Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[08/01/23 08:30 a.m] Typing📲



WHATSAPP NO.
+234 905 527 3614.



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
SAFREEYYAH
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
(🏡 home of hospitality👐 and harmony).

👆Gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🕊.


(Yan annuri I really love you everything about you is so good but one thing is wrong that you are not mind wannan haka yake).


Yusrah Musa Abubakar.

DEDICATED TO
MY MUM I LOVE YOU WITH ALL MY BODY AND HEART YOU ARE THE BLOOD THAT SCULATED IN MY HEART YOU ARE MY LIFE I LUV U💝 MAMANA.




Some say hello some say hay but in islamically said:Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu.



In the name of Allah the most benefits and the most merciful da sunan Allah buwayi gagara misali tsira da aminci su tabbata ga masoyin mu Muhammad rasulullah s a w we love our Nabeey we like him and peace be upon him AMEEN🙏👏.




🕌🕋🕌
Happy Juma'at Mubarak to all Muslims and it's Friday don't forget to recite suratul-Al khaf, I am so blessed to be a Muslim Alhamdulillah.



(*(*()*)*) (*(*()*)*) (*(*()*)*)
📖Littafin 👉 Safreeyyah is a fiction
'kagaggen labari mai zaman kanshi sa annan banyi amfani da tunanin wani ba zallar basirar da Allah yaban ce please 'yar uwa ko d'an uwa marubuci ko marubuciya irina wanda taga littafin kuma taga wata kalma daidai da (A)👈 wanda tayi yanayi da wani littafin ta data taba rubutawa to tayi hakuri 🙏kuskuren basira aka samu tunanin mu yazo daya😜, na gode Yusrah ce👌.


Ayi hakuri idan an samu typing error🚨.


#YUSRAHMS#
NO.01👉 02


Zaune take a kofar daki ta rafka tagumi naban tausayi da alama ko sanin hawaye sun jike mata fuska batai ba saboda irin tunanin datayi zurfi a cikin sa bangare guda kuma wutar data hura ce batasan ta mutu ba.



Fitowar wata mata daga daki kenan ganin abinda ya faru da wutar ta yasa ta karaso a fusace tana sauke mata wani irin duka a bayan ta cikin tsawa tace"lallai Safara'u tunanin ubanki kike har kika bar min wuta ta mutu saboda baki gaji arziki ba shegiya dangin tsiya wallh ko kukan jini zaki wahala yanzu kika fara sha .



A matukar zarane wannan kyakkyawar budurwar ta dago da manyan idon ta farare tas wanda a yanzu kukan da take sun koma ja tana kallon wacce ke tsaye a kanta batai zato ba ta sake jin saukar mari a fuskar ta wanda saida ta kifa kasa daga kan kujerar da take.



Rai bace matar tayi kanta tana kara rufe ta da duka tace "shine zanyi miki mgn ki tsare ni da wadannan mayun idon naki masu kala dana mujiya bankadaddiya wallh na sake fitowa naga wutar nan ta mutu saina kusa kashe ki "ta karasa mgnr tana kai mata hauri da kafa ta kuwa same ta a ciki.



Ba shiri ta saki kara tana rike cikin sbd azaba agurin ta kwanta tana murkususu tsallake ta matar tayi tana cewa"Allah yasa ki mutu kafin na fito da wallahi naji dadi na rabu da kaya me za'ai da rikon dan wani hakan ma dan kishiya aikin banza gayyar tsiya"daki ta wuce bata damu da yadda taga tana juya kanta alamar wani abu ya same ta ba.


I

Shigowar wani dattijo kenan ganin ta kwancce yasa ya saki ledar dake hannun shi kayan cefanan daya sayo suka tarwatse a kasa da saurin sa ya karaso yana daga ta ganin yadda jini ke fita a hancin ta cikin tashin hankali ya soma kwalla kira "ke Asabe ke Asabe kina ina ne me ya samu Safara'u jini yake fita daga hancin ta".


Jin shiru ba'a amsa masa ba gashi ta fara amai harta bata masa kaya sai kawai ya mike yana daga ta Aisha ce ta shigo daidai zai fita a gidan rike da Safara'u.



