Join Our WhatsApp Group

KAZAR KARFI Complete Hausa Novel Document by KAZAR KARFI


KAZAR KARFI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 24077



KAZAR KARFI

Reading Time: 2 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 129.93 kb

File Type: txt

Views: 754+

Download: 179+

Last download: 16 hours ago

Description/Story: KAZAR KARFI--> 01
.
SHAFI'U DAUDA GIWA
.
AMADU BALIGI" shine shugaban
matasan dake tashar dan
amarya" tun a shekarun baya
kafin siyasa ta kankama shine
saurayin dake fada aji a hanyoyi
da dama
Alal misali Idan aikin gayya ta
taso za'a gyara hanyoyin
kauyensu a fitar da magudanan
ruwa Amadu baligi shine akan
gaba wajen gayyato matasa da
karuwai ako ina da kuma nemo
makada wadanda zasu dinga
gabzar ganguna suna karawa
ma'aikatan kwarin gwiwar kartar
kasa suna ihu da kirari
.
Idan kaka tayi aka kawar da amfanin gona aka kawo gida
Amadu baligi shine yake fita ya
nemo mawaka da 'yan rawa suzo kauyensu su kafa dandali a
wani gidan danni wanda idan dare yayi aka tayar da karamin
jannareto aka fara waka da cashewa samarin dake lardina na nesa dana kusa sukan zo su biya
kudi su shiga suyi kallo da lika
kudi kuma idan aka gama waka
da safe komai aka samu Amadu
baligi yake tarawa ya sallami
mawakin da yaransa" sannan
sauran abinda ya ragu kuma nasa ne
Idan mutane suka fara gajiya da
wake-wake sai Amadu baligi ya
kafa gidan dambe ko kokawa
wanda anfi samun alkairi don
kuwa masu kudin kauyen sukan
sa gasar babura da shanu gaduk
jarumin da yayi kisa mai kyau"
kuma kome aka samu ta hannun
Amadu baligi yake biyowa"
.
Sanin kowa ne cewar duk wata
sabuwar karuwar da tazo tashar
dan amarya" dole ne Amadu
baligi yasan da zuwanta" a
matsayinsa na shugaban matasa"
ko kuma shugaban 'yan iska"
kamar yadda dattawan dake da
mutunci a kauyen suke kiransa"
.
Amadu baligi gwani ne shi kanshi
wajen dambe da kokawa" yasha
fita wasa har xuwa jamhuriyar
nijar kuma yayi kaye da kisa ba
sau daya ko sau biyu ba" Ganin yafi samun alheri a gida wajen
jagorancin duk wani aikin tabara
ya sashi ya kwance wa hannu sa damara ya dawo yana shugabantar matasa duk abinda yace shi akeyi a kauyen"
.
"To amma tun sanda siyasa ta
kankama sai Amadu baligi ya fara samun fada a wajen
shugabannin kauyukka musamman ciyamomi da
kansiloli Idan shugaba yazo
kamfen dole ya fara neman Amadu baligi don kuwa shine
muryar matasa Idan akayi nasara aka kafa gwamnati" Amadu baligi yana samun alheri"
don kuwa yana samun kyautar
kudi da sabbin babura akai-akai
wasu suna cewa duk wata yana
samun kudi a wajen 'yan siyasa fiye da naira dubu dari da
hamsin
mutane idan sukaji haka zasuyi zaton duk a fadin lardin tashar dan amarya babu wani matashi
mai kudin Amadu baligi to amma a zahiri abin ba haka yake ba don kuwa sau da yawa
sutura takan yankewa saurayin
kuma yasha kwana bashi da ko
anini saiya roki na karin kumallo
a wajen mutane
.
Tayaya kuwa kudi zasu zaunawa
Amadu baligi bayan kullum idan
ya zauna a tamfal din caca tun
safe baya tashi sai dare yayi" su
kunna fitila karuwansa shida a
garin" kuma kowacce saiya bata
kudin cefane kullum tunda dai ya hanasu mu'amala da
kowanni namiji shiyasa kudi basa rayuwa a hannunsa kamar yadda wuta bata rayuwa cikin
ruwa
