Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muga wanne kalar aiki ne"



Ana gobe sunan yaran Fatima danginta sunzo dan wasu ma cewa sukai sai sun tsaya sun kalli hawan sarki zasu koma,.


Suna zaune a palor ana ta hirar yaushe gamo Safah da Zarisha suka zo fita".


Har sun wuce Fatima tace yauwa Zarisha ki turo min umman ku idan kun koma kice ina neman ta".

"To Zarisha tace suna fita".


Wata mace dake zaune ce tace wadannan yan matan kuma fa sarki nada yara mata dama"?.


Murmushi Fatima tay tana girgiza kai tace a'a 'ya'yan bayi ne me kika gani".


Dan zaro ido Khadija dan Allah da gaske wadannan din har ina ayyana na zabawa Khaleepha na daya".


Dariya Fatima tay to mene a ciki zaki iya aura masa da bayi da sarki duk daya ne sai wanda yafi wani kyakkyawar zuciya mafi tsoron Allah".


"To ai matsalar ba daga ni bane daga yayan kine bazai amince ba".


Kai Fatima ta daga indai da gaske kike zanyi masa magana idan mukai waya".


Yar dariya Khadija tay daidai jakadiya ta shigo sai bata fadi abinda take son cewa ba saita fice.



Amfal na zaune a palon su da dare shi kadai wata zundumemiyar budurwa ta shigo tana cewa" Amfal ni nazo tunda kai bazaka neme niba yau kwana na uku da zuwa Ammy ce ta hana ni fitowa".


Cikin mamaki Amfal ya dago yana cewa" Mara'kisiyya kece yaushe rabona dake shekara kusan biyar".


Da 'yar shagwaba tace ba kaine baka zuwa masarautar muba kamar baka da kakanu".


Ina sam ba haka bane baza ki gane ba aiki ne yake min yawa".


Haba Amfal wanne irin aiki kuma ina Abdul-jabbar yake banji motsin saba".


Cikin tsokana saboda yasan Mara'kisiyya nason Abdul-jabbar yace tun yaushe ya tafi barzahu aiya dade da mutuwa tun wajen karfe takwas na dare bayan mun dawo daga masallaci bazan iya fada miki ba shiyasa na kasa kiran ki a waya".


Saboda tsabar rudewa bata iya fahimtar zancen saba mikewa tsaye daga zaunen da take tay har tana sarkewa tace.


"Ya mutu😨 fa kace Amfal da yaushe na shiga uku".


Dariya ce ta kusan kubcewa Amfal yay saurin rike ta cikin dakiya yace" me yasa kike son tuno min mutuwar dan uwana ne na fada miki tun karfe takwas saidai hakuri nasan kinyi dakon sonshi rabon baza ku gana ba kila saida safe".


Duk da hakan da yace bata fahimce shiba hannu ta dora aka cikin tashin hankali ta juya da gudu tabar palon.


Dariya Amfal ya sheke da ita yana cewa haba gara da baki gane ba yar caza kai bros na bacci da haka na fada miki da yanzu kinsa dole ya tashi".


Da gudu Mara'kiyyah taje ta fada kan Ammy dake zaune a palor tana kurma wani uban ihu wanda saida ta bawa Ammy tsoro.


Tambayarta ta farayi ke lafiya me ya faru wani abin tsoron kika gamu dashi ya firgita ki menene"?.


Hawaye ne shar shar suke zuba daga idonta muryarta na rawa kamar yadda jikinta keyi tace"

"wayyo Allah na Ammy shikenan na shiga uku na fito rana yaya zanyi da zuciya ta dama Abdul-jabbar ya rasu baki fada min ba🙊"?.

Sai kuma ta fashe da wani matsanancin kuka me taba zuciyar me sauraronta kana gani kasan ba karamin so takewa Abdul-jabbar ba".


Wani irin kallon kin fara hauka ne Ammy ta mata cikin tsawa tace" ke dalla rufe min baki uban wa ya fada miki ya mutu zaki zo ki dame ni da sakarci wawiya kawai".


Cikin kuka Mara'kisiyya tace wallahi Ammy bada wasa nake ba yanzu nan naje part dinsu Amfal yake fada min wai ya dade da mutuwa".


A ran Ammy tace yana kan hanya dai ya kusa basai an kira masa ba tana nan tafe.


Takaici ne ya kamata ganin yadda mara'kisiyyan ta zage bil hakki tana kuka bata san lokacin data sakar mata mari a fuskarta ba.


Cikin fada tace" mahaukaciya kika zama ne kome dan uban ki so kike ki dora min hawan jini ina ruwan ki idan ma mutuwar yay meye damuwar ki".


Dole na damu Ammy tunda ina son shi".


Tureta gefe Ammy tay tana mikewa cikin bala'i tace tun wuri ki goge wannan banzan son ya zama muguwar kiyayya tsakanin ki da Abdul-jabbar Allah ya sauwake na hada zuriya dashi idan mafarki ma ki ke toki farka dan wallahi muddin ina numfashi a duniya baza ki auri Abdul-jabbar ba".