Hankali tashe tace "baffa lfy me ya same ta "bashi da bakin mgn kawai cewa yay taje gida maza tace yayan ta Murtala yazo zai kaisu chemist za a duba ta.



Da gudu Aisha ta juya tana kuka yayin da baffa ya fita da ita kofar gida da yake makaranta ce dashi dukkan almajiran dake karatu acan dan nesa da gidan karkashin wata babbar bishiyan dorawa suka taso da saurin su suna cewa"malam lfy?"kai ya daga musu gabadaya ya kasa mgn.




Suna haka saiga murtala da wani dan jitan dinsa na talakawa bayan sa kuma Aisha da babarta basu tsaya tambayar me ya faru ba kawai dora safara'un sukai a bayan mashin din babar Aisha ta hau domin ta rike ta Baffa da aisha suka bisu a baya.




Jin mashin ya tashi yasa Asabe fitowa tana jan tsaki tai gurin wutar ta tana gyara itatuwan ta sun riga sun daina ci ita kadai sai tsine tsine take kuma tana fatan Allah yasa kada su dawo da Safah a raye saida ta maida wutar yadda take ta mike kenan ta gano kayan miya a barbaje alamar ya shigo rudewa tasa ya zubda bai kawo mata ba karasawa tay da kwano tana bi tana debewa tace"dole ka zubar mana tunda na taba 'yar gold mai ido da kwalli ta gaban jirgi ta gaban mota zaka dawo ka same ni indai na amsa suna na Indo.




Tofa muje zuwa me hankali ya hau kura😂😜.


Taku ce ta kullum Yusrah yar musa bin abubakar muhammad .




Wata tsaleliyar tsadaddiyar mota ce wacce akafi sani da Mercedes-Benz take shara gudu akan wani kyakkyawan titi daya sha kwalliya ta ko'ina sosai motar ke gudu kamar sama zata tashi har wani tsalle take ita kadai.



Motoci kuwa dama sun tsaya kowa ya parker a gefen titi dan sun san waye mai wannan motar bazai wuce yariman su ABDUL-JABBAR ba kuma hakan ya tabbatar musu da ya dawo yana gari .



A wani irin kayataccen get ya tsaya yana horn da karfi kamar yadda yake da sauri aka bude masa tare da risnawa duk da basa ganin sa da gudu ya shiga masarautar wani titi ne shima mai kyau ya karya kwana ya shiga gurin tafiya mai nisa yai kafin ya iske inda motocin mahaifinsa suke yai parking da kyau wanda saida saurayin dake kusa dashi ya kusan bigewa da kujera.



Fitowa sukai kusan kamar su daya saidai Abdul-jabbar yafi dayan fari kayan su irin daya sai sheki suke rike hannun juna sukai yayin da Amfal ya kalle shi yana cewa "kai gaskiya bros ka rage gudu a mota wallh banyi tunanin zamu zo gida lfy ba na dauka sai munbi ta asibiti nifa idan ba rudewa nayi ba ji nake motar kamar tsalle take".




Murmushi yai yana kallon sa ba tare da yayi magana ba suka shiga fadar mahaifin nasu wanda masu tsaron kofar da sauri suka bude musu kana suka duka domin kwasar gaisuwa suna cire musu takalmin su.




Mahaifin nasu na ganin su ya saki murmushin jin dadi yana mikewa tsaye ya bude musu hannu rungume shi suka wanda suna jin lokacin dayai ajiyan xuciya a rayuwa yana matukar son wadannan zaratan samarin kyawawan 'ya'yan nasa burinsa fatan sa addu'ar sa a kullum Allah ya kara hada kansu.



Zama sukai suna sashi a tsakiya bayan sun gaida shi har lokacin murmushin sa na nan akan fuskar sa kayan marmarin dake gefe ya dauko apple guda daya yana kaiwa saitin bakin Abdul-jabbar rike hannun nasa Abdul-jabbar yay shima ya kai apple din saitin bakin Amfal karba Amfal yay daga nan shima Abdul-jabbar din ya karba sarki kuma yaci a karshe wajen saitin inda suka gucira kafin ya aje sauran.