.
Amadu ya samo sunansa na BALIGI ne tun yana yaro dan
shekara sha biyu" wannan ya
samo asali ne a zamanin da yke
shiga cikin manyan kartin dake
zuwa kamun gafiya a kauyen wadanda basa yadda yara suna
binsu sai Baligai tsararrakinsu"
.
Babu irin dukan da Amadu
baisha ba a wajen azzaluman
kartin kauyen wadanda suke
korarshi ya koma gida idan ya
biyo su shi kuma yana sake binsu
A ranar da wani a cikinsu yace
dashi basa zuwa kamun gafiya
tare da yara sai "BALIGAI" sai
Amadu yace dashi-
"Nima ai "BALIGI" Ne!
Fadar hakan ya bawa kowa dariya a cikin kartin kuma tun
daga lokacin suka 'yantashi ya
rika binsu din kamun gafiya yana
yi msu kananan aikace-aikace"
dangin debo ruwa a rafi da
kuma iza wutar gasa nama idan
sunyi sa'ar kama abubuwan da
suka fita nema a ramukan da ke
a bayan garin
Kamar yadda kowanne mutum a
duniya yake da ka'idojin aikinsa
ko sana'arsa haka shima Amadu
baligi yana da tasa dokar wacce
ta dade takai shekara da shekaru a kauyensu babu wanda ya isa ya karyata ko kuma ba'a
riga an samu wanda zai karyata ba har yanxu"
.
Dokar ita ce yana maraba da duk wata karuwa wacce ta sauka a garin komai tsufanta da
muninta" kamar yadda yasha
fada" Amma bai yarda wata
"GILLI" tazo ta zauna ba kuma bai yarda wani yazo da ita garin ya ajiyeta ba"
.
Sau da yawa wadanda basa
cikin harkar bariki dole ne sai nayi musu dogon bayani kafin su iya bambance tsakanin
"KARUWA" da "GILLI"
.
KARUWAI-: Sune wadanda suke
fitowa yawon dandi bayan sun taba yin aure sun fito"
.
GILLI-: Bata taba yin aure ba" yawancinsu yara ne kanana
wadanda shekarunsu ya kama daga goma sha hudu zuwa sha biyar" wadanda suke kangarewa su fito
shalli da sharholiya"
sune yawanci akan samu a rabe
tare da iyayen dakin su mata agidan karuwai saboda idonsu bai riga ya bude sun san yadda
rayuwar bariki take ba da yadda
ake samun kudi a wajen maza ba
.
Sune yawanci suke bin mawaka
sunayi musu rawa" 'yan kallo
suna manna musu kudi a goshi
Idan an tashi wasa a kawo kudin
abinci a basu su kama gabansu
ba tare da sun tsaya tunanin ko
nawa mawakin ya samu a
dalilinsu ba su dai ko ina dare yayi musu nan ne gidan su
kuma anan zasu kwana kamar
kajin turawa ne Idan mai kula
dasu ya mutu kowa nasu ne indai zai basu abinci ya faranta musu rai
.
Sune wadanda yarintar soyayyar
gida bata gama sakinsu ba ko
mutum bashi da kudi sai su like
mishi wani kuma yazo da kudi su zageshi ta uwa da uba irin wannan rashin hankali da rashin sanin mutuncin sana'a yake
yawan hadasu fada da manyan
karuwan dake rike dasu
wadanda suke basu wurin zama idan kaje gidan mata kaga
karuwa ta kama gilli tana lakada
mata duka kamar zata kasheta"
Ko kuma kaga ta debo kayanta ta
watso mata su waje tana zaginta to karka tsaya wahalar
tambayar kowa yadda akayi don
kuwa dalilin bai wuce kuruciyar
da gillolin suke yi ba wajen rashin ba masu kudi hadin kai
suna bin yara kanana wadanda basu da komai sai kodadden
wando da fasashen takalmi"
.
"To amma shi a bangaren Amadu
baligi ba rashin hankali ko yarintar gilla yasa baya son su zo kasarsa ba" haka kawai yaji baya
so yaga karamar yarinya ta fito
dandi duk da lalacewarsa baya
so yaga yara sun lalace" su dai
manya tunda sun riga sun gama
lalacewa to gwara abin ya tsaya a
