Join Our WhatsApp Group

CANJIN RAYUWA Complete Hausa Novel Document by CANJIN RAYUWA


CANJIN RAYUWA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 133517CANJIN RAYUWA

Reading Time: 11 Hours

Added On: 07, Sep 2023

Author: Halima K Mashi ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 679.69 kb

File Type: txt

Views: 9092+

Download: 9198+

Last download: 1 day ago

Description/Story:
CANJIN RAYUWA
Halima /k Mashi
Creat:- Shuraih Usman
Littafi na daya 1
Domin dauko wasu hausa ebooks din ko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin hausa ebooks, sai ku ziyarci shafinmu na internet akan wannan Adireshin zaku samu http://shuraih.waphall.com


CANJIN RAYUWA (1)
Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu.in an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar. kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin. ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi.ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi shiru. sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri.in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (2) sannan ya kashe wayarsa. ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so.a fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya. Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa. Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family. hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (3) Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani.hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya,ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta,bare wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa dakinmu,hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin. hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke. hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa. sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (4) Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai yazo ya fada min. Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare. Direba yayi sallama cikin girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in'ina yace eh naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya ce zan kiyaye insha allah. Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma,
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (5) Shima pink bai rufe dogon gashinta ba. Kafarta sanye cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun 'yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade. shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi datti,ya yi 'yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi. Ta kalli mijinta, sannu da zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining.
[01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (6) Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata.ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba?ya kalle ta cikin 'yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani.ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko?ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba.amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba. Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata?na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata?MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can. Sauda!alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da 'yarki ta cikinki amma ba ki...


Read / Download CANJIN RAYUWA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

1 Comments On CANJIN RAYUWA
avatar
mariya-6-8

2 months ago

Reply

In HAUSA language

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album