Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gajiya dakai ba dan baka san yadda nake sonka bane da zaka dawo part dina gaba daya da zama da nafi jin dadin hakan".


Shikenan Ammy za'ai duk abinda kike so amma yanzu nayi girma da zaman part dinki zan rika zuwa kullum sau biyu".

Dadi ne sosai ya kama Ammy taita jansa da hira dan kada ya tashi ya tafi gurin Abdul-jabbar shima Amfal din yana sani ya biye mata".


Typing 👉📲



SAFREEYYAH



MRS AL'AMEEN AHMAD CE



#YUSRAHMS#
NO.77 👉78
Safah na cikin bacci taji ana kiran sunanta a firgice ta farka maimakon taga Zarisha ko jakadiya sai taga wata baiwa da batasan ta ba da kuma su Basira Fuskar su fal da annuri".


Zakiyya da take ta murmushi tace gata nan itace Safan da kike nema sannan ta kalli Safah ke kuma yar samun guri saiki tashi ki bita lambar ki ta fito".


Kallon baiwar dake tsaye a kanta Safah tay cikin jin nauyin jikinta tace kece kike nema na lafiya".


Bani bace nima yar sako ce wani dogari ne sai ki taso karki bata masa lokaci".


Mikewa Safah tay tana fita yayin da suka rufa mata baya duuu kamar kuda har gaban mutumin cikin zumudi Basira tace gata itace wannan".


Kallonta mutumin yay kece Safah"?.


Kai ta daga amma magana ma ta kasa yi domin sun fara caza mata kwakwalwa ita da batasan kowa waye yake neman ta"?.


Wata zuciyar tace mata kila wannan muguwar matar ce".


Dawo da ita daga tunani mutumin yay ta hanyar cewa muje inda ake kiran ki" wucewa yay tabi bayan sa har part din da take aiki yace kalli can".


Kallon gurin Safah tay yace ga wanda yake neman ki can" yana fadin haka ya fice.


Cikin faduwar gaba Safah ta nufi inda yake tsaye ya kame a ranta tace wannan ai dan sarki ne mezan masa Allah ka tsare ni daga sharrin sa kasa ba lalata min rayuwa zaiyi ba".


Sallama ta masa tana durkusawa muryar ta har rawa yake saboda tsoron abinda zaice mata.


Can kasa sosai ta tsinkayi daddadar muryar sa yace biyo ni".
u

Wani irin makyarkyata da karkarwa jikinta ya dauka dakyar ta mike tana bin bayan sa har suka shiga ainashin part din nasu".


Dakatawa yay tare da juyowa yana kallon ta fuskar shi a mugun hade yace" waye yasa ki kika kashe min doki fada min gaskiya"?.

Kallonta takai kan dokin da yake kwance sade-sade alamar ya dade da mutuwa Cikin wani irin yanayi na tashin hankali da rudanin data shiga a zabure bata san lokacin da tace.


"ranka ya dade ni kuma wallahi bani bace bansan komai ba ka yarda dani".


"Kina nufin wadannan da suka ga lokacin da kika fita daga part din karya suke miki".


Cikin mamaki taga Basira da Zakiyyah suna mata gwalo a fakaice".


Sai wani dogari dake gefe yace ke yarinya waye ya miki karyar baki shigo bane nima na ganki da idona lokacin kin fita kina waige-waige ba shakka kece kika kashe dokin nan".

"Wallahi tallahi ranka ya dade bani bace ta nuna su Basira wadan nan ma'kiya nane sharri sukai mi..........


Bata iya karasawa ba sakamakon wani zazzafan mari daya sauka a kuncin ta".

A firgice ta dago tana kallon sa idonsa yayi jawur nuna ta yake da yatsa ya kasa magana.

Da sauri Amfal daya hango abinda ke faruwa ya karaso gurin tare da janye shi ganin yana sake shirin marin ta".

Kokarin kwacewa yake kamar wanda ya fara fita cikin hankalinsa yana cewa" Amfal sake ni kafin na sauke dukkan fushina a kanka ni zata kashewa doki wace ita".


