marubuci ba...?'' Sannan sai ya
fara da cewa.
.
''Shekaru Ashirin
Da Biyar Da Suka Shude.....''
LINZAMIN SHAIDAN-02
.
'Nas ina son kadauki zuciyarka ka maida ita
can baya kimanin shekaru kusan
ashirin da biyar ke nan da suka
wuce Haka nan Nas
ina son ka aiyana cikin zuciyarka
cewa a cikin wani babban
asibitin kashi na kudi kake''
''Duk nayi abin da kace'' Nace da
shi. Har yanzu tunani nakeyi
tababbe ne amma shi ko a
jikinsa, sai kawai ya daga kansa
yaci gaba.
''A cikin wani katon asibiti ne
zarurrukan labarin suka fara
'kulluwa. Tun goshin magariba
na ranar garin ya yi baki kikkirin,

domin a cikin watan Augusta ne,
dan haka da zarar gari ya bata
rai sai kaji an saki ruwa babu ko
wani 'kwakkwaran gargadi. To
amma sabanin sauran ranaku a
wannan ranar tun magariba ake
ta rugugin aradu kamar sararin
samaniyar zata fashe gida biyu,
har zuwa karfe tara na dare ana
barazanar amma ba'a saki ruwan
saman ba sai tara da minti
ashirin na dare. Da yawa daga
cikin ma'aikatan dake a sibitin
basu ji dadin ranar ba, domin
wasu ruwa yayi musu dukan
tsiya akan hanyarsu ta zuwa
gurin aiki, domin karbar
wadanda suke aiki tun karfe
biyu na rana har zuwa tara na
dare. Ya yin da kuma suma
wadanda ke tafiya gidajensu a
lokacin suka ci dan banzan
dukan ruwa, musamman ma
wadanda gidajensu ba'a cikin
harabar asibitin suke ba.
Ba'a taba asibitin da ya tara
'kwararrun likitoci ba irin
wannan duk fadin kasar nan
haka nan matsala in dai ta kashi
ce a jikin mutum koda kashin
dagargajewa ya yi in dai yana
gurin bai zube ba to za'a mayar
da shi su hadashi guri guda
tamkar yadda kake hada
zararrukan labarinka guri guda
ka kawo karshen matsalar. Ba a
dade ba sai ruwan ya fara karfi.
Hakan ce ma tasa da yawa daga
cikin ma'aikatan da ke aiki a
asibitin masu motoci sai tsayawa
suka yi a ranar suna jiran ruwan
ya tsagaita kafin su tafi duk
kuwa da cewa lokacin tashinsu
ya yi.
.
A dai-dai wannan lokacin
da ake sheka uban ruwan ne
wata Malamar asibiti ta shigo
farfajiyar cikin sauri dauke da
lema a hannunta, amma duk a
banza domin ruwan ya gama
jikata jagaf. Ta ratso ta tsakanin

shuke-shuken furannin da suka
yi sahu-sahu ko ina a farfajiyar
asibitin ta nufi inda dakin
'karbar 'yan hatsari na gaggawa
yake, inda kuma anan ne yake
aiki. ''Daman ke na ke jira
wallahi.... Nasan ruwan nan ne
ya sa ki makara. Dubi fa har
kusan tara da rabi.....''. Wata
Malamar asibiti da ke tsaye jikin
wata 'kofa ta gilashi tace. ''Haba
Falmata, duk gaggawarki ki dai ai
kya bari ruwan na ya dan
tsagaita..... Baki ga fa nima da
yadda na 'karaso ba.....''
''A'a Asabe wallahi tafiya zan yi..... Kin
ga yarinyata yanzu nasan tana
nan tana cin uban kuka a gida.....
Ni kam tafiya zanyi...... Allah ma
yasa daman tun safe dana ga
alamun hadari na zo da rigar
ruwa...''. Cikin 'yan mintuna sai
ga Falmata sanye da rigar ruwa.
''To Allah bamu alheri Asabe, ni
na tafi''. Da haka ta fice ta shiga
cikin feshin ruwan. Asabe ta bita
da kallo har sai da ta bace a cikin
'kananan 'kwayoyin ruwan.
Sannan sai ta saki tsaki ta juya
zuwa cikin dakin gaggawa da
majinyata ke kwance.
.
Dakin dogo ne, mai tsayin gaske,
akwai dan bangare da aka ware
a cikin dakin ta hanyar katange
gurin da gilashi, wanda anan ne
Malaman Asibitin da ke kula da
marasa lafiyar suke zama. Sauran
gurin kuma gadaje ne sama da
guda goma sha biyar. Kusan
kowannensu dauke yake da
majinyata ana kara musu ruwa
kafin a shiga dasu dakin da
za'ayi musu aiki. Wasu
hannayensu a rugurguje, wasu
'kafa a balle, ko kuma 'kafafuma gaba daya, wasu ko suna ihu
suna ''Wayyo Kwankwasonsu!''
Kai abin babu kyan gani Nas.
Asabe ta fara bin gadajen da
majinyatan suke kwakkwance
tana dubansu gami da yi musu
allurori. Koda yake banda Asabe

