Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaro yazo yace tazo shine data fita bata dawo ba.


Manyan fitulun kama barayi suka dauka domin nemo ta suka fara zaga garin amma shiru babu koda wani abu dazai nuna alamarta har wajen gari suka fita suka kwalla mata kira saidai labarin daya ne babu ita".



Batun Safah kam iya bala'in nisa sun bawa kauyen domin sun fita daga yankin adamawa gabadaya basu sani ba ita tana neman tsira da rayuwarta shi kuma yana neman cika burinsa na kashe ta.


Wata iriyar tsawa sukaji an buga musu "kai ku tsaya anan kada kowa ya motsa" cak suka tsaya kowa nafidda numfashi a matukar gajiye Safah ta fadi a gurin tana kuka wannan wacce irin kaddara ce take samunta a rayuwa wai yaushe ne zata huta yaushe ne zataji dadi yaushe ne zatay rayuwa irin wacce kowa yakeyi bata tunanin zata huta a duniya".




Basu farga ba suka ga mutane na bullowa tako'ina masu mummunar shiga sun rufe fuskokinsu babban dake tsaye yana juya bindiga da muryarsa mara dadi yace"ku kamo min su yau madai bamu fito a banza ba".


Jin abinda wannan basamuden yace yasa kukan Safah ya karu yayin da suka damki mk wanda ganin idan ya sake zai asarar rayuwarsa burinsa bai cika ba yasa cikin zafin nama ya sokawa wanda ya rikeshi ta gaba wuka yana hankada shi baya tare da zare bindigar aljirunsa ya harbi dayan a kafa a fusace ogan ya saice shi da bindiga amma mk ya goce ogan ya samu yaronsa a gefen ciki ganin duk sun fadi yasa mk ya juya tare da zubawa aguje sauran suka bishi a baya don kamoshi.



Mikewa Safah tay numfashinta na fita dakyar saboda wahala gashi da alama taji ciwo a kafarta sakamakon jan kafar da take ta soma tafiya shan gabanta mutum biyu sukai suna nuna ta da bindiga daya daga cikinsu yace" ina zakije? bayan abokin tafiyarki ya kashe mana mutane akan ki zamu dau fansa".



'Dana kunamar bindigar sukai kowa ya saice ta suna shirin saki ogan ya dakatar dasu yana cewa" wannan zamu samu kudi da ita waccen mutumin nake so su kamo muyi gunduwa-gunduwa dashi ita kuma ku wuce da ita gidan tsaron mu kila gobe musa kandas ta saida mana su tunda akwai ladies biyu a hannun mu" dariya suka fashe da ita suna saka Safah gaba suka tafi wani gida cikin dajin suka shiga da ita shiru kamar ba kowa daki suka bude suna jefa ta ciki suka kulle babu abinda ya dame su.


Babu komai a dakin sai datti da kwarika suna ta yawo guri daya Safah ta takure hawaye sunki tsaya mata tayaya ma zata yafewa mk a rayuwa shine silar bakin cikin ta duk wata wahala da zata shiga sanadin sa ne kuka ta fashe da shi tana durkusawa a gurin tuna baffanta cewa gobe ne daurin aurenta wanne irin hali zai shiga idan aka wayi gari ya rasata yanzu wadannan mutane ina zasu kaita wacce kalar rayuwar zata tsinci kanta a gaba.



Mk kam duk gudun barayin nan da harbin da suke sakar masa bai tsaya ba saida ya koma har kauyen su Safah gurin motar sa ganin yadda ake haska fitilu tako'ina zuciyarsa ta fada masa cewa Safah suke nema dariya yay baiko damu da ciwon jikinsa ba yaja motarsa da mugun gudu yabar kauyen yana cewa" ko yanzu burina ya cika Safah bazata taba dawowa gare ku ba wadannan garadan nasan fayde za suyi mata karshen wasan su kasheta shikenan an shafe labarin ta" kara shekewa yay da dariya yana dukan sitiyari saboda wani farin ciki da yakeji ya mamaye shi.