Kara rike shi Amfal yay dan bai taba ganin sa cikin irin wannan yanayin ba yace indai zaka rabu da ita bros na yarda ka sauke fushin a kaina".


Kallonta Abdul-jabbar keyi tun dazu cikin kunar rai damar kwacewa yake son samu ya shake mata wuya ko zai daina jin radadin da zuciyarsa ke masa".

"Muje bros" Amfal yace yana jansa.


Nuna ta yay da yatsa muryar sa ta canza sosai yace" tunda nake aduk duniya ban taba jin na tsani kowa ba kece mutum ta farko a rayuwata da nake 'ki na tsane ki wanda yake sonki ma bana kaunar sa kuma ki jira gamo na dake.


saura ni zaki kashe kin kashe min dokin da na ke tsananin so kamar raina shine nake gani kyautar mahaifiya ta na tsane k..........


Bai karasa ba ya zube jikin Amfal idonsa a rufe.


Cikin rudewa Amfal ya soma jijjiga shi "bros bros please dan Allah ka bude idonka kadau hakuri".


Ganin duk jikinsa ya saki yasa Amfal yace wa dogarin dake tsaye kama min shi mu shiga ciki zuwa palor".


Taya shi munafikin dogarin yay suka shiga dashi yayin da Safah ta durkushe a gurin tana sakin wani sabon kukan damuwa da tashin hankali wanda ba'a sa masa rana".


Dan hada ido su Basira sukai suna murmushi Zakiyyah tace" Safah me wayo kin ga ne cewa ba'a hada kafada damu yanzu kinga makomar ki da me kike tunani? Zamu barki kara zube bamu dau matakin abinda kikai mana ba"?.


Basira ce tace ke zakiyyah kyaleta haka mu tafi kar wani yaji ki sa mu shiga uku ke kuma mun barki lafiya ko yanzu mune mukai nasara akan ki".


Juyawa sukai suna fita yayin da Safah ta bisu da kallo wato sune sukai wannan aikin domin su munana mata su sakata a tsaka me wuya.


Mikewa tay tana tafiya dakyar gabanta tana ganin dishi-dishi a ranta tace ba komai akwai Allah shine zai saka min tunda bani da alhakin ku zaku gani".


Basu zame ko'ina basai part din Ammy suka labarta mata komai basu taba ganin annurin fuskarta ba tunda suke sai a ranar sannan ta basu kyautuka da yawa wanda ya basu mamaki.


Suna fita shima dogarin nan ya shigo ya fada mata Abdl-jabbar ya suma kuma an yayyafa masa ruwa amma ko kadan baiyi motsi ba kila ya mutu.


Shikam wannan kyautar da Ammy ta masa bata faduwa bayan fitarsa har ruwa ta zuba a kasa tasha tana dauko carbi tare da addu'ar Allah yasa karya farfado daga suman ya wuce kabari.



Safah na zaune a daki ta zuba tagumi naban tausayi shigowar Zarisha kenan ta tsaya turus tana kallonta cikin mamaki tace.

"Safah lafiya kawai muna tsaye na neme ki na rasa ashe kin gudo badai tsoron bindigar ne yasa kika zo kika takure kanki a daki ba ai shikenan an gama sai babbar salla kuma ki fito mu shiga cikin masarauta inda baki taba zuwa ba yawo har wajen baba na zan raka ki".


Ganin bata dago ba balle ta mata magana yasa ta karasa tana dago da fuskarta ta bude idon da sukai ja Safah tay tana kallonta wasu hawayen na taruwa mata".


Zaro ido Zarisha tay subahanallahi Safah lafiyar ki kalau kuwa kuka kikai kome kiga yadda idanuwan ki suka rune"?.


Kai Safah ta girgiza lokaci guda kuka data ke rikewa ya sake kwace mata tace.

"Zarisha sharri akai min wani ne yaje ya kashe dokin dan gidan sarkin nan kuma akace nice harda shedu".


A zabure Zarisha ta mike" innalillahi wa inna ilaihi raji'un wanne irin doki kuma kika kashe".


Muryar Safah data riga ta dashe dakyar Zarisha ke jinta tace "dokin daya gama tsere dashi dazu wallahi duk wanda ya aikata wannan aikin ya cuce ni".


