Join Our WhatsApp Group

YARO BAI SAN WUTA BA Complete Hausa Novel Document by YARO BAI SAN WUTA BA


YARO BAI SAN WUTA BA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 41599



YARO BAI SAN WUTA BA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 212.85 kb

File Type: txt

Views: 582+

Download: 301+

Last download: 8 hours ago

Description/Story: YARO BAI SAN WUTA BA.....
.
Page 1
.
.
.
'(M. F)'
Su ne siraran haruffan dake a jikin duk wani abin kwalliya ko kayan qarau din dake a cikin katafaren gidan. A bayan kujeru, a qasan kilisai, da dardumai, a jikin gilasai da qofofi. Kai hatta kwatamin wankan gidan sai da aka yi masa kwalliya da da'irar ciyayi masu nuna wadannan haruffan guda biyu.
.
Baqo ne kawai zai xo ya wuce gidan, bai san me wadannan haruffan suke nuni dashi ba, to amma duk wanda ya kwana ya tashi a shahararriyar unguwar da tayi fice a birnin Ikko, wato (Victoria Island), ya san ko wanene Muhsin Fataye. Wanda shi ne yake inkiya da haruffa biyu na (M. F).
.
Alhaji Muhsin Fataye matashin attajiri ne dan shekara talatin da shida, wanda idan mutum ya ce zai tsaya lissafa kadarorinsa, da gine-ginensa na alfarma a garin Lagos to aiki ja ya same Alhaji Muhsin Fataye matashin attajiri ne dan shekara talatin da shida, wanda idan mutum ya ce zai tsaya lissafa kadarorinsa, da gine-ginensa na alfarma a garin Lagos to aiki ja ya same shi.
.
Abin da kawai yayi fice akansa kuma kowa ya sani shi ne, kasancewarsa babban ma'aikaci a madatsar ruwa ta tashar jiragen ruwa da kuma hada-hadar shigowa da kayayyakin waje xuwa cikin gida Najeriya. Duk da kasancewarsa bayerabe, yana jin hausa sosai, sbd duk kusan rayuwarsa tun yana yaro a Kano yayi. Aiki kawai ya dawo dashi Ikko, amma mahaifinsa dan kasuwa ne a Kanon dabo har Abin da kawai yayi fice akansa kuma kowa ya sani shi ne, kasancewarsa babban ma'aikaci a madatsar ruwa ta tashar jiragen ruwa da kuma hada-hadar shigowa da kayayyakin waje xuwa cikin gida Najeriya. Duk da kasancewarsa bayerabe, yana jin hausa sosai, sbd duk kusan rayuwarsa tun yana yaro a Kano yayi. Aiki kawai ya dawo dashi Ikko, amma mahaifinsa dan kasuwa ne a Kanon dabo har ynx.
.
Wata tara kenan da yin auren sa na biyu, wata bahaushiya ya samu a Kaduna, wacce ya hadu da ita a wani bikin amininsa wanda suka yi Jami'ar Bayero tare.
.
Yana matuqar son amaryarsa kamar yadda itama take son sa. Kuma bai samu wata matsala da matarsa ta farko ba mai suna Kudiratu. Ko da yake ba a gida daya suke zaune tare ba. Kowacce tana nata katafaren gidan, to me zai yi masu zafi tunda dai komai na duniya sun samu?
.
Alh. Muhsin kwana biyar-biyar ya tsara zaman sa da matanshi, kowacce idan yaxo gidanta ya kan yi kwana biyar.
.
A cikin irin wadannan ranakun ne sanda yana a wajen amaryarsa ya tashi da safe yayi wanka ya sa manyan kaya farare da hularsa ha6ar kada, wacce yake lanqwasheta gefe daya. Ya fito falo yana gyara daurin agogonsa, a lkcn ne amaryar tasa ta fito da turare a hannunta tana yi masa murmushin da ta saba na soyayya.
.
Ya riga ya saba da wannan turaren da take sa masa na qauna, kowacce rana in dai zai yi wanka yasa kaya, to ko ya fesa nasa turaren ya zama dole itama ta dauko nata ta fara fesa masa.
.
Ya tsaya jiranta ta qariso riqe da qaramin turarenta a cikin wata siririyar kwalba mai baqin murfi. Da xuwanta gabansa ta bude turaren ta saita gefen babbar rigarsa ta dannan kan gwangwanin, turaren ya fito da qarfi caa!!
.
