Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

humm kada ki damu wannan somin tabi kika gani indai har zan baki umarni ki karya min dokata ina matsayin shugabar ki to kuwa kina tare da wahala kuma zaki kasance cikin ukuba ta babu wanda ya isa jayayya dani ko waye shi dan haka ina mai gargadin ki da ki kiyaye gaba".


Shin jiya raini ne yasa da na baki umarnin cewa ki jira ni ina zuwa kikai tafiyar ki saboda bankai matsayin ki bini ba kuma uban waye ya fidda Abdul-jabbar daga nan yakai shi sashin hajiya ko duk zakice min bake bace na sani dare ne bazai taba iya komawa da kansa ba fada min me yasa kika aikata haka!? A tsawace ta karasa maganar wanda Hanne saida tayi zaman dabas a kasa saboda firgici.



Muryar ta na rawa ta soma magana"dan girma Allah ranki ya dade kiyi hakuri nayi zaton da naga baki fito ba ko kinyi bacci ne shiyasa na tafi da niyyar yau da safe na dawo ba ina nufin karya umarnin kiba ki gafarce ni uwar gidan mai martaba Abdul-jabbar kuma ba nice na kaishi gurin hajiya ba harna fice yana palon nan bansan komai akan haka ba ranki ya dade gaskiya nake fada miki".


Huci Ammy ta fitar tana kallon hanne tace"naji zonan inason zamuyi magana dake ta sirri mene sunan ki"?da sauri hanne ta matso inda Ammin tace mata tana cewa "suna na HANNE" .
Gyara zama tayi tana yin kasa da murya tace"yauwa hanne wata magana zan fada miki kinga duk fadin masarautar nan a yanzu babu wanda yasan sirrina da kudiri na da kuma shirina akan abinda nake kullawa akan Abdul-jabbar saike dan haka zan 'yanta ki na kuma baki babban mukami zaki zama amintacciya ta zan hada hannu dake domin na cimma buri na akan shafe Abdul-jabbar kuma bana bukatar kowa yasan haka, kin jini kin haddace abinda na fada miki"?.


Hanne da har lokacin jikinta bai daina rawa ba tace"eh ranki ya dade zan iya kowanne irin aiki idan kika sani kuma baza a samu kuskure ba bazan taba saba lamba ba".



Kai ammi ta rausaya hakan yayi tashi kije saina neme ki kuma koda wasa kada ki kuskura ki fadawa wani wata magana wannan tsakanin mune daga ni saike bana bukatar kowa".

Godiya hanne tay tana mikewa ta fita tana komawa bangaren su na bayi ruwa mai zafi ta samu ta dumama jikinta tana tunanin maganar da sukai da ammi lallai tana tsoron ranar da asiri zai tonu ace harda ita a masu aikata muyagun laifuna amma dole tabi ammi ba yadda ta iya kodan tsira da rayuwar ta.


Lokacin da hanne ta dawo daga tunanin ta kwafa tay cikin takaici tana cewa"wallh Adama duk abinda kikai min bashi kika ci akwai ranar biya tana nan zata zo bakisan nima ba kanwar lasa bace kowa yaci tuwo dani miya yasha miyar ma ban rage ba kwanon ya side muje zuwa ga fili kuma gamai doki saura sukuwa".





Mrs Al'ameen Ahmad ceπŸ‘

ONE LOVE WE WILL MEET TOMORROW😜 YAN UWA.


TYPINGπŸ“²


πŸ‡
πŸ‡ SAFREEYYAHπŸ‡
πŸ‡


πŸ’«πŸ’« ANNURI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«


STORY & WRITTEN
BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR
»«Mrs Al'ameen Ahmad ce»«



Dedicated to
My mum i love u with all my life may Allah accept your du'ah and help you u anywhere u are mamana πŸ‘.



Abubuwan nasiha guda biyar masu tasiri ga rayuwar mai hankali.
Duniyar da za'a barta😧
πŸ‘‰ meya kawo hadama?
Rayuwar da zata kare😟
πŸ‘‰ina wani farin ciki?
Ana sauraron mutuwa😭
πŸ‘‰ina wata walwala?
Jikin da zai zama gawa😒
πŸ‘‰Me zaisa alfahar?
Karshen da makomar sa kabari😭
πŸ‘‰me ya jawo girman kai?
Duk wanda ya manta da wannan😠
πŸ‘‰to ina yabar hankalin sa?πŸ€”.




πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•‹ πŸ•‹ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•‹
πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•Œ πŸ•ŒπŸ•‹ πŸ•Œ
==================================
πŸ‘ May Allah open the door of success and happiness for all of you(Muslims) may Allah accept your du'as and protect you and your families from all calamities amin, start you day beautifully with fajr prayer and quran recitation, o Allah s w t make us among those who never miss salah Ameen ya AllahπŸ™.
*JUMA'AT MUBARAK*
πŸπŸ‡πŸ“πŸπŸ’πŸπŸ‰πŸŽπŸŠ.




πŸ€— Ina kuke 'knawayen asali ku fito ku taka rawa, 🎢🎹🎻🎷🎀 ga page dinku ya bayyana ku kadai naba dukkan sa as you wish kuyi yadda kuke so dashi mallakin kune har next page na baku just for remember"πŸŒΉπŸ˜œπŸ’.


Hauwa'u Mu'awiyya Umar Kano (maman Al'ameenπŸ’•)
Hafsat Haris (maman Aliyu)
Fatima Idris (maman Usman)
Suwaiba Yusuf (maman Auwal)
Salmah Hayat (maman Afnan)
Latifah Nura (maman boy)
Asma'u Abdullah (maman mhmmd)
Saudat Yusuf Dutse
Khadijah A Yusuf
Zainab Sunusi Dutse
Khadijah Adams Dutse.

😘Mrs A Ahmad ce
=""==""==""==""==""=



#YUSRAHMS#
NO.25πŸ‘‰ 26
Da dare Safah da baba maryam na zaune a daki suna hira sukaji sallamar mk cikin mamaki baba tace"musaddiq kaine shigo mana ince dai lafiya ko hajiya ce ke nema na".
Shigowa mk yay wanda gaba daya hankalin nakan Safah wacce ke kwance kan katifa da wata rigar bacci a jikinta mai kyau kanta ba kwali kuma a tsefe yake tayi donut dashi baki sitik mai santsi sai sheki yake wani irin abu yaji yana tsirga masa wanda ba shakka yau da ace babu baba maryam a dakin nan bayajin akwai wani abu dazai sa ya dagawa Safah kafa dole saiya kasance da ita.


Baba maryam ce data lura dashi tace"musaddiq nace dai lafiya ko"?da sauri ya dauke kansa daga kallonta ya dawo kan baba maryam duk da hankalinsa da nutsuwar shi na wajen Safan dama saboda ita yazo bazai iya bacci ba har idan bai sakata a idonsa ba kallon baba maryam yay yana cewa"amm babu komai dama nazo na sake duba tane yaya kafan nata"?.


Cikin fara'a baba maryam tace"ayya musaddiq da sauki gaskiya ka kyauta wallh yaro mai hankali nagode sosai da kulawa"kai ya daga tare da. kallon Safah cikin daga mata gira yace"ya jikin naki"? Dakyar Safah tace"da sauki tana sakar masa harara, murmushi yayi yana mikewa yace"ga tsaraba nan a bawa mai jinya saida safe"godiya baba maryam ta masa tana cewa"kuma harda abin arziki mun Allah ya kara budi" amin yace yana fita.


Duba kayan baba maryam ta leda biyu daya babba daya karama babbar ta fara budawa dogayen riguna ne guda biyu masu tsada daidai tsayin Safah da takalmi abinda ya bawa safah haushi harda breziyaπŸ˜‚ a ranta tace"jifa dan iska me zanyi da kayan ka".
Dayar ledar kayan baba maryama ta bude sai gashi ta fito da katuwar kaza mai kamshi ga kuma robar ice-cream guda biyu baba maryam tace"kwarai wallh Safah kiga dan albarka ya kawo miki abin arziki gobe kiwa hajiya godiya kuma shima ki masa gaskiya mutanen gidan nan nada karamci".


"Tashi kici" hade rai Safah tay "ni bazan ci kayan sa ba kawai daga ya kawo abu saina kama ci bansan meye a ciki ba duniya daba tabbas" kallo.n ta baba maryam "haba Safah amma kinsan bazaisa maganin mutuwa a ciki ba ko"?cikin shagwaba Safah tace"Allah baba nidai........katse ta baba maryam tay "Allah keme?karki rantse bansan shirmen banza tashi kici inda yana nan ai bazai ji dadi ba sai yaga kamar kina zargin sane".



