Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baba maryam tay jin abinda Safan ke cewa tace" ke kinci gidan ku safah murtalan kike kira kamar tuntube saboda kin fishi tsayi? kila duk 'ya'yan da zaku haifa suma gajerun ne sai naga karshen ba'a kema kin samu iri".


Dariya Safah tay tana rufe idonta baba maryam tace" ato abindai da kunya zagin suruki a gaban miji".


๐ŸŒนYusrah Musa Abubakar Gimba๐ŸŒน
Till we meet tnk for your support.



๐Ÿ’ซANNURIWRITER'SASSOCIATION๐Ÿ’ซ
(Home of hospitality and harmony
gidan๐Ÿก karba hannu biyu๐Ÿ™Œ da zaman lafiya๐Ÿ’).



๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
SAFREEYYAH
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


########## ##########
######## ########
##### #####
### ###
## ##
# #



๐Ÿ‘ ALLAHUMA BIKA ASBAHNA WA BIKA AMSAINA WA BIKA NAHYA WA BIKA NA MUTU WA ILAIKAN NUSHUR.


Sallim ala abban su nana binta mafi cika da girma a duk halitta ai nuru babullah mafi nagarta dashi halittu suka samu gata.



#YUSRAHMS#
NO.41๐Ÿ‘‰ 42
Abin mamaki hajiya na zaune a palor da safe washe garin daurin aure ba kowa ita kadaice baki na bangaren su Alawiyyah kuma bata tashi daga bacci ba.

Da gudu Abidah ta shigo tana kuka ta fada cinyar hajiya jikinta sai kakkarwa yake.

Cikin tashin hankali hajiya da take tunanin mk ko sakin Abidah yay ta soma tambayarta.

"Abidah lafiya? meya faru? me akai miki? ina mk din? meya kawo ki kina kuka da wannan safiyar ko sakin ki yay"?.


Kai Abidah ta girgiza murya na rawa kuma cikin kuka tace" mum bazan iya zama dashi ba kashe ni zaiyi Allah na fasa auren idan yazo kisa ya sake ni bazan koma gidan sa ba".


Hajiya da duk Abidah ta gama dama mata lissafi ta gaza gane inda Abidan ta dosa tace" meya miki kike kuka ko dukan ki yay saboda rashin hankali"?.



Kai Abidah ta girgiza" a'a mum tun jiya da aka kaini bayan tahowar su aunty Khadijah ya shigo dakin da nake yace min saina zabi mutuwa da zaman gidan sa idan ban sani ba to nasani tun wuri ni bai dauke ni komai ba ni sex machine dinsa ce domin bani da wani muhimmanci sai haka shine ya dace dani hukuncin da zanta karba kenan ba dare ba rana domin ba sona yake ba shine yamin fayde๐Ÿ™Š kuma ko tausayina baiji ba ya mammare ni yanzu kuma ya sake min wani fayden๐Ÿ™ˆ shine ya shiga wanka na samu na gudo don Allah hajiya ki taimake ni kisa shi ya sake ni bana son sake zama dashi".


Sosai ran hajiya yay masifar baci jin abinda Abindan tace kallonta tay tana cewa" kinga kwantar da hankalin kiyi hakuri ki nutsu muyi magana na fahimci zancen ki yi shiru haka nan babu inda zaki zaizo ya samen.........




Bata karasa ba taji ance" gani nazo mum ina kwana gaskiya nagode ashe gata kuka min da kuka min auren nan Allah ya saka da alkhairi cikin kwando kwando irin na tumatur๐Ÿ˜‚ ina dadyn mu shima na jinjina masa da hannu biyu na kuma gode masa don kun iya zaben mace" ya karasa maganar kamar zai sheke da dariya ganin yadda hajiya tay.


Mayar da kallon shi gun Abidah yay wacce ta gama shan jinin jikinta yace" ke kuma mara kunyar karya ni zaki zo kiwa sharri wai na miki fayde ko? ai kina fitowa na biyo bayan ki kuma naji duk abinda kika fada da iznin uban wa kika fito baki tambaya ba kina matar aure"?.