kansu amma banda yara"
Amadu baligi kakkarfa ne baki
kuma mummuna wanda ko a jajayen idanunsa kawai aka tsaya ya isa ya tsorata duk wata mace
tabi umarninsa indai tana so ta zauna lafiya a kasarsa bai taba rabuwa da singileti ba da ita
yake kwana da ita yake tashi
kuma komai sanyi komai zafi
"To ko a lokacin da akayi bikinsa
a watannin baya tun ranar daurin auren har zuwa tashin
bikin da singileti ya gama angwancinsa ya shiga dakin
amaryarsa ba abinda ya dameshi"
.
Ana kan haka ne a yammacin
wata ranar lahadi yaje 'yar bajau
suna caca shi da mutanensa"
wani yaronsa mai suna "DAMMA"
yazo ya sameshi yace dashi
"Sarki kayi bakuwa fa a kasarka" Amadu baligi ya tambayeshi yana kallon kartar dake a hannunsa ba
tare da ya dago kanshi ba"
"wacece?"
Damma yayi murmushin
takadarancin abinda zai fa" wata GILLI ce" ina jin ba'a dade
da yayeta a nono ba"
Amadi baligi ya dago kanshi ya
kalli Damma yace dashi"
"kaje kace da ita ni sarki nace ta
gaggauta barin kasata tun kafin
inzo in sameta" kace da ita ta koma gida tun kafin muyi ido
biyu" "Damma ya koma ba'a jima ba ya
dawo wajen cacar yace da Amadu baligi sarki tace wai ba inda zataje ko
kasheta za'ayi
tun kafin Damma yakai karshe
Amadu baligi ya watsar da kartar
dake a hannunsa ya tashi cikin
sauri"
"muje inga kowacce 'yar iskar
yarinya ce wannan"
Damma ya takewa sarki baligi
baya suka nufi gidan karuwan
dake gefen garin nesa kadan da
gidajen matan aure"
.
*SUNANTA TALATU*
Sekarunta zasu iya zama kodai tsakanin goma sha hudu zuwa goma sha shida" tana
sanye da kodaddiyar atamfa mai
ruwan toka" wacce zaninta yasha yagewa anayi masa faci daga kasa"
Gajeriya ce" dirarra mai nagari
wacce kai tsaye bazai yiwu mutum ya yanke hukuncin fara
ya cancanta a kirata ko kuma baka ba
A yanayin fatarta fara ce" to amma wani abu da ya lullube
fatarta dake kama da rashin kwanciyar hankali da yunwa
shiya dabirta sakamakon da
mutum zai iya bata a kamaninta to koma dai me yake damunta
bazai yiwu ace da ita mummuna ce ba ko ba komai tana da
faffadar fuska wacce ke dauke da
manyan idanu da kuma dan
madaidaicin bakinta" tana da saurin fara'a da murmushi
bazata iya jure hada ido da mutum tsawon dakika uku ba ba tare data fara yi masa murmushi ba koda kuwa bata
taba ganin mutum ba
tana dauke da leda gari yayi zapi"
kuma ganin yadda ledar ta koshi fal kamar xata yage xa'a
fahimci kayanta ta zubo a ciki"
suturu da kuma 'yan abubuwan
da baza'a rasa ba" koda kuwa
mudubi ne da hoda"
.
"Tun shigowarta garin da dan
acaba ya kawota gidan matan"
saita sami gefe guda tayi tsaye
bata yiwa kowa magana ba" tana
kallon duk abubuwan dake kaiwa da komowa babu wacce
ta kalleta sau biyu a cikin tsofaffin karuwan dake a gidan" don kuwa sun san kowacece da
ganinta GILLI ce kuma ba zama zatayi ba" sunsan da SARKI
BALIGI yayi ido biyu da ita zai
koreta tabar garin kota shirya
kobata shirya ba"
Jefi-jefi mazan da basu nema da
mace a gidan sukanje inda take
suyi mata magana" amma bata
saki jiki da kowa ba" to dama dai
a haka suke zuwa da dan kullin kayansu suyi shiru ayita magana suna ji su wuni a zaune a waje
daya suna jin kunyar magana da
kowa" da an basu kwana uku zasu goge su zama 'yan gari"
wanda ya tafi ya barsu a haka da
