Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

FIL'AZAL Complete Hausa Novel Document by FIL'AZAL


FIL'AZAL

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 36775



FIL'AZAL

Reading Time: 3 Hours

Added On: 04, Jul 2024

Author: Sa'adatu Bintu Abdullahi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : 08101626484

Book License : Free

Category: Romance 18+ Novels

File Size: 212.54 kb

File Type: txt

Views: 4125+

Download: 4190+

Last download: 6 hours ago

Description/Story: 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
FIL’AZAL
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
💖💖💖💖💖💖💖💖
(Romantic and love story)

SAADATUBINTUABDULLAHI✍🏽(Writer of Kyautar Allah)

Bismillahirrahamanirrahim🤲🏼
AlhamduLillah am back again.
Free page1
*Kaduna state, Malali GRA Sani Sami Close.*
A hankali yake sakkowa daga kerarriyar matattakalar benen, kafafuwannan nasa fari karr kmr a lashe kai bakace ya taba taka kasa bama da kafafuwan nasa,. Yayinda lallausar hannunsa me kama da lambun farar Audiga yake rike da wayoyinsa guda biyu, daya kirar Samsung dayar kirar Iphone X. Yanada kudin daze rike wayar billions of naira , sbda shidin ba karamin me rufin asiri bane, ubangiji ya masa Arziki sosai fiye da tunanin me karatu, Arziki irin wanda ya gajesa a gun mahaifinsa Sarki jikan sarki. Kwata-kwata shi ba mutum bane da duniya ke gabansa, hasalima duniyar bata masa dadih, a kullum in zaka kalli fuskarsa Zakasan kawai rayuwa yake a duniya amma Sam bayajin dadinta, Daka kallesa dole Zakasan yana cikin Jarrabawar rayu. Sanye yake da wani danyen boil light ash color , irin ligt dinnan sosai. Boil din me sheki da tsantsi, dinkin riga da wando. anyi masa dinkinne irin na dattako, wato de dinkin manyan mutane, yayinda aka kewaye wuyar rikar jikin nasa da wani siririn aiki baki mara hayaniya, irin na manyan mutane. A yadda naga boil din nasa na sheki ya tabbatarmin da dolema zeyi tsananin tsada,. Kansa sanye da black din huta wadda tasha zanen aiki irin na zamani, aikin hannu ce hular ammafa irin wadda turawa sukayi Aikin danni ban taba ganin hula me kyau irin ta kansa ba. Lallausar fararen kafafuwansa sanye da black shoe me kyau dagani shoe din bame nauyi bane, Sam shi bayasan abubuwa masu nauyi shiyasa yana tsananin san boil yard ba kasafai ya fiye mu’amala da shadda ba sbda tana masa nauyi , Sam besan harkar hayaniya, saboda shi mutum ne da bayasan abinda ze takurasa, sbda yanada tsananin Jin zafi, a bedroom dinsa kusan AC uku garesa, manya-manya, baya iyayin bacci in AC be ratsashi ba, duk inda yake shiga akwai AC a gidansa, hatta da corridor dinsa akwai AC, Kitchen AC, toilet AC, matansa sam basa iya jimawa in suka shigo part dinsa sbda tsananin sanyi kai kace a cikin frij kake, ko a cikin ruwan teku. seshi din daya saba zama yake iya zama. Kuma ba wani jiki bane dashi, bashi da kiba kuma shi ba siriri bane, irin mazannan ne masu cikar zati da cika ido amma Sam bashi da kiba, sede yanada kirar karfafa,. launin fatarsa irin launin ruwan fari ne, ga farar fata ga Hutu AC to AC, Innalillahi wa’inna ilaihirraju’un! Wayyo Kyau!! , jikinnan luwai-luwai, kamar ataba jini ya bulbulo!, tako ina a jikinsa luf-luf yake da Gashi musammanma hannayensa da kafafuwansa yanada Gashi zara-zara tamkar akama a kitsa.. Yanada tsananin kyau, kyaun da harshena baze iya misaltasa ba, dogo neshi sambal ba gargad’a, yanada Dara-daran idanuwa, luhu-luhu, yayinda idanuwan nasa suka kansance a kullum sanye cikin farin siririn glass, medical glass, sometimes be cika gani kwarai ba inba glass a idonsa, musammanma in da daddare. Yanada dogon hanci yayinda yakeda madaidaicin baki, yanada kasumba, madaidaiciya, bakaramin kyau kasumbar ta kara masa ba Ainun, ya d’an manyanta amma hakan be girgiza tsananin zallar madarar kyaunsa ba, kyaune ya hadu da Hutu da kudi. , a kallah ze Kai 50yrs. Amma Inba an gaya maka ba baka isa ka gano hakanba, shekarun nasa sun buya a cikin kyaunsa da hutun dake tattare dashi, kai inka gansa ka rantse da Allah cikakken balarabe ne, saboda kyaun nasa ya wuce shahara, kyaun nasa yayi ratsa-ratsa da imanina, bantaba ganin tsarin halitta irin nasa ba, lafiyayyen namiji azahiri ga cikar zati kai dagani dole zakasan inside zeyi girman jarumar. (BURA)