Yana kallon su yace "Allah yayi muku albarka 'ya'yana ya tsare min ku daga sharrin makiya ya baku mata na gari masu kyan hali kamar yadda kuke.




"Ameen Abban mu mun gode Allah ya saka da alkhairi.



Kai ya jinjina daidai shigowar wata mace ta kalle su sau daya kafin ta mayar da kallon ta kan Abdul-jabbar a ranta tace"ka dauke min da har tsawon kwana uku kun dawo amma bai nemi ya ganni ba wato kana son raba ni da shine sbd kai baka san dadin uwa ba to wallh baka isa ba".




Ganin kallon da take masa yasa cikin muryarsa mai firgita mata dodan kunne a duk lokacin data jita yace",barka da shigowa Ammi fatan lfy a gare ki "kara kallon sa tay gira ya dage bai sake mgn ba ya dauke kanshi daga saitin ta .




Dan tsaki taja kadan tana zama ta kalli sarki da shikam farin ciki ne tsantsa yake nunawa cikin yake tace"barka da hutawa ranka ya dade ashe yan lelen naka sun dawo amma basu ko leko ni ba"ta karasa maganar kamar zata zubda hawaye sbd bata san sanda maganar ta fito ba dan Allah ya tsari gatari da saran shuka tacewa Abdul-jabbar danta inaaa har abada.




Emir(emiya sarki) bai tanka mata ba kamar yadda suma basuyi mgn ba taji haushi dan sarai ta dade da fahimtar idan tana gurin basa maganar arziki ta rasa dalili mikewa tayi bata sake cewa komai ba ta nufi fita.


mikewa Amfal yai yana cewa"ammi kafin mu shigo kisa a hada mana abinci dan Allah banza tay masa zata fita taji Emir yana cewa"a'a ki barshi ga nawa ya ishe mu"aikam fuuuuu ta fice da sauri cikin bacin rai ita da danta yana masarautar amma sai tayi kwana nawa bata ganshi ba kamar bai damu da ita ba dole ta sake shiri tasan yadda zatai ta raba su ko ta wacce hanya ce.





Alhmdllh Murtala yakai Safara'u chemist kamar yadda baffa yace kuma an duba ta dalilin fitar jini a hancin ta marin da Asabe ta mata ne da yake chemist ne ba asibiti ba kuma shima chemist din kusa da garin su yake a ranar suka koma gida yayin da Atine ta nemi Baffa ya kyale su tafi da Safara'u can gidan su.



Amma yace a'a zai kula da ita insha Allahu badan sun so ba suka hakura yana rike da hannunta suka shiga gida Asabe dake kwance kan tabarmar kaba a kofar daki da yake lokacin zafi ne ganin sun shigo yasa ta tashi zaune tana gyara daurin kwali.



Cikin salon munafinci tace"a'a ni 'yarnan daga ina tun safe ina ta zulumin ina kuka shiga na tambayi almajiran ka suka ce basu sani ba sunga dai murtala yazo da mashin ya dauke ta sun tafi wani guri ince dai lafiya dai ko"?.




Kallon mamaki Baffa ke mata lallai matar nan ta raina masa hankali banza ya mata bai bata amsa ba ya zaunar da Safara'u yana shiga dakin da take kwana ya dauko wata karamar katifa ya fito da ita saida ya gama mata shimfida sannan yace ta zauna.




Kofi ya dauko yana hada mata shayin daya sayo ya bata yana bare mata ayaba da lemo domin idan bai sani ba a yau bata ci komai ba saifa yanzu.



Asabe dake kallon ikon Allah ta rike kugu tana cewa"kwarai malam wai a hakan kasan Allah amma baka da adalci wato ita da yake kaine ka haife ta saika sayo mata kayan dadi ni kuma dayake tsinto ni kai shine ina maka magana ka bawa iska ajiya ta".


