Join Our WhatsApp Group

SAFREEYYAH Complete Hausa Novel Document by SAFREEYYAH


SAFREEYYAH

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 108972



SAFREEYYAH

Reading Time: 9 Hours

Added On: 29, Jan 2024

Author: Yusrah Musa Abubakar ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : ANNURI WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : +2349055273614

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 595.4 kb

File Type: txt

Views: 469+

Download: 464+

Last download: 18 hours ago

Description/Story: [08/01/23 08:30 a.m] Typing📲



WHATSAPP NO.
+234 905 527 3614.



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
SAFREEYYAH
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
(🏡 home of hospitality👐 and harmony).

👆Gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🕊.


(Yan annuri I really love you everything about you is so good but one thing is wrong that you are not mind wannan haka yake).


Yusrah Musa Abubakar.

DEDICATED TO
MY MUM I LOVE YOU WITH ALL MY BODY AND HEART YOU ARE THE BLOOD THAT SCULATED IN MY HEART YOU ARE MY LIFE I LUV U💝 MAMANA.




Some say hello some say hay but in islamically said:Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu.



In the name of Allah the most benefits and the most merciful da sunan Allah buwayi gagara misali tsira da aminci su tabbata ga masoyin mu Muhammad rasulullah s a w we love our Nabeey we like him and peace be upon him AMEEN🙏👏.




🕌🕋🕌
Happy Juma'at Mubarak to all Muslims and it's Friday don't forget to recite suratul-Al khaf, I am so blessed to be a Muslim Alhamdulillah.



(*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*)
📖Littafin 👉 Safreeyyah is a fiction
'kagaggen labari mai zaman kanshi sa annan banyi amfani da tunanin wani ba zallar basirar da Allah yaban ce please 'yar uwa ko d'an uwa marubuci ko marubuciya irina wanda taga littafin kuma taga wata kalma daidai da (A)👈 wanda tayi yanayi da wani littafin ta data taba rubutawa to tayi hakuri 🙏kuskuren basira aka samu tunanin mu yazo daya😜, na gode Yusrah ce👌.


Ayi hakuri idan an samu typing error🚨.


#YUSRAHMS#
NO.01👉 02


Zaune take a kofar daki ta rafka tagumi naban tausayi da alama ko sanin hawaye sun jike mata fuska batai ba saboda irin tunanin datayi zurfi a cikin sa bangare guda kuma wutar data hura ce batasan ta mutu ba.



Fitowar wata mata daga daki kenan ganin abinda ya faru da wutar ta yasa ta karaso a fusace tana sauke mata wani irin duka a bayan ta cikin tsawa tace"lallai Safara'u tunanin ubanki kike har kika bar min wuta ta mutu saboda baki gaji arziki ba shegiya dangin tsiya wallh ko kukan jini zaki wahala yanzu kika fara sha .



A matukar zarane wannan kyakkyawar budurwar ta dago da manyan idon ta farare tas wanda a yanzu kukan da take sun koma ja tana kallon wacce ke tsaye a kanta batai zato ba ta sake jin saukar mari a fuskar ta wanda saida ta kifa kasa daga kan kujerar da take.



Rai bace matar tayi kanta tana kara rufe ta da duka tace "shine zanyi miki mgn ki tsare ni da wadannan mayun idon naki masu kala dana mujiya bankadaddiya wallh na sake fitowa naga wutar nan ta mutu saina kusa kashe ki "ta karasa mgnr tana kai mata hauri da kafa ta kuwa same ta a ciki.



Ba shiri ta saki kara tana rike cikin sbd azaba agurin ta kwanta tana murkususu tsallake ta matar tayi tana cewa"Allah yasa ki mutu kafin na fito da wallahi naji dadi na rabu da kaya me za'ai da rikon dan wani hakan ma dan kishiya aikin banza gayyar tsiya"daki ta wuce bata damu da yadda taga tana juya kanta alamar wani abu ya same ta ba.


I

Shigowar wani dattijo kenan ganin ta kwancce yasa ya saki ledar dake hannun shi kayan cefanan daya sayo suka tarwatse a kasa da saurin sa ya karaso yana daga ta ganin yadda jini ke fita a hancin ta cikin tashin hankali ya soma kwalla kira "ke Asabe ke Asabe kina ina ne me ya samu Safara'u jini yake fita daga hancin ta".


