Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ayya Allah ya sauwake kace banyi karya ba bros jiya ka angwance ka rakashe barka da kokari babban yaya".


Tea din da Abdul-jabbar ya kurba ne ya sarke shi tuni ya fara jera tari tare da dafe kirjin shi jin abinda Amfal din ke fada".



Da sauri Amfal ya mike yana dauko masa ruwa ya bashi tare da dan bubbuga masa bayan sa da tafin hannu a hankali.


Sauke ajiyar zuciya Abdul-jabbar yay ya dago yana kallon Amfal daya zuba masa ido yace".


"Wato so kake ka karasa ni da maganganun ka ko dama jiya ciwon kan da aka samun har nai bacci bai tafi ba shine yauma kake kokarin dora min wani da uban me na angwance an fada maka kowa irin kane".


Kunshe dariyarsa Amfal yay sorry bros naji kana neman likita shiyasa na tambaye ka".


Abdul-jabbar bai sake magana ba ya rabu dashi.


Sallamar da Zainab tai yasa ya mike yana kallon Amfal yace to dansa ido komai da ruwan ka bari naje".


"Saida ya bari ya juya zai tafi yace" doctor Zeey please ki fara yi mata ruwan zafi kafin komai ina tunanin shine maganin".


Ba arziki yasa Abdul-jabbar wata zabura data kusa bashi dariya da gudu ya mike ganin ya nufo shi ya shiige bedroom tare da cewa.

"sorry bros nasan ba fada mata zakai ba yadda kake da kunya".


Sak Abdul-jabbar yai ya tsaya guri daya yana kallon kofar gaskiya Amfal idan ka biye masa saiya dora maka hawan jini hajiya tana kokari da take iya biyewa shirmen sa".


Kyalewa yay ya fita a kofa ya samu Zainab na jiransa wucewa gaba yai tabi bayan sa.


Part dinsu ka shiga har cikin bedroom a wurin daya fita ya barta bata tashi ba mamaki yaji.

wannan yarinyar mutum ce kuwa shin bata gajiya kamar me jikin katako.

"Ok doctor gata nan ki duba ta".

To ranka ya dade" zeey ta fada tana nufar inda take zaune.

Wanda Safah ta zaro idonta waje jin abinda yace tadan saci kallonsa hankalinsa baya kansu yana wani gurin daban.


To da yaushe tace masa bata da lafiya zai kira likita kodai ramawa dokinsa zaiyi?.

Afirgice cikin tsoro ta dago jin zeey na cewa" ranki ya dade koma gado saina duba ki".


Kai Safah ta girgiza da sauri kamar wani zai riga ta tace" nifa kalau nake ba inda yake min ciwo".


"Ahakan ranki ya dade ga alama nan idanuwan ki. sunyi ja kuma sun kumbura da dai kin bari an dubaki".


"A'a dan Allah kije ni wallahi lafiya ta kalau".


Juyawa zeey tai tana kallonsa tace" ranka ya dade kaji abinda madam din tace".


Fuskarsa a daure batare daya kalli inda suke ba cikin bada umarni yace" ki duba ta nace".


Dole cikin lallami doctor zeey ta sunkuya tana dagota domin ta taimaka mata ta koma gadon saita dubata.


Kara Safah ta saki da karfinta wacce tasa zeey matsawa baya da sauri ta na cewa" na roke ki daki barni karki daga ni dan Allah".


Ba zeey din ba hatta shi lamarinta ya bashi tsoro a wannan karon dan dubanta yay cikin alamar tambaya.


Wato wannan yarinyar shagwababbiya ce ba'ai mata komai ba amma ji yadda take matsar kwalla.

Takawa yai cikin nutsuwa har yaje gabanta batare da= ta sani ba domin idonta a rufe yake tana aikin goge hawaye.



Jitai anyi sama da ita bude ido tai a gigice tana kallonsa tasan kila allura zaisa ai mata yana dire ta akan gadon cikin raunin murya tace.

"Wayyo Allah na kafa ta".


Zubawa kafar ido yai ganin tadan kumbura ya fahimci ciwo taji ko shine dalilin da yasa bata san tashin.

"Zoki duba ta".


