Join Our WhatsApp Group

KWANAN GIDA Complete Hausa Novel Document by KWANAN GIDA


KWANAN GIDA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 20142



KWANAN GIDA

Reading Time: 1 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Muhammad Lawal PRP ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 102.38 kb

File Type: txt

Views: 833+

Download: 190+

Last download: 2 days ago

Description/Story: Kwanan gida

Muhammad Lawan Prp

KWANAN GIDA
Babi Na Farko

"Ke karuwa ce! Bakar ashana kona gari... Da halinki gwamma gobara ran sallah. "
Maganganun saurayin suka ci gaba da yi mata kararrawa a kunnuwanta. Kwakwalwarta ba ta saba da karbar maganganu masu zafi irin wadannan ba, bayan cakudewar da rayuwarta ta yi da munanan abubuwa da suka zagaye ta suka hana ta sakewa, a karon farko ta yi nadamar shigowarta bariki.
Barikin boye!
Barikin da iyayenta ba su san tana yi ba, mutanen unguwarsu ba su san tana yi ba, duk da shigarta barikin da faruwar al'amarin sun kasance ne a cikin kwanaki kadan, amma ji take yi ba za ta iya bari ba. A mafi yawan lokuta tana fakewa da guzuma ne tana harbin karsana ;ta sha fakewa da zuwa makaranta tana samun abin da take so daga mutanen da suke karbar abin da take da shi a wurinta.

Za ta iya tuna ranar farko da mutum na farko da ya fara sanin ta 'ya mace, wato saurayinta Rabi'u ;wanda ta aminta da shi ta mika masa soyayya ta damka masa amanarta babu haufi, har ya yi nasarar bata mata rayuwa, bayan ya yi amfani da tsantsar kwadayinta tare da kaifin basirarsa ya yaudare ta da kyautar sarkar gwal ta mata, wadda kudinta ya kai dubu hamsin. A karshe tana ji tana gani ya nuna mata sarkar ta bata.
A dole ta hakura bayan ya yi alkawarin sayo mata wata.
Mutum na biyu da take zargi da bata mata rayuwa ;ita ce babbar kawarta kuma aminiyarta Nusaiba. Ita ta dora ta akan harkar good evening (gaisuwar yamma).
Ah to! Ina ruwan biri da gada?
Wata rana ne Nusaiba ta same ta a dakinta cike da damuwa, domin tun bayan karayar arzikin mahaifinta gabadaya gidan nasu suka shiga damuwa ; maraici, da kadaici suka dabaibaye su.
Nusaiba ta ba ta shawarar hanya mafi dacewa da za ta warware matsalarta.
"Haba Nusaiba! Ba ki ganin abin da Rabi'u Mangyal ya yi mini? Amma kike gaya minmin hanyar da zan bi wadda ba bullewa take ba? "
" Matsalarki daya Rabi'atu ; kullum idan ana nuna miki hanyar da za ki rage matsalolin rayuwa sai ki dinga tunanin abin da zai faru gaba. Ki gaya min idan akwai wata mace baliga da za ki iya shaidar ta a wannan zamanin, komai kankantar shekarunta kuwa, hatta matan aure da su ake damawa a ciki. Idan matar aure ta aikata ta aikata ta yi babban zunubi, Amma ke, a karkashin ikon wa kike da har za ki nemi daga hankalinki? Ki duba yadda rayuwarki ta koma baya, ba wani wanda zai tallafa miki, karatun da kike yi nema yake ya gagara. Idan ba ki warware matsalolinki yanzu ba sai yaushe? Ko sai ikonki ya bar hannunki ya koma karkashin wani? Da sandar da ke hannunka fa da ita kake jifa. Haba Rabi'atu ki dawo daga duniyar dimuwa da kika jefa kanki ko kya samu sa'ida a rayuwa. Abu ne fa na lokaci kankani, ba shiga sojan badakkare za ki yi ba."
Rabi'atu ta yi shiru tana sauraren hudubar kawarta, lokaci guda tana hasko yadda ta taso cikin gata da yadda karayar arziki ta wargaza kwanciyar hankalin gidansu ta yi dai-dai da zumuncin danginsu da talakawan unguwar ('yan maula).
Rabi'atu ba ta san dacin talauci ba a farkon rayuwarta, wannan ya sa ta kasa jure masa, a duk lokacin da bukatar kudi ta zo mata sai ta ji kamar ta dora hannu a ka ta saka ihu, wannan ya mayar da ita makwadaiciya akan mallakar abin duniya, zuciyarta kuma na gaya mata wata rana arzikin mahaifinta zai dawo, watakila ma ta hanyarta, sai dai har yanzu ba ta ga alamu ba. A da ta yi tsammanin abin zai kasance ne bayan ta kammala karatu ta samu wani gwaggwaban aiki. To amma ga shi tun ba a je ko ina ba karatun nata ya cije.
Don haka lokacin da Nusaiba ke ba ta shawara, duk da ta jinjina shawarar amma sai take ganin Nusaiba na da gaskiya, kuma ko babu komai ma wanda ruwa ya ci in ka ba shi takobi kamawa zai yi. Don haka za ta jarraba ta gani, amma na lokaci kankani ne, daga zarar ta samu ta kammala karatunta za ta...
"Tunanin me kike yi ne Rabi'at? Kina da matsala wallahi," Nusaiba ta katse ta,"ni zan dauki jakata in tafi idan tunani za ki tsaya yi."
Ta mike tsaye bayan ta dauki jakarta.
Rabi'at ta yi saurin rike ta, "Kada ki tafi kamata, ta ya ya kike ganin za a bullo wa abin?"
"Ba kina zuwa makaranta kullum da yamma ba? " in ji Nusaiba.
" Kina nufin daga makaranta sai mu wuce? "
" Kash! Ba kya gane karatun sosai ;shiyawa za ki yi kamar zanyi ki je makaranta, da zarar kin fita sai ki yi min waya, zan gaya miki inda za mu hadu, sauran bayanin kuma ruwa ya fi shi saukin sha. "