Alh. Muhsin yana tsaye yana jiranta ta gama kafin suyi magana, sai yaga ta juyo da gwanwanin dai dai kanshi zata fesawa hularsa. Ta danna gwangwanin, maimakon turaren ya feshe hular, sai ya tsartu a saitin idanunsa biyu. Yayi saurin rufe idanunsa yasa hannu ya dafe fuskarsa da ya ji radadi ya gauraye idanunsa. Ganin haka yasa amaryar ta tsaya da fesa masa turaren, ta tambaAlh. Muhsin yana tsaye yana jiranta ta gama kafin suyi magana, sai yaga ta juyo da gwanwanin dai dai kanshi zata fesawa hularsa. Ta danna gwangwanin, maimakon turaren ya feshe hular, sai ya tsartu a saitin idanunsa biyu. Yayi saurin rufe idanunsa yasa hannu ya dafe fuskarsa da ya ji radadi ya gauraye idanunsa. Ganin haka yasa amaryar ta tsaya da fesa masa turaren, ta tambayeshi.
.
"Ya shigar maka ido ne....ban sani ba Alhaji, bude idonka in goge maka....oh...."
.
Har zai bude idanun, sai kuma ya ji kamar ana yankarsa da reza a ciki, ya dawo ya ji kamar ana soka masa allura. Yasa daya hannun ya dafe idanun nasa ya fara qaraji, yana juye-juye a falon.
.
Amaryar tasa ta rude ta fara kuka, ta dauko tawul ta jiqa shi da ruwa, ta fara qoqarin 6an6are hannun mijin nata zata goge masa idanun, ya qi tsayawa sbd ji yake kamar idanunsa zasu tsiyayAmaryar tasa ta rude ta fara kuka, ta dauko tawul ta jiqa shi da ruwa, ta fara qoqarin 6an6are hannun mijin nata zata goge masa idanun, ya qi tsayawa sbd ji yake kamar idanunsa zasu tsiyaye.
.
Qarajin da yake yi da kuma kukan da amaryar take yi ya jawo hankalin wani maqwabcinsa, ya shigo gidan a rude yaga abin dake faruwa.
.
A lkcn tuni Alh. Muhsin ya fadi qasa yana birgima, yana dafe da idanunsa yana kururuwa.
.
Maqwabcin nasa bai tsaya sauraren matar ba dake ta 6urari ya dauke shi yayi waje dashi yana kwadawa direbansa kira, ya fito da mota yayi sauri su je asibiti.
.
Awa daya bayan sun kai shi wani asibitin ido dake a garin. Likitoci suka amshe shi suka fitar da sakamakon da ya firgita kowa.
.
"Ba turare amaryar tasa ta fesa masa ba, wani azababben sinadari ne wanda aka yi shi musamman don makanta mutane, duk idon da aka fesawa ba zai qara ganin komai ba a duniya.!
.
Wannan maganar da ta fito daga bakin likitocin ta sabbaba kace-nace a tsakanin amarya da 'yan uwan mijinta wadanda suka shigar da qararta a kotu. Amaryar ta kare kanta da rantsuwar ita turare ta san ta fesa masa, kuma tunda suka yi aure kullum idan zai fita sai ta fesa masa turare. Ynx ne aka samu matsala tsautsayi ya ratsa ta fesa masa a ido bata sani ba.
.
Aka shiga kotu aka fara fafatawa. Da amaryar ta dauko turaren taxo dashi ne aka ba qwararrun masu auna sinadarai suka yi aiki akan shi, sai suka ce turaren baya dauke da wata guba, babu komai a cikinsa. Likitocin da ke yiwa Alh. Muhsin Fataye aikin idon, suka xo suka qaryata bayanin da cewar.
.
"Turaren da ta bayar a kotun ba shi bane turaren da ta fesawa mijin nata ba."
.
Hakan yasa dole aka tura jami'an tsaro gidan nata domin su je suyi binciken qwaqwaf ko wata qila za a ga ainahin turaren da aka ce yana dauke da guba a cikinsa.
.
.
Lp=2YARO BAI SAN WUTA BA......
.
Page 2
.
.
.
Hakan yasa dole aka tura jami'an tsaro gidan nata suka je suka yi binciken qwaqwaf ko wata qila za a ga ainahin turaren da aka ce yana dauke da guba a cikinsa, , amma da suka je basu ga komai ba.
.
Da aka dawo kotu ne Lauyan dake kare amaryar ya tabbatarwa kotu cewar lallai wacce ake zargi bata da laifi.
.
"Ta yaya zata mayar da mijinta makaho bayan duka-duka watansu tara da yin aure? Dama kashe shi tayi sai ace dukiyarsa take so, amma idan ta makantashi me zata samu a sakamakon hakan?"
.