Shiru Abidah tay ta kasa ko tari sai kallonsa da take" cikin tsawa yace" uban me kike kallo ba magana nake miki ba"?.



A firgice Abidah ta sake kakkame hajiya cikin tsoro tana fashewa da kuka ganin yayo kanta.


Cikin fada hajiya tace" kasan Allah mk ka fara kaini bango za kaci ubanka dama kai maka ita akai cewa gata nan ka kasheta kome? ka shiga hankalin ka fa mk kafin nadau mataki wannan ai shashanci ne".



'Dan hade rai mk yay yana cewa" haba mum wato nine mara gaskiya bayan taimakon ta nayi itafa ta nace tace saini tana sona kuma kika hana ni zabina kika aura min ita to meye lefina bayan jihadi nay".


Kallon Abidah yay "ke kuma baki nasara ba saiki sake shiri don nafi karfin karyar ki taso mu tafi kwanan ki daya gidan miji har kika fito yawon muluguigui da munafinci saboda ke tantiriya ce zaki bayani".


Jin abinda mk yace ta taso su koma yasa ta rike hajiya tana cewa" dan Allah hajiya ki cece ni karki bari ya tafi dani bazan koma gidansa ba ya sakeni".



Kasa magana hajiya tay mk da yake dariyar mugunta cikin zare mata ido ya karaso yana 'bam'bare ta daga jikin hajiya ya mikar da ita tsaye kamar tsinke ya dauke ta tare da kallon hajiya yace" sorry mum ba laifina bane itace ta jawo komai amma kiyi hakuri kuma kada hakan ya dameki ki min fatan alkhari da addu'a mai kyau kinga ke mahaifiya tace don may be yanzu idan na koma kwallona ta shiga raga๐Ÿ€ kinga kema kin samu jikalle".


Ko
bari ya karasa hajiya batai ba ta toshe kunnen ta dariya yayi yana juyawa ya fita a palon da Abidah na gunjin kuka".


Tagumi hajiya tay domin mk yafi karfin ta bata da bakin magana saidai Abidah tayi ta hakuri dashi sauke ajiyar zuciya tay tana kallon kofar tace "Allah ya shiye ka mk gaskiya lamarin ka da gyara"ta karasa maganar tana girgiza kai dan saidai hakan".

++++++++++

Kamar yadda baba maryam ta cewa Safah bayan biki da kwana hudu suka je kasuwa sayayya duk abinda ya kamata ta sayowa safah ta sayo mata a gida ma hajiya ta hada mata abin arziki sosai saidai taji matukar rashin dadi da baba maryam tace mata Safah baza ta dawo ba aure za'ai mata kuma tadau alkawarin idan lokacin bikin yayi zata zo har kauyen su ayi da ita.


Ranar da zasu tafi gida bayan sun gama shiryawa gurin hajiya suka shiga mata sallama cikin damuwa ta kalli baba maryarm tana cewa"harkun gama shirin yanzu sai tafiya shikenan".

Baba maryam da itama duk jikin ta yay sanyi ganin yadda hajiyan ta damu da tafiyar Safan tace"eh hajiya duk kayan mu ma mun fita dasu suna harabar gidan so nake na fita na samo mana karamar mota wacce zata kaimu har kauyen sakamakon kayan Safah nada yawa".

Kai hajiya ta daga tana cewa"basai kun nemo mota ba ga driver muje na masa magana saiya kaiku".


"Hajiya kuma harda wahala haka dakin bari mun sami motar hidiman zatai yawa".

"Haba maryam ai tunani na mun zama daya daku dan kawai an kaiku gida ba wani abu bane kyautatawa ma nada dadi".


Mikewa baba maryam tay tana cewa"to hajiya mun gode Allah ya kara arziki mun tafi sai wata ran".