Tura baki Safah tay"to dama mene inba abin zargin ba" salati baba maryam tay"ke naci gidan ku rufe min baki bansan soko" dariya Safah tay "kin cinye gidan mu kenan Baffa na nacan yana kwana a waje Allah sarki"bude robar ice-cream din baba maryam tay tana sa karamin cokali ciki ta mika mata karba Safah tayi badon taso ba ta soma tana cewa"saidai yaci darajar ki nasha kayan sa saboda ke" baba maryam dake kallonta ta girgiza "kai Allah ya shirya minke Safah" murmushi tay ba tare da tayi magana ba naci gaba da shan ice-cream din.




Washe gari Safah bata shiga gurin hajiya ba saida yamma ta tarar tayi bakuwar wata budurwa yar gidan kanin ta tazo mata ziyara daga mubi saidai Safah ta lura yar jin kaice sai wani shakar iska take a gadarance tana tauna chewingum ta soke daurin kwali a gaban goshi kana ganin ta ba sauki.



Shigowar mk kenan ta mike cikin murnar ganin sa zata rungume shi ya dakatar da ita da hannunsa yana kallon Safah yace"big girl ya jikin naki fatan kafan ya warware"?shiru safah tay tamkar bada ita yake ba yayin da Abidah tay sak tana binta da wani irin kallon mamaki tace"naji kace mata big girl ba house girl dinku bace meya hada ta da wannan sunan kuma yaya mk"?.

Zama mk yay cikin halin ko'in kula yana cewa"gashi nan kinyi tambaya kuma kin baiwa kanki amsa house girl ce sai akaiya"? kalle ta dakyau itadin babbar yarinya ce mai aji ma kuwa ta wuce rainin kowacce kucaka" yana fadin haka ya mike yabar palon cikin takaici Abidah ta bishi da kallo harya bacewa ganin ta kafin ta dawo da dubanta kan Safara'u kamar zatai magana sai kuma taja tsaki itama tabar palon.

Dariya Safara'u tay tana cewa"lallai yarinya kina ruwa kasan bado wallh bamai cetoki indai mk ne zaki bayani domin saidai naba wani labarin sa".

YΒ»*Β« Β»*Β« Β»*Β« Β»*Β«

Watan su Abdul-jabbar guda a garin malam na Allah kuma ya kama yau zasu tafi bayan sun gama shiri malam ya zaunar dasu nasiha mai ratsa jiki yayi musu addu'a mai kyau da fatan alkhairi bayan sun shafa fatiha sukaiwa Hadiza sallama suna fita a gidan kasa hakuri tayi da sauri ta dauko mayafin ta har jikin motocin da suka zo daukar su itama tayi musu rakiya da kukan ta shi kanshi malam na Allah daurewa yake saboda ita mace ce mai rauni shiyasa nata ya fito fili amma shima yana kukan zuci.



Murmushin karfin hali yay yana kallon ta yace"in banda abinki Hadiza ai rabuwa ba mutuwa bace hakan ba yana nufin baza mu sake ganinsa ba a'a inda rai ana tare zai sake dawowa gare mu kiyi hakuri kinji"kai Hadiza ta daga tana goge hawayen fuskarta ta kalli Abdul-jabbar tana cewa"Allah ya kiyaye hanya ya tsake ku daga sharrin dukkan abin 'ki a duk inda kuka tsinci kanku".


Murmushi Abdul-jabbar yay yana kallonta yace"amin mun gode da addu'ar ku Allah ya saka da alkhairi sai wata rana"juyawa yayi gurin na Allah yace"mun tafi Allah ya kaddara saduwar mu" amin na Allah yace yayin da Abdul-jabbar ya juya yana shiga mota suna kallonsu suka tafi ba halin dakatar dasu tun suna ganin motocin har suka bacewa ganinsu sannan suka juya zuwa gida jiki a sanyaye.



Fitowar safah daga kitchen kenan taji ance" hey kitchner dan kawo min abin sha mai sanyi sosai ki taho da cup hurry up and back quick" da mamaki Safah ke kallon Abidah a ranta tace"humm yau gata biyun mk lallai na tsane ku" Abidah ganin ta tsaya tana kallonta yasa cikin wulakanci tace"ke house girl baki ji abinda nace ba kika tsayar wannan mayun idon naki a kaina ?".