Da haka Nusaiba ta shawo kan kawarta suka fara sana'ar da suke ganin ribarta a yanzu, riba kan riba ;domin suna kashe kishirwar da ke damun su sannan kuma ga sinadaran rayuwa (kudi ).

Mu je zuwa.KWANAN GIDA

MUHAMMAD LAWAN PRP

2.

Yamma ta yi. Rana ta sunkuya. Zirga-zirga ta yawaita a manyan titunan garin Kano, saboda dawowar mutane daga wurin harkokinsu, walau na kasuwanci ko aikin ofis. Gosulo ya yi yawa, kowacce danja ko madakata ta manyan titunan motoci ne jere a tsaye cak! Saboda tsabar cunkoson ababen hawa.
A can titin unguwar Nassarawa inda su Nusaiba ke tsaye ita da kawarta Rabi'atu da sauran abokan harka ba haka abin yake ba, akwai karancin ababen hawa.
Lokaci - lokaci masu kudi kan tsaya da manya-manyan motoci domin daukar abokan harka. Idan haka ta faru matan da ke tsaye suna jiran gawon shanu kan rugo da gudu ga duk wadda motar ta tsaya kusa da ita don zaton saboda ita aka tsaya. Wadansu daga cikin matan, matan aure ne da kan baro gidajensu saboda tsabar kwadayi, da kuma zawarawa,'yan kwalisa, sai kuma 'yan matan da suka bude ido irin su Nusaiba.
Nusaiba ta gyara tsayuwarta bayan ta turo dankwalinta gaba, "Ina fata kina kula da yadda ake harka?"
Rabi'at ta kyabe baki. Ita abin haushi yake ba ta ;ganin yadda' yan mata suka maida kansu kamar wani tumatirin kasuwa a gefen hanya, amma daga zarar ta tuna ba tsayuwar banza take ba, domin tana ganin yadda Nusaiba ke facaka da kudi sai ranta ya yi fari, ta san nan gaba kadan ita ma idonta zai bude. Ta san tana da kyawun dirin da duk wanda ya kalle ta sai ya sake kallonta. Haka nan matsattsun kayan da ta sa sun taimaka wajen fito da kugu da cikar kirjinta. Ta yi imani babu dadewa za ta kashe wa Nusaiba kawarta kasuwa, bariki za ta fara yayinta, domin kuwa ta fi ta kyau nesa ba kusa ba.
"Ina kula. Amma na ga ai ba wasu yara sosai, duk dattawa nake gani. "
Sai da Nusaiba ta yi dariya kafin ta ce," Kada ki zama wata sabon yanka rake mana kawata! Ai wadanda kike rainawa su ne abokan tafiyar, ba ki ga abin da matasan irin su Rabi'u saurayinki suka yi miki ba? "
Rabi'at ta hade rai, domin duk sadda aka tuna mata da Rabi'u takan ji tsanar sa ta karu a zuciyarta fiye da lokacin da ya ci amanarta. Don haka a yanzu da Nusaiba ta tuna mata shi sai ta ji tana kaunar ko ma waye ya dauke ta za ta bi shi a je a shakata, kuma zai rage mata radadin damuwar zuciyar tata.

