Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MA AIKACIYAR GOMNATI Complete Hausa Novel Document by MA AIKACIYAR GOMNATI


MA AIKACIYAR GOMNATI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 111282



MA AIKACIYAR GOMNATI

Reading Time: 9 Hours

Added On: 13, Aug 2024

Author: Asma Baffa ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : +234 8061929616, 08033933642, 09032409668, +227 90795939

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 587.86 kb

File Type: txt

Views: 802+

Download: 2575+

Last download: 4 days ago

Description/Story: COMPILED BY
ESHATT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTS
WASAPP 08066360176


MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

1


By
Asmabaffa


Masoyana naga sakonku sosai na yabo da jinjina kan novel dina na maraicin rahma,ban San Kalmar da zanyi amfani da ita ba wajen gode muku,na gode kwarai Allah ya bar kauna,Allah ya biya muku dukkanin bukatunku na alkhairi.




LONDON na nufa a 80 jirgi ya saukeni da kyar na hada kudin zuwa ma sabo da jin dadinku readers bazan bari ya wuce Ku ba,wani gida Wanda ya amsa sunansa gida ko a kasar ba duk gida ba,ko ina ya tsaru wani handsome na hango narke a 3seater yana latsa wata dankareriyar iPad ga wata computer new design itama iPad a gefe yana ta aiki ciki hade da danna waya,tun daga yatsunsa nasan kudi da Hutu hade da jin dadi sun ratsashi,don guy karshene wajen haduwa da kyau OMAR MOHD OMAR kenan dan kimanin 35yrs sunan kakansa yaci.Baban sa mohd Omar Ibrahim shahararren dan boko ne kuma dan kasuwa kuma dan siyasa,shi kadai tilo iyayensa suka Haifa kafin rasuwarsu,yan asalin jahar gombe ne,fulanin gombe,babansa ya tsaya masa yayi karatu kafin rasuwarsa,yanzu kam mohd Omar sai yan uwa da suke gombe kawai suka rage masa,yana musu alheri da ziyartarsu, dattijon kirki yayi aikin gomnati kala kala,ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka ambassador ne na Nigeria a Russia.ga kamfanoni da yawa,harkar business iri iri,ya Tara dukiya kadarori barkatai,a takaice dai hamshakin me kudine na gasken gaske dake zaune a abuja birnin tarayya.yana da mata biyu hajia amina itace uwar gida tana da yara uku dan Allah bai bata haihuwa da yawa ba,Omar shine na farko,sai abdullah dan 18yrs sai autarta suleim yar9yrs.matarsa ta biyu hajia rahina yaranta duk matane guda 5 sadiya 27yrs,Aisha 25yrs,zainab 23yrs,naja 21yrs sajida 15yrs autarta.hajiya amina yar kauyen gombe ce,dan haka batayi karatu ba iyakacinta secondary shima bayan mohd Omar ibrahim ya aureta ya sata tayi.ita bata aiki bata zuwa ko ina ta rike yaranta ta basu tarbiya tare da mijinta,

Rahina kuwa da yaranta uku manya duk suna aikin gomnati sunyi degree,kullum sai iyayi a hau mota fuuuuuuu ko wacce ta tafi aiki,in salary yazo ai ta gasa da juna. Baffa yayi yayi su fito da miji tunda sunyi degree amma sunki,shi yasa gidan ya Tara mata rida rida.gashi na bangaren amina sune sukafi kowa kyau,musamman Omar,shi yasa suka kara tsanarshi.

Basa zaman lfy ko kadan, dan hajiya rahina bata kaunar hajia amina da yaranta,dan amina tana da maza ita bata dasu,ganinta zata fita cin gado,gashi alhaji mohd yafi son amina da yaranta musamman Omar,da wannan yasa rahina dagewa lallai yaranta mata baza suyi aure ba sai ko wacce tayi degree tana aikin gomnati,suma yaran nata a akidar haka suks taso kuma halinta kaf suka dauko,ga karya,rashin mutunci da nuna su wasu ne,a junansu ma basa zama lfy,daga munafunci sai fada a titi,sai gasa da junansu ko wacce naso taga tafi kowa,gasu da bin malamai uwarsu ta dorasu,ita kuwa Allah sarki haj amina mutuniyar kirki ce mace ta gari,abin duniya bai dameta ba,ga hakuri da addini.addua kawai take zabgawa kanta da yaranta musamman Omar dan sunfi kishinsa,shi kam Sam baya shiga harkar kowannensu sai iya nasu dan yaga kannen nasa ba tarbiya.

