Join Our WhatsApp Group

TUN A DUNIYA Complete Hausa Novel Document by TUN A DUNIYA


TUN A DUNIYA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 39682



TUN A DUNIYA

Reading Time: 3 Hours

Added On: 21, Sep 2023

Author: Shafi'u Dauda Giwa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Gidan Littafi

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Action Novels

File Size: 220.11 kb

File Type: txt

Views: 642+

Download: 234+

Last download: 13 hours ago

Description/Story: TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
01
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE
.
.
=====><=======
:
DA misalin karfe hudu da rabi na yamma fatima ta
karasa kofar gidansu kawarta Ummulkhaeri dake
cikin gwammaja" bayan ta sauka daga motar da ta
hawo daga kurna babban layi" inda anan gidansu
yake"
Ta samu mahaifin Ummulkhaeri a xaune yana
karatun wani littafin addini akan darduma" tayi
masa sallama da taxo shiga gidan" sannan ta
durkusa har kasa domin ta gaeshe shi"
"sannu ßaßa"
mahaifin Ummulkhaei wato malam Aßdullahi" ya
dago kansa" da yaga fatima ce sai ya saki fuskar
shi" ya amsa sallamarta"
"A fatima ce?"
ta ce.
"nice ßaßa" ina wuni?"
ya amsa mata da cewa"
"lafiya lau" yasu Alhaji duk suna lapia?"
fatima tace
"suna nan kalau"
yace da eta"
"to madallah"
.
.
Fatima ta tashi ta shiga cikin gidan a yayin da
malam kuma yci gaba da karatunsa"
Da shigarta gidan tayi sallama" mama Raliya
mahaifiyar Ummulkharti ta amsa sallamar daga
cikin dakinta inda take xaune akan kujerar keken
dinkin dake gabanta" tana kokarin shigar da xare a
cikin allurar keken"
Da farko mama Raliya bata dauki muryar ba sai da
ta sa hannu ta yaye labulen dakin sannan ta ga
ashe Fatima ce" tayi dariya cikin fari ciki da ganin
babbar kawar 'yarta a duniya wacce suka saba da
ita shekara da shekaru"
.
.
Fatima lale marhabin"
tace da ita" bata daina murmushi ba" ta mayar da
hankalinta a kanta" tana jiran karasowarta cikin
dakin"
Fatima ta cire takalminta ta shiga cikin dakin
mama Raliya hade da sallama cikin ladabi"
mama Raliya ta amsa tana mai tattara hankalinta
kanta"
"sannu da xuwa"
Fatima tace"
"yauwa" sannan ta durkusa har kasa"
"Ina wuni mama"
"lafiya lau" mama Raliya ta tambayeta"
"Ince dai su Hajiya suna nan kalau"
"suna nan lafiya " tace tana gaisheku"
mama Raliya tace"
"Ina masawa" sannan tace da fatima wacce ta jawo
karamar kujera dake a kusa da ita ta xauna"
.
.
"Oh fatima shi kenan kuma daga kun gama
makaranta sai ya yada juna" bake ba" ba umma
ba"
jiya nake tambayarta kina nan kuwa" tunda kuka
gama jarabawa ban sake saki a idona ba"
Fatima ta sunkuyar da kanta tana murmushi"
"mama bana nan ne tunda mukayi (candy) naje
hutu can garinsu hajiya dake kusa da dutse jihar
jigawa"
shekaranjiya na dawo"
mama Rakiya tace"
"Allah sarki" to ya kika baro 'yan uwan naku?"
"Na baro su lafiya"
mama Raliya tace da fatima"
"yanxun nan ta shiga wanda" ki jira ta yanxun nan
zaki ganta ta fito" ai taji maganarki"
.
.
Fatima ta amsa da "to mama" taci gaba da xama
tare da mahaifiyar kawarta suna hira kafin
Ummulkhaeri ta fito daga wanka"
Fatima da Ummulkhaeri kawayen juna ne na
amana" tun daga makarantar firamare har xuwa
yanxu da suka kammala karatunsu na sakandire"
suna xaman jiran fitowar sakamakon jarabawarsu"
.
.
Duk da ba unguwa daya suke ba" sun fara karatu