Kallon mmk Baffa ke mata "amma wallh Asabe baki da tunani ko kadan sbd shashanci yarinyar bata da lfy baki fada min kuma yanzu kice wai bani da adalci idan da kuma gawar ta na zo na samu fa shi kuma kice min me kinga Asabe ki fita idona idan kika kaini bango zan dau mataki a kanki karki manta yarinyar nan marainiya ce.




Kuka Asabe tasa"wato abin harda zagi fada baizo ba gori yazo sbd ni ban taba haihuwa ba nagode da ci min fuska "daki ta shige yayin da baffa yaci gaba da kula da Safara'u saida ta koshi sannan ya daura mata gidan sauro ta kwanta shi kuma ya koma zauren gidan inda ya saba kwanciya.



Bayan kwana biyu Safara'u ta dawo daidai saidai rashin mutuncin Asabe babu abinda ya canja saima gaba da yake dad'a yi kullum.




Murtala na son safara'u amma ita kam a nata bangaren da sauki mutuwar bako a gari tafi son Adamu kuma kamar yadda tafi son Adamu Asabe haka take so dan murtala yana da dan abin hannu Adamu kuwa sai zaman majalisa kadai ya sani".



Typing 📲
@¥$® ♏✔$^ ^%✅🅱^©^®

🍇🍇🍇🍇🍇🍇
SAFREEYYAH
🍇🍇🍇🍇🍇🍇


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫


📚👌 Yusrah Musa Abubakar


Gaisuwa gare ku yan Annuri masoya na kwarai ina matukar jinjina muku na gode da kauna Allah ya kara barin mu tare AMEEN.🙏
SAFEEYYAH ALIYU
HAJARA ABLA'S
INDO CE
HAJARA B/KD
MARYAM ALIYU
AISHAT ABUBAKAR KEBBI
ZARAH MUSA DAN ADAM
NAJA'AT MUSA ABUBAKAR
FATEEY MUSA ABUBAKAR.


HAKIKA BANDA KAMAR KU KUNA RAINA IRIN SOSAI DIN NAN ONE LOVE 💞YAN UWA.



#YUSRAHMS#
NO.03👉 04
Zaune wata tsohuwa take wadda tadan manyanta a wani tsararran palor ita kadai take da radio a kusa da ita tana saurara.


Sallama akai tare da cewa "mu shigo ko mu tsaya"?murmushi tayi dan ta gane mai muryar tace"wanda bai maganar ba ya shigo kai kuma aku mai bakin magana zuwa zakai ka dame ni dan haka koma ban gayyato kaba".



Shigowa Amfal yai yana dariya bayan sa Abdul-jabbar zama sukai kusa da ita wanda kafin suyi mgn tace"wai dan Allah ku kuwa zakuiyi aure kalle ku gird'a gird'a amma babu mai zancen zaiyi mata to sai yaushe ko saina mutu"?.



"Eh jira muke saikin wuce kabari tukuna kafin muyi dan muna yin aure saikin dorawa matan mu hawan jini shi yasa munfi son saikin gangara .




Harararsa tay tana cewa"idan bakin ciki kake min yaro ba yanzu zan mutu ba saina ci lokacin yayan ku ma ran karfe gare ni ".



"Taf waya fada miki aikam ran roba gare ki kuma bari kiga nagwada wani abu" sanda ya dauko kamar zai rima mata ba shiri yasa ta ihu tana kankame Abdul-jabbar wanda ke kallon su tun dazu suna burge shi saidai bazai iya surutu haka ba .



Murmushi yayi yayin da Amfal ya aje sandan yana cewa"haba hajiya mai ran karfe da kin bari na gwada ashe dai da gaske kina tsohon mutuwa".



Hararar sa tayi tana gyara zaman ta tace"kana jin mu ko Abdullahi daya rade ni kucewa uban ku me kun kashe masa uwa".



Allah Amfala ka kiyaye ni ku tashi ku tafi ma na gode da ziyara sai anjima mikewa sukai hajiya ta bisu da kallo tana cewa miskili Allah ya baka mace mai surutu sai naga yadda zakai"



Dan dakatawa yayi ba tare daya juyo ba yace"saina kawo miki ita kuje ku karata dan bazan taba auren mace mai surutu ba gadai wanda zaki wa fata madam "



Dakuwa hajiya ta masa"kuma nice madam din "?Amfal zaiyi mgn hajiya tace"dan Allah kuje nagode ".