Tashi hajiya tay suna fita tare har harabar gidan kallon safah data hakimce tay tana fadin"Safah da haka zaki tafi ko sallama ba muyi ba kuma ba dawowa zaki ba".


Dan kallonta Safah tay cikin rashin jin dadi tana cewa"kiyi hakuri hajiya dama yanzu zan tashi na shiga sai kuma naga kun fito insha Allahu zan rika zuwa muku lokaci-lokaci".


Driver hajiya taiwa magana tana cewa"to shikenan Safah Allah ya nuna mana lokacin saina zo bikin ki gaida gida".



Dole da yake kayan da yawa sai babbar mota aka dauka musu hajiya na tsaye suka mata sallama suna shiga motar hajiyana kallo suka fita a gate suna dago mata hannu amma ba damar dakatar dasu haka ta juya cikin gida kamar mara lafiya duk jikinta ya saki.



Safah kam suna fita daga gidan ta kifa kanta ta soma kuka kawai itama sai yaudin taji rashin dadin rabuwa dasu.


Cikin rarrashi baba maryam tace"haba Safah kiyi hakuri mana rabuwa ba mutuwa bace ai a tunanina yanzu keda hajiya kun zama daya sai zumunci kuma kina jitace zata zo bikin kiko? ki kwantar da hankalin ki man bayan yanzu zaki ga Baffan ki dasu Hadiza ga kuma wadan mijin naki murtala da kika raina".


Daina kukan Safah tay ta kama dariya baba maryam tace" ummh wato na soso miki inda yake miki kaikayi" dan rufe baki safah tay"Allah ba haka bane kawai ni baffa na nadamu na gani ba kowa ba".


"Saurin me kike yanzu kuwa zaki ganshi".



Kwatance baba maryam ta rika yiwa driver har suka shiga kauyen mota bata tsaya ko'ina ba sai kofar gidan malam Abubakar (baffa).



Baffa na zaune a tsakar gida gurin wata ni'imtacciyar bishiyar zaitun daya dade da shuka ta domin har 'ya'yan ta anaci duk shekara idan lokacinsa yayi.



Asabe na gefe tana gyaran shinkafar sayarwarta tace" ohni 'yasu duniya ina zaki damu mutum da girman sa a saye shi da dubu biyar" sai kuma tay dariya tana kallon baffa daya dago shima yana kallon ta don yasan dashi take zai magana tace" nifa zaka dade kana jin haushi na dan gaskiya nake fada maryam ta yaudare ka da dubu biyar ta gudu maka da 'ya tana can ana koya mata yadda ake bude ido da iya zaman bariki gashi kai kuma ka taho gangarar mutuwa saboda halin rayuwa kila gobe kaji ka a kabari shine zan baka wata shawara nace ko zaka bani wasiyya na ajewa safan taka dan kila sai bayan ranka sannan ta dawo kauyen nan idan ma zata dawo kenan".



Ganin ya mata banza tace" yauwa ni kuwa malam dama inata so na tambaye ka wai kwanakin baya da dadewa naga wasu samari sun zo gidan nan su biyu su kuma daga ina? ahlin waye ko surukan kane daga Adamawan safan ta turo maka su ku gaisa"?. .


har lokacin baffa bai kulata ba tabe baki tay tana maida hankalin takan aikin ta ga dariyar murna fal cikin ta kasa rikewa tay ta saki dariyar sosai tana cewa" Allah malam idan na kalle ka tausayi kake ban bawai dariya nake maka ba kuka nake taya ka na rashin diyar ka ayya yi hakuri ba dawowa zatai ba".


Ba zato suka ji sallama wacce da sauri suka kalli hanyar kofar gidan Safah ce baba maryam na waje wajen debo kaya a mota mikewa tsaye Asabe tay a zabure tare dayin wani ihu tana murje idonta da kyau sannan ta sake bude su ganin ba mafarki take ba yasa tace" Safara'u kece nake gani ko gizo kike min"?.



