Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inta riketa zata ji jiki da sauri tay wuff ta fada daki.


Dakatawa mariya tay tace ai dakin tsaya dana nuna miki wacce ni ashe bari ba shegiya bace da ubanta kura ma tasan gidan me babban sanda tunda kina da sha'war jin karfina zan nuna miki ko ba yau ba".



Komawa marya tay tana daukar nata kayan tay daki tabar na Asabe a gurin Asabe dake lekenta ta window da sauri ta fito ta debe nata kayan itama tay dakiπŸ™ˆ.

INA GODIYA FANS
TNK FOR YOUR SUPPORT.


YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA

πŸ•ŒπŸ•‹πŸ•Œ
πŸ™Œ May Allah open the door of success amin may Allah help you and your household amin it's friday don't forget to recite suratul-al khaf πŸ‘.

JUMAATMUBARAKπŸ“Ώ.β˜•πŸŒ―πŸͺπŸπŸ”πŸ—πŸ¦πŸ‡πŸŒπŸπŸ‰πŸŠπŸ²πŸ›πŸœ



#YUSRAHMS#
NO.69πŸ‘‰70
Farin cikin me martaba baya boyuwa da dare dakyar yabar su Amfal suka tafi part dinsu gari na wayewa yasa akai kiran su sai a gurinsa sukai alzikar domin bazai jure sai rana ta dago ba.



Amfal daya kasa nutsuwa tun dare yake so ya tambayi Emir sai yanzu yay kuru yace Abba yaya wannan abu kuwa.


Dagowa Emir yay yazu ba masa ido cikin alamun tambaya sannan yace yana nan ya kamata kuje ku ganshi.


Abdul-jabbar dake kallon su baiyi magana ba dan lamarin su sai su.


Mikewa sukai cikin farin ciki Amfal yace "bros muje mu dawo yau zaka ga komai".


Hade rai Abduljabbar yay bayan sun fita yace "waikai me kuke boye min ne kaida Abba"?.

Cikin maganar kurame Amfal ya nuna masa da hannu cewa ba komai.


Dan tsaki yay daidai zasu shiga part din Fatima yace "Amfal meke damun kane inda ba kowa kuma me zamu dauka anan"?.


Murmushi Amfal yay "eh ba kowan zamu dauka kaidai muje kawai ka zuba ido kai kallo kaga abin mamaki".


Daidai sun shiga palon Abduljabbar yaga mace zaune taci ado cikin dakakken less kallon Amfal yay da mamakin sa da yaki boyuwa ga tambaya a ransa.


Da ido Amfal ya masa magana sannan yadan daidaita nutsuwar shi sukai sallama.


Dagowa tay tana kallonsu sai kuma tay murmushi tace "oyoyo Hassan da Husaini ku karaso mana 'ya'yana na kaina saukar yaushe"?.


Karasowa sukai suna zama Amfal da bakin shi bai mutuwa yace "auntyn mu barka da gida fatan mun sameki lafiya amaryar Abban mu"?.


Dan zaro ido Abduljabbar yay cikin mamakin jin abinda Amfal yace wai amaryar Abban su yaushe yay aure bai sani ba.


Maganar Fatima ce ta dawo dashi daga zancen zucin da yake.

"Lafiya kalau ya kuke ya aiki"?.


Sauke ajiyar zuciya Abduljabbar yay bayan sun gaisheta cikin mamakin da yakI barin sa yay sukuni yake kallonta ya kasa magana daga ita sai Amfal ke zance shikam shiru yay yana binsu da ido.


Bayan sun fito Amfal kece wa bros meyasa kayi shiru ne ka barmu muna ta zance mu kadai"?.

To ya kake so nayi Amfal kasan bazan iya zance irin naku ba mene zaisa ka takura min".


Amma bros saika rika tsoma mana baki lokaci-lokaci gashikuwa itama me baki ce mun samu gurin hira".

Bros kasan nine nace Abban mu ya kara aure"?.

Kallonsa Abduljabbar yay yaushe haka ya faru ban sani ba?.

Amfal dake murmushi yace. lokacin da zamu tafi ban yiwa Abba rada ba har kana tambaya ta abin kenan".