"Allah bazan tafi ba saina fada hajiya ina sonki kuma bros dina ma yana sonki ma'ana dukkan mu muna sonki sai anjima ki huta lfy yau kisa a kawo miki abincin mutum uku dan anan za muci abincin dare".



Murmushi tay "to naji sai anjima na gode"


Fita sukai suka shiga sashin Ammi a palon suka same ta ganin su yasa ta hade rai tana cewa"me kuma ya kawo ku guri na ku koma inda kuka fito bana bukatar ganin ku".



Da mmk Amfal yace"wai dan Allah Ammi me kike haka gaida ke fa muka zo yi sai kice bakya bukata".


Harararsa tay"eh nace bana bukata idan kuma zaka sani dole sai naji babana"murmushi Amfal yai yana sakin hannun Abdul-jabbar ya karasa inda take yana zama tare da rike hannunta.


Yace"yi hakuri Ammi yanzu zamu tafi basai kin kore muba dama haka ne idan mutum baida uwa saidai yay tabin rabi ana korar sa kamar wani kolo dan kawai mu marayu ne"ya karasa mgnr yana kallon yadda ta zaro ido jin abinda yace.



Kara hade rai tayi tana cewa "a gidan uban wa ka zama maraya bayan ubanka na nan kuma nima mahaifiyar ka ina nan".



kai ya girgiza "a'a Ammi mahaifi dai yana nan amma mahaifiya ta bata raye domin bani da bambanci da maraya kuma nida Abdul-jabbar abu daya ne mahaifiyar sa ta rasu bai san dadin uwa ba kamar yadda nima ban sani ba domin baki jani a jikin ki mun shaku ba ".



Dafe kirji Ammi tay cikin tashin hankali tana kallon Amfal tace"na shiga uku ina mafarki ne ni kake fadawa wadannan maganganun Amfal ka fara hauka ne ko wannan mara mutuncin ne ya fara koya maka shaye shaye don labari yazo min cewa babu abinda baya sha a UK gaskiya ne".




Mikewa Amfal yay yana cewa "eh ba haka bane mukam mun tafi dama sallama muka zo miki dan gobe gidan gona zamu wuce mu huta sai minyi sati zamu dawo ki huta lafiya"ya karasa maganar yana kissing hannunta karasowa Abdul-jabbar yai yana cewa"sorry Ammi kiyi hakuri"bata iya magana ba shima kiss ya bata mai matukar dumi da shiga rai kafin ya kalli Amfal alamar su tafi.




Mikewa yay suna fita daga part dinta tafi mintuna goma da suman zaunen da tay daga baya ta sauke wani irin numfashi tana kallon inda yai kissing dina kafin ta goge tana mikewa ta fara zaga falon cikin juya maganar Amfal wato yana nufin ita photocopy ce bata da wani amfani lallai hakan ya matukar furgita mata lissafi dole tayi damara ta fara yaki domin ta kwato danta ya dawo gare ta yasan darajar ta.




Tunawa tayi lokacin da Emir yace mata"Adama ina son Abdul-jabbar zai tafi karatu zan sashi a makarantar koyan aikin soja amma mene shawarar ki akan haka ya dace ko a'a".



Murmushi Ammi tayi"eh to ranka ya dade ina ganin hakan zaifi domin Abdul-jabbar da soja ya dace kuma me zai hana ka saka su tare da Amfal gabadaya "kai Emir ya daga masha Allah hakan yayi nagode da shawara za'a saka su ".




Murmushin samun nasara Ammy tay cikin jin dadi ta koma part dinta ta sani ba karamar wuya zata sa a ganawa Abdul-jabbar ba lallai akwai ta da kwakwalwa.




Hanne ce ta shigo tare da cewa"ki gafarce ni ranki ya dade ance kina nema na"?.