Cikin bacin rai Safah ta juya zuwa kitchen ta dauko mata kamar yadda ta ajiye mata zata juya ta dakatar da ita da fadin"oh nice zan zuba da kaina waike me kika dau kanki kada ki manta matsayin ki yar aiki sunan ki tunda kuwa kika amshi wannan sunan ni a gurina kina tare da kaskanci aidama shi kwadayi mabudin wahala ne tunda kika zabi irin wannan rayuwar kuma mk yaki bani muhimmanci saboda ke to mu zuba ni da ke aga wanda zaiyi nasara wallahi kafin nabar gidan nan saina saita miki hanya da kafafun ki zaki gudu daga gidan nan".



Ko dagowa safah batai ba balle Abidah tace taji zafin abinda ta fada mata ko tadau maganar ta da wani muhimmanci kawai hauka ta manna mata tana zubawa ta mike zata bar wurin Abidah tace"kuturun uban can harni zanyi magana ki mayar ni mahaukaciya yau sai naga uban daya goya miki baya a gidan nan".


Kallonta safah tay babu wani alamar bacin rai a tare da ita tace"gashi kin baiwa kanki amsa jakar aji ki sani cewa ni nafi karfin cacar baki da irin ki baki isa kice zaki juya niba kedin banza kinyi tsararo baki kaiba ina alfaharin kasancewa ta diya mace ba asararriya sokuwa irinki ba"tana fadin haka ta juya cikin murmushi zata bar gurin.

Finciko ta Abidah tay cike da masifa tace ni kike fadawa magana haka yaushe kika samu wannan mukamin"? Har lokacin Safah murmushin ta na nan akan fuskarta tana duban Abidah data gama burkicewa tace"karya na fada wallh har kin bani dariya ji yadda kika rike ni kamar wacce nai miki sata sake ni dalla malama na tafi uzuri na"

"Ni kike cewa dalla malama dan uwar ki yau kuwa saina kusan kashe ki a gidan nan saikin fada min wanda yake zuga ki a gidan nan"hannu ta daga zata mari Safah taji an rike hannun da sauri ta juya ganin mk tsaye yasa tace"ka sake min hannu wallh yau saina balla yarinyar nan saina nuna mata isa ta da matsayi na zata ga kala ta harni zata tsaya tana fada ina fada matsayin ta na house girl".


Murmushi mk yayi yana kallon Abidah yace"abinda tay shine daidai hukuncin daya dace dake kenan kinga gaba koba anan ba idan kika hadu da yar aikin da kika raina ma wayo sai kiji shakkar ta maganar saikin ga wanda ya goya mata baya a gidan nan gani nine sai akai ya"?.

Kallonsa abidah keyi yaya mk da gaske kaine a gabana kake fada min son ranka akan wata yar aiki bare wacce baku hada jini ba ko mafarki nake dan Allah ka farkar dani"?.


Kai mk ya girgiza yana kallonta yace" no you are not ba mafarki kike ba zahiri ne kalleni dakyau dan ki samu tabbacin haka"Abidah bata iya kallon sa ba sai kuka data fashe dashi da gudu tabar palon tana shiga part din su salmah.

Dawo da kallon shi kan Safah yay yana cewa"big girl ashe kin kware a iya magana har haka amma ni bakya kula ni me yasa"?shiru Safah ta masa ganin ya matso inda take yasa da sauri ta matsa baya kara binta yayi cikin hanzari ta fice daga palon, zama yay yana sauke ajiyar zuciya tare da kallon kofar data bi a ransa yace"humm yarinya ki gama zille zillen ki rana ta dazan cimma buri na ta kusa zuwa kwanaki sun kusa cika" murmushi yay yana hango irin farin cikin da zai tsinci kansa a wannan rana.




Mrs Al'ameen Ahmad Aliyu ce.


Tnx for loving me
Be with me at always my lovers
We will meet next page.

TNX.