😘MRS AL'AMEEN AHMAD CE.


πŸ‡ SAFREEYYAHπŸ‡


πŸ•ŒπŸ•‹πŸ•Œ
It's friday don't forget to recite suratul al-khaf Happy juma'at mubarak.



πŸ“šπŸ“ YuSrAh MuSa AbUbAkAr GiMbA😝


Ayi hakuri idan an samu typing errorπŸ“²


Wannan page din naku ne manyan iyaye kuma masoya ina muku barka da juma'a.
Sha'awa shu'aibu
Suwaiba shu'aibu
Hauwa'u shu'aibu
Sawaida shu'aibu
Huwailah shu'aibu
Rahma shu'aibu
Z/Ya'u shu'aibu
Isah shu'aibu.



#YUSRAHMS#
NO.49 πŸ‘‰ 50
Allah sarki su murtala babu inda basu duba ba har jikin asuba amma ko wata yar sheda basu samu ba dole suka hakura zuwa wayewar gari idan akai sallah su fita har wajajen kauyukan da suke makwabtaka dasu suyi cikiyar ta.



Da gari ya waye Safah na jiran a zo a budeta amma haka ta wuni sai bayan sallar azahar sannan wata mace tazo ta budeta tana cin cingum tace" barka da zuwa yan mata gaki da kyau lallai zaki farashi fito ki wanka nan da yan mintuna zaku barnan din".


Saboda tsabar galabaita Safah batasan me take cewa ba burinta shine ta samu abinci da ruwa fitowa daita kandas tay tana dauko wata shinkafa a kwano ta mika mata sakamakon yunwar da ke damun ta bawani tsayawa ta soma ci sai data gama sannan ta kawo mata ruwa tasha.



Shiru Safah tay tana sauke ajiyar zuciya kandas dake kallonta tace" yan mata tashi zaki kiyi wanka ba sake kwana zaki anan gidan ba".


Idon Safah fal da hawayen takaici tuna yaune daurin aurenta wanne hali baffanta zai shiga da murtala da kuma sauran jama'a tasani jiya bazasu iya bacci ba.



Bude baki tay zatay magana cikin tsawa kandas tace" ke uban me zakice kike bude baki kamar wacce take gargarar mutuwa nayi miki uziri saboda ke bakuwa ce bakisan dokar gidan nan ba yanzu ke baki da wani yanci ki rika daukar kanki baiwa sai yadda akai dake wuce ga bandaki nan kiyi wanka kuma kada ki kuskura ki wuce mintina biyu tak idan kuma kika haura zaki ga abinda zai faru".



Wucewa Safah tay tana shiga amma bandakin sam ba wata tsafta dakyar tana dauke numfashi tayo alwala ta fito dan bazata iya wanka ba.


Wasu fatararrun kaya kandas ta bata cewa ta cire less din jikinta tasa su cikin damuwa da bakin ciki tanaji tana gani dole ta tasa ka matattun kaya tabar kyakkyawa wanda jiya kadai ta fara saka su.


Sai bayan sallar isha kandas tace su fito su uku duk yan mata a wata kwarakon mota ta debe su kowacce an daure mata ido da hannu don kar suga inda za'a kaisu.


Sundai ji tsayawar motar kuma anfito dasu ana tafiya dasu mai nisa daga nan suka tsaya kandas ta daga waya tana cewa" eh mun karaso".



Suna nan tsaye ta wata irin kofa wasu mutum biyu suka fito suna wa kandas nuni da cewa suje jansu aka farayi suka shiga wannan kofar sannan suka mayar suka rufe da flowers kamar yadda take da suka cigaba da tafiya har suka je wata kofa ta baya.



Godiya kandas ta musu tana cewa" idan na fito zan baku sallamar ku" tana fadin haka ta bude kofar tana shiga zaune take ta hakimce akan kujera tana musu kallon sama da kasa.


