Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

HUSNAH KO BADIYAT Complete Hausa Novel Document by HUSNAH KO BADIYAT


HUSNAH KO BADIYAT

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 33780



HUSNAH KO BADIYAT

Reading Time: 2 Hours

Added On: 06, Jun 2024

Author: Yusrah Musa Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ANNURI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 234 905 527 3614

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 181.41 kb

File Type: txt

Views: 651+

Download: 530+

Last download: 3 days ago

Description/Story: [08/23/05 08:18pm] Yusrah Musa Abubakar.

Cikin biyu ✌️
* HUSNAH KO BADIYAT*


}{SHORT STORY}{

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
Home of hospitality and harmony

Mrs Al'ameen Ahmad ce
WHATSAPP NO: 234 905 527 3614.

YUSRAH MUSA ABUBAKAR
MAMAN FATEEMA ELHAM
(*()*) (*(*()*)*) (*()*)

In the name of Allah the most benefits and the most merciful we love our nabeey we like him and peace be upon him ameen.

Dedicated to
ANNURI'S WRITER'S ASSOCIATION GROUP MAY ALLAH ACCEPT YOUR DUAS MAY ALLAH HELP YOU AND PROTECT ANY WHERE YOU ARE AMEEEN👏.


Mrs Al'ameen Ahmad ce 🌹.

PAGE 01 to 05.
Wani 'karamin gida ne mai dakuna biyu wanda kana gani iya yanayin sa ko ba a fada ba kasan gidan haya ne duba da cewa komai a matse yake.


Zaune wani farin tsoho yake gefen sa kuma wata mata ce itama fara da sanda a kusa da ita Wanda alama ya nuna tana da ciwon kafa dashi take amfani gurin tafiya.

Hira suke sosai jin sallama yasa suka amsa baba dake kallon saitin inda akai sallamar yace.

"Sannu da gajiya kinji Asma'u ya karatu"?.

Zama wata kyakkyawar budurwa ta tana kallon su cikin nutsuwa tace "alhamdulillah baba ya gida kuyi hakuri ban dawo da wuri ba na barku da yunwa jarrabawar yau dince ta dauke mu lokaci kuma zan taho Fatima tace na tsaya idan aka zo daukar ta sai mu taho tare".


Murmushi baba yai yana cewa "kai Husnah irin wannan dogon bayani haka ai sai kisa kaina yai ciwo buri na ace kin dawo lafiya shine fata na".

"Lafiya kalau baba kallon matar tai cikin muryar shagwaba tace "innah muna ta magana kinyi shiru kin 'ki saka baki ko laifi na miki"?.

Dariya Innah tai tana cewa "oh ni Husnah rigima kin girma fa kodan baki da 'kani shiyasa kike jinki yarinya to ya makaranta fatan kin dawo lafiya".

Kaita daga "lafiya na dawo Innah ta bari na tashi na sama muku abinda zaku ci".

Hanyar kitchen ta nufa yayin da suka bita da kyakkyawar addu'ar jin dadin kula dasu da take da nuna musu kauna.

Saida ta Dora farar shinkafa sannan ta fito tana yin alwala ta shiga daki domin yin sallah.


Bayan ta idar fitowa Tai tana komawa kitchen ta duba sannan ta leko tana cewa.

"Gaskiya yau miya za ai domin shinkafar tana kyau bari naje na sayo".

" Husnah mu da muke tsofi basai kinyi mana wani 'kyale-'kyale ko fara kika mana da yaji zamu ci".


"Allah baba ta miya zata fi dadi Bari na je nasayo Dan yau harda nama zaku ci" tana fadin haka da sauri tai waje kafin baba yai magana.

Kai Innah ta girgiza tana duban baba tace "abin da take so yau din muci kenan saidai Allah ya mata albarka".

Da kamar minti biyar ta dawo tana dariya ta shige kitchen tana fara hada miyar.


Saida ta gama sannan ta xubo a babban faranti tazo tana zama a tsakiyar su tare da gaurayawa cikin so da kauna suke cin abincin.


Yayin da idwn ta debo saita bawa Innah a baki sannan ta sake debowa ta bawa baba.

Suna matukar jin dadin yadda take nuna kulawar ta a gare su suna farin ciki da samun ta matsayin d'iya a gare su.

Saida suka gama ta tabbatar sun koshi ta dau ture din tana komawa kitchen ta wanke kayan data 'bata ta fito kenan.


Yaro ya shigo yana cewa "wait wani yace Husnah tazo".

Hade rai Husnah tai tana kallon sa tace "kace bata nan".

"To yaron yace zai juya baba ya dakatar dashi yana cewa.

"Asma'u baki san waye ba kije ki duba".

Kallon baba Husnah tai tace "baba bazai wuce Sadiq ba domin na wuce shi a majalisar kofar gidan alhajin da muke hayar gidan nan a gurin sa".

"To me zaki masa yake neman ki"?.
Husnah dake hararar kofar gidan kamar shine a gurin tace "babu abinda daya taba hada mu bansan neman me take min ba".

Tana fadin haka ta shige daki shiru baba yai zuwa wani lokaci yace.

"Lamarin yaron nan yana bani mamaki to kodai sonta yake nifa bana San irin wannan abun ina zaune da yarinya ta lafiya azo a daga min hankali".

Innah ma da yawan n turowa da Sadiq din take neman Husnah tace "nikam da tun kwana baya zanyi magana kuma na fasa amma muci gaba da addu'a idan shine alkairi a gare ta Allah ya Tabbatar idan babu alkairi Allah ya raba ta cikin ruwan sanyi".