TYPINGπŸ“²



πŸ‡ SAFREEYAHπŸ‡


πŸ’«ANNURI WRITER'S ASSOCIATIONπŸ’«πŸŒŒ


πŸ’•Yusrah m AbbakarπŸ’•


Ku kara hakuri dai reader's naga kowa ya damu kan rashin haduwar Safah da Abdul-jabbar pleaseπŸ™‡ ku dan kara hakuri lokaci nanan zuwa inda jirgin sama ✈ yaje to kunkuru 🐒 ma za'a ce masa barka da zuwa😜 lokacin haduwar tasu ne bai karaso ba amma ya kusa am so sorry my fans lovers.




#YUSRAHMS#
NO.27πŸ‘‰ 28
Ammy na zaune kamar a mafarki taga Amfal ya shigo gurin ta a zabure ta mike tsaye tana fadada murmushin ta ganin ba tare da Abdul-jabbar suke ba sai tayi tunanin ko Hanne taje gurin wani malamin wanda ya fara aiki da kuwa tayi farin ciki.


Karasowa yay har inda take yana zama yace"barka da hutawa Ammy fatan kin wuni lafiya"? Baki ammi ta washe cikin nuna tsantsan jin dadi lallai wannan malamin ya iya aiki za'aje dashi .
Kallon sa tay da farin cikin ta wanda yaki boyuwa tace"yauwa dan albarka Amfal ko kaifa yanzu baka ji irin dadin da naji ba da kazo gaishe ni amma da ko kallon arziki ban samu a gurin ka haba Amfal me yasa nice fa na haife ka baka da uwar data wuce ni duk duniya amma meyasa saika shafe kwana uku kana gidan nan ina nan baka leko ni kaga lafiya ta kullum kana gurin Abban ka ko gurin hajiya ni kuma kona mutu ko nayi rai babu ruwan ka dani".



Saukowa daga kujerar da Amfal yake yayi yana durkusawa a gabanta yace"kiyi hakuri ammina bazan sake ba daga yanzu kullum zaki rika gani na nasan cewa banda uwa saike kuma ina neman afuwan ki"ya karasa maganar yana rike hannunta,.


Wai Ammi ji take kamar anyi mata bushara da aljannah anya da gaske ne Amfal ne yau suke zance haka cikin walwala lallai aikin malam ya fara ci dole ta sake zage dantse tunda hankalin sa ya fara juyowa kanta bari ya fita ta kira hanne ta mata albishir sa'an nan ta bata kyauta mai tsoka kara kallonsa tay zatai magana taji yace.

Ammy kisa a yanka min fruits mana saboda an kusa kiran sallah domin shan ruwa"jiki na mazari Ammy tace"to Amfal bari na gyara maka da kaina ban yarda baiwa ta taba abinda ka bukata a gurina ba nice zan hada maka mai tsafta".



Mikewa tayi tana karasawa inda tulin kayan marmarin suke ta soma gyara masa tana yankawa a karamin bowl Amfal na kallonta "yauwa ammi kuma ki hada min da lemo mara gas amma mai sanyi yau dukkan abin shan ruwan na part dinki ne nasan zaifi dadi".


Kai ammy ta jinjina dan ta tabbatar da gaske aikin ya fara ci a ranta tace bari na gwada mu gani indai Amfal ya fara janye jikin sa daga gurin Abdul-jabbar idan ta masa maganar sa bari taga a yadda zai amsa, cikin fara'a tace" amma dai Amfal kai kadai zan hadawa banda Abdul-jabbar saboda yayi kadan na bata lokaci na akan sa".

'Yar dariya Amfal yay yana kallon yadda ta cika bowl din da kayan marmarin wanda ya sani idan itace zata sha tana daga kishingide za'a rika yankawa ana bata a baki amma ji yadda ta gyara a dan kankanin lokaci ta gama had............
Katse masa tunani tay da cewa" ina magana kayi dariya kawai baka ban amsa ba"?.


Mikewa yay yana zuwa inda take yace" Ammy bafa nine zansha ruwan ba bros dina ne yayi azumin litinin shi zan kaiwa bari na tafi kinga an kusa kiran sallah kuma baisan nazo nan ba kar yayi ta nema na ya rasa ni bazai ji dadi ba zai shiga damuwa ni kuma bana son hakan".