Kasa magana Zarisha tay saboda takaici haka suka zauna kamar kurame a dakin shiru.


Zuwa wani lokaci Safah ta soma kwara amai kamar an bude kan famfo har tsoro aman ya bawa Zarisha ga jikinta kuna tun tana iya yinkurin aman har tazo saidai ya mamalo mata a jiki cikin yan sakanni ta canza duk kuzarin ta ya kare.


Ga wata rawa da jikinta keyi Zarisha na goge mata jikinta taga idanuwan ta suna juyawa da karfi ta soma kiran sunan ta.


"SAFAH! SAFAH!! Dan Allah ki bude idonki".

Jin shiru yasa ta kwantar da ita tana mikewa da gudu ta fita daga dakin tana kuka ta tafi neman jakadiya.


Har washe gari Abdul-jabbar baisan inda yake ba abin yana bawa Amfal tsoro amma da yake baya son case din ya fita koda gurin Emir ne yasa ya yanke shawarar yau da dare zai dauke shi a mota ba wanda ya sani su tafi asibiti.


Yana zaune ya zuba tagumi a palor yaji tafiya ta bayan shi da sauri ya waiwaya ganin Abdul-jabbar yasa ya mike yana riko shi suka karaso ya zaunar dashi yana cewa.

"sannu bros ya jikin naka"?.


Kai Abdul-jabbar ya daga murya a hankali yace "da sauki Amfal kawo min ruwa".


Mikewa Amfal yay yana bude fridge ya dauko masa mara sanyi yana zubawa a cup ya mika masa".


Karba yay kurbar sa daya ya furzar dashi yana jifa da kofin kamar wanda yasha magani yana kallon Amfal yace.

"Ruwa fa nace ka miko min"?.


Cikin mamaki Amfal dake kallonshi yana tunanin ko baya cikin hayyacin sa ne yace.

"To ai bros ruwan na miko maka".


"Haka ake ruwan? me sanyi nake so".


Sauke numfashi Amfal yay jin ba wani abu bane ya sake mikewa ya bude fridge din duk ba ruwa me saukin sanyi harda wanda ya dan fara kankara.

Amma dole haka ya dauko masa roba guda jikinta har raba yake zai zuba masa a kofi kamar wancan yace masa".


"Bani a robar kawai".

Bashi yay tare da zuba masa ido domin yasan ruwan bazai shawu ba sanyin sa yay yawa sosai.

Amma ga mamakin sa sai yaga ya kafa yana sha tamkar wanda yake shan mara sanyi dire robar yay yana kallon Amfal yace.


"Karo min wata".


"Iye"? Amfal yace cikin alamar tambayar kalau kake kuwa".


Sake maimaita mishi yay "nace ka karo min wata".


"Amma bros ruwan yayi sanyi da yawa baka tsoron ya maka illa"?.


"Amfal karo min daya".

Jin ya sake maimaitawa yasa ba musu ya mike yana kara dauko masa ya bashi itama sai robar ya ajiye.


Sauke ajiyar zuciya yay yana dan rufe idonsa kadan ba duka ba Amfal dayay shiru yana kallon shi yace "sannu bros yaya jikin naka ko asibiti zamuje a sake duba ka"?.


Kai ya girgiza batare daya bude idonsa ba yace" da gaske dokin nan ya mutu"?.


Dan dafe kai Amfal yay cikin damuwa ya tashi ya dawo kusa dashi tare da rike hannunsa yace".


"Bros dokin ka ya mutu kayi hakuri Dan Allah ka zama me tawakkali da daukar kaddara me kyau ko akasin ta sai Allah ya musanya maka da mafi alkairi ka cire duk wani kokwanto aranka kada kace zaka dau mataki akan yarinyar nan ta yiwu ba itace ba wani ne daban koma dai waye ka kyale shi da wanda ya halicci dokin ka manta da komai dan Allah".


Kai Abdul-jabbar ya daga shikenan Amfal nagode zanyi amfani da abinda kace na bari akan koma waye din ya kashe min shi na barshi da fitowar rana da faduwar ta".