"Amin" baba yace daga haka suka dau wata hirar dabam suka manta da wannan zancen.


Mrs Al'ameen Ahmad ce 🌹
YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA


Na gode da kulawa tnk 4 ur supports may Allah open the door of success and happiness 4 all of u Muslim Amin👏🥀✨.

ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
Home of hospitality and harmony

Allahumma salli wa salli ala sayyidina Muhammadin sayyidil mursali na.


Mrs Al'ameen Ahmad ce 🌹
PAGE 06 to 10

Wani 'kayataccen gida ne Wanda ya shahara wajen tsaruwa da kyau fadar kalar daular sa bata 🕚 ne.

Zaune wani farin kyakkyawan saurayi yake cikin palon da laptop a gabansa yana aiki bayan sa wata budurwa ce ta tsaya ta bayan kujerar ta sakalo hannuwanta ta wuyan sa tana kallon abinda yake yi.

Fitowar wata mata ganin su yasa ta girgiza kai tana karasawa tace.

"Sannun ku da hutawa".

Duk su biyu dagowa sukai suna kallon ta taci gaba "wato Zarah dama da nace kije kitchen gurin Rabi ta rika koya miki yadda ake sarrafa komai shine kikayo nan kinsan dai abin kunya ne ace kamar ki ayi auren ki baki it's komai ba".

Sakin wuyan sa Zarah tai cikin shagwaba tace "Allah umma naje tun dazu gajiya nai shine shine naxo in huta ban dade da zuwa ba kuma ki tambayi ya Aliyu kiji".

"Ni bazan bata lokaci na natambaye shiba bayan bakin ku daya maza tashi ki koma bansan shirme".

Mikewa tsaye tai tana cewa "Amma umma Badiyat tana can tana bacci ita baza ta zo ayi aikin da ita ba"?.

Kai umma ta daga "eh baza tazo ba ina ruwan ki da ita ko ce miki tai bata iya girki ba"?.

Zarah zata magana umma ta katse ta "nace maza ki wuce yanzu ko".

Juyawa tai Tana nufar hanyar kitchen din umma data mayar da hankalin ta kansa tace.

"Haidar ka shagwaba yarinyar nan da yawo gashi har yanzu taki maida hankali ta koyi girki".

Shiru yai Saida ta sake magana ya dago yana kallon ta cikin muryar shi nutsatstsiya yace.

"Umma duk duniya bani da wacce zan kalla naji dadi ko nayi alfahari idan ba Zarah ba ita kadai ce sister na yar uwata jini na 'kanwa ta dukkan soyayya ta tana gurin ta da ban debe kewa da ita ba dawa zan debe"?.

Cikin tsokana umma tace "idan wacce zata debe maka kewa kake nema sai kai aure".

"Ba yanzu ba umma".

"To sai yaushe"?.

"Ba Rana bana jinsa kusa".

Juyawa umma tai zata bar gurin tace "shikenan Haidar Amma nikam ina jinsa a kusa" tana wucewa ciki.


Rufe laptop din yai yana jingina bayansa jikin kujerar tare da rufe ido alamar ya gaji hutawa zaiyi.

Da kamar minti goma wata budurwa ta shigo palon tana hamma alamar daga bacci ta tashi ganin sa shi daya yasa ta karaso tana zama kusa dashi.

Tace "good morning ya Aliyu fatan ka tashi lafiya"?.

Bai ko motsa ba balle tasa ran zai bata amsa.

Muryarta a damuwance tace "wai dan Allah ya Haidar meyasa kake min haka ne sai ka rika share ni idan na maka magana nima fa yar uwar kace kamar yadda kake ji da Zarah ya kamata ka saurari hanzari na".

Jin har lokacin ya mata banza bai tanka mata ba yasa ta kalle shi idonta na kawo hawaye.

Daidai shima ya bude idon sa sai cikin nata dauke kai yai yana bude laptop yaci gaba da aikin sa kamar baisan da wanzuwar wata halitta a gurin ba.

Cikin jin haushi ta mike tana barin gurin ta nufi dinning tana 'kwalawa yar aiki Kira".


A guje ta karaso tana durkusawa gaban ta numfashin ta kamar zai fita tace.

"Gani aunty".

Xama Badiyat tai tana cewa "yi serving dina abinda ya Aliyu yai breakfast dashi".

Shiru yar aikin tai cikin jin tsoron me zata ce tsawa Badiyat ta daka mata tace.

"Ke dabba uban me kike kallo cewa nai ki serving din".

Jikinta na rawa kamar yadda muryar ta keyi tace "kiyi hakuri yau baiyi breakfast b.............


Bata karasa ba Badiyat ta dauke ta da mari cikin bacin rai tace "bace min da gani kafin na zubar miki da hakora banza jaka yar kauye kawai akuya".

Da gudu tabar gurin rike da kunci tana kuka batasan me taiwa wannan budurwar ba tun ranar da tazo gidan nan shikenan ta hana ta jin dadi gara ta cewa baba raba ta gaji tayi magana a sallame ta ai talauci ba hauka bane.

Mikewa Badiyat Tai tana komawa cikin palon ta zauna tasan saboda ita ne Haidar ya daina cin abincin gidan Amma baby komai tara shi take.


Zarah ce ta fito tayi tumu tumu
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download HUSNAH KO BADIYAT

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album