ma akwai wasu (Nurses) din
guda biyu wadanda duk suma
anan suke aiki. 'Daya bahaushiya
ce, dayan kuma namiji ne
inyamuri, sunansa Peter.
.
Aka saki wata katuwar aradu
wacce ruguginta ya girgiza
dakin. Haka nan kuma yasa
Asabe dan jinkirtawa da tsinin
allura a hannunta dan gudun
kada taje tayi ba'a dai-dai ba. Dan
hakika tsawar ta girgiza
ta......don in har akwai abu daya
da ta tsana a duniya tsawa ce.
A dai-dai lokacin ne 'kofar dakin
majinyatan ta bude, sannan suka
fara shigowa daya na bin daya
a baya, kai kace tafiyar
tururruwa. Su hudu ne suka
shiga dakin sanye da bakaken
kwat-kwat da wando. Ko
wannensu sanye da bakin
tabarau, fuskokinsu kuma duk
bakakene masu gizo da duzuduzu din gashin baki kamar
ciyawa, in ka dauke daya daga
cikinsu wanda shi fari ne
matashi, baifi shekarunka ba Nas.
Lokacin da suka shigo dakin tafiya suke irin ta fatalwa. in har haka ya dace na fada, domin su
kansu Malaman Asibitin basu san
da zuwansu ba sai kawai jin
numfashinsu suka yi a kansu.
Asabe ce ta fara juyowa sannan
sai sauran Malaman Asibitin
suma suka juyo cikin mamaki.
Mutanen hudu suka dubi
Malaman Asibitin da fuskar
katako. Nan da nan sai mamakin
Malaman Asibitin ya fara
narkewa zuwa fargaba.
''Me.....kuke so....?''. Asabe tace
dasu cikin 'karfin hali. Ko kusa ko
alama basu yi mata kama da
mutanen da ta saba gani ba.
Farin saurayin dake cikinsu ya
dube ta da kyau, sannan sai yace,
cikin wata irin sassanyar murya.
''Marar lafiya muka kawo muku''.
Kusan minti biyu Malaman
Asibitin basu tanka ba. Can dai
daga 'karshe Asabe tace. ''Yana

ina?''. ''Yana cikin mota yana
zubar da jini''. Saurayin yace da
ita. Lokaci guda kuma ya dubi
sauran mutanen uku dake tsaye
kamar gumaka idanuwansu a
boye cikin tabarau yace. ''Ku
shigo musu da shi su tsaida
jinin''. Tun kafin ya rufe bakinsa
suka juya suka sake ficewa cikin
uban ruwan da ake shekawa,
sannan sai saurayin ya juyo ya
dubi Asabe ga mamakinta sai
taga yayi mata murmushi yace.
''Kada ku damu da shirunsu,
haka nan Allah yayi su kamar
kurame''. In har murmushin da
ya yiwa Asabe farin ciki, to wuka
akan wuyanka ma zata iya saka
ka farin ciki.
.
''Yal......yalla6ai kun
san fa bama karbar mutum indai
hadari ne sai anzo da 'yan
sanda''. Peter yace gami da share
gumi. Ko shakka babu yasan
wadannan mutanen basu da
cikakkiyar gaskiya. ''Kada ka
damu dan samari, ko nawa ne
zamu iya biyanku, amma ku
mance da maganar 'yan sanda
duk wannan bata lokaci ne kuma
bata taso ba. Majinyacin namu
yaji rauni sosai, harbinsa akayi a
'kafa''. Yayi shiru yana duban
fuskokinsu gami da jin dadi
cikin zuciyarsa dan ganin duk
sun gama tsurewa. Shi kuwa
yasan alkawari ne ko a mutu ko
ayi rai sai an cirewa dan uwan
nasu alburushin da suka sami
matsugunni a cinyarsa, domin
mutumin yana da matukar
muhimmanci a gurinsu, in ba
dan haka ma ba da tuni sun
harbe dan banza. Yace cikin
zuciyarsa. ''Yallabai ai dole ne sai
an kawo 'yan sanda.....da'' Peter
ya sake cewa bakinsa na rawa.
''Shut up!''. Mutumin ya buga
masa tsawa. ''Mun san cewa mafi
yawan asibitocin kudi kukan
'karbi 'yan hadari ko da kuwa ba

