Join Our WhatsApp Group

TA LEKO TA KOMA Complete Hausa Novel Document by TA LEKO TA KOMA


TA LEKO TA KOMA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36419



TA LEKO TA KOMA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 26, Jul 2023

Author: Nazir Adam Salih ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 191.56 kb

File Type: txt

Views: 624+

Download: 306+

Last download: 5 days ago

Description/Story: TA LEKO TA KOMA complet
Na Nazir Adam Salih
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) nazir adam Salih


La'sar sakaliya mai dauke da lillimin gajimare, tana daya
daga cikin lokutan da haidar ya fi so a rayuwarsa. Sau da
yawa bai yi niyyar fita yawo ba, idan ya ga irin wannan
yanayin sai ya ji ba a bin da yake so kamar ya fita ya dan
zaga. Wajen yawon sa bai wuce bakin kogin kwara. Kogin
wani dan tattaki ne kadan daga unguwarsu. Hakika yana
matukar son kyakkyawan yanayi irin wannan musamman
ma a bakin kogin kwara.
To a cikin daya daga irin wannan yammacin ne, bayan
Haidar ya yi wanka ya shirya sannan ya dauko dan
karamin littafinsa na Hausa wanda idan ya je bakin kogin
shakatawa zai karanta, sai ya ji dirin mota a kofar gida
"Yauwa, shi kenan ma." Ya ce cikin zuciyarsa, a zatonsa
abokinsa ne Aliyu ya biyo zai dauke shi. Saboda sau da
yawa tare suke fita a duk lokacin da damar hakan ta
samu. Nan da nan ya fito tsakar gidan da sauri, a daidai
lokacin da suka ci karo da mahaifiyarsa Aishat.
"Ina za ka je?" Ta tambaye shi.
"Baba ina son za mu fita bakin kogi shakatawa ne"
ya ce da ita cikin ladabi.
"Ga Aliyu canma a waje yana jirana"
"Kada ku sake magariba ta yi muku a can, ka san babanka
idan ya dawo da wuri bai gan ka ba zai iya tambayar inda
ka shiga."
"Ba zan dade ba"
yace da ita, a daidai lokacin da ya nufi kofar gidan da
sauri cikin kaguwa. Ya yi mutukar kaduwa lokacin da ya
isa kofar ya tarar ba Aliyu ne ke jiran sa ba. Mai jiran nasa
na tsaye a gaban motar tana kada dan mukullin motar.
Tana sanye da duguwar riga baka, kanta lullube da farin
gyale fuskarta boye a bayan bakin tabarau irin na mata,
wanda ya yi matukar fito da kyakkyawan dogon hancinta
mai kama da biro.
Duguwa ce fara, mai dara-daran fararen idanu kamar
kankara, tana da yawan gashin gira, da kuma dan
madaidaicin bakinta mai dauke da kyawawan jerin
hakora. A cikinsu akwai wata yar wushirya dake dauke
hankalin maza kamar yadda mayen karfe ke jan karfe,
surayya kenan, ko kuma kamar yadda suka ce ko kuma
suka sake mata suna "Monika" daya daga cikin mata ajin
farko, na masu zaman kansu. Zai yi wuya ka gane hakan
idan ba an fada maka ba.
Abin mamaki idan ka gane cewa a boye a bayan
kyakkyawar surar surayya monika, akwai matsanancin
halayyar son dukiya, da son rayuwa a duniya, monika
tana cin kudi kamar yadda wuta ke cin auguda. Daya
daga cikin abubuwan da monika ke kashe kudinta akai shi
ne sutura da abin hawa, akwai jita-jitan dake cewa duk
wata sai ta sauya mota, an ce kuma wai tana da suturori
masu tsadar gaske sama da dari biyu, wan abu muhimmi
kuma dake tattare da surayya monika shi ne, ko a cikin
yan bariki, ba kowane ke iya harka da ita ba, sai masu
dukiyar gaske, sau da yawa surayya tasha karya kananan
yan barikin masu kudi. Duk da yake surayya ba ta fi
shekara daya da rabi da fitowa yawan bariki ba, hakan bai
hana masu hannu da shuni da dama sanin ta ba. Abu
daya samar yan bariki suka tabbatarwa kansu, shi ne