Kai Abduljabbar ya girgiza sannunka da kokari kayi babban jihadi tunda gashi naga kamar zamu samu kani kwana kusa".


Zaro ido Amfal yay kaiii bros taya ka gane bayan kaiba likita bane"?.


Dan hararar sa Abdul-jabbar yay suna shiga part din Ammy tana ganin su taji farin ciki ya mamaye ta saboda tasan yanzu aikin boka zai fara".


Dan gyara zaman ta tay tana murmushi da fara'arta tace dama yanzu nake cewa tunda baku shigo minba kila kuna gurin me martaba bari naje ashe kuna tafe sannun ku da dawowa".


Kallon juna sukai cikin mamakin kalamanta Amfal yace oyoyo Ammy na ya kike ya gida".


Kasa nutsuwa Ammy tay saboda duk tunanin ta ko aikin boka yaci.

Zatay magana Amfal yace kiyi hakuri nasa Abba ya kara aure ko? haka ne ya dace sarki bai kamata ya zauna da mace daya ba ni idan na tashi yin nawa auren zan ninka Abban mu hudu zan aura domin tsaro".


Wani irin mikewa tsaye tay har saida Amfal ya matsa baya da sauri".

Shaka takai masa muryar ta na rawa cikin tsawa tace kaine dama ka zuga shi ya kara aure saboda baka kauna ta anya Amfal kai dana ne ba'ai min canjin ka a asibiti ba?.


Ba wani canji da akai miki Ammy ni dan ki ne kawai so nake ki gyara halin ki".

Cikin kunan rai Ammy ke kallon shi zatay magana saiga hawaye shar shar yana zuba".

Kiyi hakuri dan Allah Ammy ki yafewa Amfal ke mahaifiyar sa ce" Abduljabbar ya fada yana hararrar Amfal din ganin yadda ya wani koma gefe ya rike kugu kamar ba shine ya jangalo komai ba".


Ammy batay magana ba kawai Amfal ta zubawa ido babu kokiftawa".


Ganin Amfal din na shirin magana yasan kila wani abin haushin zai sake fada mata janye shi yay suka fita a part din yana kallonsa cikin girgiza kai yace.


Wai dan Allah Amfal miyasa baka da saiti sai yaushe zakai hankali ne idan baka kama kafar Ammy ka mata biyayya ba taya kake tunanin samun rahma".


Hade rai Amfal yay bros baza ka fahimta ba Ammy zuma ce saida hayaki idan ban katse mata hanzarin ta tun wuri ba nan gaba zata iya aikata abinda za azo ayi da nasani manta da hakan muyi abinda ya kamata".


"Na manta da hakan muyi abinda ya kamata Amfal kanka daya kuwa meke damun tunanin ka ne yaushe ka canza"?.


Dariya Amfal yay Allah bros ka fahimce ni ko sau daya ban canza ba haka yanayina yake bazan iya biyayya wa Ammy ba har saita gyara halayen ta".


Kallonsa sosai Abduljabbar keyi yace halinta name zata gyara Amfal na fahimce ka baka da wata hujja dan haka shashanci ba naka bane ka tsaya ka rike Ammy".


"To shikenan bros zanyi abinda kace komai ya wuce muje dan wallahi azumin nan harfa ya soma gara ni".


"Aiko ka gamu da aiki domin sai yanzu ma sha biyu tayi".


Wucewa sukai Amfal na cewa muje gurin hajiya a can zanfi saurin ganin tafiyar lokaci".


"Eh saboda zaka je ka hana mata nutsuwa dole kace haka nikam yanzu dokuna na zanje na gano".


Zaro ido Amfal yay suna tafiya yace kana nufin bana dakai za'ai hawa bros abinda bai dame kaba".


"Fadi ka kara bana haka nan naji ina matukar kaunar tseran doki bansan me yasa ba ko mene dalili naji masarautar ma gaba daya ta canza min kamar da sabon abu a cikin ta mai muhimmanci".


Rolling ido Amfal yay cikin tsokana yace" a'a fa bros fadi gaskiyar ka na daure yace a sassauta kodai-kodai".


Hade rai Abduljabbar yay kodai-kodai me"?.

Rufe baki Amfal yay uhm uhm ta kurame nayi shiru🀐.