Kallon ta safah tay batare da tay magana ba ta karasa inda baffa yake shima ya saki allo yana mata kallon mamaki dan gani yake kamar bada gaske bane Safah ce a gaban saba yafi tunanin ko aljana ce taji isgilin da Asabe ke masa tazo a suffarta.



Zama tay kusa dashi tana rike masa hannu cikin murmushi tace" baffa na barka da gida ina kwana fatan na same ka lafiya"?.


Sauke ajiyar zuciya yay ganin dai itance a zahirance yace" Safara'u kece da gaske a gabana ba mafarki nake yiba ina maryaman take ko ke kadai kika taho"?.


Kafin Safah ta bashi amsa baba maryam ta shigo rike da kaya a hannun ta bayan ta almajiran baffa ne suma kowa ya dauko ajiyewa sukai suna komawa don su kara debo wasu yayin da baba maryam ta karasa gurin baffa tana zama cikin fara'a tace" ina kwana Abubakar fatan na same ku lafiya"?.


Cikin jin dadi baffa ya dubi baba maryam yana cewa"lafiya 'kalau maryama ya hanya sannun ku da zuwa".


Zama baba maryam ta gyara tana kallon baffa tace" yauwa Abbakar sannun ka domin kaine ka cancanci awa sannu domin ban kyauta maka ba kuma ina mai baka hakuri na wuce ka'idar dana dauka a gurin ka wallahi yanayi na aikin ne a hakan ma yau da zamu taho ba kaga irin damuwar da hajiyan tay ba musamman da taji nace mata Safah ta taho kenan baza ta koma ba aure za'ai mata".



Murmushi baffa yay" a'a maryama karki damu babu abinda na taba ji game da tafiyar ku kullum addu'a ta shine ku dawo lafiya cikin aminci kuma Allah ya amshi rokona na gode sosai ji yadda 'yata ta sake kyau da girma farkon shigowar ta badan sallama ta fara yi nadau muryarta ba da bazan gane taba inba tai magana ba ta canza sosai".



'Yar dariya baba maryam tay daidai almajiran sun gama shigowa da kayan ta soma budewa tana fito da dinkuna kala biyar duk shadda sun sha aikin wuta sai fitar da sheki suke tace" baffa wannan naka ne cikin dukiyar safah wacce tay aiki a gidan da mukaje ta dinko maka wadannan kuma sauran buhunan akwai kayan abinci data sayo nan ma da kudinta kuma ta sai wasu kayan na bagaren abinda ya shafi kayan daki da sauran su sannan hajiya tayi mata kyautar kudi dubu hamsim gashi tace a bata ga nata ragowar kudin aikin tane sannan ga wasu kayan data dinkowa kakanun ta su Hadiza ga kala biyu kuma shima ta yowa Asabe wannan shine bayanin baffa".



Farin ciki sosai baffa ya nuna dajin dadin sa ga baba maryam ya kuma yi mata godiya da jinjinawa a gareta lallai tayi halacci kuma itadin mace ce wacce za'a dauki duk yarda a bata.



Suna cikin zance suka ji Asabe ta fashe da kuka tana zaman yan bori a kasa dukka juyawa sukai kowa na mata kallon mamaki baba maryam data fahimci kamar kukan takaici take yasa cikin basarwa tace" subahanallahi Asabe me kike haka? kamar wata yarinya ko baki da lafiya naga kina hada zufa"? ta karasa maganar tana mata kallon bakin ciki saidai ya kashe ki.



Kai Asabe ta girgiza tana share hawaye tace" a'a maryam ba jinya nakewa kuka ba kukan dadi ne ganin Safara'u ta dawo kullum muna cikin tunanin ta kinga malam har jinya da rashin lafiya mai tsanani yay saidai a kwantar saidai a tayar baya iya cin komai yana sambatu kodai yarsa baza ta dawo ba wani lokacin ma cewa yake Adamawa zaije ya taho daita nice mai rarrashin sa cewa ya kara hakuri zaku dawo shine tuna hakan ya sani kuka".