Jin shiru ba'a amsa masa ba gashi ta fara amai harta bata masa kaya sai kawai ya mike yana daga ta Aisha ce ta shigo daidai zai fita a gidan rike da Safara'u.



Hankali tashe tace "baffa lfy me ya same ta "bashi da bakin mgn kawai cewa yay taje gida maza tace yayan ta Murtala yazo zai kaisu chemist za a duba ta.



Da gudu Aisha ta juya tana kuka yayin da baffa ya fita da ita kofar gida da yake makaranta ce dashi dukkan almajiran dake karatu acan dan nesa da gidan karkashin wata babbar bishiyan dorawa suka taso da saurin su suna cewa"malam lfy?"kai ya daga musu gabadaya ya kasa mgn.




Suna haka saiga murtala da wani dan jitan dinsa na talakawa bayan sa kuma Aisha da babarta basu tsaya tambayar me ya faru ba kawai dora safara'un sukai a bayan mashin din babar Aisha ta hau domin ta rike ta Baffa da aisha suka bisu a baya.




Jin mashin ya tashi yasa Asabe fitowa tana jan tsaki tai gurin wutar ta tana gyara itatuwan ta sun riga sun daina ci ita kadai sai tsine tsine take kuma tana fatan Allah yasa kada su dawo da Safah a raye saida ta maida wutar yadda take ta mike kenan ta gano kayan miya a barbaje alamar ya shigo rudewa tasa ya zubda bai kawo mata ba karasawa tay da kwano tana bi tana debewa tace"dole ka zubar mana tunda na taba 'yar gold mai ido da kwalli ta gaban jirgi ta gaban mota zaka dawo ka same ni indai na amsa suna na Indo.




Tofa muje zuwa me hankali ya hau kura😂😜.


Taku ce ta kullum Yusrah yar musa bin abubakar muhammad .




Wata tsaleliyar tsadaddiyar mota ce wacce akafi sani da Mercedes-Benz take shara gudu akan wani kyakkyawan titi daya sha kwalliya ta ko'ina sosai motar ke gudu kamar sama zata tashi har wani tsalle take ita kadai.



Motoci kuwa dama sun tsaya kowa ya parker a gefen titi dan sun san waye mai wannan motar bazai wuce yariman su ABDUL-JABBAR ba kuma hakan ya tabbatar musu da ya dawo yana gari .



A wani irin kayataccen get ya tsaya yana horn da karfi kamar yadda yake da sauri aka bude masa tare da risnawa duk da basa ganin sa da gudu ya shiga masarautar wani titi ne shima mai kyau ya karya kwana ya shiga gurin tafiya mai nisa yai kafin ya iske inda motocin mahaifinsa suke yai parking da kyau wanda saida saurayin dake kusa dashi ya kusan bigewa da kujera.



Fitowa sukai kusan kamar su daya saidai Abdul-jabbar yafi dayan fari kayan su irin daya sai sheki suke rike hannun juna sukai yayin da Amfal ya kalle shi yana cewa "kai gaskiya bros ka rage gudu a mota wallh banyi tunanin zamu zo gida lfy ba na dauka sai munbi ta asibiti nifa idan ba rudewa nayi ba ji nake motar kamar tsalle take".




Murmushi yai yana kallon sa ba tare da yayi magana ba suka shiga fadar mahaifin nasu wanda masu tsaron kofar da sauri suka bude musu kana suka duka domin kwasar gaisuwa suna cire musu takalmin su.




Mahaifin nasu na ganin su ya saki murmushin jin dadi yana mikewa tsaye ya bude musu hannu rungume shi suka wanda suna jin lokacin dayai ajiyan xuciya a rayuwa yana matukar son wadannan zaratan samarin kyawawan 'ya'yan nasa burinsa fatan sa addu'ar sa a kullum Allah ya kara hada kansu.



Zama sukai suna sashi a tsakiya bayan sun gaida shi har lokacin murmushin sa na nan akan fuskar sa kayan marmarin dake gefe ya dauko apple guda daya yana kaiwa saitin bakin Abdul-jabbar rike hannun nasa Abdul-jabbar yay shima ya kai apple din saitin bakin Amfal karba Amfal yay daga nan shima Abdul-jabbar din ya karba sarki kuma yaci a karshe wajen saitin inda suka gucira kafin ya aje sauran.