Zubewa kandas tay tana kwasar gaisuwa tace" ranki ya dade ga guda uku na kawo miki marasa ganda masu aiki tukuru ba ganda".


Cikin isa tace" naji amma dukda haka baza suyi farahi ba domin da dayanzu ba daya bane hankalina ya kakkaso bana cikin nutsuwa ta".



Kwance musu daurin hannu da idon kandas tay yayin da matar ta bata wani katon akwati faldakudi ta bata karba kandas tay tana godiya ta fita matar dake kallon su a wulakance tace" ga wani daki can kuje ku huta koma nace kuje kuyi baccin jin dadi na karshe a duniya"inda ta nuna musu suka nufa kowa hankalinta a dagule basu tsinke ba saida suka ga wani dan takurarran daki wanda baifi yaci karamar tabarma guda daya ba haka suka kwanta a matse ga zafi da alama esin dakin aka cire domin wahalallu ake sawa kawai.



Shima,mk sakamakon raunin daya ke jikinsa yasa bai shiga adamawa da wuri ba saida gari ya waye kai tsaye asibiti yakai kansa domin a duba lafiyarsa ya samu raunika sosai don haka gado likitocin suka so bashi amma yaki sam yace kawai shi su wanke masa ciwukan sa ya tafi gida dole suka bishi yadda yace.


Yana shiga gida Abidah dake zaune a dinning ta mike da sauri ta karaso cikin firgici ganin yadda mk din ya koma tace" ya musaddiq na shiga uku me ya same ka kaga yadda ka koma kamannin ka duk sun canza wai ina ka shiga ne mum sai kira na take a waya ta gaji tazo nan da kanta jiya wuni tay ko zaka dawo amma shiru sai hakura tay".



Zama yay ba tare daya kulata ba ya cire rigar jikinsa yana kwanciya akan kujera ganin ya mata banza tace" ya musaddiq wai bakaji abinda nace maka bane gaskiya ni bana son shariya kodai fashi da makami ka koma"?.


Bude idonsa da sukai jawur kuma suka kumbura saboda rashin baccin da baiyi ba yayi yana kallonta yace" barnan gurin bansan shashanci idan kika sake na tashi saina huce dukkan takaicina akan ki".



Barin gurin Abidah tay tana cewa" dadina dakai babu wata maganar farin ciki tsakanina dakai ina matsayin matar ka kullum sai jaraba da zagi nima dai da laifina zan shareka na daina shiga sabgarka sai muje a haka" idan dutsi yay magana shima ya mata dan tsaki tay tana barin palon ma gabadaya ta shige bedroom.




tun asaba suke jiran a bude su suyi sallah amma shiru har gari ya waye sosai rana ta fito suna jiyo maganganun matar da aka kawo su gurinta jiya sai dariya take alamar duniya ta mata dadi ba abinda ya dameta amma su gasu ba sallah ga yunwa bamai taimakon su.


Karar bude kofa sukaji don haka kowa tasha jinin jikinta budesu wata yar aiki tay tana cewa" ku fito" mikewa sukai da sauri suna bin bayanta har palon zama sukai suna gaida wacce suka tabbata itace ta saye su jiya .



Bata amsa basai binsu da wani irin kallo take batay magana ba da ido taiwa mai aikin ta magana nan da nan sai gashi ta kawo musu kayan karyawa na alfarma mikewa hajiyan tay tana barin gurin.



Kallon su mai aikin tay tana cewa" kuyi sauri idan hajiya ta fito ba jira tafiya kawai zakuyi cikin damuwa suka kalli juna kowa tana saka da warwarar ina kuma za'a kara kaisu daga nan?.