Shafa bayan dokin Abdul-jabbar keyi bai tanka masa ba yace.


"Ina tsananin son dokin nan Amfal saboda kyautar mahaifiyata ce a gare ni".


Murmushi Amfal yay kaji dadin ka niko babu abinda zan kalla matsayin Ammy ce ta bani".


"Ba kai yadda zata baka komai nata ba ne amma a yadda na fahimta Ammy na sonka kaine kake da matsala".


Cikin son abar maganar Amfal yace nima dole nayi hawan nan kodan saboda kai bros".


Kallonsa Abduljabbar yay danya fahimci baison suja maganar yadan girgiza dakai yana cewa" yayi Amfal abar maganar na gane basai kabi ta bayan gida ka fuske ba Allah ya shirye mu ni da kai".


"Ameen Amfal yace yana rufe baki dankar yaga yana dariya.


Zaune Safah take kana ganinta kasan tana cikin damuwa Zarisha dake kusa da ita tace.


Wai Safah me kike yi haka ne dan kawai anyi miki canjin gurin aiki shine zaki zauna kina caza kanki ga wuyar azumi"?.


Sauke ajiyar zuciya Safah tay ba haka bane Zarisha damuwa kada wannan matar taji labari taje har inda aka mayar dani ta cimin mutunci".

Kai Zarisha ta girgiza ko daya Safah kada ki ruda kanki kisa tunanin ki guri daya inda aka kaiki gune me aminci part din yayan sarki ne".


Zaro ido Safah tay badai samarin da kike fada ba sun dawo ne"?.



"A "eh sudai yau kwanan su biyu".


Cikin muryar tausayawa Safah tace na shiga uku na wanne gararin rayuwa nake fadawa"?.


"Kai dan Allah kawata mene abin ukun kuma kamar wanda zaki halaka".


"Dan uwan halaka ne zarisha part din da duk maza ne kawai taya zan samu nutsuwa"?.


"To shikenan kinga kwantar da hankalin ki zan rika raka ki kina yin naki aikin hakan yayi"?.


Dan shiru Safah tay tana kallon Zarisha daga baya kuma ta daga kai alamar ta amince.


Murmushi Zarisha tay amma Safah kina da abin dariya sai kace yar kauye kuma yaya zaki ranar da kikai aure fa"?.


Jiki a sanyaye Safah tace na yanke kauna da hakan wazai aure ni karki manta baiwa ce ni yanzu bani da wani yancin kaina aure nasan har abada kima daina wannan zancen".


Dariya Zarisha tay waye ya fada miki wallahi a cikin 'ya'yan bayi indai kin samu wanda kike so zaki iya yin auren ki".


"Daina wannan maganar Zarisha koda na samu bazan yiba nida aure mun raba hanya ya dade da ficewa daga kaina".


Cikin tsokana Zarisha tay gyaran murya tace uhm uhmm fa karki zura mu a kwalba rana tsaka muga kina soyewa da wani".


Har cikin zuciyarta da gaske Safah tace ba wannan maganar kuma zaki gani nina fada miki nida aure nayi gabas yayi yamma tunda ban samu muradin zuciya taba".


"Oh hubbynki waye shi"?.


"Ba ruwan ki bai shafe kiba" Safah ta fada tana dan hararar Zarisha".


"Dariya tay tace idan tay tsami ba muba har makota sai sunji".


Haka da wannan surutun muje ki ga wani wuri".


Humm abin yazo kodai gurin nasa zamu je"?.


"Eh can zamu je" Safah ta fada tana mikewa fita sukai daga dakin nasu Zarisha na dariyar tsokana.


YUSRAH MUSA ABUBAKAR


[23/04/10] +23490 552 736 14


#YUSRAHMS#
NO.71πŸ‘‰ 72
A burkice cikin tashin hankali Ammy ke zaga palon muryar ta har rawa take wajen fita tace.


"Yaushe hakan ta faru wacce asarar nake me nake kallo na shiga uku ni Adama kafin na kashe wata wutar sai wata ta kunno kai to waima makancewa nayi ne ban taba ganin cewa wannan matar tana da ciki ba kome sai haihuwa naji kwatsam kamar mafarki wallahi bazai yiwu ba bari naje gare ta".