tare a kurna a dalilin xaman da Ummulkhaeri tayi
a wajen kanin mahaifinta wanda ya rike ta har
xuwa lokacin da ta gama firamare" sannan ya
dawo da ita gidansu wajen mahaifinta dake
Gwammaja"
Ganin yaddda suka shaku sosae kuma suke so su
rika yin makaranta daya" Da mahaifin Ummulkhari
yaji an saka fatima a wata sakandire (private) je-ka
ka-dawo" sai shima ya nema wa Ummulkhaeri
makarantar" domin tahi dadin tsayawa tayi karatu"
idan tana tare da kawarta fatima"
.
.
Haka suka kasance tare har suka kawo yanxu"
idan aka basu (assignment) a makaranta" sai su
hadu a gida suyi tare" ko fatima ta biyo
Ummulkhaeri hida" ko ita Ummulkhaeri din tabi
fatima can gidansu"
Wannan kawance dake tsakaninsu yasa iyayensu
suke jin dadi" musamman iyayen Ummulkhaeri
sun dauki fatima kamar 'yar su da suka haifa ta
cikinsu"
Idan tayi kwana biyu bata xo gidan ba" sai su
tambayi Umma ko lafiya fatima ta dauke kafarta
daga gidan"
.
.
Fatima yarinya ce mai ladabi da biyayya da kuma
kunya" shekarun su daya da Ummulkhaeri" wato
shekaru sha-tara" amma fatima tafi ta girman jiki
da kuma tsawo" sannan kuma ita fara ce" a yayin
da umma ta kasance wankan tarwada"
Fatima tana xaune a gaban mama Rakiya suna hira
Ummulkhaeri ta fito daga bayi cikin sauri daure da
xani iya kirjinta" ruwan da bai gama tsanewa ba
yana digowa daga cikin kitsonta" tun kafin ta
karaso ta fara murmushi data hango fatima"
"yar halak kinki ambato" ashe rai kanga rai?"
Ummulkhaeri ta shigo dakin mahaifiyarta tana
dariya"
fatima ta harare ta sannan ta ce"
"Ai ni ba wajen ki naxo ba" naxo ne in gaishe da
su mama in koma"
mama Raliya tayi dariya" ta saba jin irin wadannan
korafin da wasan idan fatima da Ummulkhaeri suka
hadu"
.
.
"Haba aminiyata" laifin me nayi maki kuma yau ina
murna da ganinki" kamar ranar sallah" amma xaki
bada ni"
fatima tace"
"to amma yanxu saboda Allah kin kyauta kenan"
Ace wai tun daga ranar da muka yi (final paper)
din mu" baki sake xuwa gidanmu ba ko sau daya"
Ummulkhaeri ta lallasheta"
"kiyi hankuri aminiyar" naji ance baki nan ne"
tunda mukayi (candy) kina jigawa haba! Kema kin
san da ace nasan kina nan ai dole ne in kawo
maki xiyara"
.
.
FATIMA ta rage fushin da ke a fuskarta ta ce-:
Duk da haka Umma" ai na dade a gida kafin in tafi
dutse" naso ace mun hadu kafin in tafi amma kika
ki xuwa" akwai maganar da nake so muyi dake
mai muhimmanci"
Umma ta dafa kawarta ta lallasheta"
"to aminiyata naji na dauki laifina" kiyi mani afuwa
ba xan kara ba"
A lokacin ne mama Raliya tace da su-:
"kun ga dai yanxu aiki xanyi" ina so ne in karashe
dinkin wasu kaya guda biyu" ku tashi ku tafi
dakinku" idan kuka fara surutunku sai kusa kan
mutum yayi ciwo"
.
.
Fatima da Umma sukayi dariya" suka fita daga
dakin" Umma ta rike hannun kawarta suka nufi
dakinta dake a karshen dakunan gidan" Da
xuwansu bayan sun shiga sun xauna su duka a
bakin gado" sai fatima tace-:
"Gaskiya xaman gida ya para amsarki Umma"
kinga kuwa yadda kikayi wani haske da kiba"
wallahi kin canxa kamar ba ke ba"
Umma tayi dariya"
"Lallai fatima wato abin ma har da kodawa?"
yaushe muka gama karatun da xaki ce haka?"
duka-duka bamu wuce kwana arba"in da yin (send
off) din mu ba"
Tana fadin haka sai ta jawo kwandon kayan
shafawarta ta dora shi akan gadon a gepenta" ta
dauki man shapawarta (skin light) ta bude ta matso