surayya monika tafi karfinsu, lallai kam tafi karfinsu, in ka
dauke mutum daya wato Haidar, so! Wannan kalma ta so
tana tattare da abin al'ajabi, haka kawai rana daya duk
irin mummunan son abin duniya na monika, sai ga shi ta
hakura, tana bin saurayin da bai kai ko yaronta ba wai
tana son sa.
Wannan ba karamin koma baya ba ne ga surayya,
musamman ma idan aka yi la'akari da irin ajinta a gurin
alhazan birni, sai ga shi lokaci guda ajin ya zube a gaban
dan matashin saurayi Haidar, wanda shi a gurinsa
surayya kamar karfen kafa ce, ba wai donba tada kyau
ba, a'a, shi dai kawai ba ya kaunar ta ne.
Cikin ziyarorin da ta kawo masa a kalla guda ashirin,
kullum sai ya gargade ta da ta dauke kafarta daga
gidansu, domin tuni mutanen unguwa sun fara
maganganu, wanda daga karshe har maganar ta kai
kunnen iyayensa.
"Haba Haidar" Babarsa ta ce da shi. "Yanzu ace ka rasa
wacce za ka aura sai karuwa, marar mutunci? Kada ka
sake to abin ya yi nisa ka ji ko? Ko da da kanta ta zo ta
same ka, kar ka sake ka kulata shashar banza, ta gaji ta
daina zuwa"
A cikin yawa-yawan zuwan da surayya ke yi wajen Haidar
tuni har mahaifiyar Haidar ta fara fada mata bakaken
maganganu. "Kada ki bata min da kin ji ko shi ba dan iska
ba ne irinki" Ita kuma Surayya, sai ta sunkuyar da kai kasa
sannan ta ce da ita cikin ladabi "Ki yi hakuri baba wallahi
dan babu yadda zan yi na daina son sa ne don haka nake
zuwa"
Kamar kullum yauma sai ga shi ta zo ta ga abin begenta
Haidar "Anya kuwa wannan alaka zata ci gaba tsakanin
Haidar da Surayya yarinyar da yan bariki suke kira da
monika? Abin duk ya fara ne kamar wasa, kuma shi ne ya
yi sanadiyyar rikicin da ya shafi jama'a da dama dake
unguwar Banasariyya, wacce ke dab da gabar kogin
kwara.
Gaidar ya dubi Surayya sannan ya ce cikin fushi "Me ya
dawo da ke kuma marar zuciya? Ba na ce kar ki kara
dawo min nan ba!"
"Haba Haidar... Kai yanzu kana ganin ya dace ka yi min
irin wannan karbar?" ta ce da shi cikin sassanyar murya
mai dauke da tsananin takaici
.
Har yanzu dan mukullin motar na hannunta, sai dai ta
daina kada shi, tana tsaye ne kawai tana kallon sa.
.
NAZIR ADAM SALIH (NAS)
"HAIDAR." Ta yi kiran sunansa. Bai amsa ba,
sai ta ce "Haidar so ne ya sa ni zubar da ajina a gabanka,
kuma ya sani jure wulakancin da kake yi min kai da
mahaifiyarka."
.
"Shin daman zuwa ki ka yi ki yi min rashin kunya, ko
kuwa kin zo ne ki rama wulakancin da babar tawa ta ke yi
miki."
"ko kusa ba haka ba ne masoyina." Ta ce da shi, "Abin da
ya kawo ni shi ne shaukin ganin ka da kuma so da bege
da ke addabar zuciyata. Wallahi Haidar duk wulakancin
da za ka yi min ban damu ba, in dai har zan saka a idona
to burina ya cika."
"To ya isa haka uwar dadin baki." Haidar ya ce da ita. "Ni
zan tafi, amma ina son na gargade ki da cewa daga yau
kar ki sake zuwa nan, wannan shi ne na karshe, in kuma
ba so ki ke ranki ya baci ba to ki dauki shawarata. Ke
yanzu Surayya ki na ganin ya dace ace dan mutunci kama
ta ya aure ki? Kin san fa duk garin nan babu wanda bai
san ke yar bariki ba ce, haba!"
"Haidar na roke ka don girman Manzo ka daina yi min
kallon mutuniyar banza, wallahi da ka san yadda nake
masifar begen ka da ba ka fada min wadannan
maganganu ba, na san matsayina a gurin mutanen garin
nan, amma bai kamata a ce kai wanda nake kauna na ajje
komai da komai saboda kai, amma ka ke kira na marar