Ko minti biyu basuyi a gurin ba ta fito cikin shiri bata kalli inda suke ba ta fice a palon girgiza kai mai aikin tay tana kallon su cikin tausayawa domin tasan inda hajiya zata kaisu daga nan tace" bazata kula kuba ku tashi kubi bayanta sai wata ran".



Mikewa sukai jikinsu duk yay sanyi suka fita kamar marasa lafiya a mota suka sameta tana gidan gaba ta hakimce da da wani uban glass a fuskarta shiga sukai driver yaja suka wuce.



Tafiya mai nisa sukai sannan motar ta tsaya suka fito wani lungu suka shiga inda ko mashin bazai biba a kofar wani ash din gate suka tsaya hajiya ta dan kwankwasa budewa akai mutumin daya leko ganin wacce ke tsaye yasa ya washe baki yana bude kofar yace" barka da zuwa hajjaju kice wasu muka samu sannun ku yan mata ku shigo".



Matsawa yay suka wuce suna shiga gidan iya ganinka matane kala daban-daban wasu na wanki wasu na shira wasu na abubuwan dake gaban su kana gani kasan gidan bariki ne suna ganin hajiya kowa ta mike jiki na rawa suka somayi mata sannu da zuwa kujera suka aje mata ta zauna tana dora kafa daya kan daya ta zare glass din idonta tana binsu da kallo daya bayan daya tace" ina marwa? ina samha"?.



Da sauri suka mike suna cewa" ran hajiya ya dade da girman kujerarki gamu ai mana afuwa idan munyi ba daidai ba".



Tsaki tay cikin masifa ta soma magana" wai meyasa kuke haka ne nace ku rika tsaftace gidan nan amma ku kalli yadda kukai sake ya baci yanzu can wajen gurin wanki ne duk kunbi kun bari an lalata min gidan nan taya kwastomomi zasu rika zuwa ko koyi ba kwayi dasu hajiya badawis komai na gidanta a tsari amma banda ku to wallhi ku gyara tun kafin naci mutuncin ku".


Jin abinda hajiya ke cewa yasa cikin yanayin bada hakuri Marwa tace" munyi kuskure hajiya amma zamu gyara zamu sake jajircewa ba laifinmu bane muna can ciki wani mai kudine yazo abinci muke shirya masa anan zai kwana yace aikin sati yazo wanki kuma Seeya ce take anyi mata magana ta rabu da mutane saboda tana gadarar itama shugaba ce a gidan".



Seeya dake zaune jin za'ai mata sharri yasa ta mike tana kara jan damara tace" kan ubancan ni zaki munafinta inaji sau nawa ana wanki a gurin baki taba hanawa ba saidan yau nayi da yake duk gidan nan ni kika raina nice karamar danganki mai dadin tsallaka to yau koni koke saikin fada min uwar me nay miki kika tsane ni a gidan".



Marwa dake mata kallon karamar yar iska tace" karya aka miki dan kinga idon hajiya shine zaki wani wayance karamar yar bariki nidaI kinsan ba sa'ar yinki bace nafi karfinki shashasha wacce bata da kasuwa".


Cukumewa sukai zasu fara dambe cikin tsawa hajiya tace" dalla malamai kuban hankalinku nan dama zuwa nay don kuyi fada ni kuma ina zaune ina kallon ku kamar mai kallon show ku bari idan na tafi sai kui wacce zakuyi banzaye kawai".



Sake juna sukai suna huci kowa na hararar kowa ji suke kamar su kara dambuwa suna tunanin matakin da hajiya zata dauka saidai su bari bayan tafiyarta su fidda raini.


Bayani hajiya ta shiga yi musu dalla dalla na iya tarar bako dajan hankalin kwastomas sannan ta kalli marwa tana mata nuni tace" ga sababbin dalibai na kawo ina da yakinin dukkan su yan mata ne ki koya musu darasi sosai za'a samu kudi dasu".


Amsawa marwa tay yayin da hajiya ta mike tana maida glass din idonta bata sake magana ba ta nufi hanyar fita bin bayanta sukai yi mata rakiya.