Kyakyawa ne na karshe ko shi yayi Kansa iya yanda zaiyi kenan,omar fari ne amma ba kal ba,dan baza ace masa chocolate ba dan ya wuce yakai fari za a kirashi,dogone amma ba zankaleleba dai dai,ba ramamme ba kuma ba me kiba ba,a tsakiya yake da kirjinsa me fadi normal,hancinsa me kyau da tsari kuma baiyi tsini can da yawa ba,gashin kansa Wanda ya tarashi luf dashi baki ga santsi da laushi kamar na India,girarsa me yawa ga kyau,idanu dara dara farare kal,habarsa me dan tsayi,bakinsa das dan daidai lips dinsa su ba pink ba amma kamar light pink.baza Ku sha mamaki ba readers sai danaga yayi daria kusan sumewa zakuyi yanda hakoransa suke yar yar farare kal kal,ga wani dimple nasa,skin dinsa sumul luwai sai taushi laushi da sheki,tana sulbi,kafarsa da yatsu hannayensa duk abin kallo ne da birgewa,cinyarsa da kaurinsa gashi kwance masu kyau,kirjinsa kuwa da sauran jikinsa das suke ba komai luwai luwai.duk inda kuke kallon da tunanin kyau na Omar ya wuce nan.kowa sai ya kalleshi,hattana fararen fata dake London yaba masa sukeyi wajen tsaruwa da kyau,

Ta bangaren halaye kuwa Omar kusan 95% yake,baya shan komai,baya ko saurarar mata duk yanda suke rubibinshi, yama tsani yan mata shi,basa gabansa,baya shiga harkar kowa,bai damu da matsalar wani ba,sai in ka nemi taimako wajensa zai baka,matsalarsa akwai zucia da saurin fushi,ga girman kai,da rashin fara'a dan baya daria ba komai ke sashi murmushi ba.yana da tausayi in yaganka cikin masifa amma shi baya shiga rayuwar wani bare ya kai masa agaji sai ka nema zai maka,baya son surutu da hayaniya.yayi karatunsa na degree a London ya karanta economics,yanzu yayi masters tuni.bangaren addini kuwa ba a cewa komai yana da haddar ya kai izu 40,banda sauran wasu littafai na addini daya haddace,kuma ba laifi yana aiki da ilminsa,yana kuma addini sosai,baffa ne ya matsa masa kan lallai sai yayi aure,yana 30yrs ya nemo masa auren yar gidan wani governor wato sahar,yar boko ce itama dan medicine ta karanta tana aiki a wani babban hospital dake abj,tana da private nata guda biyu..

Sahar kyakyawace ba laifi chocolate ce amma tsabar body cream ta dawo fara tas,ga daukan wanka ammafa in zataje aiki.bata ganin kowa da mutunci ganin tana juya naira,motocinta 4 laba laba,duk ma'aikantan gidansu tsoronta sukeyi,sabo da cin mutunci,bata da tarbiya,ba kamun kai,dan a wurin aiki har tafawa take da maza,give me five saleem bam kaji sun kashe.

Haka maza suyi ta yaban kyanta da turarenta gaskia kin hadu,mijinki ya more,tayi ta zancen batsa da mazan aiki.wasu kamilallun matan ma'aikata sunsha bata shawara amma taci musu mutunci,

Tsiyar sahar bata tsaya nan ba har kan mijinta Omar bata ganinsa da gashi ko kadan,bai San mene aure ba,bai San dadinsa ba,bai San love ba bai tabayi ba,dama baffa ne ya lika masa dole,

Sahar addini bai dameta ba,ita kawai kudi da aikin gomnati,ga kawaye marasa tarbiyya,a rana sai ta fita sau biyar kullum bata gida,da anyi magana tace aikinta.

Taki yarda ta haihu Sam tace ina bata shirya ba,bataso ta lalace,Omar ma sabo da kudinsu ta yarda ta aureshi,dan ita burinta kudi.Omar gajiya yayi da bakin cikin halinta ya tafi London ya huta,ita kuwa ko a jikinta,ya mata fada da nasiha taki ji,bata bari ya kusanceta sai in bukatarta ce,ko tana son karbar kudi wajensa,shi kuwa baya sonta bashi da feeling a kanta yanayi ne don sauke hakkin dake kansa,shi yasa ma yake tunanin anya yana da lafiya kuwa danshi bai taba jin sha'awar matarsa ba Sam,mata kuma ko inda suke baya kalla bare ya gano matsalarsa.


Amma babban abokinsa sultan yace dan baya son matarsa ne shi yasa,duk ranar daya hadu da real love dinsa zatayi busting dinsa sanannan zai tabbatar lfy yake.Omar kuwa gani yakeyi karyane kawai.yaki yarda kwata kwata,yaje hospital da dama a turai sunce lfy lau yake. Wannan kenan kadan daga the most handsome and sexy OMAR.


Ku biyoni readers yanzu akafara Taku har kullum

Asmahbaffa.
[5:06PM, 3/10/2018] ‪+234 808 522 6395‬: ⓂⓂⓂ
MA'AIKACIYAR
GOMNATI
ⓂⓂⓂ

2

By
Asmabaffa


Nigeria na dawo abuja garin da ake ji da naira.wajen gari na fita gidajen masu rangwamen gata,wanda suke kaiwa da kyar suna yar sana'a,da suke haya a wajen abuja Kafin a karasa cikin garin abuja,dai dai gefen titi na hango wata yarinya tana saida apple da dafaffen kwai,a titi take bi tana mikawa ta window na mota,apple and egg tana bi mota mota a round tana dagawa masu mota domin su siya,

Kallonta nayi
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MA AIKACIYAR GOMNATI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album