Matsowa zeey tai cikin dar-dar ta soma auna ta Safah kam ta sadaukar kawai jira take taga an zaro allura.


Sosai ta bincike ta har sake dubata tai amma bata ga komai ba mikewa tsaye tai cikin sauke ajiyar zuciya tace.


"Ranka ya dade ba abinda yake damunta kalau take saidai tana bukatar hutu sosai ma'ana baccine bata samu isashshe ba wanda hakan yake neman dora mata zazzabi da ciwon kai .


"Yanzu maganin cutarta bacci ya kamata ace ta samu matsalarta kenan ranka ya dade".


"Ok doctor thank na gode".


"Babu damuwa ranka ya dade madam na barki lafiya bari naje na gaishe da hajiya". Tana fadin haka ta bude kofa ta fita.


Zama yai a bakin gadon batare daya mata magana ba ya rike kafar dake da kumburin ya matsa da dan karfi.


Wata karar ta saki cikin tsananin azaba batasan lokacin data rike masa hannu ba.


Cigaba da matsawa yai yana danjan yatsan kadan kuka ta fashe dashi ita kadai tasan abinda takeji.


Sosai ya matsa kafar harta dawo kumburin ya ragu safah kam har hawaye ne ya daina fita a idonta sai juya kai da take kamar me ciwon ciki.


Sakar mata kafar yai yana mikewa dama ita kam yana saki tai baya luuu ta kwanta tare da rufe idonta.


Toilet ya wuce batare da yace mata kala ba tun tana sauke ajiyar zuciya har baccin da batai ba daren jiya me shegen nauyi ya dauketa.


Wanka yayo yana fitowa ya wuce gaban mirror inda wayarsa take ganin lokaci ya kusa kurewa yasa cikin gaggawa ya shirya cikin kayan soja marmari daga nesa.


Yai bala'in kyau sosai taje gashin kansa yai yana fesa turare tare da daukar wayarshi bakin gadon ya koma ganin baccin ya dauketa.


Ya gyara mata kwanciya yana ja mata bargo ya rufe mata rabin jikinta bai sake kallonta ba ya juya ya fita daga dakin.


Amfal na ganin shi yadan saki murmushi tuno abinda ya faru dazu yace" bros kaima ka shirya kenan ya jikin aunty nawa fatan taji sauki"?.


Bai amsa mishi ba ya sauya zancen da cewa" ka jira ni a part din hajiya zan sameka".


"Ok bros Allah ya bata lafiya bari naje sallama da Ammy kafin naje gurin hajiyan tawa".


Tare suka fita shiyai part din Ammy shi kuma ya tafi bangaren Abbansu".


Cikin kauna me martaba ya tare shida fara'arsa yace" maraba da dana me hankali Allah ya albarkaci rayuwarka".


"Amin abba nagode da kyakkyawar addu'arka zuwa gareni a koda yaushe Allah ya kara nisan ta kwanan ka tare damu".


"Amin amin babana kun shirya kenan amma wannan tafiyar bai kamata yauba tunda weekend ne dakun bari sai gobe".


"Ai abba dole ce ta kama a yau din aka bukatar mu basai ranar monday ba shine dalilin tafiyar mu yaudin".


"To shikenan Allah ya tsare hanya lagos ne naji dan uwanka yace ko"?.


"Eh can ne sati biyu ne nake tunanin zamuyi".


"Yayi kyau Allah ya taimaka".


"Amin abba saimun dawo".


Zai mike me martaba ya dakatar dashi da fadin" am nace babana kayi hakurin abinda ya faru ka rungumi kaddara ka dauki rayuwa a sannu sai tazo maka da sauki.


Nasan na bata muku kaida dan uwanka sakamakon ban fada muku cewa daurin aurenku za'ai ba akan hakan hakan ina sake baku hakuri musamman.


"kai matar ka bata kasance jinin sarauta ba baiwa ce ba kamar Amfal ba amma kaima idan kana bukatar karin aure ko yanzu ne ina da abokai masu 'ya'ya mata da yawa saika zabi wacce kake so a cikinsu indai hakan zaisa zuciyarka ta samu nutsuwa.


Ya karasa maganar yana rike masa hannu fuskar sa ta nuna damuwa da hakan karara.