mutunci ba, haba Haidar, don Allah ka daina tunanin abin
da ya wuce, ka san cewa kuwa tun lokacin da son ka ya
mamaye zuciyata na ji duk na tsani kaina, kuma duk wata
sha'awar bariki ta fita daga raina." Ta dan yi shiru sannan
ta dan matso ta durkusa a gabansa ta dafa takalmansa,
sannan ta ci gaba, "Haidar ka yi min rai ka ceci rayuwata,
Haidar ka daina ƙi na, in ma ba za ka so ni ba to ka daina
wulakanta ni, in dai ba so kake ciwon zuciya ya kashe ni
ba. Na yi ma alkawarin in har za ka aure ni daga yau ba
zan sake yawon bariki ba, daman ba nisa na yi ba, son
zuciya ne ya kai ni, amma na tuba Haidar na daina, ba
don komai ba sai don begen ka da kaunar ka. Wayyo
masoyina Haidar ka so ni ka kuma aure ni, kai ma za ka
sami lada a wurin Ubangiji," Sannan hawaye ya fara
kwarara akan kyawawan kumatunta.
Haidar ya dube ta sai ya ji ya dada tsanar ta ba don komai
ba sai don shi a wurinsa kamar mayaudariya ce, wacce ke
son ta yaudare shi ta kuma hada shi da iyayensa.
.
"Sai dai ki auri dan iska kamar ki amma ba ni ba, ki je can
ki yaudari alhazan birninki masu katon ciki." Sannan ya
zare takalminsa daga karkashin hannayenta da ke dafe,
bai ko kara duban ta ba sai kawai ya nufi hanyar da za ta
kai shi bakin kogi.
Surayya ta tashi jiki a sanyaye cikin takaici hawaye na
kwarara a idonta, a dai-dai lokacin ne taji kamar motsi a
bayanta, ta juya ta fuskanci kofar gidan su Haidar,
mahaifiyar Haidar na tsaye a kofar gidan sanye da
shudiyar doguwar riga wadda ta dora da zanen atamfa a
kanta, "Nan da nan Surayya ta durkusa har kasa da niyyar
ta gaida ita "Karma ki durkusa munafuka" mahaifiyar
Haidar ta ce, "ni zaki nunawa bariki bace min da gani
mutuniyar banza, ni ɗana ba dan iska bane.
.
****** ******* *******
.
Ya aka yi, yaya kuma aka yi, ita kanta ba ta san yadda aka
yi ta tuko kanta zuwa gida ba, tana isowa katon gidan
maigadinta Ma'azu, ya bude mata kofa, sannan ya daga
hannunsa, cikin girmamawa, bata kalle shi ba, abin ya
bashi mamaki, domin ga al'adarta, duk lokacin da ya
bude ma ta kofa, sai ta tsaya ta tambaye shi ko akwai
wanda ya zo neman ta, in kuma sako ne ma aka ajiye ta
karba, sabanin haka sai ga shi yau ba ta ko kalle shi ba.
Ta yi fakin da motar a gurin na musamman da aka tanada
don ajje motoci, sannan ta fito ta rufe kofar motar da
karfi, hakan shi ya tsorata yan tsuntsayen da ke wasa
akan fulawowin da ke farfajiyar gidan suka tashi sama far
suna rera wakoki cikin yarensu. Surayya, monika ta nufi
kyakkyawan farin ginin dake farfajiyar gidan irin ginin
mutanen Sin ne (Chaina) yana da rufin ja da kuma farin
fenti, wanda aka yi masa ado da fenti ruwan kofi, kofofin
da kuma tagogin gidan na mulmulallen jan katako ne,
mai sheki, shi ma yana dauke da launin kasa-kasa.
Monika, ta nufi kofar dakin tana takawa a hankali, iskar
dake kadawa na wasa da gashin kanta mai sheki, wanda
ya bayyana a sarari a sakamakon zamewa da lillibin kanta
ya yi, ba takuma damu ta maida shi ba. Ta bude dakin
sannan ta shiga tangamemen dakin shakatawar mai
dauke da hadaddun kujeru sama da ashirin da biyar,
kujerun na shudin karen miski ne, hakan shi ya basu
damar dacewa da farin fentin dake dakin sun yi wa
sararin dakin kuri, sau da yawa idan mutane suka shiga
dakin, kujerun kan tuna musu da majalisar dinkin
duniya.
Tana zuwa ta zarce dakin kwananta kai tsaye ta fada akan
makeken gadon rubda ciki, ta fara kuka