a zo da jami'an tsaro ba....shi
yasa muka zo nan, don haka dole
ne na maimaita, ''DOLE NE! KU
MAGANCE SHI KO KUNA SO KO
BAKWA SO, KAJI KO!!''.
.
Peter yaji kamar 'kafafunsa ba za
su iya daukarsa ba don haka sai
ya nemi wata kujerar roba dake
nan kusa da shi ya zauna.
''Kayi hakuri.....yallabai''.
Yace dashi muryarsa na rawa.
''Ya kuma rage naka'' Mutumin
yace, sannan sai ya harde
hannayensa a 'kirjinsa yana
kallonsu da fuskar katako. Duk fa
abin nan da ake yi a kunnen
wasu kadan daga cikin
majinyatan masu rangwamen
jigata ake yi, to amma duk da
hakan bata hana wadanda ke
shan azaba ci gaba da
gurnaninsu ba, domin su bama a
cikin hankalinsu suke ba.
Asabe ta rikice tsantsa dan ji take
kamar zata fadi. Har yanzu
ruwan ake ta tafkawa kamar da
bakin teku. 'Kofar dkin ta bude
da 'karfin gaske, sannan
mutanen uku suka shigo dauke
da wani sunyi cali-cali, mutumin
sai ihu yake yana cewa, ''Wayyo
'kafata!''.
''Ku dorashi a can''. Asabe tace
da su gami da nuna musu gado.
Zuciyarta sai wasi-wasi take, ko
shakka bata yi tasan duk yadda
akayi mutanen nan basu da
gaskiya. Me yiwuwa ma 'yan
fashi ne, domin in ba haka ba
yaya zasu kawo mutum an
harbeshi kuma su hana a 'kirawo
'yan sanda. ''Wayyo!....oh!
......ah!.....'kafata......''
Tunaninta ya
katse sakamakon ihun marar
dadin ji dake fita daga
makogwaron mutumin. ''Ku
tsayar masa da jinin mana kun
tsaya sai kallonmu kuke kamar
wasu aljanu.... Ko baku taba
ganin mutane bane!!''. 'Daya

daga cikin ba'ka'ken mutanen
nan ya buga musu tsawa. ''Sai an
'kirawo likita''. Asabe tace tana
dubansu a tsorace zuciyarta nata
wasi-wasin yadda zata sami
hanyar tsira daga hannun
wadannan masu kama da iblisai.
''A ina likitan yake?''. Saurayin
fari ya tambayeta. ''Mace ce....
Anan baya gidanta yake.....sai dai
ko in buga mata waya....''.
Mutanen hudu suka dubi juna
suna zance da idanu, domin a
yanzu sun fahimci cewa ashe
duk cikin wadanda suka ritsa
din ma babu likita....in kuwa har
suna so a cire masa alburusan da
ke 'kafarsa to dole ne sai sun
sami likita. ''Ku tsaida masa
jinin..'' 'Daya daga cikin mutanen
yace...
INZAMIN SHAIDAN-03
.
In kuwa har
suna so a cire masa alburusan da
ke kafarsa to dole ne sai sun
sami likita Ku tsaida masa
jinin. Daya daga cikin mutanen
yace gami da nuna daya
Malamar Asibitin da kuma Peter
da hannunsa ''Ke kuma 'yar
tsakuwa muje ki kirawo likitan
naga ai kina da kan talfon a nan
ma ko?' Yace yana mai nuni da
kan wayar dake kan tebur a cikin
dan zagayayyen gilashin da aka
ajiye a matsayin Ofis Mutumin da
suka zo dashi...


Read / Download LINZAMIN SHAIDAN

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album