Murmushi Abdul-jabbar yai yana kallonsa yace" abba karka damu akan haka banji komaiba farin ciki ma nayi domin dukiya ko mulki ba shi bane dace da mace ta gari yafi kwanciyar hankali".


"Gode muku ya kamata nayi saboda baku aura min mace da baza taga mutunci naba ko ta rika nuna kafada ta daidai take da tata ita jinin sarauta ce nima haka".


"Amma wacce kuka aura min tasan darajar dan adam kuma itace ta dace dani da yanayina da tsarin rayuwata itace kalata".


"Dalili kuwa shine matar mutum kabarin shi tunda har kaga ubangiji ya zaba min ita matsayin mata to itace mafi alkhairi a gareni sama da 'ya'yan masu mukami.


"Bana bukatar karin aure daga kanta mace daya ta isheni rayuwa bana son hayaniya.



"indai bata fini karancin kwana ba ta rasu ta barni babu abinda zaisa na kara aure.



"Nagode sosai da zabin ku kuma nayi matukar farin ciki Allah ya biya ku abba bari naje mu tafi lokacin mu ya kure".


Kai me martaba ya jinjina cikin jin dadin kalaman shi ya masa kyakkyawar addu'a sannan sukai sallama ya fita zuwa part din hajiya.


Daga kofa ya tsaya yana kallon Amfal yace" lokacin mu ya kure taso hajiya saimun dawo".


A kaikaice hajiya ta kalleshi "wai Abdullahi meke damunka ne kwana biyu shiru yau na dauka zanga ka kawo min kishiyar tawa sai naji shiru".


"Sorry hajiya muna sauri ne saimun dawo zan kawo miki ita".


"Suna fita hajiya tace" oh ni Hauwa'u ina ganin duniya mutum ya ware yay maka magana ka bashi gaheruwar amsa".

"Shikenan Allah ya kiyaye ya dawo daku lafiya shine fata na".


Tun daga bakin kofar shiga part Ammy kake jin hayaniyar marakisiyyah da ihunta cikin kuka tana fisge-fisge duk ta watsa gashin kanta.


Isar Ammy tay afusace ta mike tana zuwa ta banka kofar bedroom dinta ta shiga cikin tsawa tace.


"Dan ubanki rufe min baki shashashar yarinya mahaukaciya so kike ki aje min abin fada na karajin bakin ki ya furta sunan Abdul-jabbar saina fasa shi".


Burgima sosai marakisiyya keyi saman gadon duk ta wargaza dakin tayi masa kaca-kaca tashi zaune tai tana kallon Ammy tace".


"Wallahi Ammy kin cuce ni kin cuci rayuwata da zuciyata kin rabani da wanda nake so nake mafarkin samu abin alfahari na meye ribar ki".


"Tun yaushe nake son Abdul-jabbar badan kina nuna min bakin hali ba da yanzu na dade da auren shi.


"Kuma yanzun ma ba hakura naiba duk shegiyar baiwar da kika aura masa saina ci ubanta na karya ta saiya saketa".


A hanzarce Ammy tace kul kada ki kuskura ki fara ranki zaiyi mummunan baci ke kin wuce ajinsa me zaki dashi badan kinsa shashanci aranki ba sakarya kawai".


"Ammy ke kike ganin haka saboda bai miki ba yasa kika kasa tsayawa ki fahimci irin baiwar da yake da ita kuma bazan taba barin saba".


"Lallai kuwa kina daf da barin masarautar nan baki isa na zuba miki ido ki maida ni wata sakarai ba zan kira wanda ya isa dake yazo ya tafi dake".

"Babu inda zanje ina nan koma wa zaki kira".


"Shikenan zan nuna miki iyakar rashin kunyar ki tunda niban isa dake" tana fadin haka ta bude kofa ta fice.


Dora hannu marakisiyya tai aka tana cewa na shiga uku wacce tsinanniyar baiwar aka aura masa wallahi bazan rabu da ita ba saina murde mata wuya ta lalata min mafarki na Abduljabbar nawa ne bana wata banza ba saina aureshi".


Ta kara rushewa da kuka tana kifa kanta akan filo jin zuciyarta na zafin radadi kamar ta fito waje.


