Join Our WhatsApp Group

MUTUNCI KO SO Complete Hausa Novel Document by MUTUNCI KO SO


MUTUNCI KO SO

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 3601MUTUNCI KO SO

Reading Time: 0 Hours

Added On: 10, Oct 2023

Author: Yusuf Abdullahi A Jibaga ,

Ebook Compiler : Shuraihu Usman

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 19.51 kb

File Type: txt

Views: 755+

Download: 91+

Last download: 2 days ago

Description/Story: This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
MUTUNCI KO SO

Cikin hanzari na fito daga dakina, na doshi
mahaifiyata, bayan na durkusa na gaisheta
nace mata zan tafi wurin aiki, tace yau ba
zaka tsaya ka karya ba? nace mata Wallahi
na makara ne sauri nake, tace to Allah ya
kiyaye hanya.

Kai tsaye wurin babur dina na nufa, na
tadashi kenan zan fita naji mahaifiyata ta
kwalamin kira, na sauko na isa wurinta tace
dama na manta jiya Safina ta zo nemanka
bata sameka ba, shine ta bayar da wannan
tace a baka, ta mikomin wata leda. Saboda
saurin da nake, ban ko tsaya duba ledar ba,
aljihu na sakata na kara gaba.
Koda na isa ofis na tarar aiki ya tarar min
saboda haka ban tsaya komai ba aiki kawai
na fara. Ban tuna da ban karya ba sai misalin
11:00 sannan na bukaci abinci, bayan naje
na siyo abinci naci, sannan fa na tuna da
ledar da Safina ta bayar a bani, hannu na
saka a aljihuna na dauko ledar na kwanceta,

alewa ce na gani tare da katin gayyata, gefe
daya kuma wata gajeruwar wasika ce. Kai
tsaye wasikar na fara karantawa kamar
haka:salam yusuf ya ka ke? nayi ta nemanka a
waya, ban samu kuma naje gida ban sameka
ba, dama katin daurin aurena ne nake so na
baka, kuma kayi hakuri kar ka ga ban sanar
da kai da wuri ba, Wallahi daurin aure ba
zata yai min, sai na jika..
Hankalina ba karamin tashi yayi ba da na
karanta wasikar, zuciyata kasa gasgata
abinda idanuwana suka karanta a jikin
wasikar ta yi. Katin na dauko na karanta.
Sunan Safina na gani baro-baro a matsayin
amaryar da za'a daurawa aure, nan da sati,
nafi sama da rabin sa'a gangar jikina tana
kokowa da hankalina kafin daga bisani su
samu yin sulhu a tsakaninsu, kai tsaye
wayata na dauko na kira lambarta said dai
nayi rashin sa'a wayar a kashe take.
Mantawa nayi gaba daya da aikin da ke
gabana na shiga karanta wasikar jaki
(tunani), ya za'a yi Safina tayi min haka? Me
nayi mata? Ashe dama ba sona ne take ba
yaudarata ne ta ke? In kuwa haka ne tabbas
Safina ta kai makura a yaudara, gefe daya
kuma sai na fara ganin wautar kaina, ya aka
yi na amince da cewar tana so? Ya aka yi na
sakankance cewar ita ce matar da zan aura,
ya aka yi na saka tunanin gina tubalin
rayuwata da ita a zuciya, lallai na zama
sakarai na karshe da na hakikance cewar
Safina ba ta da wani a zuciyarta bayan ni.

Da wadannan sake-saken na bata sauran
lokacin da nake da shi a ofis.
Tashina daga ofis kai tsaye gidansu Safina
na wuce, na sami yaro na aika yai kiranta,
sai ga ta ta fito da fara'arta, dama yusuf kai
ne? Shi ne ka tsaya a waje ka ki shigowa, mu
shiga ciki mana, tana yin maganar ne ba tare
da ta dubi yanayin fuskata ba, lokacin da
idanuwanta suka kai kan fuskata sai ta sha
jinin jikinta, lokaci guda fuskarta ta juye zuwa
damuwa, ta shiga tambayata lafiya?
Gaskiya ce ta yimin yawa lallai yarinyar nan
'yar rainin hankali ce ta yaya zata tambayeni
lafiya, bayan tafi kowa sanin dalilin shiga
yanayin da nake ciki, hasalima ita ce ta
sakani ciki, a zahiri kuma sai na ce mata kina
so ki ce dani baki san dalilin shigata damuwa
ba kenan? Gaskiya Safina kin bani mamaki
ban yi zaton zaki iya yimin haka ba. Cikin
firgici da rashin sanin laifin da tayi ta jehomin
tambaya, me nayi ma yusuf? Haba Safina kar
ki mayar dani karamin yaro mana, yanzu don
Allah Safina ko kunya baki ji? Ki tunkareni da
katin daurin aurenki? haba yusuf meye abin
jin kunya?, a ganina ai abin farin ciki ne a
gareni, abin farin ciki kuwa duk wani
makusanci fada masa ake yi, to meye laifi
don na gaya maka, kina so ki ce min dama
ba sona kike yi ba yaudarata ne kike yi
kenan? Idan kuwa haka ne tabbas kin cika
mayaudariya, haba Safina ina kika kai
soyayyar da muka shafe shekaru muna yi?
Ina kika jingine wannan doguwar alakar da ke
tsakaninmu? Wace makoma kika tanadar wa
wannan alaka, da kuma ni kaina?
A'a yusuf kar ka ce haka, ban yaudareka ba,