Marwa kuma ta kallesu tana cewa" barka da zuwa muje na kaiku gurin daya dace daku inda manyan hamshakan mutane suke zuwa sannan ku kasance masu biyayya kuma kada tsautsayi yasa mutum ya bamu kudi yazo zai ta baki, kice a'a bakisan da wannan ba tunda naga dukkannin ku yan mata ne ".



Wasu zafafan hawaye ne suka zuba a idon safah jin abinda marwa ke cewa lallai tasan rayuwarta tazo karshe dan komai zasuyi mata baza ta taba yarda ta bawa wani banzan kato kan taba.



Fincikarta marwa tay tana cewa" ke banza uban me kike tunani ina magana kin tsaya so'ko'ko ya kawar bora dalla wuce muje idan har kika ce taurin kai zaki nuna kece zaki sha wahala a barikin nan wawiya kawai".



Safah bata iya magana ba sai bin bayan marwa datay jikinta duk a mace tuna kalar rayuwar data sake tsintar kanta a ciki da yanzu yau ta wayi gari a dakin auren ta amma wai yau itace mai daki a gidan karuwai share hawaye tay daidai sunzo wasu sabin dakuna duk a kulle suke da key budewa marwa tay tana cewa shiga ina zuwa".


Shiga safah tay yayin da sauran ma marwa ta budewa kowacce kofa guda tana cewa bari ta dawo daga yau za'a fara koya musu kissa dan kila idan sukai kasuwa a yau ma sai kwastomomi sama da goma su fara layi.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE.


#Comment
#Vote
#Share
#And fallow.


TypingπŸ“

AπŸ’« WπŸ“ AπŸ‘ͺ
πŸ‘πŸ€—πŸ’•.



#YUSRAHMS#
NO.51 πŸ‘‰ 52
Zaune baffa yake murtala na gefensa gabadaya yabi ya rame ya firgice tun ranar da safah ta bata bai sake runtsawa ba kullum shida abokansa suna cikin gantalin neman ta amma shiru ba wani motsi kamar mushiriki yaci shirwa.



Cikin tausayawa baffa yake kallon murtala ganin duk yadda ya galabaita ya sanI shine ya haifi Safah duk wanda zai sota ko ya nuna mata kauna a bayansa yake to amma ya rumgumi kaddara zaici gaba da addu'a idan safah na raye Allah ya dawo masa da ita cikin aminci.



Tarin murtala ne ya dawo da baffa daga tunanin da yake ganin yadda gudan jini ke fita a bakin murtalan idan yay tari yasa baffa yace" murtala kada ka kashe kanka kayi hakuri kadau kaddara kaifa musulmi ne kuma kasan Allah kayi kokarin cin jarrabawar ka sai ka samu nasara ka dogara dashi saiya isar maka ka rokeshi saiya amsa maka Safara'u 'yata ce nine na haifeta kuma ina sonta fiye da komai amma nadau hakuri nasan kaddara mai kyau da mara kyau dan haka kaima ka kasance jajirtacce kuma tsayayyan musulmI kayi tawakkali ubangiji na gani dajin komai kuma shine zai dawo mana da ita Safara'u zata dawo gare mu insha Allahu kaji.



Kai murtala ya daga bai iya magana ba saboda wani irin turirin zafi da 'kuna dake fita a kirjinsa .