shi a tafin hannunta" lokacin da take mutsike da
tafin hannunta ne ta fara shapawa a hannunta da
wuyanta xuwa fuskarta" sai fatima take tambayar
ta-:
"Yaya maganar ci gaba da karatu Ummu?"
.
.
Wannan maganar da nake fada maki xamu yi" nayi
wa Hajiya maganar Inaso a siyo min (form) din
(school of health) amma banji tace komai ba har
yanxu"
Na fahimci bata cika son inci gaba da karatu ba"
kamar aure take so in yi"
Umma ta ke dhapa mai a kafafuwanta tace da
fatima" to idan hakan suka fi so ba shinkenan ba"
ni dai dama baba ya fada min tuntuni baxan ci
gaba ba" don yana maganar indai yaga mujahid ya
samu aure a wannan shekarar" to tare yake so ayi
bikin da nasa" asa rana daya ya huta"
.
.
Fatima tayi ajiyar xuciya tace da kawarta Umma'-:
"Gaskiya nidai da xa.a bi xabina nafi so inci gaba
da karatu Umma" saboda kin gani fa ko wani
kwakkwaran saurayi bani dashi a halin yanxu"
saboda nasan xanci gaba da karatu" ba wanda
nake tsayawa saurara!!"
Umma ta dauko madubi ta fara gyara gashin kanta
a lokaci guda tace da fatima-;
Duk wannan ai mai sauki ne" in dai aure xakiyi
baxaki ci gaba da karatun ba" samun miji mai
sauki ne tunda ma akwai wadanda suke son ki"
kece baki kula su saboda kina sa rai xakici gaba
da karatu" Amma idan har kowa yayi aure xa.a yi
miki" nan da nan xaki ga samari suna xuwa
wujenki"
.
.
Fatima ta dan bata ranta tace-:
Duk ba wani ya jawo mani wannan matsalar ba sai
xaßßa"u" ita ce ke tara wa mutane samari kullum a
waje" shiyasa Hajiya tace dani da ita" duk hadamu
xa.ayi bana a aurar damu" ta gaji da ganinmu a
gabanta"
Umma ta dan yi murmushi" tuni ta gama shapa
man" da ma ba wani waje xata je ba" ta dan yi
wanka ne kwao din tahi dadin jikinta"
Da fatima bata xo ba" da karatu take so tayi"
dama daxun nan da rana ta aiki kaninta Abba yaje
kasuwa ya siyo mata sababbin littatafan da suka
fito guda uku"
.
.
Umma ta tashi ta dauko karamar rigarta ta bacci ta
saka" sannan ta sa (skirt jeans) dinta mai ruwan
kasa" Fatima tana xaune tana jiranta" a lokacin ne
ta tuno da irin xaman da takeyi da xaßßa"u a gida"
Xaßßa"u kanwar mahaifiyar fatima ce" amma
budurwa ce tsarar fatima" lokacin da inna uwale
kakae su fatima taxo haihuwar xaßßa"u ne ta rasu
a wajen haihuwa"
tun xaßßa"u tana jaririya sai aka ba Hajiya binta
rikonta" a lokacin ita kuma Hajiya ßinta tana goyon
fatima" tsakaninsu ita da xaßßa"u wata biyar ne"
Don haka sai Hajiya ßinta ta hada su baki dayansu
ta shayar da su a lokaci daya" tunda dai babu inda
xa.a kai xaßßa"u"
Hajiya ßinta itace babba a wajen mahaifiyarsu data
rasu" kuma daga sannan xuwa yanxu xaßßa"u tana
wajenta" tare suka taso ita da fatima kamar
tagwaye"
:
.
Banbancinsu kawai shine ita fatima tadan fi ta tsayi
kuma da yake xaßßa"u tayi rashin lafiya mai tsawo
sa.ar da take yarinya" fatima ta wuce ta a karatu
da aji daya" don haka ita xaßßa"u sai a shekara
mai xuwa xata gama tata makarantar" wacce ita
ma je-ka-ka-dawo ce" amma ba makarantar da su
fatima sukayi ba"
Idan ba an fadi ma mutum ba" ba wanda xai iya
gane cewa xaßßa"u ba haifaffiyar gidan su fatima
ce ba" wasu da yawa suna daukar xabba"u kanwar
fatima ce" domin kuwa tun suna yara tare suka
taso kuma Alhaji sunusi mahaifin fatima baya
banbanta masu komai" tare yake yi masu" kamar
su dukansu shiya haifesu"
.
.
Fatima da xabba"u basu cika jituwa ba" kuma