Yana kallon su yace "Allah yayi muku albarka 'ya'yana ya tsare min ku daga sharrin makiya ya baku mata na gari masu kyan hali kamar yadda kuke.




"Ameen Abban mu mun gode Allah ya saka da alkhairi.



Kai ya jinjina daidai shigowar wata mace ta kalle su sau daya kafin ta mayar da kallon ta kan Abdul-jabbar a ranta tace"ka dauke min da har tsawon kwana uku kun dawo amma bai nemi ya ganni ba wato kana son raba ni da shine sbd kai baka san dadin uwa ba to wallh baka isa ba".




Ganin kallon da take masa yasa cikin muryarsa mai firgita mata dodan kunne a duk lokacin data jita yace",barka da shigowa Ammi fatan lfy a gare ki "kara kallon sa tay gira ya dage bai sake mgn ba ya dauke kanshi daga saitin ta .




Dan tsaki taja kadan tana zama ta kalli sarki da shikam farin ciki ne tsantsa yake nunawa cikin yake tace"barka da hutawa ranka ya dade ashe yan lelen naka sun dawo amma basu ko leko ni ba"ta karasa maganar kamar zata zubda hawaye sbd bata san sanda maganar ta fito ba dan Allah ya tsari gatari da saran shuka tacewa Abdul-jabbar danta inaaa har abada.




Emir(emiya sarki) bai tanka mata ba kamar yadda suma basuyi mgn ba taji haushi dan sarai ta dade da fahimtar idan tana gurin basa maganar arziki ta rasa dalili mikewa tayi bata sake cewa komai ba ta nufi fita.


mikewa Amfal yai yana cewa"ammi kafin mu shigo kisa a hada mana abinci dan Allah banza tay masa zata fita taji Emir yana cewa"a'a ki barshi ga nawa ya ishe mu"aikam fuuuuu ta fice da sauri cikin bacin rai ita da danta yana masarautar amma sai tayi kwana nawa bata ganshi ba kamar bai damu da ita ba dole ta sake shiri tasan yadda zatai ta raba su ko ta wacce hanya ce.





Alhmdllh Murtala yakai Safara'u chemist kamar yadda baffa yace kuma an duba ta dalilin fitar jini a hancin ta marin da Asabe ta mata ne da yake chemist ne ba asibiti ba kuma shima chemist din kusa da garin su yake a ranar suka koma gida yayin da Atine ta nemi Baffa ya kyale su tafi da Safara'u can gidan su.



Amma yace a'a zai kula da ita insha Allahu badan sun so ba suka hakura yana rike da hannunta suka shiga gida Asabe dake kwance kan tabarmar kaba a kofar daki da yake lokacin zafi ne ganin sun shigo yasa ta tashi zaune tana gyara daurin kwali.



Cikin salon munafinci tace"a'a ni 'yarnan daga ina tun safe ina ta zulumin ina kuka shiga na tambayi almajiran ka suka ce basu sani ba sunga dai murtala yazo da mashin ya dauke ta sun tafi wani guri ince dai lafiya dai ko"?.




Kallon mamaki Baffa ke mata lallai matar nan ta raina masa hankali banza ya mata bai bata amsa ba ya zaunar da Safara'u yana shiga dakin da take kwana ya dauko wata karamar katifa ya fito da ita saida ya gama mata shimfida sannan yace ta zauna.




Kofi ya dauko yana hada mata shayin daya sayo ya bata yana bare mata ayaba da lemo domin idan bai sani ba a yau bata ci komai ba saifa yanzu.



Asabe dake kallon ikon Allah ta rike kugu tana cewa"kwarai malam wai a hakan kasan Allah amma baka da adalci wato ita da yake kaine ka haife ta saika sayo mata kayan dadi ni kuma dayake tsinto ni kai shine ina maka magana ka bawa iska ajiya ta".