Asabe dake gefe dadi ya cika ta sai dariya take kasa kasa tace" kaima dai wallahi murtala da abin bada mamaki kake kamar ba musulmi ba sai kaje ka dorawa kanka cutar hawan jini kila ita safan da kake damuwa a kanta tana sane ta gudu kasan tafi karfin ka tunda taje birni kanta ya waye me zatay da dan kauye irin ka shawarar dazan baka ka daina bata lokacin ka akan ta ka mance da wannan ka nemi wata yarinyar tunda ga yan mata nan birjik a gari kayi auren ka duk maryama ce ta cuci mutane da taje ta koyo mata iya zaman bariki gashi tun kafin ayi auren ta nuna bazata iya zaman karkashin wani katon kauye ba ta kama gaban ta ta gudu gurin saurayin ta tabarka da hamma bayan ta gama talauta ka ta lalata ma kadara tsiyar 'yar bariki kenan yaudara kawai kaima ka manta da komai ka daina wahalar da kanka a banza kalli fa yadda inkai tari jini ke fita a bakin ka ko tsoron jininka ya kare ka mutuba kay..............




Dakatar da ita baffa yay cikin takaicin kalmomin dake fitowa daga bakinta marasa dadi na muniya dacin zarafi na koda yaushe bazata fadi alkairi akan Safah ba yace" ya isheki haka Asabe ban taba nuna miki bacin raina ba amma yau ta faru ta kare nagaji nakosa da halinki tunda har bazaki taba yin hankali ba Asabe kije na turaki gidanku ba kuma maganar aje gaba a dawo baya ina nufin na sakeki saidai ni na fiki tunani yanzu ma bango kika kaini kuma bazan dawo dake ba kisa a ranki bani bake babu wata sauran alaka tsakanin mu tashi ki tattara kayanki bana bukatar sake ganinki a rayuwata gara na zauna ni daya ya fiye min kwanciyar hankali ke ba matar farin ciki bace".



Tunda ya fara magana hannun Asabe yake kanta har yakai aya sannan ta fashe da kuka cikin magiya tace" dan Allah malam kayi hakuri wallahi bazan sake ba natuba ka mayar dani dakina abin kunya ne ace tsofai-tsofai dani na tafi gidan mu matsayin saki haka zai zama abin kwatance da nuni a wannan munafin kauyen".



Sosai bacin rai ya rufe baffa baya jin zai iya sake zama da Asabe gara yay wani auren ko damuwarsa ta ragu duk kalar magiyar da asabe keyi a banza baffa kam ya gama kulewa dole ta fara tattare yan komatsanta ta nufi gidansu.



Kallon murtala baffa yay wanda kamar baisan abinda yake faruwa ba yace" ina mai sake baka hakuri kaji komai na Allah ne bana jin ko kadan Safara'u dasan ranta ta barmu akwai wani abu a duhu amma rokona shine Allah ya bayyata kaima ka dage da addu'a in Allah ya yarda Safara'u zata dawo gare mu cikin aminci".



Har lokacin murtala babu magana sai dakyar ya dago hawaye na zuba a idonshi yana kallon baffa yace" baffa bana tunanin zan so wata yarinya bayan Safara'u bana jin zan iya auren wata daban idan ba kayi min addu'a ba baffa banajin sonta zai barni naci gaba da rayuwa kuma alkawarina ne wannan ko shekara goma zatay bata dawo ba zan jira ta zan jira ta baffa bazan yi aure ba".


Kai baffa ya girgiza dan wannan lamari yana bashi tsoro kofar dakin Asabe ya kalla ganin takalman ta yasa yadan daga murya yadda zata jiyo shi yace" zan fita yanzu zan dawo ki tabbata banzo na sameki a gidan nan ba idan kuma kina ganin kamar wasa ne ki bari na dawo na tarar dake sai kinga abinda zai faru".



Kuka Asabe dake cikin daki ta sake fashewa dashi jin abinda baffan ke cewa ko sauraronta baiyi ba ya mike yana kallon murtala yace" muje na raka ka gida karka damu kaji Allah shine gatan kowa babu abinda zai faru sai alkairi duk wanda ya dogara ga Allah zai isar masa".


Rike hannun murtala yay suka fita daga gidan yana cewa almajiran sa su shiga su taya Asabe deban kaya sannan suka wuce kuka kam Asabe tayi har muryarta ya dashe amma a banza haka dole tana gani ta jide kayanta tabar gidan.