Jin ance su Abduljabbar sunbar masarautar yasa jakadiya taje part din da safah take danta dubo ta wajen karfe biyu da rabi na rana.


Amma cikin mamaki taji shiru kamar ba kowa ga abincin breakfast nan ko tabawa ba'ai ba an kawo abincin rana anyi joining dinsa.


Cikin wasi wasi tace anya safah kalau kuwa buda bedroom din tai ta shiga ganin ta kwance tana bacci yasa bata tashe taba ta juya tana fita.


Masu gadin kofar taiwa gargadin cewa duk wanda yazo kada su barshi ya shiga sannan ta koma cikin gida.




#Team Safah
#Team Abdul-jabbar



#YUSRAHMS#
NO.83👉 84
Murtala ne zaune akofar daki ya zubawa guri daya ido baya ko kyaftawa badan idan ka dube shi dakyau zakaga yana numfashi ba sai ace mutuwar zaune yai.


Fitowar maman su adaki ta kalleshi tana girgiza kai/ tare da dauko kujera tana zama kusa dashi bai kula ba saida tadan taba shi sannan ya sauke ajiyar zuciya.


Ita kanta numfashin ta sauke na tsoron kada wata muguwar cutar ta kama shi na wannan yawan tunanin da yake tace".


" Murtala ya kamata ka rage yawan tunanin nan haka ansan da ciwo amma kai musulmi ne ya dace ka rungumi kaddara idan darai Safah zata dawo mana".


"Ka duba hatta mahaifinta ya hakura ya sallama yayi aurensa harda dadi ga kanwarka Aisha rashin Safah wacce irin jinya ce batai ba wa yake zaton zata tashi bayan an tsorata da ciwon nata".

"Itama gashi tadau hakuri da kaddara har ana zancen bikinta dan Allah kaima badan niba kayi hakuri ka daure ka danne zuciyar ka".


"Ka lalibi yarinya kai aure zama haka nan bazai yuwu ba idan kai auren zaka rage damuwa".


Daga yanayin da murtala yake girgiza kai kallo daya zakai masa ya baka mugun tausayi ba karamar azaba yake shaba da dakon kaunar safah a ranshi".


Dakyar ya daga idonshi da sukai masa nauyi ya kalli mahaifiyarsa muryarsa na fita can kasa sakamakon dadewa da yai baiyi magana ba yace".


"Umma ni musulmi ne nadau kaddara saidai babu macen da zata iya maye min gurbin safah a zuciyata bazan yi aure ba dan Allah ku fahimce ni.


Jiki a sanyaye tace shikenan murtala Allah ya takaita maka wahala amma ina tausaya maka matsayi na na uwa bazan so ace wani abu ya faru dakai ba".


Daga haka tai shiru kawai ta zuba masa ido wanda gaba dayan hankalin sa baya tare dashi.



Har bayan sallar magriba jakadiya na zagayowa amma safah na nan yadda take tsoro ne ya kamata dan haka ta shiga tana kiran sunanta.


"Safah ke Safah yata". Ganin bata ko motsa ba yasa jakadiya dan bubbuga ta.


Dakyar ta buude ido jakadiya dake tsaye tace" wanne irin bacci kike kamar kindau bashin sa tashi haka tun safe na shigo kina fama har magriba".


Da sauri Safah ta tashi zaune cikin mamaki tace magriba ko sallar azahar banyi ba".


Zuro kafafunta tai amma saita kasa mikewa cikin raki tace wash Allah kafata".


Hadda yarfa hannu cikin zargi jakadiya ke kallonta kodai Abdul-jabbar ya tara da yarinyar nan🙊🙈 idan ba haka ba me zaisa tace kafarta na ciwo.


Danta tabbatar yasa ta sake kallonta dakyau tana cewa" menene a kafar taki"?.


Safah dake kallon kafar da tuno ciwon ja matan dayai dazu tace.

"Umma jiya ne bayan fitarki naji tafiya to shine na tsorata na diro daga kan gadon kafata ta goce shi kuma ya kama dazu ya jajja min".


"Kin tabbata"?.
.

"Allah umma da gaske nake".