Hanyar bedroom Ammy ta nufa tana cewa shashashar yarinya zaki koma inda kika fito dan baki isa kizo ki bata min shirina ba".


Kuka marakisyya keyi sosai na fitar hankali ta kife kanta saman kujera tana cewa.
"lokacin mutuwa tane yazo gara nasha guba rayuwa ta bata da amfani indai babu Abdul-jabbar a tare ni".

Tnk for your support 💞

SAFREEYYAH


#YUSRAHMS#
NO.75👉 76
Washe gari ansha dandazon suna duk da azumi ne yara sunci Hassan&Hussaini daga wasu masarautun ma me martaba yayi baki da yawa yan taya murna da wadanda basu samu damar zuwa ba suka aiko da sakon nin gaisuwa.


Emir na zaune Fatima na kusa dashi sunsa yaran a gaba suna kallonsu cikin farin ciki samarin sane suka shigo".


Cikin murmushi ya rike hannun Abdul-jabbar yana kallonshi yace ga mahaifiyar ka nan zaune dana dama wannan ranar nake jira na cika alkawari na".


Cikin mamaki Abdul-jabbar dake kallon Emir yace Abba dama mahaifiya ta na raye ka boye min bata mutu ba me yasa kayi haka"?.


Girgiza kai Emir yay cikin tausayawa yace kwantar da hankalin ka ka fahimce ni kaji ba ina nufin Fatima wacce ta haife kaba a'a ita wannan ta dade da rasuwa".


Wannan kuma mata tace daga masarautar Adamawa na auro ta so nake daga yau ka riketa kamar wacce ta haifeka ka rika mata kallon uwa a gare ka zatay abinda kowacce uwa kewa danta".



Zata zame maka garkuwa ba taba rika wulakanta ko ka cutu ba fatan ka fahimce ni"?.


Shiru kawai Abduljabbar yay ya zuba masa ido wanda shima Emir yana son yaga Abduljabbar din na kallonshi domin irin idanuwan mahaifiyarsa ne dashi kuma har kallo ma irin nata yake yi hakan yana sa ya tuno da ita".


Katse musu shiru Fatima tay da cewa dana dan Allah ka dauke ni matsayin mahaifiya a gareka zanyi maka dukkan gatan da uwa kewa danta".


Kasa magana Abduljabbar yay sai hannunta daya rike tare da daga kai alamar ya amince".


Da muryar shi data sauya yanayi yace nagode Abba da wannan kyauta da kamin lokacin da banyi tunani ba kuma nayi alkawarin mata biyayya kamar yadda kowanne da yake wa mahaifiyarsa zata same ni me ladabi a gare ta".


Kai Emir ya jinjina cikin jin dadi yace Allah ya albarkaci rayuwar ka".


Fatima dake murmushi tace nagode dana Allah ya tsare min kai".


Dakyar yace amin saboda wata hajijiya da yake gani mikewa yay yayin da Amfal ya mike cikin farin ciki suka fita".


Suna shiga part dinsu ya daina ganin komai sai duhu luuuuu ya tafi zai fadi cikin sauri Amfal ya tare shi yana cewa sannu bros kabi a hankali".


Kan kujera ya ajiye shi yana cewa bros lafiya naji jikin ka ya fara dumi karfa ace zazzabi zakai gobe sallah shikenan hawa ya barmu".


Shiru Abdul-jabbar yay ganin baiyi magana ba kuma idonsa a rufe yasa Amfal tashi ya shiga bedroom dinsu sai gashi ya fito da ruwa da kuma karamin towel.


Zama yay a kusa dashi ya soma shafa masa ruwan ta ko'ina zuwa wani lokaci ya sauke ajiyar zuciya tare da bude idonsa yana kallon Amfal.


Wanda shima shi yake kallo cikin murmushi ya hada hannunsa da nashi yana cewa.


"Bros ina taya ka farin ciki kaga kaima yanzu ka samu uwa wacce zata rika debe maka kewa da kuma kace kasan baza ka taba samu ba gashi Allahu ya baka a lokacin da bakai zato ba".


Yanzu kam zan iya komawa gurin Ammy domin kaima ka samu mahaifiya to nima zan bata dukkan lokacina".


Har lokacin kallonsa Abduljabbar keyi Amfal da mamaki ya kama shi cikin ranshi yace.

"kai lafiya kodai bros ya kurmance ne wata zuciyar tace ka gwada shi ka gani".


Kara matsawa kusa dashi yay yace bros na manta ban fada maka ba mara'kisiyya tana masarautar nan jiya ina zaune da dare tazo neman ka amma nace mata ka mutu tun karfe takwas shine ta fita tana kuka".


Zaro ido Abdul-jabbar yay wanda ya kusa baiwa Amfal dariya amma saiya maze yaji me zaice masa".


Numfashi Abdul-jabbar ya fitar yana cewa da gaske kake ko kuma dan kaga yadda zanyi ne ka fadi hakan"?.