Cikin jin dadi Amfal yace yauwa bros ka kyauta Allah yana son masu yafiya idan an zalunce su".



Safah kam nata zazzabin daya hauta azimun ne domin ko abinci taki karba ta ci ba magana sai kallo da ido iya damuwa jakadiya da Zarisha sun shiga kuma tunda babban abune suna tunanin wanda zasu tara da maganar.


Tea Zarisha ta hada tana tashin ta zaune amma saita girgiza kai alamar baza ta sha ba tana kallon jakadiya tace" wallahi umma ba nice na kashe masa doki ba".


Cikin tausayawa jakadiya tace na sani Safah kuma na yarda dake taya zaki iya kashe doki kamar wani kiyashi ko cinnaka shima dan a rude yake idan ya dawo dai-dai zai fahimta.


"Safah na kuka tace umma taya zai fahimta nifa baiwa ce ba wata magana ce take hada mu baa ni banda ranar ma ban taba jin muryarsa ba yace duk duniya nice mutum ta farko daya fara jin ya tsana".


Zarisha tace saime dan yace haka tunda ba kece kika kashe shiba dama meye hadin hanyar mota data jirgi kina baiwa yana dan sarki ba lallai ma ku sake haduwa ba duk wata hanya da kika san zaki hadu dashi ki soke binta part din na suma karki sake zuwa aikin a nemi wata asa".


Dakuwa jakadiya ta mata kinci gidan ku zarisha da zarar magana rufe min baki".

Safah ta kalla kinga yi hakuri 'yata komai yai farko zaiyi karshe wata rana gaskiya zata bayyana karbi kisha idan ba haka ba bazanji dadi ba".


Daukar tea din tay a bisa dole ta soma sha badan tana so ba saidan abinda jakadiya tace tadan ji sassauci tanan".



Baba Maryam ta koma Adamawa domin kowa ya hakura da batan Safah ya dangana dole itama taa koma gurin neman kudinta amma duk ranta a dagule".


Hajiya Binta na zaune mk na bata hakuri akan abinda daya faru domin har yanzu fushi take dashi maryama tazo wucewa dakatar da ita tay ta hanyar cewa.


"Maryama kodai baki da lafiya ne duk kinyi baki kin rame kuma ina ta zuba ido zanga kiran ki idan bikin safah ya matso sai naji shiru gashi na kira wayarki a kashe fatan kunyi bikin lafiya"?.


Kuka baba maryam ta fashe dashi tana zama a gurin tace "ai hajiya saidai ki taya mu jaje munyi biki ko munga tashin hankali da al'ajabi ana gobe daurin auren yarinyar nan wani ya kira ta a waje daga fita shikenan aka neme ta ko sama ko kasa babu labarinta har yau".


Dafe kirji hajiya tay na shiga uku ta bata kenan kome ba'a ganta ba".


Baba maryam da abin ya dawo mata sabo tace wallahi shikenan yarinyar nan kila dan mafiya ne ko fayde ya mata bamu da tabbacin tana raye ko kuma ta mutu".


Mk dake gefe yana sauraron su sai yaji duk jikinsa yay sanyi tunda yasan shine silar komai ga wata irin nadama da dana sani data lullube shi lokaci guda ya nemi nutsuwarsa ya rasa.


A ransa yace lallai na aikata kuskure na cuci mutanen nan na zalunci yarinyar nan hakkinta kadai bazai barni ba".

Yaya mahaifin ta yaji? wanne hali ya shiga? Yaya wanda zai aureta yaji daya san za'a sameta daya fada musu gaskiya saidai baya jin zata iya


Tseratar da kanta daga hannun wadannan mutanen balle ya kashe wasu daga cikinsu kuma gashi tare suke da ita kila sundau mataki a kanta sun kasheta ko sun mata fayde".


Runtse ido yay da karfi yana jin dama bai aikata hakan a gareta ba taya zai nemi yafiyarta idan kuma ta mutu fa?.


Salati da sallallami sosai hajiya keyi yayin da baba maryam ta kunce gefen zaninta tana ta faman goge hawaye".