ni Wallahi ban yi tsammanin Mutuncin da ke
tsakaninmu a wajenka ya rikide ya koma
soyayya ba, da na san haka da tuni na
fatattaki wannan tunani daga ranka, ni
Wallahi a matsayin dan uwa, Yayana na
daukeka kuma abokin shawarata, ban taba
daukarka a matsayin masoyi ba, kuma ni
kaina na dauka a hakan ka daukeni, haba yusuf
yaushe wani abu wai shi So ya taba
shiga tsakaninmu? Idan har kallona ka ke yi a
matsayin masoyiya, tabbas kai ne ka yaudari
kanka.
Ku biyoni don jin ya ya wannan alakar ta ke,
shin soyayya ce ko kuwa

zanci gaba gobeMUTUNCI KO SO 2
Tun lokacin da na baro gidansu Safina na
sami kaina cikin damuwa mutuka, na shiga
tunane-tunane, in saka wannan, in kwance
wancan, lokaci daya sai kwakwalwata ta
shiga tariyo min abubuwan da suka faru
shekaru uku da suka wuce. Haduwata da
Safina kenan.
A makaranta mu ka hadu, ba zan taba manta
wata ranar talata ina zaune a barifikeshin
bulok (verification block) ina jira malaman da
ke yin barifikeshin su fito domin a yi min
barifikeshin din. Tun daga nesa idanuwa
suka haskomin wata kyakkwar sura, suturce
cikin jar atamfa. A zahirin gaskiya ban taba
ganin halittar da ta yi kyanta ba, jar atamfar
ta yi mutukar fito da kyawun surarta, wankan
tarwada ce, siririya sai dai ba sosai ba, mai
matsakaicin tsawo ce, tana da dara-daran
idanuwa, mamallakiyar doguwar fuska ce,
dauke da madaidaicin baki, hade da dogon
hanci, a takaice dai ko ita ce ta halicci kanta
iyaka kenan, duk na fahimci wannan ne a
kallon da nayi mata wanda bai wuce na
dakika biyar ba.
Ga mamakina sai naga ta tunkaroni, kai
tsaye sallama ta fara yi min tare da gaisuwa,
daga bisa ta jehomin tambaya, don Allah ina
ne barifikeshin bulok? Nan ne, na bata amsa
a takaice, za'a yi maki barifikeshin din ne?
Na tambayeta, eh! Ta bani amsa,
ni kaina shi zan yi, ina jira su fito ne, me zai
hana ki zauna mu jirasu, bata musamin ba ta
samu wuri kusa dani ta zauna, hala a wane
difatimen (depertment) ki ke? Na ci gaba da
jan ta da hira, Computer Science, ta amsa
min, amma yau kika fara zuwa ko? Me yasa
kai min wannan tambayar? A can nake kuma
ban taba ganinki ba sai yau, shi yasa na
tambayeki, eh haka ne gaskiya yau na fara
zuwa, ko ina ma ban sani ba a makarantar
nan, ko wurin da zamu dauki lakca ma ban
sani ba.
Wani farin ciki na ji ya kamani, saboda ganin
na samu damar da zan cusa kaina a wurinta.
Haka dai muka ci gaba da hira har lokacin da
masu barifikeshin suka fito, ta shiga layin
mata, ni kuwa na shiga na maza. An riga
kare mata da kusan minti biyar sannan a ka
karemin, ko da na sauko na sameta tana
jirana, difatimen muka nufa, bayan na nuna
mata duk wasu wurare da ya kamata ta sani.
Washe gari ko da na shiga makaranta na
sameta a aji, rakube ita kadai, kasancewar
kowa bata sani ba a ajin, sai fa ni da muka
hadu jiya, kai tsaye wurinta na nufa, bayan
mun gaisa na sami wuri na zauna muka fara
hira
bayan mun dan taba hira ta bukaci da na
rakata a saka mata hannu a difatimental
dinta (depertmental).
Daga ranar kyakkyawar alaka ta kullu
tsakanina da Safina, har ya zama cewa idan
har ta shigo makaranta bata ganni ba, ba ta
jin dadi, hakan kuwa ya faru ne kasancewar
ni na ke taimaka mata wajen karatu,
kasancewar na fita ganewa.
A bangarena kuwa sai na fara tunanin cewar
tauraro na ya haska, ko ba komai abin
alfahari ne a gareni a ce ina tare da Safina,
zamana da Safina ta tallafawa karatuna
mutuka ta gefen kudi, domin kuwa duk wasu
kudade da za'a bukata, ita ce take biyamin
su, kama daga kudin handi awut (hand out)