Kallon mmk Baffa ke mata "amma wallh Asabe baki da tunani ko kadan sbd shashanci yarinyar bata da lfy baki fada min kuma yanzu kice wai bani da adalci idan da kuma gawar ta na zo na samu fa shi kuma kice min me kinga Asabe ki fita idona idan kika kaini bango zan dau mataki a kanki karki manta yarinyar nan marainiya ce.




Kuka Asabe tasa"wato abin harda zagi fada baizo ba gori yazo sbd ni ban taba haihuwa ba nagode da ci min fuska "daki ta shige yayin da baffa yaci gaba da kula da Safara'u saida ta koshi sannan ya daura mata gidan sauro ta kwanta shi kuma ya koma zauren gidan inda ya saba kwanciya.



Bayan kwana biyu Safara'u ta dawo daidai saidai rashin mutuncin Asabe babu abinda ya canja saima gaba da yake dad'a yi kullum.




Murtala na son safara'u amma ita kam a nata bangaren da sauki mutuwar bako a gari tafi son Adamu kuma kamar yadda tafi son Adamu Asabe haka take so dan murtala yana da dan abin hannu Adamu kuwa sai zaman majalisa kadai ya sani".



Typing 📲
@¥$® ♏✔$^ ^%✅🅱^©^®

🍇🍇🍇🍇🍇🍇
SAFREEYYAH
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫


📚👌 Yusrah Musa Abubakar


Gaisuwa gare ku yan Annuri masoya na kwarai ina matukar jinjina muku na gode da kauna Allah ya kara barin mu tare AMEEN.🙏
SAFEEYYAH ALIYU
HAJARA ABLA'S
INDO CE
HAJARA B/KD
MARYAM ALIYU
AISHAT ABUBAKAR KEBBI
ZARAH MUSA DAN ADAM
NAJA'AT MUSA ABUBAKAR
FATEEY MUSA ABUBAKAR.


HAKIKA BANDA KAMAR KU KUNA RAINA IRIN SOSAI DIN NAN ONE LOVE 💞YAN UWA.



#YUSRAHMS#
NO.03👉 04
Zaune wata tsohuwa take wadda tadan manyanta a wani tsararran palor ita kadai take da radio a kusa da ita tana saurara.


Sallama akai tare da cewa "mu shigo ko mu tsaya"?murmushi tayi dan ta gane mai muryar tace"wanda bai maganar ba ya shigo kai kuma aku mai bakin magana zuwa zakai ka dame ni dan haka koma ban gayyato kaba".



Shigowa Amfal yai yana dariya bayan sa Abdul-jabbar zama sukai kusa da ita wanda kafin suyi mgn tace"wai dan Allah ku kuwa zakuiyi aure kalle ku gird'a gird'a amma babu mai zancen zaiyi mata to sai yaushe ko saina mutu"?.



"Eh jira muke saikin wuce kabari tukuna kafin muyi dan muna yin aure saikin dorawa matan mu hawan jini shi yasa munfi son saikin gangara .




Harararsa tay tana cewa"idan bakin ciki kake min yaro ba yanzu zan mutu ba saina ci lokacin yayan ku ma ran karfe gare ni ".



"Taf waya fada miki aikam ran roba gare ki kuma bari kiga nagwada wani abu" sanda ya dauko kamar zai rima mata ba shiri yasa ta ihu tana kankame Abdul-jabbar wanda ke kallon su tun dazu suna burge shi saidai bazai iya surutu haka ba .



Murmushi yayi yayin da Amfal ya aje sandan yana cewa"haba hajiya mai ran karfe da kin bari na gwada ashe dai da gaske kina tsohon mutuwa".



Hararar sa tayi tana gyara zaman ta tace"kana jin mu ko Abdullahi daya rade ni kucewa uban ku me kun kashe masa uwa".



Allah Amfala ka kiyaye ni ku tashi ku tafi ma na gode da ziyara sai anjima mikewa sukai hajiya ta bisu da kallo tana cewa miskili Allah ya baka mace mai surutu sai naga yadda zakai"



Dan dakatawa yayi ba tare daya juyo ba yace"saina kawo miki ita kuje ku karata dan bazan taba auren mace mai surutu ba gadai wanda zaki wa fata madam "



Dakuwa hajiya ta masa"kuma nice madam din "?Amfal...


Read / Download SAFREEYYAH

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album