"Shikenan kuma safah baiwar Allah ashe munyi bankwana da ita na karshe kenan bazamu sake haduwa ba Allah ya bayyana ta maryam idan har tana raye".


" Amin baba maryam tace tana sake tare hawayen dake zubo mata na tuna rayuwar da sukai a baya yanzu ya zama tarihi".



Satin su uku suna fama da jinyar Safah kuma jakadiya na bakin kokarinta wajen ganin ta kula da ita tamkar yadda zata kula da Zarisha.


Hanne batai salla a gidan sarauta ba tunda ta tafi da sunan zuwa gurin boka ana saura kwana uku salla bata dawo ba sai yau.


Ammy data tsareta da idanuwa tace "sannu hanne da 'kin dawowa daga aiken ki sai kikai zaman ki a gurin bokan ko".

"To wallahi duk ranar daya dirka miki ciki ki kuka da kanki karki soma doso ni babu abinda ya shafe ni dan nice nake aiken ki bance kije ki samu guri ki zauna ba saiki kiyaye".



Wani irin takaici ne ya kama hanne jin abinda Ammy ke cewa a ranta tace.

"Humn dan adam kenan shiyasa ban yarda dake ba nasan zaki iya juya min baya idan wata muniyar ta sameni koda kuskure bazan amince dake ba".


Amma a fili bata nuna damuwar komai ba tay murmushi tana cewa.

"Haba ranki ya dade tsofai-tsofai dani na tsaya ina aikata haka"?.


Cikin kwarin gwiwa Ammy tace" kwarai kuwa tsofin ba sune manyan tantiran ba".


Hanne zatay magana ta katse ta da cewa" meye labari yanzu a ina muka tsaya me boka yace"?.


Hanne data gama kulewa cikin son tabar gurin ta dauko wata daurin leda tana mika mata tace".

"Gashi yace a rika lura a tabbata yana sha kullum kada ya kuskure rana daya har kwana bakwai shikenan zaiji ba wanda ya tsana kamar shi duk duniya".


"Waye wanda za'a bawa maganin a cikinsu" Ammy ta tambaya tana kallon hanne".


Dan shiru hanne tay tana tunani sannan tace" yariman ki zaki baiwa kinga shine zaifi sauki inji boka".


"Shikenan tashi kije saina sake neman ki" mikewa hanne tay tana fita dariya fal cikinta ta shiga bangaren su".


Fitowar marakisiyya kenan taci kwalliya sosai ta sa kaya yan uban su zata fita Ammy ta dakatar da ita.

"Ke ina zuwa haka da wannan kwalliyar kira min Amfal ku taho tare ".


DancijebakimarakisiyyataytanakallonAmmydayanayincewakinatakuramintace.

"Zanje part din su Amfal ne daga nan na wuce na gaishe da hajiya".


Tsaki Ammy tay waike hajiyan nan kamar kanwar uban ki kullum bini-bini kina yawo a part dinta kamar me neman arziki".


Dariya marakisiyya tay niko nake neman arziki a gurinta tunda jikanta nake so shine jigo na".


Waike baki daina son shegen yaron nan ba kinga ki kiyaye ni".


"To wai Ammy mene aibun Abdul-jabbar da bakya so na aure shi"?.


Takaici ne ya kama Ammy tace ban sani ba dan ubanki".


Kafada marasiyya ta daga to tunda baki sani ba saiki barni na auri abina badi iyanzu kiga dan boy din mu yana zagawa".


Wannan karon zaro ido Ammy tay uban dan boy dinku zan ga ni to bari kiji idan ma mafarki kike saiki farka Abdul-jabbar baida da bazan taba barin sa ya haihu ba har abada".


Wani kallo marakisiyya ta mata tana cewa "ki taka sannu sannu baki isa ki hana Allah abinda yaso ba insha Allahu Abdul-jabbar sai kinga dansa da idanun ki".


Mikewa Ammy tay a fusace wanda yasa marakisiyya fita da gudu tabar ta tsaye kamar ta hadiyi sanda jikinta na tsuma.


Bacin rai da takaici sun lullube ta idonta harda sauran hawaye bata so marakisiyya tazo yanzu ba gashi tana neman lalata mata tsarinta taya zata amince jininta ya hadu data wanda bata kauna?.