Wata irin ashar Ammy ta sakar masa jin abinda yake cewa cikin kunar rai da bakin ciki ta mike idon ya yayi ja ranta a mugun bace muryar ta a tsawace tace" Amfal yaushe na zama mahaukaciyar ka harni zakaiwa wasa da hankali kasa na bata lokaci na nayi maka wannan wahalar sannan kace bakai zaka sha ba wani banza can wofi zaka kaiwa amma yau badon kai dana bane kuma ina sonka wallh da saika gwammaci mutuwa akan ukubar dazan sa a dandana maka".


Daukar fruit din Amfal yayi yana kallonta yace"kiyi hakuri ammi hakan bazai sake faruwa ba yanzun ma kuskure ne kuma zan kiyaye gaba".
Juyawa yayi zai tafi Ammi tace"Amfal kodai kana shan wani abu"?murmushi yayi ba tare daya juyo ba yace" babu abinda nake sha Ammi sai coffee ki huta lafiya"tun kafin tayi magana ya fice wani irin yanke jiki tay ta fadi a gurinπŸ™Š.



Amfal na shiga part din hajiya ya ganta zaune akan kujera gefen ta Abdul-jabbar ne shima yadan jingina kadan da kujerar daman yasan yana nan saidai da alama ba zance suke ba.

Hajiya na ganin sa tace "aifa shikenan tunda kazo yanzu saika addabi kowa da surutun ka murmushi Amfal yay yana zama kusa da Abdul-jabbar yace" hajiya tawa nikwa na Allah naga Annabi kiga doron baya na".
Kallon sa hajiya tay" dan ubanka doron bayan naka ka boye karna gani bana bukata".


Dariya yayi yana ajewa Abdul-jabbar fruits din daya shigo dashi yana cewa"barka da shan ruwa bros Allah yasa ladan nida kai zamu samu".
Hajiya dake kallon dukkan su biyun cikin jin dadin yadda suke tafiyar da rayuwar su tace" me kuwa zai hana ku raba ladan saboda ka kawo masa yayan itatuwa sannu gwani mai ido a tsakar ka".

Gyara zama yay yadda zai fuskance ta da kyau yace" tofa yau nake ganin sa ido anan hajiya kodai kina kishi ne nasan dai kushewar badi sai badi dan bake na kawowa ba dan uwana na sani shine zan baiwa komai nawa ba kishiyar saura ba kuma nasan idan nazo gurin ki kina jin dadi taimakon kifa nake na debe miki kewa kuma da kika ce ina damun mutane saidai kisa munjaye kice muna damun mutane ni da ke kome kika ce"?.


Oh ni 'yar gidan Sama'ila yau na gamu da gamo na anya Amfala kai kadai ne kuwa baka da mutan boye"?.
"Ji hajiya da wani zance da duk zaman da muke dake dama bakisan ina da aljanu ba alhali kullum tare kuke kwana a gurin ki suna gadin ki sai yau kika sani tab kice duk wannan zantukan da suke miki cikin dare bakya ji lallai kuwa anayi babu ke kodan laifin bros ne dabai fada miki ba tun wuri amma yunzu saiki shiri tunda kin sani yau kar kiyi bacci sunce wasan kura zasu zo suyi miki".


Hajiya da tunda ya fara magana bakin ta yake bude har yakai aya a firgice tace" na shiga uku ni hauwa'u da gaske kake"?.

Kai Amfal ya daga "da gaske nake hajiya please kinga yau kece da kanki zaki tarbe su saiki shirya musu kayan cinye cinye da shaye shaye harda abincin india suka ce suna so nidai babu ruwa na dan na fita na fada miki idan kikai musu kuskure suka shanye miki hannu da kafa shikenan kina gani ba yadda zaki kin zama gurguwa komai saidai a maki kina zaune gaskiya hajiya ina tausaya miki dan kawai sunga kin zama tsohuwa shine suke so su shanye miki jini a kaiki makabarta kita tsugune a cikin kabari sai ranar da kwanan ki ya kare sannan ki bingire kasa ki fadi".


Hannu hajiya ta dora a kai tana ihu"wayyo Allah shikenan ta faru ta kare la'ilaha illallahu yau zanyi mugun gani da idona a gidan nan shikenan ni 'yar sama'ila da mairo naga ta kaina" ganin yadda duk ta susuce yasa Abdul-jabbar rike mata hannu yace" hajiya Amfal bada gaske yake ba

Please Login or Register in order to submit comment