Fita tay da saurinta tana shiga part din Fatima kallon bayin dake aikace aikace tay wanda tun kafin tayi magana suka sha jinin jikin su suna ficewa daya bayan daya.


Wata irin daskarewa guri daya Ammy tay kamar an sata a cikin firiza ganin bama da daya ta haifa ba biyu ne duk maza.


Wata hajijiya ce ta debe ta sai gata tay zaman dabas a kasa kanta na juyawa idonta kamar su fito waje dan firgici.


Dan murmushi Fatima tay tana kallonta tace sannu da zuwa uwar gidan me martaba ga kujera kika zauna a kasa".


Cikin dan sauran karfin da Ammy ke dashi tace" wallahi tun wuri ki nemawa yaran nan ubansu idan ba haka ba zasu girma shegu ba yayan mijina bane kuma bazai yiwu ki kakaba masa ba".


Sosai Fatima ke kallonta wato ita wannan kullum alkhairi baya taba kawo ta sai tsiya da rashin arziki tace.


"Haba uwar gidan me martaba yuwuwa kai wadannan yaya dai nan gani nan bari ba yadda zaki dasu zakaran da Allah ya nufa da cara sai yayi dan haka bana son wata magana tashi ki koma inda kika fito a gaida na gaba".


Mikewa Ammy tay tana nufar yaran tace bari na nuna miki iyakar ki na kashe su sai naga me zaki".

Daga mata hannu Fatima tay kada ki kuskura ki karasa kusa da yaran nan idan kuma ba haka ba na lahira saiya fiki jin dadi tunda na fuskanci ba kanki daya ba kina da sakarkarun aljanu to zanyi maganin ku daga ke harsu".


Cak Ammy ta tsaya tana cewa ke harkin isa kice zaki magani na".


Kai Fatima ta jinjina kwarai harma nafi yadda kike zato kuma idan kina ganin wasa ne wannan hannun naki ya taba min yara ki ga yadda ake wasan tsutsa a rana".


Azafafe Ammy tace kinsan wace ni kike fada min dukkan abinda yazo bakin ki".


"Fatima dake kallonta tace na sani mana zan fada miki koke wace kedin gurbatacciyar mahaifiya ce wacce ta kasa rike danta balle ta rike dan wani".


Wannan karon kasa daurewa Ammy tay tana yin kukan kura tay kan fatima tana cewa wato kin asirce min miji saida kika sa ya debe dukkan sirrina dashi ya fada miki".



"Zuwa tay da dukkan karfinta zata zubu akan fatima dake zaune taji an dage ta cadat anyi baya da ita.


Juyawa tay a firgice duk zaton ta me martaba ne ganin Abdul-jabbar yasa tay mugun hade ranta bacin rai sosai ya mamaye.


Jikinta na sewa kamar tasha tsumin mafarauta tace" babu ruwan ka dama kai da tamu dakai kayi kokarin kashe wutar dake gabanka ka daina hangen ta wani".


Zuba mata ido yay yadda take magana kanta tsaye babu ko kara.


Kau dakai Ammy tay ganin kallon nasa yay yawa ita kuma idonsa firgita ta suke yasa ta mike cikin harara tace" wallh ki jira dawowa ta gareki saikin yi nadamar zuwan ki duniya".


Tana kaiwa nan ta fice tana huci.


Juyawa Abduljabbar yay yana kallon Fatima da hankalinta ke kan yaranta yace" kiyi hakuri dan Allah karki biye mata babu abinda zata yi miki kada kisa damuwa a ranki akan maganar data fada yanzu".


Murmushi Fatima tay tana girgiza kai dan lamarin Ammy ko kadan bai dara ta dariya ma take bata dan bai sani bane tace.


"Kada kaji komai ba wata matsala aina riga na saba da wannan yanayin nata ba yau ta fara ba".


Shiru Abdul-jabbar yay yana kallon yaran cikin burgewa domin rabon da yaga jaririn yaro harya manta gasu jininsa kannin sa ubansu daya yana farin ciki da hakan.


Bai sake magana ba ya fita daga part din nata yana mamakin halin Ammy shin meke damunta ne data kasa aje tunanin ta wuri daya?.