rashin jituwarsu yana da nasaba ne da abubuwa
da yawa"
Na farko-: halayensu ba iri daya ba ne" xabba"u ta
cika kiriniya da rashin kunya" a yayin da fatima ta
kasance mai kamun kai da kawaici" ko kawayensu
ma ba daya bane" kowacce da irin kawayenta" ba
su cika yawo tare ba" Indai ba Hajiya bace ta aike
su tare suje su dawo"
.
.
Wani lokacin" musamman lokacin da suke yara"
sun sha suyi fada" kuma koda yaushe hakan ta
faru a tsakaninsu" Hajiya vinta fatima take ba
rashin...................TUN A DUNIYA"
.
.
.
РÁĞE
02
WĨŤH
ÁßßÁŃ ßÁŚМÁŔH
ĎÁŃ
МÚŤÁŃ YŐßE"
.
.
WANI LOKACIN" musamman lokacin da suke yara"
sun sha suyi fada" kuma koda yaushe hakan ta
faru a tsakaninsu" Hajiya ßinta fatima take ba
rashin gaskiya" tana yin haka ne domin fatima ta
rika girmama xabba'u kada ta raena ta don taga ba
'yar gidan ba ce"
Duk da fatima ta girmi xabba'u" Hajiya binta ta
hana ta ta rika kiran sunanta tsirara sai ta hada da
(Aunty)" ko kuma Umma xabba'u" saboda kanwar
mahaifiyarta ce uwa daya uba daya"
.
.
Wannan shiya jawo rashin jituwa tsakanin 'yan
matan biyu" xabba"u ta raina fatima saboda taga
Hajiya binta ta bata dama sosae a gidan" Xabba"u
takan sa fatima aiki" kuma bata isa tace baxata yi
ba" saboda idan Hajiya taji sai ta bata mata rai"
wadannan abubuwa suna damun fatima" saboda
xabba'u tana takura mata a gidansu kuma tana
jawo mata fada da xagi haka kawai saboda tana
takamar ita kanwar mahaifiyarta ce"
fatima bata san cewar tunani take yi ba saida
Umma ta girgixa ta sannan ta dawo hayyacinta
cikin sauri"
"Fatima lafiya ina tayi maki magana amma naga
kinyi shiru" wai tunanin me kikeyi haka?"
Umma ta mayar da hankalinta sosae akan fatima
wacce ta sake yin dogon ajiyar xuciya"
"Ba komae Umma kawai ina tunanin yadda xanyi
ne akan wannan maganar"
.
.
Umma ta dafa ta cikin damuwa tace da ita"-:
"kin san banaso inga kina bata ranki fatima" don
Allah ki kwantar da hankalinki komai kikaga ya faru
da mutum can haka Allah ya kaddara xai faru a
kanki"
Idan auren shiyapi alkhaeri" to kawai muyi addu.ar
Allah ya xabar maki miji nagari" Idan kuma karatun
ne to mu roki Allah yasa Hajiya ta dawo ta barki
kici gaba" amma banaso inga kina irin wannan
tunanin" kada wata matsalar ta sake ki"
Fatima tayi wa Umma godiya" bayan sun kare hira"
xuwa can kusa da faduwar rana sai tace xata koma
gida" fatima ta tashi ta dauki hijabinta data cire ta
ajiye" ta sake xura kanta ta sa"
Umma ta ce"
"Ai nagode sosae" kuma In Allah ya yarda nima
xaki ganni nan da kwana uku"
Fatima tace-:
"In ma baxaki xo ba ai kinsan kwanan xancen" don
kuwa kada kiyi tsammanin nan da shekara daya
xaki sake gani na anan gidan"
.
.
Umma wacce ita ta saka nata karamin hijabin" ta
raka ta suka fito wahe" sun nufin dakin mama
Raliya kenan xasu je fatima tayi mata sallama" sai
ga mujahid yayan umma" ya fado gidan cike da
farin ciki"
Mujahid wankan tarwada ne mai manyan idanu
wanda kamanninsa suka xo iri daya da kanwarsa
Ummulkhaei" shekarunsa Ashirin da takwas" yayi
digirinsa a shekarar da ta gabata kuma ya dara
aikin bankin da ya samu wata uku da suka wuce"
tun kafin tace dashi sannu da xuwa ya ciro sabon
makulli ya daga shi saitin idanunta yace da ita
cikin wasa da farin ciki-:
"Albishirinki"
tace-:
"Goro fari fat!
Mujahid yace da eta"
"An bani sabuwar mota wacce xan rika xuwa aiki"
Umma ta rike numpashinta"