Satin su Safah biyu ana koya musu yadda zasu rika tarar kwastomomi idan sunzo duk damuwa taiwa Safah yawa tabi ta rame ta lalace har zazzabi tayi fin kwana uku amma babu mai kula da ita haka ta karaci jinyarta ta warke ga wani shege magani da ake basu duk dare kafin su kwanta wai dan in anfara harka dasu suyi kasuwa da tsada.



Misalin karfe takwas na dare a kasar India Amfal ne tsaye jikin window yana kallon garin cikin nishadi da debe kewa juyowa yay yana kallon Abduljabbar dake ta jan tsaki tun dazu sakamakon yayi kiran wayar daya barwa su malam na Allah yaji a rufe kuma so yake ya tambayi yaushe ne bikin Safah ko kwana daya su dauka shi da Amfal suje daurin aure yana son haduwa da yarinyar nan yana bukatar ganinta a rayuwa.


Dan gyaran murya Amfal yay ganin ya shiga tunani da yawa yace" bros yadai meke damunka tun dazu naga baka sukuni kodai kana kewar gida ne ni kaina ina son muje gida a kwana kusa dan naga new aunty na amma nasan kila wata uku gaba ma albarka".



Kai Abduljabbar ya girgiza baiyi magana ba don iya damuwa ya shiga na rashin shigar kiran nan yasan dai ba cajine babu ba may be kawai rufe ta sukai.



Zama kusa dashi Amfal yay yana cewa" sorry bros ka kira aunty na da baka so nasani saika aureta taki shiga ko karka damu wata rana sai labari idan ka aureta sai tazo ta gundire ka kamar dankalin hausa".



Ganin yaki kula shi yaci gaba" bros gaskiya kampur dinnan ta burgeni akwai dadin zama har bana so mu koma Goa ina ga idan nay aure anan zamuyi honeymoon nida sweety na kome kace"?.



Dan harararsa Abduljabbar yay yana cewa" ka gani ko kullum baka da aiki sai zancen mace anya baka wanka kuwa koni maiji ka isheni amma ba matsala da mun koma zan sanar da Abba ga abinda kake so ni kaina na huta da wannan shashancin naka".



Dariya Amfal yay wallhi bros da naji dadi kayi taimakon musulunci dama inda nake so azo kenan ashe kana da saurin gane yanayi please kamin wannan taimakonπŸ™ˆ.



Kai Abduljabar ya daga masa ba tare da yayi magana ba ya jawo wasu takardu gaban sa ya soma dubawa.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE
YUSRAH MUSA ABUBAKAR.


MASU COMMENT THANK U SO MUCH NA GODE BAZAN IYA MISALTA FARIN CIKI NA GARE KU BA.

πŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’š πŸ’šπŸ’šπŸ’š πŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’š
πŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’š πŸ’šπŸ’š πŸ’šπŸ’šπŸ’šπŸ’š
πŸ’šπŸ’šπŸ’š πŸ’š πŸ’šπŸ’šπŸ’š
πŸ’šπŸ’š πŸ’šπŸ’š
πŸ’š πŸ’š

WATTPAD: MRS AL'AMEEN AHMAD CE

#YUSRAHMS#
NO. 53 πŸ‘‰ 54
Gidan bariki zaune marwa take a tsakar gidan yayin da kowa take harkokin data ga dama Samha ce tazo kusa da ita tana zama tace" marwa wata guda kenan muna koyar da yaran nan da hajiya ta kawo mana yanzu muka gama waya da ita tace daga yau su fara karbar baki kuma aja musu kunne su tabbata suna kissar da zasu samo kudi da wuri su biya kudin gyaran jikin da akai musu sannan su fara nemawa hajiya nata ya kike gani mu kira su mu sanar dasu ba sai dare yayi ba yau zasu fara shiga harka kome kika

Please Login or Register in order to submit comment