"Shikenan to tashi kiyo alwala kizo ki rama sallolin da ake binki ina jiran ki a palor".


" To umma Yanzu zan fito ". Juyawa jakadiya tai tana fita.


Ita kuma Safah ta mike cikin mamaki sai taji kafar yayi sauki alwala tayo ta fito da sauri-sauri ta shimfida sallaya saboda kada ayi kiran ishsha.


Saida ta jero dukkan bashin sallar sannan ta jira ishsha'i tayi zafi ne ya dameta duk da sanyin dake bedroom din na esi sakamakon wanka da batai ba saita jita wani iri.


Gashi tunanin yadda zatai wankan take kada ya shigo ya sameta hakura tai ta fita jakadiya dake zaman jira tace.

"Da kinyi wanka zaki fi jin karfin jikin ki".


"Eh zanyi yunwa nake ji".


"Ga abinci tun na karyawar ki gana rana ga kuma yanzu na dare".


"Kallon tulin kayan abincin Safah tai kamar wanda mutum goma ne zasu ci sannan tace".


"Ni umma tea nake bukata".

Flask din jakadiya ta dauko tana hada mata tea me kauri ta bata".



Rabi tasha ta aje cup din abinci mekyau jakadiya ta zuba mata shima ta fara ci tace ta koshi.


Mikewa jakadiya tai ta ce bari nasa azo a debo kayan kije ki koma baccinki saida safe".


"To umma Allah yakai mu mu kwana lafiya" bedroom din ta koma cikin gaggawa ta shiga tayo wanka saidai tsiyar kayan sawa.


Shiru tai cikin tunani da ace zata gane bangaren da bayi suke da taje ta amso kayanta gashi bata so yazo ya sameta da towel dinsa.


Ganin bata da mafita yasa tadan zauna agefen gadon tana jingina bayanta tareda rufe ido kafin wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita ahaka.


Ammy na zaune a palonta ita kadai matar Amfal ta shigo gaishe da ita cikin fara'a ta tare ta barka da kwana yata.


Zama khairat tai da dan murmushi a fuskarta ta gaishe da Ammy wacce bakinta yaki rufuwa ganin yadda khairat din ta tsala ado.


Sai taji inama ace Abdul-jabbar suna nan yaga bambancin baiwa da jinin sarauta yasha haushi🙄.


Katse mata tunani Khairat tai da fadin" Ammy inane part din yayan sa zanje mu gaisa da matarsa".



Tsuke fuska Ammy tai waya fada miki yana da yaya shi kadai na haifa bashi da wani yaya".


Cikin mamaki Khairat tace amma naji shekaran jiya dazai tafi Lagos naji yana zancen tare zasuje da. yayansa Abdul-jabbar".


Cikin basarwa Ammy tace oh na manta ma dashi ke kuma me zakiwa matarsa baiwa ce ba sa'arki bace kinfi ta matsayi da komai kada ki sake wata mu'amala ta shiga tsakanin ku.


"Karki sakar mata fuska balle har taga farin hakorin ki ta rabe ki danta samu daukaka daga ita har Abduljabbar din ki manta dasu ki bawa iska ajiyar su.


Sauke ajiyar zuciya Khairat tai tare da jinjina kai wannan wacce irin mace ce a yadda taji Amfal na kambama Abdul-jabbar lallai akwai soyayya da shakuwa me karfi a tsakanin su.


Dan kallon Ammy tai tace to zanyi duk yadda kika ce".


"Yauwa yata Allah ya miki albarka kin burge ni nasan zaki taya ni yaki na".


Fitowa marakisiyya tai daga bedroom tana zama tace .

"barka dai amarya yakike zaki samu albarka amma idan kika rike gaskiya ina fada miki haka a matsayi na na yar uwarki musulma ba ina baki umarni bane.


"Duk rintsikada ki aikata abinda zaki zo ki dana sani aure ya kawo ki ba wani shirme ba kisa tunanin ki guri daya Amfal zaki matukar jin dadinsa idan kika rike shi".


"Amma kiyi hakuri fatan ban miki shishshigi ba"? Marakisiyya ta fada tana satar kallon Ammy kamar zatai dariya ganin yadda tai sakwakwa😂 tana kallonta.