Yana son sani kuma zai binciko ko me take aikatawa da abinda take yi a sirrance wanda babu wanda ya sani yana da tantama sosai akan Ammy".


"Yanzu dan Allah Zarisha na tambaye ki ke kanki ba kiji dadi ba da kika amincewa Safwan mutumin kirki wanda ba ruwan sa".


Kauda kai Zarisha tay cikin basarwa tace" ba wani jin dadi bayan kece kika matsa min dole zaki min za'kin baki".


Dariya Safah tay lallai matar nan ni zakiwa bagu bayan ga farin ciki nan kwance akan fuskarki".


Duka Zarisha ta kaiwa Safah tana cewa" wato Safah kinga gurin kwana na shiyasa kike min abinda kika ga dama zan rama wata rana".


Dan gocewa Safah tay tana fara ido tace" to da me kike tunani na gani mana babu sauran abun daya rage".


"Kuma na ji ki na cewa zaki rama wata rana taya kenan madam din Safwan"?.


Ta fada tana sake yin dariya da gudu ta tashi ganin Zarisha ta mike tana cewa" bari dai yau mudan hada dantse dake Safah gara mu fidda raini".


"Allah bazan yarda ki kama niba amaryar Safwan kina jida karfin amarci naje ki kassara ni".


Tare suka kasa da gudu suna dariya cikin jin dadi irin na 'kawaye".


Yau Zarisha bataje taya Safah aiki ba ita kadai take yi ga gajiya tay tilis sakamakon la'asar tayi nisa an kusa shan ruwa".


Zama tay tana kallon bakin dokin da gashin jikinsa ke sheki ga koshi daya tara har tumbi yake ajiyewa.


Zuba masa ido tay sosai dan tunda take aiki a gurin bata taba kare masa kallon kurulla ba sai yau gaskiya dokin ya burge ta".



Amfal na tsaye jikin window yana kallon waje lokaci guda yace.


"Kai kai kai cankadi zanzari ka gani kuwa bros"?.


Abduljabbar dake zaune ba tare daya dago ba yace" taya zan gani ina nan mene anan din daya firgita ka haka"?.


Amfal da shima bai dauke idonsa daga kan abinda yake kallo ba yace" aiko zo ka ganewa idonka abin mamaki".


Tasowa Abdul--jabbar yay yana cewa Amfal Allah yasa ba shashanci zaka nuna min ba".


Kai Amfal ya girgiza ba shashanci bane bros kalli wajen dokin ka".

Kallon gurin Abduljabbar yay.


Amfal yaci gaba dan Allah kaga wata zazzafar yarinya bros beauty haka indai akwai irin wadannan a masarautar nan babu inda za muje".


Tsaki Abduljabbar yay yana dan dukan kafadar Amfal yace dan uwana Allah ya shirye ka".


Dariya Amfal yay amin bros dan inaga nikam nayi tsintuwa a cikin bayi zan zaba na aura kome kace babban yaya ina neman shawarar ka".


Komawa cikin palon Abduljabbar yay yana zama yace a'a saidai ka nemi basir ko bayamma ka tsaya iya shawara ga ciwon ciki da kullewar mara".


Sosai Amfal ke dariyar sa yace kayi gaskiya bros me gyara maka gurin dan lelen dokin kace kodan haka bazaka goya min baya na shiga daga ciki ba".


Tabe baki Abduljabbar yay tare da rufe idonsa bai sake magana ba danya fahimci Amfal ba wuyar azumin yake jiba shiyasa yake wahalar dashi da magana".


Wucewa Amfal yay yana cewa shikenan bros ka huta bari naje nai wanka kafin a kira sallah amma wallahi saimun dora da zancen yarinyar nan".


Da kallo Abduljabbar ya bishi cikin sauke ajiyar zuciyar caza masa kai da yake yace Allah ka shirya min dan uwana Amfal ka zama headache ciwon kaina saidai nayita hakuri dakai".


Safah data shagala sosai wajen kallon dokin domin gashinsa baki kirin yake gashi an daura masa abin ado a kafa ji tayi ina ma tana da waya da saita yi masa salfie.