Wani kallo baffa ya mata na zallar mamakin karyar datai masa kuma a gaban sa zaiyi magana baba maryam itama da tai watsi da zancen Asaben ta sashi a kwandon shara don tasan ba gaskiya bane tace" to yayi ai dama haka ake son mutum yana kula da tarbiyyar yaransa baiyi laifi ba yayi daidai balle nasan hakan bazai yuwu ba kawai zancen kine mara kan gado kin rasa abin fada kunya ta kama ki abu ga marar hali bera๐Ÿ a kasuwa shine kika bullo ta nan".



Sak Asabe tay kamar ruwa ya cinye ta tana zare ido maida hankalinta baba maryam tay kan baffa tana cewa"to Abbakar nizan tafi gidan Hamza sai gobe naje gidan kawu Hakilu kuma ina nan saina huta kafin na koma Adamawa yaushe ne bikin don hajiya tace min idan na tambaya na kirata a waya na fada mata itama zata zo".



Kai baffa ya jinjina cikin fara'a yace" insha Allahu nan da kwana sha biyar tunda yau watan kwanan sa biyar sai ayi da ashirin"mikewa baba maryam tay to shikenan Allah ya nuna mana bari na karasa"godiya baffa ya mata yayin da Safah ta mike tana dauka mata jakarta don tayi mata rakiya suka fita a gidan.



๐Ÿ™†๐Ÿ‘ Mrs Al'ameen Ahmad ce
We will meet again lovers my everything is for you.



Ana tare๐Ÿ‘ญ๐Ÿ’.



TNK 4 ๐Ÿ’ž me.



Typing๐Ÿ“ฒ
10:10pm sunday march 2023



๐Ÿ‡๐Ÿ‡ SAFREEYYAH๐Ÿ‡๐Ÿ‡



โœจANNURI ๐Ÿ“WRITER'S ๐Ÿ‘ชASSOCIATION
Gidan karba hannu biyu da zaman lafiya group din annuri na marhabun lale da ba'kinta๐Ÿค—.


YUSRAH MS ABUBAKAR GIMBA


Ayya nagode da kulawa kwana biyu bakwa gani na online naga sakonni da yawa kuma nagode wallhi kwanakin nan bani da lafiya ne amma insha Allahu zan daure na rika yi muku typing ko baida yawa ne.



GA NAKU PAGE DIN SISTERS DINA NA JINI ALLAH YA KARA HADA KANMU AMEEN.
Naja'at Aminu
Naja'at Ishaq
Mariya Yakub
Sarah Yakub
Fatima Umar
Nasiba Magaji
Fadilah Saleh
Aishat dan baba.



DEDICATED TO.
MY MOTHER MAY ALLAH HELP AND BLESS YOU MAMANA I LUV U WITH ALL MY LIFE MY EVERYTHING IS 4 U MAMA.


๐Ÿ‘Allahumma bika amsaina wa bika asbahna wa bika nahya wa bika na mutu wa ilaikal masir.



๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’
๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’๐Ÿ’


#YUSRAHMS#
NO.43๐Ÿ‘‰ 44
Bayan sati biyu Fatima na zaune tare da bayin ta suna dan taya ta hira sakamakon Emir baya nan yayi tafiyar kwana biyu zuwa Germany suna cikin bata labari Ammy ta shiga cikin tsawa ta kalli bayin dake kewaye da Fatima tana cewa" ku dabbobi ku barnan kafin sakan daya bana bukatar kowa".



Cikin mamaki Fatima ke kallonta ita kuma wannan lafiya kodai tabin hankali ya soma kamata zata shigowa mutane guri bako sallama kamar wacce ta shiga coci.



Da gudu gudu bayin suka fita jikina rawa yayin da Ammy ta mayar da kallon ta kan Fatima tana cewa" ke kuma na dawo gareki wato har suna kika canza waike gimbiyar sarki ko saboda samun guri akuya๐Ÿ da tukin tuwo to wallhi baki isa ba kinyi kadan ki sani wannan sunan nawa ne don haka kiyi gaggawar goge shi a bakin bayi kafin kiga irin matakin dazan dauka wanda bazai miki dadi ba".