Murmushi khairat tai nagode sosai da shawararki yar uwa kuma naji dadi insha Allahu zanyi amfani da duk abinda kika ce min".


Cikin bacin rai Ammy tace waike dan ubanki waya sako dake kinsan Allah marakisiyya duk ranar da kika kaini bango sai jikin ki yayi mugun tsami".


Zaro ido😨 Marakisiyya tai kamar gaske ganin a gaban bakuwa ne kuma suruka karta yarfa Ammin yasa tace" wayyo yihakuri Ammy bari ma na koma inda na fito.

Mikewa taitana kallon khairat tace" sai anjima surukata zan shigo na gaishe dake" tana fadin haka tabar gurin.


Ammy da bata so khairat ta fahimci wani abu tace" rabu da shirmenta kinji Ummul-khairi ba kanta daya ba bata da lafiya a kwakwalwarta bamuyi tunanin zata samu lafiya haka bama".


"Ayya Allah ya kara mata lafiya Ammy bari naje na koma ki huta lafiya".


"To khairat nagode da ziyara kiyi amfani da abinda nace miki fa kinji".


"To Ammy insha Allahu" tana fadin haka ta fice.


Sauke ajiyar zuciya Ammy tai bayan fitar khairat tace".


"Amma marakisiyya kwai yar iskar yarinya ji yadda taso bani kunya agaban ta dole nayi taka tsantsan idan naga tana gurin kila da gaske hauka ya fara kama ta".



Tun ranar daya matsa mata kafa Safah bata sake ganinsa ba haryau mamaki ne ya kamata kodan tasan za'ai haka dama me zaiyi da baiwa irinta yana matsayin dan sarkin masarauta guda.


Cikin damuwa ta kalli jakadiya tana cewa" umma zan koma gurinki da zama".


"Meyasa Safah me zaki a can din".


"Ni umma na gaji da zaman nan din ni kadai kwal kamar wata mayya nasan dama niba matarsa bace basai ya kaurace min ba".


"Ke waya fada miki kaurace miki yay🤔 tun washe garin da aka kawo ki part din nan ranar da
kikai ta wannan baccin suka bar masarautar nan shida dan uwansa aiki ne ya tare su".


"Wai dama tun washe gari suka bar masarautan nan amma komai idan zanyi saboda tunanin kada ya shigo ya same ni a darare nakeyi".



"Tab an gaishe ki Safah ki kwantar da hankalinki Abdul-jabbar bame zafi bane kamar yadda kika dauke shi. kibi a sannu ki daina wahalar da kanki".


"Umma koba dade koba jima kinsan zai auri jinin sarauta me matsayi da mukami irin shi niba kowa bace ba yadda za'ai ya karbe ni matsayin matarsa".


"Karshe nasan makomata daya auri wacce yake so zai sake nine kuma karshen wulakanta ni na zama me musu hidima muna nan wata rana sai haka ta faru".



"Murmushi jakadiya tai haka dai kike tunani ke karamar yarinya ce shiyasa baza ki gane ba amma idan lokaci yai zaki fahimta".


"Naji kina batun kayan sawarki na gurina ai doka ce kisa su kina baiwa yanzu kuma ke matar dan sarki ce kin wuce ajinsu".


"Allah umma ni ina son kaya/ na".


Cikin son abar maganar tace to shikenan za'a kawo miki amma kin duba bedroom din ba kayan ki ko daya".


"A'a ban duba ba".


"To kije ki duba bari na koma gurin aiki na".


"Umma ya Zarisha kuwa"?.


"Zarisha tana lafiya Safah tace ma na gaishe dake dazu da naje wajen bangaren su".


"Idan kin koma kice ina gaida ita Safah ta fada kamar zatai kuka tuna shakuwarsu".


"Karki damu zan fada mata" jakadiya na fita Safah ta mike tana shiga bedroom.


Duba wardrobe din ta farayi cikin mamaki kuwa taga bangare guda kayan mata ne masu kyau da tsada tuli guda saidai bata jin nata ne kila wacce zai aura nan gaba ya saiwa.