Kai Ammy ta daga eh ina neman ki hanne dama mai martaba ne ya kira ni dazu akan wai yana neman shawara ta zai tura Abdul-jabbar aikin soja nace masa eh sbd ina ganin wannan hanyar kadai zanbi na kuntata wa Abdul-jabbar nasa a gana masa azaba ya kasa jin dadin zaman duniya ya gwammace mutuwa da rayuwa".




Kara dukawa hanne tay "haka ne ranki ya dade to amma indai kina son hakan saidai kar Amfal ya bishi domin idan suna tare burin ki bazai taba cika ba GAmfal da Abdul-jabbar akwai kauna da shakuwa mai karfi tsakinin su kuma zai wahala nan gaba ki samu kan Amfal domin Abdul-jabbar yana da shiga rai kamar yadda mahaifiyar sa take".




Mikewa Ammi tay tana cewa"da kyau hanne tunani mai kyau zan koma gurin mai martaba na fada masa cewa Amfal bangaren likitanci zaiyi shine kadai hanyar raba su na gode sosai hanne tashi kije kuma kada ki bari kowa ya sani ni da ke ne idan maganar nan ta fita kinsan sauran".



Jiki na rawa hanne tace"a min afuwa ba wanda zaiji hakan".


"Ok yayi jeki".



Bayan fitar hanne Ammi tay shiri ta koma gun Emir da salon jawo hankali saidai ta makaro baya magana biyu yace shawarar farko data bashi yafi so iya tashin hankali Ammi ta shiga har bacci ta daina yi amma hakan baisa ta juya ra'ayin Emir ba kuma tana ji tana gani suka tafi UK a tare yayi da har ramar bakin ciki tay kullum tana cikin saka da warwara".




Sauke ajiyar zuciya Ammy tay bayan ta dawo daga dogon tunani ta kalli kofar da suka fita rai bace ta soma magana "laifi nane tun farko dana bawa mai martaba gurguwar shawara amma ba komai indai ana tare Abdul-jabbar nayi alkawari baza ka taba jin dadi ba duk hanyar da nasan zaka kuntata zan bita komai had'ari kuwa saina kaika kasa".




Har kamar ni Adama wai dan dana haifa zaice bani da wani amfani a gunsa saboda da kai lallai Abdul-jabbar ka kira mutuwar ka saika gane kuren ka domin kai d'ana bai ganin daraja ta ".


MRS AL'AMEEN AHMAD CE👌.

ANA TARE INSHA ALLAH.


Yaukam na gama typing sai idan Allah yaja kwanan mu zuwa gobe saimu dora inda muka tsaya.😜



Typing📲



🍇🍇🍇🍇🍇🍇
SAFREEYYAH
🍇🍇🍇🍇🍇🍇



ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💫


📖🖊 Yusrah Musa Abubakar



BARKAN MU DA KWANA 'YAN GROUP DINMU NA ANNURI AND VIP WOMEN24 TV DA GROUP DIN HAJARA @BLA & NI,'IMATULLAH FANS GROUP GA GAISUWA MAI TARIN YAWA DAGA YUSRAH .💞🍇💝.


Start your day beautifully with fajr prayer and quran recitation.
O Allah s w t make us among those who never miss salah🕌 AMEEN🙏👏.


Yan uwa mu dage never stop learning because life never stop teaching.



Yusrah Musa Abubakar

#YUSRAH#
NO.05👉 06
Shiru tayi sai kawai wani abu ya sake fado mata lokaci mai tsawo daya wuce ta riga maman Abdul-jabbar auren Emir kuma ta dade bata haihuwa bayan mutuwar uwar gidan sarki ya auri maman Abdul-jabbar ta wata hanyar ban mamaki da ba zata manta ba.



Mai martaba yaje ziyara masarautar adamawa ya kuma yi kwanaki sakamakon dama can shida sarkin adamawa abokanai ne na hakika bayan yayi sati ya nemi komowa gida .




Bayan sunyi ban kwana da sarkin adamawa kuma yayi masa rakiya mai dan nisa suka sake yin ban kwana barowar su adamawa kadan suka riske wani karamin

Please Login or Register in order to submit comment