Kau dakai Fatima tay kamar bada ita take ba ta bawa iska ajiyarta cikin takaici Ammy tace" malama ba kiji abinda nace bane"?.


Ba tare data kalleta ba tace" au sorry maman Amfal sannu da zuwa ga guri ki zauna bari insa a kawo miki abin sha mai dumi domin naga kamar sanyi ke damun ki".


Ashar Ammy ta saki" nice zanyi magana kice sanyi na damuna wato ga mahaukaciya ko gargadi nazo nai miki daf da duka hawainiyar ki ta kiyayi rama ta wannan kinibibin da kisisina da kike a gaban mai martaba kamar wata tsohuwar karuwa ya ishe ki haka baki isa ki nuna min komai ba nina wuce inda kike zato na".



Dariya Fatima tay tana kallon ta tace" tofa yauga hauka dangi dangi sannun ki da kokari tun dazu kina ta haushi saidai bana fahimtar abinda kike cewa magana kike ko bakin kine a haka dan na fahimci kamar bakya cikin hankalin ki kije a baki ruwa da abinci kici idan kin dawo daidai saiki zo muyi maganar domin ni a yanzu bani da lokacin shirmen ki dama waya zanyi da rabin raina dalilin bayi na taya ni fira yasa na hakura kinga yanzu kin taimaka min bari naje naji ya lafiyarsa idan kin gaji da tsaiwar ga guri nan ki zauna ko ki kwanta nina shiga daga ciki".


Tana fadin haka ta mike rike da waya tana danna kiran Emir tare da karawa a kunne tace hello dear gaskiya nayi kewar ka yaushe zaka dawo na shiga maraici da yawa daidai ta bude kofar bedroom ta shiga zata rufe saida taywa Ammy gwalo๐Ÿ˜ sannan ta rufe tana dariya domin da gaske da Emir suke wayar handfree tay don Ammy ma taji muryar sa.


Wani irin bacin raine da takaici ya dabaibaye Ammy ita kadai ta rika waige waige kamar me neman wani abu ganin gurin cin abincin Fatiman an shirya shi kuma da alama bata ciba a fusace ta nufi gurin ta soma watsi da kayan tana tarwatsawa saida ta baje komai sannan ta koma kan kujerun palon tana hade su wasu kuma ta wuntsila su saida ta gata ta gama lalata mata palon tayi kaca kaca dashi sannan ta fice tana zage-zage.




Bayan tahowar su safah daga Adamawa mk bai sani ba saida daga baya ya sani ba karamin tashin hankali ya shiga ba har rama yay kamar mara lafiya musamman daya ji hajiya tace baza ta dawo ba aure za'ai mata.


Yau week end Alawiyyah na gidan mk gurin Abidah suna zance Alawiyyah ke cewa" nifa ba wuni nazo miki ba tafiya zanyi saboda taya mum aiki".


Kallonta Abidah tay" wanne irin aiki kuma ina barorin gidan naku"? dariya Alawiyyah tay" kai dan Allah harkin sani dariyar daban shirya ba wai barori sun tafi gida mana ita Safah naji mum na cewa baza ta dawo ba aure ma za'ai mata".


Mikewa Abidah tay cikin farin ciki tace" dan Allah da gaske kike Alawiyyah aure za'ai mata? wani tsalle ta daka kai amma naji dadi wallhi da baza ta dawo ba haba yarinya duk tabi ta tare gida kamar mayya".


Kallonta Alawiyyah tay" ikon Allah ke kuma wannan matar farin ciki haka me ta tare miki"? Dariya sosai Abidah keyi tana juyi tace" ba ruwan ki kedai tunda kin min albishir zan baki kyauta" tabe baki Alawiyyah tay" a'a nagode rike abarki nina wuce" bata jira jin me Abidan zata ce ba tafice a palon tana mamakin ita kuma wannan murnan barin Safah gidan name take?.