"Ina wallahi marakisiyya ko mutuwa zaki bazan barki ki auri Abduljabbar ba nafi karfin hada zuriya dashi.


Marakisiyya data tsaya sauraron abinda Ammy ke cewa tadan daga murya tace" .


"Ammy kibar wannan batun kina bani dariya hada zuriya kam wacce kike nema saidai in ciki zaki maida Abdul-jabbar ki sake haifar shi saiya zama danki amma idan ba haka ba kina auren mahaifinsa kin haifa masa kani kike maganar bazaki hada zuriya dashi ba gara ki daina wannan maganar domin baki da wata hujja nina wuce".


Tafiyar ta tay tabar Ammy baki bude hankalinta a tashe tace na shiga uku wannan yarinyar tana neman jefa ni a masifa ko Amfal da kuke jini daya bazan yarda ki aure shiba balle Abduljabbar dole na tashi tsaye akan ki".



Hango jakadiya hanne tay tana zuba sauri kamar zata tashi sama mamaki ne ya kamata dan kara hanzari tay ta same ta cikin alamar tambaya tace.


"Lantana lafiya naga kina sauri haka".


Juyowa jakadiya tay tana cewa" hanne yaushe kika dawo wallahi yarinya ce bata da lafiya gashi na baro ta ita kadai Zarisha na gurin aiki shine zan koma na dubo ta".


"Wacce yarinyar kuma dama kina da wata yar ne".


Kai jakadiya ta girgiza ko daya ba yata bace yarinyar nan da Adama ta sayeta ce aka samu wani ya kashe dokin yaron nan Abdul-jabbar ranar salla shine aka ce itace".


Dafe kirji hanne tay subahanallahi gaskiya an cuceta sharri ne akai mata kina jin abin ma kinsan makiya ne taya zata kashe dokin dame".


Dadai sun shiga dakin jakadiya tace gane min hanya hanne kema dai kya fada kin ganta nan a kwance ko tashi batai tun ranar sallar".


"Ayya sannu yarinya Allah ya baki lafiya shi kuma wanda ya aikata aikin Allah ya bankada shi ya tona asirinsa".

Hanne ta fada cikin tausayawa haka kawai taji safah ta shiga ranta.


"Amin dai Hanne Allah ya tona mai asiri ta hanya mafi muni.


Kinga fa da tana karbar dan tea ma tasha muna murna harta fara cin abinci sauki yazo lokaci guda ta sake kwanciya".


"Kai Hanne ta daga bari naje daki inada wani magani a gwada mata mu gani ko zamu dace".


Mikewa tay ta fita zuwa dan jimawa ta dawo da maganin cikin karamin kofi ta zuba tasa ruwa kadan tana mikawa jakadiya tace.

"Bata wannan din mu gani".


Karba jakadiya tay tana daga Safah da idanuwanta ke rufe tace" 'yata bude bakin ki ki karba kinji Allah zai baki lafiya ki rage yawan damuwar dake ranki".



Bude bakin Safah tay ta karbi maganin tana gama sha ko kafin jakadiya bata janye ba amai ya soma ambaliya".

Kallon hanne jakadiya tay jikin ta a sanyaye tace kinga niko hanne duk abinda tasha baya zama dawowa yake nikam ina tsoron jinyar yarinyar nan".


Kai. hanne ta girgiza tana daukar wani kofin ta sake jikawa tana bawa jakadiya tace.

"Insha Allahu lantana zata samu lafiya".


Karba jakadiya tay ta sake bata amma labarin daya ne wannan karon ma aman tay har wani kala= yake.


Ganin haka yasa hanne tace akwai wani kalar maganin bari na dauko abar wannan din".


Fita tay da sauri sai gata ta dawo shima jika mata shi sukai suka bata da sukai sa'a wannan din batay aman saba.


Dadi suka ji sosai dan haka hanne tace kinga kawai Lantana aje maganin a gurin ki zuwa an jima idan kinga ya danyi mata aiki saiki sake jika mata ki bata".