Ba a kotu ba, ko a waje abin da mutane suke ta cewa kenan. Akwai zaman soyayya a tsakanin sabbin ma'auratan. Babu dalilin da zai sa matarshi ta makantashi.
.
Shi kansa mijin nata duk da yana kwance a asibiti ba a sallame shi ba, ya goyu bayan matar tasa, kuma yana qalubalantar kotu bisa tuhumarta da suke yi. Da wata jarida ta je tayi hira dashi a asibitin, ko me zai ce dangane da wannan mugun abu da ya faru dashi, sai ya ce dasu.
.
"Ina zaune da matata lfy, bamu ta6a samun wata matsala ba. Na san tana sona, kuma ba zata iya cutar da ni ba.
.
Ta saba fesa mani turare kullum, bata ta6a cutar da ni a dalilin haka ba, kuma ba zata iya cutar dani ba. Wannan abu daya faru ba laifinta bane. Abin ya xo da tsautsayi, ko bata fesa mani turaren ba, idan lkcn makancewata yayi ba yadda zan yi, wajibi ne sai abin ya faru....don haka bata da laifi, bana zarginta."
.
Jaridar ta sake tambayarsa.
.
"Kana nufin kenan idan Likitoci suka sallameka zaka ci gaba da zama tare da ita a matsayin matarka?"
.
Ya amsa masu.
.
"(Why not) me zai hana kuwa? Zamu ci gaba da zama mana tare. Na san don na zama makaho ba zata guje ni ba, zamu ci gaba da zama kamar komai bai ta6a faruwa ba."
.
Haka kuma abin ya kasance. Alh. Muhsin ya zama makaho, ga dai idanunsa a bude, amma sun mutu, basa iya ganin komai.
.
Ya samu wani kwantareren baqin tabarau ya 6oye matattun idanunsa, ya samu sandar qarfe ta makafi 'yan gayu ya riqa laluben hanya da ita, ya dawo wajen iyalansa suka ci gaba da zama, ya tara 'yan uwansa ya basu haquri, ya ce baya son ana tayar da wannan magana, kada su tsani matarsa komai muqaddari Ya samu wani kwantareren baqin tabarau ya 6oye matattun idanunsa, ya samu sandar qarfe ta makafi 'yan gayu ya riqa laluben hanya da ita, ya dawo wajen iyalansa suka ci gaba da zama, ya tara 'yan uwansa ya basu haquri, ya ce baya son ana tayar da wannan magana, kada su tsani matarsa komai muqaddari ne.
.
Matarsa ta farko Kudiratu tayi kuka ba dan kadan ba, 'ya'yanta uku da Muhsin Fataye, gashi ynx ya zama makaho suna cikin jin dadin duniya, bata san yadda rayuwa zata kasance masu ba ynx.
.
Alh. Muhsin ya ci gaba da harkokinsa ana yi masa jagora, yana da yara masu amana a ko'ina, babu abin da ya samu dukiyarsa.
.
Duk abubuwan da ya saba yi bai daina komai ba. Idan wata yarjejeniya zai yi da wani kamfani, akan yi masa jagora ya je ya zauna ayi duk surutun da za a yi.
.
Idan zai sa hannu a takarda sai a nuna masa ita ya laluba, a dora masa yatsansa a kan takardar inda zai sa hannun.
.
Rayuwar aurensa da amaryarsa wacce ta zama sanadiyyar makancewarsa ba wata matsala, suka dawo suka ci gaba da aman soyayyarsu. Ko'ina zai je a gidan sai ta riqe masa habby ra kai shi.
.
Da yake yana son karatun jatida, kullum sai ta karanta masa sabbin jaridu da mujallun da suka fito, yana zaune akan kujera sanye da faskeken baqin tabarau ya na saurarenta har ta gama.
.
Idan zasu yi tafiya ita ce ke tuqa mota, duk wasu wajen shaqatawa da suke xuwa ada kafin ya makance basu daina xuwa Idan zasu yi tafiya ita ce ke tuqa mota, duk wasu wajen shaqatawa da suke xuwa ada kafin ya makance basu daina xuwa ba.
.
Iyakarta dai ta riqe masa sandarsa ta qarfe ya bita a baya tana yi masa jagora.
.
Duk da shi bai damu ba, amma mutane suna tausayawa yadda rayuwarsa ta koma.
.
Babban mutum mai kudi da kamala ya zama makaho!
.
Ba zai sake ganin duniya da abin dake cikinta ba.
.
.
FARAWA.
.