"Wayyo Allah na tuba." Ta ce cikin shasshekar kuka,
"Allah ka cire min son Haidar na huta da azaba, Allah na
tuba na daina aikin sabo daga yau, Allah kasa ya so ni ko
kuma sonsa ya fita daga zuciyata, sannan ta yi ajiyar
zuciya ta kifa kanta akan matashin kan dake kan gadon,
sannan ta fara tunani, har saida zuciyarta ta zama tas
babu komai sai barci daya maye gurbin wajen.............
.
Biyar da rabi saura minti daya ta farka daga
nannauyan barcin da take yi, tana tashi ta nufi
bandaki ta kwarara ruwan sanyi ajikinta, sannan ta sake
kwalliya, yadin boyal ruwan hoda ta zaba daga cikin
daruruwan kayan da ke cikin akwatinta,
sannan ta dubi kanta a cikin tangamemen madubin dake
fuskantarta, zane da rigar boyal din sun yi
matukar dacewa da ita, komai ya yi in ka dauke
idanunta da suka kukkumbura saboda kuka da ta sha,
sannan ta fito ta rufe dakin ta nufi wajen
motarta, tana tunani, "Allah ka taimake ni." Ta ce cikin
zuciyarta. Bata hakura ba, duk da wulakancin da Haidar
ya yi mata har yanzu tana da karfin
gwiwar cewa mai yiyuwa idan ta yi sauri ta same
shi a bakin kogin zai iya kallon ta da idon rahama.
Tafiyar minti goma ta kawo ta bakin kogin, samari
da yan mata suna ta sheke ayarsu, akwai kuma yan
yawon bude ido turawa suna dauke-dauken hotunansu a
gabar kogin, Haidar na zaune dab da wasu samari guda
uku, su da yan matansu suna hira, rabin kafarsa a ruwa,
rabin jikinsa kuma awaje, dukkansu suna zaune ne a
bakin gabar kogin, suna wasa da ruwa, da kafafunsu.
"Salamu alaikum." Haidar ya shaida muryarta lokaci guda
kuma ya
hada girar sama da ta kasa, sannan cikin
kakkausar murya ya ce da ita "Uwar naci sai da ki ka
dawo? Wato baki ji gargadina ba ko? Kai na hadu da
jaraba! Ke ba ki da hankali ne, dole ne soyayya ko dole ne
sai nayi soyayya da ke? Kin jarabce ni kamar bala'i, don
Allah kin ga malama ki daina tsaya min akai gara ki san
inda dare ya yi miki tun wuri, tun kafin ma ki sa mutane
su fara tunanin ko ni ma lalatacce ne kamar ki." ya dan yi
shiru yana maida numfashinsa, sannan yace "Ko ba ki ji
ba Monika nacacciya, kin zame min karfen kafa, don
Allah ki ba ni sarari na sha iska, ni
wallahi abin da nake tsoro ma shi ne kar mutane su ganni
da ke suna yi min kallon dan iska kamar ki."
.
"Ka iya kira na komai ma." SURAYYA monika ta
katse shi, "Dama ka samu, don ganin ina son ka shi ya sa
kake walakanta ni yadda ka ga dama, amma ka tuna fa, in
za ka so mutum ka so shi kaɗan ba can ba, idan ma za ka
ki mutum ka kishi kaɗan." Ta dan saurara. "Haidar!" ta
sake kiran sunansa, tuni
kwalla ta cika idonta, "Na roke ka Haidar don
girman mahaifanka ka duba irin son da nake maka, ka
daina kirana yar iska." Jin haka shi ya sa Haidar mikewa
tsaye, "Ina son ki
bace min da gani, ya ce muryarsa na rawa, "Ni na ce
bana sonki amma kin nace min har kin sa iyayena sun
fara tsana ta, ke yanzu Monika kina ganin ya dace na aure
ki a matsayinki na karuwa?"
Surayya ta fara kuka, ta durkusa gwiwa biyu a gabansa,
bayanta na fuskantar ruwan kogin
sannan ta fara rokonsa, "Haba Haidar kai ma abinda za ka
ce da ni kenan, ka rasa abin da zaka Kira ni sai karuwa?"
.
"To na yi miki karya ne?" Ya ce a fusace "Bace min da
gani, marar kunyar karya." Sannan ya kama gyalanta ya yi
sama da ita ya sharara mata mari, ba tayi ko gezau ba.
"Ni ka mara Haidar?" Ta ce...


Read / Download TA LEKO TA KOMA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album