"To hanne nagode Allah ya saka da alkhairi" jakadiya ta fada cikin jin dadi.


Mikewa hanne tay zata fita tace ba komai wallahi Lantana karki damu bari na karasa ciki zuwa dare zan dawo na sake duba jikin nata Allah ya kara sauki".


"Amin Hanne" .




[23/04/20] +234 905 527 3614



YUSRAH MUSA ABUBAKAR.



#YUSRAHMS#
NO.79👉 80
Bayan kwana biyu.



Zaune suke a palor Abdul-jabbar ya zubawa hannun sa na dama ido tun dazu ya kasa magana Amfal daya lura cikin alamun tambaya yace.


"Bros meye a hannun naka ne kake kallo kamar madubi ko tuna marin da kaiwa wannan yarinyar kake yi"?.


Sauke numfashi Abdul-jabbar yay tare da dan girgiza kansa yace itace taimin laifi amma yanzu nine da tarin na dama nayi dana sanin marin ta yafi sau a kirga gashi abin yazo yana damu na".


"To amma bros komai ya riga ya wuce saika manta".


" Amfal taya zan manta bayan hakan nacin raina".


"Abinda za'ai bros tunda kace abin yana cin ranka mezai hana muje bangaren bayI saika bata hakuri".


Zaro ido Abduljabbar yay nine zan bata hakuri kasan me kake cewa kuwa"?.


Dariya Amfal yay na sani mana babban yaya na ai durkusawa wada ance ba gajiyawa bane mene danka bata hakuri".


"Hakan bazai taba samuwa ba Amfal daina ma fada karka dora min ciwon kai".


"Shikenan bros kaima wani san taurin kaine dakai kamar yaron" shiru yay bai karasa ba".

"Kamar yaron me zaka ce"?.


Kai Amfal ya girgiza a'a bros nayi shiru abar kaza a cikin gashin ta".


"Wato cewa zakai taurin kai kamar yaron jaki ko"?.


"Umh umh nifa bance haka ba" Amfal ya fada yana rufe baki.


Abdul-jabbar zaiyi magana marakisiyya ta shigo da sallama tana zama tace" Amfal kaje Ammy na neman ka".


Juyawa tay saitin Abdul-jabbar tana kallonsa wanda shi kuma hankalin sa baya kanta tace "ina maganar mu ta tsaye ne bros din Amfal"?.


Cikin alamun tambaya yace maganar me".


Gyara zama marakisiyya tay amma dai basai na fada maka ba kaima kasan saboda dakai nake zuwa gurin Ammy hutu kuma ina son ka aure nine".


Lokaci guda shida Amfal suka zaro ido waje jin abinda tace.


Hade rai Abdul-jabbar yay yana kallonta yace wacce magana kike wannan ai ni ko soyayya babu a tsakanin mu balle harna aureki".

Shagwabe fuska tay nidai gaskiya ina sonka kuma saina aure ka gara ma ka kwana cikin shiri ba gudu ba jada baya".


"Amma baki da hankali marakisiyya kibar zancen nan tun kafin ki bata min raina bana son shashanci bazan iya auren kiba dan haka ki daina batawa kanki lokaci".


Kallon Amfal marakisiyya tay dan Allah ka fahimtar da dan uwan ka wallahi shine burina bani da mafarki sai. nashi".


"Nifa babu ruwana a cikin lamarin ku ki daina sakowa dani shi zaki fuskanta".


Amfal yasan marakisiyya nason Abduljabbar amma yasa a ransa bazai matsa saiy ya aure taba ra'ayin sane.


Kuka marakisiyya ta saki tana cewa karka min haka Abdul-jabbar ina sonka idan baka soni ba ciwon zuciya zai kama ni".


"Kinga marakisiyya da rayuwa dayin soyayya akwai bambanci ya kamata ki fahimta idan na aure ki zan takura kaina ne tunda bana ra'ayinki matsayin mata ta kisa nutsu wa ki fahimta".


Mikewa marakisiyya tay tana kuka tace wallahi bazan yarda ba saika aure ni kota halin kaka bari naje gurin hajiya na fada mata".


Tana fadin haka

Please Login or Register in order to submit comment