A hnkli ya gama sakkowa daga upstairs din. , yayin da cikin sassarfa yake tafiya amma inka kallesa zakasha a hankali yake tafiya yanada tsananin sauri, wato yanada zafin nama, ba kasafai ake iya binsa a jere ba in suna tafiya da mutane, sbda yanada sauri, abunka da dogon Namiji. Se zuba kamshi yakeyi, na perfumes dinsa masu tsananin tsada, yanasan kamshi, yana kashe kudi kwarai a kan turaruka sekace mace, in takaice muku yafi wata macenma San kamshi shifa Sam baya mu’amala da datti ko kazanta, yanada tsananin tsafta ta fitar hankali. A hankali ya sauke idanuwansa kasa ya kalli dankareren watch din dake manne a tsintsiyar lallausar tubus din hannunsa wanda ke cike da suma. dai-dai watch din hannun nasa ya buga karfe goma da minti asirin na safe,Adai-dai lokacin kuma wayarsa kirar samsung ta dau rurin bukatar agaji, Ya duba yaga lambar Dreva dinsa ne kuma babban Amininsa tin Tala-Tala Malam Abdullahi wanzan. Dagawa yayi ya kara a kunnensa, ba tare da yace komi ba. Daga cikin wayar aka fara magana “Ranka ya dade JAROOD har yanzu baka fito ba,,,Gashi Giwar sarki nata kirana..” (mahaifiyar Jarood kenan ita ake kira da giwar sarki) dan guntun numfashi yaja hadi da langwabar da Kai ya danyi jim for some seconds kana yace “Ganinan fitowa insha Allahu…” malam Abdullahi Dreva wato wanzan Yace cikin girmamawa “Allah fiddoka lafiya ranka ya dade, fari me farar Aniya dogo tsayuwarka tafi tsayuwar gajeru dubu, Allah ya ja ranka dan tsarki jikan sarki, yarima me jiran gado, tureka se Allah yayi, kai kainuwa ne ba a shukakaba sede akaga fitowarka…” wani guntun murmushi yayi , me dauke da siririn sauti, yayinda kirarin Wanzan ya bashi nishadi, ya jinjina kai kana Ya amsa da Amin daga bisani ya katse wayar. Direct ya nufa kofar dazata kaisa part din Hajiya Zulaihat wato uwar gidansa kenan ta Auren saurayi da budurwa Yana tafe yana bin ko ina da kallo a gidan, gidan ya tsaru iya tsaruwa, babu abinda babu a ciki na morewa rayuwa, komi na duniya ubangiji ya basa, sede yanaji a ransa Ina ma za a kwace komi na more rayuwa a bashi abu daya Rakk daya rasa a rayuwarsa, Wato martabarsa da kimarda ta d’ana miji, lokuta da dama shida kansa yanajin ya tsani kansa, Amma yazeyi da jarrabawa,.

Tsayawa yayi cak dai-dai tsakiyar babban falon hajiya Zulaihat. Ya juya ya kalli ko ina, komi yaji, kama daga kan kujerun falon zuwa komi da komi Army green ne and nude color, tako ina adon sarautane a falon nata. komi ya tsaru an narka Dukiya damkam a falon nata. Kallon ko ina yakeyi amma Sam hankalinsa be kam abinda yake kallo, kyakyawar zuciyarsa fal tunani tunani, nan take yaji wani siririn hawaye ya wanke masa kunci, cikin hanzarin ya zare glass din idonsa ya goge hawayen da hannunsa, hadi da saita kansa, yaja numfashi me tattare da rashin jin dadih a can kasan zuciyarsa. Ganin be ganta a falonba ya nufi bedroom dinta, daman yasan mawuyacine ya ganta a falo a wannan lokacin, yasan war haka time din bacci tane. A hankali ya tura handle din kofar bedroom din-nata yajisa a bude dan haka yasa Kai bakinsa dauke da sallama. Yana shiga Dakin beyi wata-wata ba ya kara Karfin Sanyin AC din dakin sbda ya masa kadan. tana jinsa tayi kmr batasanma ya shigo ba dayayi sallama ma Ciki-ciki hajiya Zulaihat dake kwance kan dankareren gadonta ta amsa,. Komi na dakin army green ne and nude color, Green ne favorite color din JAROOD, dan haka komi na gidan akwai green. Kasancewar dakin akwai haske kadan , hakan ya bawa JAROOD damar ganinta kwance. “Mace har mace …” ya fadi a ransa hadi da binta da manyan idanuwansa, masu kashe ruhi, da zukatan masu imani. Ta dago da kyar ta masa kallo daya ta dauke kai a zuciyarta tace “a zahiri kmr namiji nan ko duk a banza ba amfani, bura kamar lagwani a cikin kerosine,….” A hankali JAROOD cikin takunsa me fitar da Sirrin kyau ya karaso gefen gadon da take kwance ya zauna d’an nesa da ita, shi Sam baya zama kusa da mace sbda koya zauna kusa da ita bejin komi, Sam-Sam shifa wlhi bayajin sha’awar duk wata mace duk kuwa kyaunta da zatinta shi baya gani sam. Tinda uwarsa ta kawosa duniya be taba rike hannun diyya mace ba, inba hannun mahaifiyarsa ba. Tsurrr ya kara tsurawa hajiya Zulaihat din idanuwansa narkakku kmr na masu jin bacci, kallanta yakeyi Amma a kasan zuciyarsa yasan yana tausayin hajiya Zulaikha kuma yana santa, itadin tazama jurau a fagen rayuwarsa. Sam hajiya
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download FIL'AZAL

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
1 Comments On FIL'AZAL
avatar
nana-4-8

7 months ago

Reply

Mungode Allah ya qara basira

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album