A hankali wata mota mai tsada kirar Anaconda ta tsaya a kusa da su, sannan aka sauke gilasan motar, wani mutum kakkaura mai tarin gashin baki da gashin kai duguzumzum ya leko ya kare musu kallo daga sama har kasa, sannan ya yi wa Rabi'at sigina da kwayar idonsa.
Nusaiba ta dauko madubi tana kallon fuskarta a wani salo na basarwa.
Rabi'at ta lura da yadda sauran matan da aka dauka a gaban idonta suke yi, kuma tun kafin su zo nan kawarta ta nuna mata babu sanayya a harkar bariki.
Don haka da mutumin ya kira ta ba ta kalli Nusaiba ba kawai sai ta nufi motar kai tsaye ta bude ta shiga.
Mutumin ya ja suka tafi.
Wani otal suka nufa. Bayan ya ajiye motarsa a wajen adana motoci suka karasa, ya kama musu daki kwana guda, aka ba shi mabudi. Suka nufi inda ayarin dakunan ke jere reras!
Lokacin da ya bude dakin suka shiga tuni an fara kiran sallar Magriba a wani masallaci da ke kusa da otal din.
Rabi'at ta ajiye jakarta a kan wani katon gado mai lallausar katifa.
"Sunana Alhaji Yunusa. Kuma ni dan kwangila ne, "dattijon mutumin ya ce mata," in dai har na samu yadda nake so a wurinki to kina da naira dubu hamsin. "
Rabi'atu ta ji wani sanyi a ranta. In dai don ya yi abin da Rabi'u ya taba taba yi mata ne har kuma ya ba ta hamsin ai kuwa ba ta yi asara ba. Amma duk da haka tana mamakin yadda babban mutum kamar wannan yake neman 'ya' yan cikinsa. Ko ba shi da iyali ne? Ta yi saurin kawar da wannan tunanin.
'Ba abin da ya shafe ki ba ne, ' wata zuciyar ta ce mata haka. Illa dai dada gyara zama da ta yi.
Ya dube ta, kamar ya san tunanin da take yi.
"Ina da mata biyu da' ya 'ya biyar. Kin san me ya sa na dauko ki? Matana ba su iya salon kwanciya irin wadda nake so ba. Ga masifa da jarabar son kudin tsiya. In ba wurin irin ku wayayyu ba ba mu cika samun abin da muke so ba. "
Rabi'at ta yi murmushi, ita duk ba wannan ne ya dame ta ba, ta matsu a zo wurin, domin samun abin da ta fito nema, ko ta samu ta koma makaranta.
Alhaji Yunus ya dube ta bayan ya cire doguwar rigar dake jikinsa.
" Bebina ke kuma ya ya sunan ki?" ya fada cikin salon kashe murya, wai a dole shi saurayi ne.
"Sunana Usaina."
Tuni kawarta Nusaiba ta koyar da ita cewa, ba a amfani da sunan gaskiya idan an shigo bariki saboda gudun bacin rana.
"Usaina Bebi, kina da kyau fa! " ya fada a cikin wani salo na koda ta.
" Mhm! " kawai ta fada, amm a zuciyarta tunanin dubu hamsin din da ya fada take yi, tana kasafin abin da za ta yi da kudin da zarar sun shigo shigo hannunta. Ta san idan ta yi la'akari da tarin bukatunta babu inda za ta je mata, kai! A biyan kudin makaranta da litattafai ma za su iya narkewa, ban da bukatuncikin gida dake jiran ta kashe su kamar wutar gobara.
Sai a sannan ne wata fargaba ta yi wa zuciyarta dirar mikiya;yanzu idan aka tambaye ta a inda ta samu kudi take facaka da su me za ta ce wa mutane ko iyayenta? Kawai ki ce musu saurayinki ne ya ba ki. '
Saurayinta? Wa ke nan?
' Alhaji Yunus dankwangila mana! Kuma har ma ya ce idan ya samu dama zai turo a daura aure, kin ga daga nan sai ki shiriritar da zancen... '
"Usaina ba za ki yi wanka ba? " tambayarsa ta katse mata tunani.
Bai saurare ta ba sai ya nufi banxakin dake dakin daga shi sai singileti da gajeren wando,'" Bari in dan watsa ruwa. "
Ta bi shi da kallo kawai. Lallai ruwan kashe gobara ba sai an samu mai kyau ba. In ba don haka ba me za ta yi da wannan magidanci? Ita sam bai kwanta mata a rai ba. Matansa na aure ma yana cin amanarsu ina ga ita karuwa? Amma da ta tuna darasun da kawarta ta gaya mata sai ta dake.
'Ba ruwan ki da muni ko rashin kyan halin mutum, ke dai in za ki kadi raba kawai ba wani shegen.'