da sauran abubuwan da ake bukata,
kasancewar iyayenta masu hali ne, nawa
kuwa talakawa ne, wannan ne ya sani
tunanin cewa tuni na samu muhalli a
zuciyarta, lokuta da yawa sai nayi yunkurin
bijiro mata da soyayyata, sai wani sashe na
zuciyata yace min, me zaka wahalar da
kanka fada mata kana sonta, bayan ka
tabbata ta dade da fada wa cikin tarkon
sonka.
Ku dai biyoni.
MUTUNCI KO SO...3
Lokuta da yawa na sha rubuta mata sakon kar
ta kwana a wayata (text) dauke da ajandar
soyayyata, amma sai wani sashe na zuciyata
ya
gargadeni, kul! Kar ka kuskura ka tura mata
wannan sako, idan har ka tura wannan sako
ko
shakka babu sai ta ga wautarka, ai irin
wannan
sako na masu yakin neman zabe ne, kai da
tuni
kayi zaben kuma ka lashe. Me zaka yi wa
kamfe.
Idan zuciyata ta yi min wannan gargadi sai na
fasa tura sakon, haka ma duk lokacin da na
kirata a waya sai nayi kudurin fayyace mata
sirrin zuciyata, amma da zarar na tuno da
waccan hudubar da daya sashen zuciyata ke
yi
min, sai in yi sauri in sauya akalar zancena
zuwa
wani zance dabam.
Akwai lokacin da muna zaune muna hira, na
sha
alwashin fada mata ko da kuwa zata ga
wautar
tawa, na ke ce mata dama akwai maganar da
na
ke so gayamaki . Ina shirin fada mata sai na
tuno
da wannan hudubar da zuciyata ke yawaita
yimin a kanta, sai fasawa nayi, na ce mata ta
dai
bar maganar, ta yi juyin duniya a kan in sanar
da
ita, na ki fada mata, karshe da naga ta nuna
damuwarta, wata karyar daban na samu na
fada
mata.
Abokanaina da yawa a makaranta sun sha
fadamin cewa Safina ba karamin so ta ke yi
min
ba, su kan bugamin misali da irin kulawar da
ta
ke yi min, da irin dawainiyar da ta ke yi min,
duk
lokacin da suka yi min wannan maganar, na
kan
tuno da wani mawaki wai shi Aminu Dumbulu
a
cikin wakarsa ta Soyayya Sauda'ï, wani baiti
da
ya ke cewa "dama kula ne soyayya, kula da ni
na
san da ka na sona" idan na tuna wannan
baitin,
na kan tambayi kaina, in ce wace kulawa ce
Safina ba ta yi min? Na kan yi murmushi in bai
wa kaina amsa da cewar tabbas Safina sonka
take.
Wace mace ce zata yi min irin kulawar da
Safina
ke yi min? Ni dai ba kudi gareni ba, balle in ce
ko
don kudina ta ke kulani, hasalima sai dai ta
bani
kudin. Abu daya ne na ke dashi wanda nake
tunanin zata iya kulani don shi, shine basirar
da
Allah ya bani, sai dai kuma duk lokacin da
zuciya
ta kawo min wannan tunanin na kan yi
gaggawar
fatattakarsa a zuciya, bisa la'akari da nayi
cewa
matan yanzu babu ruwansu da hazakarka
wurin
karatu in baka da kudi.
A shekaru biyun da maka yi na karatun
diploma,
gidansu Safina sai da ya koma kamar
gidanmu,
domin kuwa ba wanda bai sanni ba a gidansu,
a
duk lokacin da na je gidan bani da sanke, kai
tsaye na ke wucewa. Ni ma kuwa babu wanda
bai san Safina ba a gidanmu, in takaice muku
zance dai zumunci mai karfi ya kullu a tsakin
gidanmu da gidansu.
Hatta aikin da nake tutiya da shi ita ce
Sanadiyar na sameshi. Wata biyar da suka
wuce
ne, ta kirani ta waya take ce min idan na samu
dama in sameta gida akwai maganar da take
so
mu yi.
Haka kuwa aka yi, yamma nayi na sameta
gidansu, bayan mun gaisa, ta ke gayamin
cewa
dama dady ne yace in yima magana ka kawo
takardunka ya sama maka aiki, wai wani
abokinsa ne yai masa magana cewa ya kawo
takardun yaronsa ya samar masa aiki, to shi
bai
son na fara aiki mijin da zan aura daga baya
yace bai son aikin, yafi son idan ina gidan
mijina,
mijin ya ga damar samar mani aiki ya samar
mani, to shine yaga bari ya bada takardunka.