Tun farkon faruwar al'amarin, ban ta6a kawowa a raina zan fadawa duniya wannan labari ba. Wani lkcn ni kadai idan na tuno al'amarin na kan yi mamaki da al'ajabi in tambayi kaina, wai da gaske nine wanda wannan gagarumin al'amarin ya faru da ni? Na kan ji abin kamar aikin mafarki ne bai faru da gaske ba. Don haka wa zan fadawa labarin, tunda na san ba kowa zai gasgata ni ba? Shi yasa na dauki shekara da shekaru ina 6oye da labarin a xuciyata kamar kudin adashiTun farkon faruwar al'amarin, ban ta6a kawowa a raina zan fadawa duniya wannan labari ba. Wani lkcn ni kadai idan na tuno al'amarin na kan yi mamaki da al'ajabi in tambayi kaina, wai da gaske nine wanda wannan gagarumin al'amarin ya faru da ni? Na kan ji abin kamar aikin mafarki ne bai faru da gaske ba. Don haka wa zan fadawa labarin, tunda na san ba kowa zai gasgata ni ba? Shi yasa na dauki shekara da shekaru ina 6oye da labarin a xuciyata kamar kudin adashi.
.
Duk tsawon lkcn da nayi ban fito da wannan labarin ba, na san wata rana dole ne in amayar dashi, wadansu su ji, kamar dai yadda zan sanar daku a halin ynx.
.
Al'amarin ya fara samo asali ne a wani dare da na mance ko wacce rana ce. Alhamis....? Asabar...? Bana jin zan iya tuna kowacce rana ce a halin ynx, to amma dai abin da ba zan mance ba shi ne. Na san an tashi da hadari tun safe har dare yayi ana ta walqiya da cida. Ba a yi ruwan ba, kuma sararin samaniyar bai washe ba.
.
Wannan ba wani sabon yanayi bane a birnin Ikko, don kuwa sai a dauki kwana da kwanaki a haka. Ko kuma a yi ruwan, ana daukewa ba a jima ba wani ya sake saukowa.
.
Irin wannan yanayin baya hana mu fitowa ga qananun sana'o'in da muke yi. Musamman ma dai ni da nake da qaramin teburi da kujerun zama biyu, da tsohuwar laimata ta kamfanin sadarwa na (Glo) wacce ta kode duk rubutun jikinta ya fara kodewa.
.
To amma duk da kodewar da laimar tayi, kullum in har zan budeta a wajen wannan sana'ar da nake yi in zauna a qarqashinta.To amma duk da kodewar da laimar tayi, kullum in har zan budeta a wajen wannan sana'ar da nake yi in zauna a qarqashinta...
.
.
Lp=3YARO BAI SAN WUTA BA
.
Page 3
.
.
kullum indai zan budeta a wajen wannan sana'a da nake yi in zauna a qarqashinta, ko daga nesa in mutum ya qura ido zai iya ganin rubutun dake a jikin laimar da baqin fenti, wato (Kamal Communicat kullum indai zan budeta a wajen wannan sana'a da nake yi in zauna a qarqashinta, ko daga nesa in mutum ya qura ido zai iya ganin rubutun dake a jikin laimar da baqin fenti, wato (Kamal Communication).
.
Kada in yi tsallake in mance da wani abin, bari in dawo in fara baku labarin daga farko, don kusan tushen al'amarin.
.
.
'SUNA NA KAMAL.'
.
Kada ku tambayeni asalina ko garin mu, sbd a zama irin na Lagos, na kaxo-naxo, da wahala ka ji wani ya bude ma cikin sa ya fada maka gskyr inda ya fito.
.
Don haka nima ban ta6a fadawa kowa ba, kodai ban fadi gsky ba an san daga arewa nake, kuma ni Bahaushe ne wanda yaxo neman kudi.
.
Shekaruna zasu kai ashirin da bakwai a duniya, a ciki idan ka debe shekaru shida na sama, duk nayi su ne a wannan gari na Ikko. Farkon xuwa na a shekarun baya wasu 'yan garinmu na biyo, wadanda suke xuwa sana'ar gwari, wato safarar kayan lambu dangin tumatiri da albasaShekaruna zasu kai ashirin da bakwai a duniya, a ciki idan ka debe shekaru shida na sama, duk nayi su ne a wannan gari na Ikko. Farkon xuwa na a shekarun baya wasu 'yan garinmu na biyo, wadanda suke xuwa sana'ar gwari, wato safarar kayan lambu dangin tumatiri da albasa.
.
Daga baya da idanuna suka bude, sai naqi komawa...


Read / Download YARO BAI SAN WUTA BA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album