Safah ce zaune tare dasu hadiza taje musu ziyara sannan saura sati bikin ta malam ya kalleta yana cewa" Safara'u d'an uwanki Abdullahi yazo mana ziyara ya dade a nan bayan tafiyar ki Adamawa inaga dai ba rabon ku gana ko kuma sai bikin nan naki tunda yan kwanaki suka rage sai a sanar dashi kinga da zai tafi ma har wata salula ya barmin wai muna kiran sa niko bansan inda zan kunno maganarsa muji ta ba tana nan a ajiye Hadiza dauko mata wannan salular ta gani ko zata iya danno mana shi".



To Hadiza tace tana mikewa ta shiga daki Safah kam zuba ido tay cikin mamaki taga meye na Allah yake nufi da salula sai taga hadiza ta kawo mata waya keypad a kwallinta tana cewa" gata duba mana tunda ke kinje binni kila kinga ana amfani da ita mude bata shigo mana nan ba".



Dariya Safah tay tana karba tace" wai dama waya kuke cewa salula na dauka wata camera zan gani katuwa bari muga indai akwai kati na kira shi".


Bude wayar tay tana shiga cikin contect ba number sai guda daya itama ba suna tunani tayi may be ko itace number tashi dan haka kawai ta danna kira tayi sa'a kuwa ta shiga saidai harta katse ba'a daga ba dan tsaki tay tana cewa" to ai gashi na kira ta shiga amma ba'a daga ba kodai kawai ya zura ku a kwalba ne"?.


Dariya na Allah yay yana kallonta yace" eh ba'a kwalba zaki ce ba a bututun mai ko mizirari ya samu sake kunno shi mu gani" murmushi Safah tay wai sake kunno shi kamar gidan radio kara danna kiran tay wannan lokacin kuma sai aka kashe.


Na Allah ta kalla tana fadin" to gashi yanzu ma ta shiga ya katse kiran dama dai kila ya baku ne dan kuyi ta kallonta matsayin photo decoration tunda bata da wani amfan........


Bata karasa ba wayar tahau ringtone dan zubawa number ido tay bata daga ba Hadiza tace" to ya kunno naji tana kara kuma banji maganar saba ko saita gama zamu jishi"?.


Kai Safah ta girgiza dariya na cinta jin abinda Hadiza ke fada batai magana ba ta daga kiran tana sawa a handfree ta mika musu".


Kallon ta na Allah yay" me zamuyi ko haka ne kunnowar"? Ba arziki Safah ta mike da gudu tana yin hanyar kofar gida sannan ta saki dariyar da take rikewa tana cewa"kasa a kunne kayi magana zaka ji shima yayi".



"To na Allah yace yana karawa kamar yadda tace yayi yace" salama alekum Abdullahi kana jina"? daga can bangaren Abduljabbar dake zaune yana duba wani littafi yay murmushi yana cewa" wa alaika salam kakana na kaina ya kake" cikin mamaki na Allah yace" lah ikon Allah Hadiza kinji da gaske ta kunno shi".



Karba hadiza tay tana kallon wayar tace" wai Abdullahi maganar ka nake jine" eh nine meyasa idan nakira wayar saina jita a kashe"? 'Yar dariya Hadiza tay tana cewa" ai bamusan yadda zamuyi mu kunno kaba yanzun ma Safara'u ce data dawo daga Adamawa muka ce ta dannoka".



Dan shiru yay zuwa can yace" wace haka? ko yarinyar da kuke cewa sister nace" zaro ido Hadiza tay" tofa meye sister kuma"? dan rike kai Abdul-jabbar yay" ina nufin kanwa ta da kuke fada lokacin da nazo".


Na Allah yace" eh fa Abdullahi ashe baka manta ba itace".


"Ok bata wayan".



Kallonta Hadiza tay" to gwana idan kin gama dariyar zo ki karba zaku gaisa da yayan

Please Login or Register in order to submit comment