"wow! Da gaske yaya mujahid?"
yace da ita"
"tana nan a waje naxo da ita ma"
Umma ta fara murna"
"Congratulations....... Na taya ka murna yaya......"
.
.
Tana cikin xumudin taya shi murnar ne sai fatima
dake tsaye a gepe daya tana sauraren su ta
gaeshe shi"
"Ina wuni yaya?"
ya ce
"lafiya lau"
Bai gane fatima ba har xuwa lokacin da ta taya shi
murna ita ma"
"muna murna yaya! Allah ya tsare" Allah ya kara
budi"
yace cikin farin ciki"
"Nagode, Nagode"
A lokacin mama Rakiya ta leko daga dakinta"
"Hayaniyar me kuke yine haka" lafiya?"
kafin mujahid yayi mahana sai umma tayi farat ta
cewa mahaifiyar tasu"
"banki ne suka ba yaya mujahid mota"
.
.
Mama Rakiya tace"
"A.'a'a. Abin arxiki" ba shakka" Allah yasa alheri"
mujahid yace da Umma"
"yanxu kamata yayi kuxo in dauke ku keda kawarki
in kaiku inda kuke so" kuyi dani"
fatima tayi dariya" umma ta tambayi mujahid"
"yaya naji kana cewa kawata" wai kai baka gane ko
wacece wannan ba?"
mujahida ya dubi fatima sosae" yayi tunani amma
ya kasa tunda inda ya santa"
"ban gane ta ba" Umma wacece!"
mama Raliya tayi farat tace"
"Lah! Kai kuwa meya sameka"? Ko duk xumudin
sabuwar motar ne yasa ka mance da fatima?"
.
.
Mujahid ya buda baki cikin mamaki"
"fatima?" ya dubeta" yanxu fatima ce dama ban
gane ta ba?" wallahi naga tayi girma ne" in banda
kun fadamin" ko a hanya naganta baxan gane ta
ba"
fatima taci gaba da murmushi" mujahid ya santa"
tun tana karama take xuwa gidansu wajen Umma"
to amma yakae shekara hudu bai ganya ba" tun da
ya fara karatu a jami.ar tafawa balewa dake bauchi
bai sake ganin fatima ba sai yau"
.
.
Yayi mamaki da yaga ta xama hadaddiyar
budurwa" tayi hankali" ta xama mace sosae"
yace da ita"
"fatima kiyi hankuri don Allah" ban gane ki ba ne"
kinsan mun dade bamu gaisa ba"
tace dashi cikin kunya"
"ba komai yaya"
"naga kamar tafiya xatayi" kuxo muje fatima"
saimu kaiki gida nida umma a mota"
Fatima tace"
"kada mu wahalar da kai yaya mujahid" kabarshi
kawai Nagode"
.
.
Mama Rakiya tace
"A.a kuje ya kaiki gida mana fatima" tunda ga
mota kuma ai xaifi"
"to mama mun gode" bari in tafi sai kuma na
kwana biyu"
.
.
MAMA RAKIYA tace-:
"ke xa.ai wa godia fatima" in kinje kice da Hajiya
ina gaisheta"
"to mama" xataji" sai anjima"
fatima tayi sallama da mama Rakiya" Ymma da
mujahid suka raka ta xuwa waje inda xasu hau
mota su kaita gida"
.
=======>++++++<========
:
Suka shiga mota su uku" fatima ta xauba a gaba
tare da mujahid" ita kuma umma ta xauna a baya
inda tafi so"
muhajid ya tayar da xukekkiyar motar sa (camry)
ya tuka suka tafi"
Umma dake xaune ita kadai a baya tace"
"kai yaya muhajid motar taka akwai dadi gaskiya"
mujahid yace da ita cikin wasa"
"xaki fara yiwa mutane kauyancin naki ba"
Umma tace cikin shagwaba"
"kai yaya" ina 'yar birni gaba da baya" kace dani
'yar kauye"
.
.
Yayi mata dariya" a lokacin ne ya fito daga layinsu
ya hau titi yaba motar wuta suka ruga a guje
kamar suna tafiyaa cikin iska"
fatima ta ce-:
"Nima dai don kada ace mani 'yar kauye dana fadi
nawa santin" yaya mujahid wannan motar taka ko
jirgin sama ai sai haka"
mujahid ya dan juyo cikin dariya ya dubi fatima"
"Ni kuwa kinga dai har na yanke shawarar a satin
nan xan sayar da ita in canxa wata (camry 11)
nake so suka bani...


Read / Download TUN A DUNIYA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album