Ba zato taji ance yauwa karamar mara mutunci dama ke muke nema uwar tsugudidi irin kune masu zuwa lahira da 'kokon mayu kalleta da Allah".


Juyawa tay cikin mamakin waye me wannan maganar sai kawai taga su Basira wanda ba gurin dutin su ba meya kawo su?.


Cikin zare ido Basira tace" ke karamar yar tasha uban me kike wa Sadwan dazu muka ganku tare"?.


Matsowa Zakiyyah gaba tay har tana bangaje Basira tace" matsa baya Basira wannan fadan ba naki bane nawa ne domin ni ke son Safwan kada ki kuskura ki shiga gona ta"..


Dariya Safah tay tofa mahauka tan banza sakarkaru kusan da wacce zakuyi dan ni nafi karfin shashancin ku".


Zata bar gurin zakiyyah ta jawota da karfi cikin bala'i tace ke ina zaki banci uwark......


Bata iya karasawa ba sakamakon jin wani zazzafan mari a fuskarta wanda ya ratsa duk ilahirin jikinta ba arziki ta sakar mata kaya tana dafe kumatu".

Hatta Basira saida marin ya tsorata ta tace me kika yi haka zaki mare ta wallahi saikin yi nadam.....


Daga mata hannu Safah tay lokaci guda Basira tay tsit kamar an doke bakin tsanya da tabarya saboda tsoro batai zaton Safah zata iya ko mai ba".


Cikin murmushi Safah tace jira ni banza ban zo kanki ba ki taka sannu sannu domin ni tabo ce idan har tsautsayi yasa kika taka ni saina zame ki kin fadi".


Zakiyyah da tay sororo ta kalla tana cewa ke kuma jakar mata soyayya ta hada ni da Safwan akan haka me zaki idan harkin isa ke cikakkiyar yar iska ce ki dakatar dani saidai kinyi tsararo kinyi kadan baki da wannan zarrar wawiya sakarai kawai".


Juyawa tay jin an kira sallah ta barsu tsaye kamar an dasa su domin dukkan su sunsha jinin jikin su basu yi tunanin zata iya wanke su da magana haka ba da niyyar su hada mata ribitin duka suka zo karshe sune suka sha kunya.

#vote
#comment
#fallow


Mrs A A ce


#YUSRAHMS#
NO.73πŸ‘‰ 74
Tun dazu Zarisha ke dariya wanda safah ta rasa ta maye hade rai tay tana kallon ta tace.

"Zarisha ko kin samu matsala a kwakwalwar kine ke kadai sai dariya kike gaskiya zanbar miki wuri domin kin isheni".


Tafi Zarisha tay tana cewa kai dakyau 'kawar wato dama kina da fada amma da farko kikai musu shiru shiru suka raina ki".


Da alamar tambaya Safah tace su waye kike magana akai wanda suka raina ni"?.


Su Basira mana sai gashi dazu sun shiga jin tsoron ki gaskiya kin burge kuma naji dadin hakan da kika musu gaba baza su tare kiba".


Zaro ido safah tay ya akai kika sani bayan ban fada miki ba"?.


"Eh baki fada min ba nina gani da idona domin na tafi zanje gurin ki naji abinda suke cewa saina labe naga mezai faru kuma naga kinci uwarsu Safwan kuma kodan zakiyyah dake sonshi bazan bari ba dole na koyi sonshi muje zuwa yanzu aka fara wasan".


Cikin jin dadin safah tace yauwa ko kefa zarisha harkin sa naji dadi wallahi".

Zarisha tace ta faru ta kare dole naso safwan safah mun kulla kenan.


Kai Safah ta jinjina cikin farin ciki harta matsu gobe tayi taje ta samu safwan da wannan farin albishir din.


Aiki su basira keyi a part din Ammy amma sam zakiyyah kamar ba laka a jikinta ranta a bace kuma gashi idonta yadan kumbura kuma yayija alamar kuka tasha jiya da dare na fadan da sukai da safah".


Basira ta kalleta tana cewa wai meke damun kine Zakiyyah naga sam yau kinki walwala ko baki da lafiya"?.