Rufe murfin tai tare da sauke ajiyar zuciya tana fitowa palor zamanta ko minti biyu batai ba marakisiyya ta shigo bayanta Basira da Zakiyyah ne alamar sune suka rako ta".


Basira dake kallon Safah tana jin daci da kishi da makaki a zuciyarta cikin harara tace" gata nan ranki ya dade itace wannan".


Kallonta marakisiyya tai kece baiwar da aka aurawa Abdul-jabbar? Amma gaskiya an cuci masoyina me zaiyi dake ya wuce ajin ki yanzu auren kwarya tabi kwarya akeyi.


"Dan haka kisa a ranki daya dawo zaki koma cikin kaskantattun bayi inda kika fito domin Abdul-jabbar nawaa ne ni yake so kuma nizai aura bari ke kome mukami ce baki isa na hada miji dake ba balle yar bayi jikar bayi dangin bayi girman bayi".



"Ki dau shiri kuma ki saitawa kanki hanya domin daya dawo zaki bar shan wannan esin ki koma inda kika fi wayo".


Yanzu bani da lokacinki ki saurari dawowa ta na biyu bazai miki kyau ba" su Basira ta kalla wadanda suke kallon safah ganin dan kwanakin da ta samu tayi haske da kyau tace" muje".


Juyawa sukai zasu fita Safah ta dakatar dasu ta hanyar hade yatsun ta biyu ta murza suka bada sautin 'kas-'kas👍.


Tace" hi madam ji mana minti daya😂".


Ba marakisiyya data juyo a zabure ba hatta su Basira cikin mamaki suka zaro ido waje suna kallon Safah.


Wacce ta gyara zamanta tana dora kafa daya kan daya tace.


"Naji kince zaki dawo karo na biyu to idan kin dawo din me zaki iyayi"?.


"Na sani babu soyayya tsakanin ki dashi son maso wani kike masa shin ba kiji kunya ba matsayin ki na mace me aji jinin sarauta👸 kamar yadda kika fada".


"Idan razana ni kike sonyi da magana danna ji tsoron ki kafin ki na hadu da manyan hamshakan tantirai kuma basuyi nasara a kaina ba saboda ni ba sakarya bace".


"Sannan ban wahalar da zuciyata ba na lalata ta da son wanda ba sona yake ba".


"Kince an cuce shi to waye ya cuce shin dame aka cuce shi fada min".


"Zai dawo ke dashi kuyi auren kwarya tabi kwarya domin ni baiwa ce saidai ki sani na fiki kima da dajara a gurinsa duk da matsayi da kike tunkaho dashi ".


"Ban kaskantar da kaina na zubda ajina ba a gurinsa balle yaga gurin kwana na ni baiwa ce fadi ki kara amma ba'a isa a raina niba wuce nan😠".


"Duk yadda kike zaton ya dauke ki koya rike ki a zuciyar shi baki fini mukami ba domin ni matarsa ce yanzu nauyi na dukkan kulawa ta tana wuyan sa ko baya sona".


"Duk wanda zai kalle ni dole yamin kallon matarsa ke kuwa kinga baki da wannan matsayin saidai a miki kallon mahaukaciyar sa🙊".


"Me wahalar da kanta akan wanda baya ra'ayinta ni kuwa idan naga damar ya soni ta sassaukar hanya zan mallake sa saboda yanzu a hannu na yake".


"Koda sunan zai firgita ki zan fada Abdul-jabbar miji nane nawa ni kadai ni daya ina nufin ba wata ni din dai ce matarsa a yanzu".


"Koda a littafin tarihi nasan suna na yana ciki hade rubuce da nashi kuma bake ba koda zai auri mata dari nan gaba duk matsayin su a bayana sukke".


"Nice babbar su shugabar su auntyn su jagoran su uwar gidan su domin nice matarsa ta farko first wife dinsa kuma surukar sarki ta farko a kafin tarihi".


"To ya kika ji yanzu dana miki bayani ba kiji kin koma kasan kafa taba idan matsayin da kike fada ne na kere ki".


"Kina ta magana akan matsayi to bari na fada miki iyakar ki sunan ki Mara'kisiyyah .

kawai baki da wani abu da za'a raba me kwar

Please Login or Register in order to submit comment