Tana jin sautin zubar ruwan wankansa yayin da idanuwanta suka sauka a kan wata katuwar walet dinsa dake ajiye bisa wani kayataccen tebur na gilas kusa da inda ya ajiye kayan sawarsa.
Gabanta ya buga da! Ta tabbata kudinsa ne a ciki, ranta ya kwadaita mata daukar walet din ta duba. Ta kalli kofar banxakin, idanuwanta suka sake garzayawa kan walet din.
Cikin nutsuwa ta mike. Ba ta san me take shirin aikatawa ba, kawai ta ga tana tafiya, har zuwa lokacin da hannunta. Gabadaya ta ji babu imani balle tsoro a zuciyarta.
Ta bude walet din, idonta ya yi kwalli da 'yan dubu - dubu har dauri dauri biyu, akwai fasfot na fita waje da wani karamin littafin cek na banki.
A cikin abin da ya gaza minti guda ta canza wa kudin matsuguni zuwa cikin jakarta, ta zauna zuciyarta na gaya mata ta sulale ta gudu kafin ya fito daga wanka.
Zuciyarta na angiza ta zuwa ga tsrewa yayin da wani sashen ke gaya mata, 'ki mayar masa da kudinsa, kin ga ba hakkin ki ba ne.'
Rabi'at ta kasa motsawa har zuwa lokacin da ya fito.

Ina zuwa dai.Kwanan gida

Muhammad lawan prp

3.
Ya nufo ta sanye da tawul a jikinsa yana murmushi, Rabi'at ta yi mutuwar tsohuwa, zuciyarta cike da fargabar kada ya gane abin da ta yi masa.
'Da ma ke barauniya ce?' Ta so ta ji kamar haka yake ce mata, amma sabanin haka sai ta ji yana cewa.
"Bebina me ye matsalarki? Ya kamata ki yi wanka don mu nishadantu."
Yin wankanta na nufin tonuwar asirinta. Don haka a take sai kwakwalwarta ta soma aiki.
"Ba ka gamsu da kwalliyata ba ke nan?"
Ta kalle shi da murmushin 'manta sunanka'
"Ni na isa in ce haka? " ya zauna kusa da ita tare da dafa kafadunta," ai irin ku ba make up (kwalliya) kyau kuke yi. Da ma na ga kamar kina gumi ne."
Sai a yanzu ta ankara da gaban rigarta da ya soma jikewa.
Ta dube shi, "Babu komai. Na dan wanke fuskata kawai... Mhm! Dalin ka cika tambaya da yawa," ta dan kwanto jikinsa.
Ya shafi fuskarta, "Ki yi hakuri Bebina ban san ba kya son tambaya ba. Kina jin yunwa?"
"Ga shi ka kuma tambaya ta! "
"Na damu da ke ne shi ya sa daga yanzu duk abin da kike so ki gaya min, zan yi miki daga nan zuwa safe tun da kwanan gida na dauke ki. Matsalata daya; na tsani munafunci ko sata, da munafuki da barawo ba abokaina ba ne. Zan iya kashe mutum idan ya yi min daya daga cikin halayen nan."
Gaban Rabi'at ya fadi, "Kina? Kisa fa ka ce?" ta fada a razane.
Ya shafa kanta, "Bebita ke nan, kina mamaki ke nan, to ki daina, domin mutanen nan biyu su...


Read / Download KWANAN GIDA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On KWANAN GIDA
avatar
hassan-5-6

7 months ago

Reply

godiya Allah biya

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album