Hmm! Kar dai ku kosa, ku kara biyoni, don ku
fayyace wa kanku me ya kamata a kira
wannan
alakar tamu, Mutunci ko kuwa So?MUTUNCI KO SO 3

Kwarai mahaifin Safina yai min kokari wurin
samar min aikin nan, tsaye yai tsayin daka
har sai da ya ga na samu aikin, hakika
kokarin da yai min ba zan taba mantawa da
shi ba.
Wannan kokari da mahaifin Safina yai min shi
yasa ni kara hakikancewa a zuciyata cewa
Safina tana mutukar sona a zuciyarta, kuma
a shirye take da tayi duk wani abu da zai
kara kusanci a tsakaninmu.
A duk lokacin da nayi tunanin me yasa ba ma
musayar kalaman Soyayya kamar yadda
nake gani a fina-finai ko a labaran soyayya,
sai wani sashe na zuciyata yace min, ai
wannan shiririta ce kurum irinta masu fina-
finai da kuma sakarci hadi da rashin
kunya......
Shigowar abokina waziri aku cikin dakina shi ya
katse tunani daga doguwar tariyar baya da
yake. Sallama yaimin, Shiru nayi ba amsa, a
sannan ne ya fahimci damuwar da nake ciki,
tasa ni a gaba yayi da tambaya, akan sai na
fada masa Me ye damuwata? Ganin ya
matsa yasa ni fada masa abinda ke
tsakanina daSafina ban boye masa komai
ba.
Ajiyar zuciyarsa ce ta kawar da shirun dakin
bayan da na gama bashi labarin, sannan
yace hakika abokina kayi babban kuskure, a
yanda ka bani labari bana ji akwai wata
soyayya a tsakinku da Safina, mutunci ne
kawai da kuma shakuwa. Hakika yusuf
mutunci da shakuwa babu irin kyautatawar
da basa sawa.
Mutane da yawa suna fama da
kwatankwacin matsalar da ka tsinci kanka
ciki, yusuf wai me yasa mutane ire-irenku
suke kasa fahimtar menene So? Tsakanin
saurayi da budurwa, mene ne kuma Mutunci?

Ai soyayya yarjejeniya ce tsakanin zukata
biyu da kuma mamallakan zukatan, ta yaya
Soyayya zata kasance ba tare da ka tallata
hajarka gareta ba, ita kuma ta amince maka?
Dakata waziri idan na fahimceka so kake
kace dani bata yaudareni ba, kana so kace
ban san mene ne so ba kenan?haba kamar baka
san mata ba, kawai
dai taga ni talaka ne, shi yasa da mai kudi
yazo sai tayi watsi dani ta daukeshi, ganin ni
ba zan iya wadatata da kyale-kyalen duniya
ba, kar kace haka abokina, ka daina gasgata
zargin zuciyarka, macen da tayi dawainya da
kai kamar yanda ka fadamin, idan har sonka
take bana tunanin zata iya barinka ta dau
dukiya,in tambayeka mana yusuf? Waye mijin
nata? Gaskiya ban san shi ba, amma ga
katin gayyatar da ta kawomin ka duba ko ka
san shi, na mike tsaye na dauko masa katin
ya amsa ya duba, Au! Wai dama itace Safinar
da Abubukar zai aura? Ka san mijin nata
kenan? Eh unguwarmu daya, in dai Abubakar
ne bana ji ya mallaki rabin Dukiyar da ka
mallaka Abokina, Abubakar malamin
Firamare ne, ko gidan da zai zauna haya ya
kamashi. Saboda haka ka daina zarginta
kawai dai kai ne baka fahimceta ba. Watakila
da kayi saurin sanar da ita kafin haduwarta
da Abubakar ta karbi tayinka, amma yanzu
kam ka makara, sai ka dau hakuri ka kuma
roke Allah da Ya musanya maka da wace
tafita.
Ban gasgata cewa Safina ta kubucemin ba
sai da naji ana shafa Fatiha a wurin daurin
aurenta, sannan na tabbatar da cewar Safina
tayi min nisa, irin kuma nisan da baza ta
tabo dawowa gareni ba.

Wannan ne Dalilin da yasani garzayowa
Shafin sada Zumunta (facebook) domin
tallata muku wannan labari nawa, don
neman shawararku. Watakila kuma nayi
gamo da wacce zata mayemin Gubin
Safinata. Lol

toyanzu kanma nasamu gawata can tace zata iya. meye shawararku?
This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu...


Read / Download MUTUNCI KO SO

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album