sati ya zagayo inyazo zai samesu suna shan taba suna
rawa" don kuwa suna tare da
manyan shaidanu wadanda zasu
bude musu idanu su nuna musu bambancin rayuwar gida da kuma
RAYUWAR BARIKI
.
TALATU...KAZAR KARFI--> 02
.
TALATU tayi shiru taki magana
wannan bashi ne zaisa ace bazata shiga layi ba Da haka
suke farawa su dukkansu sai sun
gama ganin tafiyar ruwan kowa
daya bayan daya sannan zasu
fara yin tasu carar suma talatu tana nan tsaye a jikin
katangar gidan karuwan inda bai
gama rushewa ba ta sauyawa
ledar hannun kenan daga dama zuwa hagu saiga Amadu baligi ya shigo gidan a fusace tare da
Damma
.
Da shigowarsa gidan ya dubi
talatu tana tsaye dauke da
ledarta suka hada ido da ita
dashi tayi masa murmushi don
kuwa halinta ne dazun nan da
Damma yazo yace ta gudu kafin
sarki ya ganta tace bazata tafi
ba don haka yanzu ga sarkin yazo ya sameta Bayan sun gama kallon juna ita
da Baligi ba tare da jin tsoron
jajayen idanunsa ba da kuma
bakar fuskarsa wacce ke cike da
gargada da kwazazzaban duka a
wajen dambe sai yace da ita.
"ke bakiji sakona bane?"
talatu tace dashi cikin ladabi"
"wannan ya fada mini" talatu tace dashi"
"Indai bazaku barni in zauna anan
garin ba gwara ku kasheni in
huta da bakin cikin da ya sameni"
.
Maimakon baligi yaji tausayinta
sai yayi dariya kadan ya girgiza
kai" irin wannan tatsuniyar daba
bakin sabbin shigowa ya dade
yana jin irinsu" to amma karya
suke yi" su dukansu babu wacce zata so a tambayeta ta fadi
gaskiyar abinda ya fito da ita ta baro gida" komai zasu fada idan aka bincika za'a samu ba gaskiya
bane" wata zatazo tace iyayenta
ne suka mutu" marainiya ce babu
wanda yake kulawa da ita don
dai aji tausayinta a amsheta a bata wajen zama"
Wata zatace mijinta ne ya saketa"
kuma yake nemanta zai kasheta"
don haka tazo don buyar masa"
wata zatace auren dole za'ayi
mata kuma bata son wanda za'a
bata shiyasa ta gudu to amma fa zaiyi wahala idan aka bincika labarin ya zama gaskiya shiyasa
ga wanda ya saba da ganinsu indai bakuwar karuwa ce ko "GILLI" komai zasu fada ba abin
yadda bane kuma wanda ya tsaya bata lokacinsa akansu ya
tausaya musu shine babban shashasha a wajensu
.
Baligi ya kebe yarinyar a gepe
guda ya bar Damma a baya suka
koma kusa da wani sabon daki
da ake ginawa a gidan wanda ya
ruguje a kwanakin baya"
Daga inda suke tsaye a faffadan
gidan suna iya jin komai na
surutan da wasu karuwai hudu
suke yi tare da wani mai tsire a
tire wanda ya saba zuwa gidan
talla kullum"
.
"Talatu ta mayar da hankalinta
akan hayaniyar da matan sukeyi
da mai tsiren" tana so tayi
murmushi ga alama rayuwar matan yana birgeta" ganin yadda
suke da 'yancin yin komai babu
mai hanasu" A lokacin da take
kallon nasu ne Amadu baligi ya
fara yi mata magana"
"Ina so ki bude kunnenki da
kyau" kiji abinda zan fada maki"
Ya kara kausasa muryarsa da
yaga kamar bashi take saurare ba"
"Sunana Amadu Baligi"
Yace da ita
"Nasan wata kila kin taba jin labarina a garinku
To idan ma baki taba ji ba yanzun nan zan fada maki don
kisan koni wanene!"
Nine shugaban duk wani takadari dake a wannan gari
namu" An bani wannan sarautar
kuma na Amsheta da hannu bibbiyu"
Baligi ya saurara" sannan yace da
yarinyar
"Nasan abinda ya kawoki wannan garin" bana bukatar