Kai Zakiyyah ta girgiza muryarta cike da fushi tace" kalau nake amma wallahi Basira bazan yarda da wannan cin fuskar da yarinyar nan Safah ta min ba idan na rabu da ita ta shaki iska a cikin masarautar nan kice niba yar halak bace zata ga yadda ake daukar fansa😠".


"Taya kenan kike tunanin zaki dau fansa akan ta Zakiyyah fada na baki da baki ma kin barta ta mare ki baki rama ba balle daukar fansa".


Cikin huci Zakiyyah tace hum azumi ne ke bani wuya jiyan shiyasa dan baki san yadda na tsani yarinyar nan ba kamar na kaita lahira haka nake ji".


Dariya Basira tay duk tsanar ta da kikai Zakiyyah baki kaini ba kawai dannewa nake amma wannan karon zamu san abinda zamuyi mata na muniya wanda sai taji bata kaunar zaman duniya".


Cikin mamaki Zakiya tace to amma taya me zaki wanda zaki munana mata karki manta ba dakin kwanan mu daya ba".


Kai tsaye Basira tace sharri zamu kuga mata zamu aikata aikin rashin da'a a boye sai muce itace mun ganta da idanun mu".


Shiru Zakiyyah tay tana daga kanta alamar tunani zuwa wani lokaci tay murmushi tana kallon Basira tace.


"Dakyau wannan shirin yayi muje zuwa tsari na gaba lallai wannan karon zamu hada mata tarko mu kamata ta hanya mafi sauki".


Basira tace to kinga ni dai Allah yasa sharrin da zamuyi mata ya kaita ga gidan yari shikenan kowa ma ya huta da annoba".


"Ai wannan tafi annoba yadda kika san cuta me karya garkuwar dan adam haka take".


"Kuma koma dai menene wannan karon saita gane bata da wayo".


Fitowar Ammy yasa sukai tsit suna raba ido kamar wanda sukai wa sarki karya.


Zama tay tana kallonsu daya bayan daya domin taji dukkan abinda suka fada.

"lallai wadannan yara hatsabibai ne kuma zanyi amfani daku waje ganin burika na sun cika a masarautar nan".


Gaida ita sukai amma bata amsa ba sai tambaya data jefo musu.


"Wacce yarinya ce kuke shiryawa dukkan wadannan abubuwan da kuka lissafa zaku yi mata".


Jiki na rawa suka kalli juna yayin da Ammy tadan jingina bayanta da kujera tana rufe ido alamar amsar su take jira.


Wanda su kuma hakan ya basu damar kallonta dakyau saidai sun san bazata sake tambayar suba cikin fargaba".


Basira tace ranki ya dade Safah ce kuma laifi ta mana shine zamu rama".


Bude idonta Ammy tay wace Safah a ina take".


Kafin Basira tay magana Zakiyyah tay wuf tunda tasan Safah ba gwanar Ammy bace tace.


"Ranki ya dade wannan yarinyar da kika samu muka kira ta babangida ya mata bulala wacce take aiki a part din amaryar me martaba".


Gyara zama Ammy tay jin abar harin ta suke nufi itama zatay amfani da wannan damar tayi wani abu".


Kaita jinjina yanzu a ina take aiki ko tana can din"?.


Da sauri Basira tace a'a an mayar da ita part din su yarima tunda dadewa".


Wani kalar murmushi Ammy tay tana cewa zan baku aiki ku tabbata babu wanda ya ganku kuma koda asirin ku ya tonu karku sake kuce nice".


Jikin sune ya dau rawa jin abinda tace amma saboda ba yadda suka iya yasa suka amince".


Cikin halin ko in kula tace ku tashi ku tafi zan neme ku nan da jibi kada wani yasan da wannan labarin".


"To ranki ya dade suka ce suna fita cikin sauke ajiyar zuciya Zakiyyah tace.


Kiji muguwar mata wai idan aka kama mu kada mu sake muce itace kenan mu bari aci uban mu wallahi bazai yiwu ba".


Tabe baki Basira tay ai cikin hikima zamuyi komai yadda baza a ganmu ba idan kuma mukai nasara to lallai zata sake janmu a jikinta kinga kama Safwan ya dawo gare ki".


Kuma fa haka ne kin iya kawo shawara bari jibin tayi

Please Login or Register in order to submit comment