saikin fada min komai" to amma abinda nakeso dake
shine" ki koma gida wajen iyayenki ki rokesu gafara su
yafe miki...
Zaman bariki ba
zaman arxiki bane" muma da
kika ganmu nan a ciki don kawai abin ya zame mana bala'i ne"
amma ba dadi muke ji ba don
haka kiyi sauri ki koma yanzu-yanzun nan tun kafin dare yayi miki" banason ganinki anan!
"Talatu ta juya tana sauraron kalaman wannan kato wanda
batasan koshi wanene ba a gidan"
Amma dai da ganin yadda kowa
yake tsoronsa ga alama shine
sarki kamar yadda ya fada"
batayi masa magana ba tadai
girgiza kanta sau daya alamar ta
gamsu da bayaninshi
.
"Duk wadannan matan da kike
gani anan indai zaki tambayesu
su fada maki gaskiya" na tabbata
wannan magana dana fada maki
irinta suma zamu fada miki duk
lokacin da mace ta gudu tabar
iyayenta cikin fushi da takaici" to
duk inda zata shiga a duniya"
kuma kome zata zama bazata
taba gamawa da duniya lafiya
ba idan kuma kina jin karya
nake yi kiyi tunani a zuciyarki ki
gani" wacce mace ce ta taba yin
yawon dandi da sharholiya tayi
karshe mai kyau ?
Indai ba dainawa tayi ta zama
mutuniyar kirki ba tayi aure toki
zura mara ido kina nan zaki ga
yadda karshenta zaizo a wulakance
kada kiyi la'akari da yadda manyan karuwai suke gina
gidaje suke shiga manyan motoci suke dinka suturun kece
raini suna kashe kudi kiyi zaton
zasu dauwama a haka bazasu
taba dauwama ba wahalar da suke gudu har suka zabi yin karuwanci tana nan biye da su
kuma komai dadewa indai suna a cikin harkar sai sun wulakanta
wannan dole ne muda muke
cikin wannan harka mun san
illolinta ciki da waje shiyasa nake fada miki don ke ma ki
sani ki koma garinku tun kafin
ma ki fara har wani ya bata ki a banza
TO" akwai alamar taurin kai a
muryarta a karshe Amadu baligi
yace da ita
"kada kiyi tunanin idan kinki
komawa gida kin canza gari
bazan sani ba duk inda kika
shiga a fadin kasar nan indai
yawon dandi zakiyi dole ne in
sami labarinki kuma ko ina kika
shiga saina biki na kamaki
saboda haka ki koma gida ni SARKI BALIGI na haramta miki
dandi a duniya kuma dole ne kibi Umarnina ko kina so ko bakya so
.
Bayan Amadu baligi ya gama jan kunnen talatu sai ya tambayeta
"Kina da kudin motar komawa garinku ?
ta girgiza kai ba tare da tayi magana ba alamar bata da
kudin mota
A wanne gari kike ?
talatu tace a sanyaye
A Tsaunin Yalwa
.
Shugaban matasa uban baligai
ya ciro kudi a aljihunsa ya bata
naira dari biyar takarda daya
ki hau babur da mota ki koma
gida kada ki sake fitowa kome
iyayenki zasu miki kiyi hakuri
kada ki sake guduwa zamanki a
gida komai wuya yafi fitowa dandi
Amadu baligi ya tafi ya barta tana
tsaye tana wasi-wasi dauke da ledarta gari yayi zafi
ya samu Damma yana jiranshi a
kusa da kofar gidan wacce ta fadi tuntuni" komai dare idan mutum yazo gidan zai iya
shigowa ba doka" babu birki"
"Nayi mata fada" zata koma
garinsu yanzun nan Damma" na bata kudin mota
.
Damma yace-
"Allah ya taimaki Uban Baligai"
karatan biyu suka fice daga gidan karuwan" suka kama
hanyar komawa dandalin cacar"
suna tafiya suna hira" talatu tana
nan a tsaye tana kallon karuwan"
har zuwa lokacin da wata takadara ta daukarwa mai...


Read / Download KAZAR KARFI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album