"Hahhh wallahi bros da gaske nake ba tsokanar ka nake ba tazo".


Dafe kai Abdul-jabbar yay yana cewa please Amfal dan Allah duk wata hanya da kasan zamu hadu ko ta ganni ka toshe ta".


Cikin dariya Amfal yace taya kenan daina fita zakai saboda ita ka koma zaman daki kamar mummunar amarya ko kuma a aljihu na zan saka na rika yawo dakai".

Tsaki Abdul-jabbar yay jin abinda Amfal din ke fada yace malam tashi kaban guri ka ishe ni haka".


Mikewa Amfal yay cikin tsokana yace shikenan tunda haka kace bari naje na gayyato maka ita tazo ta baka ciwon kai".


Yana fadin haka ya fita har gware suke yana dagowa yaga marakisiyya idonta duk a kumbure cikin mamaki yace".


"Yace lafiya meya samu idanuwan ki suka kumbura haka ko kuka kikai".


Cikin damuwa marakisiyya tace ba dole ba Amfal Ammy taki fahimta ta gashi tace min bai mutu ba kai kace min ya mutu meye gaskiyar lamari dan Allah ka daina cutar da zuciya ta".


Dariya Amfal yay ok akan haka shine kika kwana kina kuka lallai yarinya kina da aiki muje part din Ammy saina fada miki gaskiyar da kike son sani".


Juyawa tay suka wuce domin Amfal bai kaunar taje ta takura masa bros dinsa dama gashi alamar zazzabi zai kama shi yasan tana zuwa zata sanya sai sun dangana da asibiti.




"Ku fito mu kwashi shoki sallah tazo gaskiya gobe akwai shagali kan bala'i ya akai amaryar me martaba ta gane cewa doguwar riga nake matukar so ta mana ko baki gani bane Safah"?.

Zarisha ta fada tana gwada kayan cikin jin dadi.


Murmushi Safah tay tana kallon ta tace na gani mana gaskiya matar nan tana da kirki dole a sara mata ta cancanti jinjina ita din jaruma ce".


"To kin gani dai na Allah basa karewa".


Sauyawa fuskar Safah tay sakamakon na Allah da Zarisha ta ambata saita tuno da ahlinta wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata badan dare bane tabbas da Zarisha zata iya ganin su.


Ganin tayi shiru yasa Zarisha matsowa kusa da ita tana haska ta da fitila ganin hawaye a fuskarta yasa cikin rudewa ta soma tambayar ta.


"Safah lafiya meya faru me akai miki kike kuka bayan magana muke ta farin ciki yanzu"?.


Fashewa Safah tay da kuka cikin shashsheka tace" Zarisha na tuna dangi nane lokaci guda aka raba ni dasu a sanda ban taba tunani ba ban kuma kawo a raina hakan zata faru ba".


Gyara zama Zarisha tay cikin mamaki tace ahlin ki dan Allah Safah ki fada min ya akai kuka rabu da su".


Kai Safah ta girgiza to kimin alkawari Zarisha baza ki fadawa kowa ba har abada koda umma kice".


Da sauri Zarisha tace" nayi alkawari Safah bazan taba cin amanar kiba zan kasance me rike miki sirrin ki".


Safah tayi matukar yarda da Zarisha kuma ta shaku da ita jinta take tamkar yar uwarta bata jin zata iya boye mata komai game da labarin ta".

Bata rage koda kamar allura cikin tarihin rayuwarta tunda ta taso bata san mahaifiyarta ba saifa Asabe dake gallaza mata har izuwa yau da suke a wannan yanayin".


Kai zarisha take girgizawa tunda safah ta fara magana itama hawayen sun wanke mata fuska tace.


"Safah da zaki amince da nayiwa umma magana ta nema miki alfarma an mayar dake garinku".


A'a Zarisha kada muyi haka dake kinyi min alkawari fa cewa baza ki fadawa kowa ba kawai ki 'kyale zama na anan dinma ina jin dadin sa".


"To amma Safah murtala fa bakya tunanin irin halin daya shiga bayan batan ki".


"Na sani zarisha zai shiga yanayin damuwa da mummunan hali domin son da yake min ba karami bane amma dole ya dau hakuri tunda kaddara ta raba mu kila ma yayi wani auren".


Zarisha zatay magana Rasheeda kanwar Safwan ta shigo tana cewa.


"Ahayye ayyuriri aunty na kinyi goshi yayana ya cakare ki da dinkin sallah".


Ta fada tana aje katuwar ledar dake hannunta.


Cikin tsokana Safah tace gaskiya amaryar Safwan kina da 'kashin arziki gobe wankan naku ne".


Dariya Rasheeda tay tana cewa wace sistar sa yace idan nazo na tambaya"?.


Zaro ido Zarisha tay tana cewa gata nan kusa dake".


Rasheeda tace to kema ga naki yace kuma na gaishe dake".


Baki bude Safah ke kallon Rasheeda ta kasa magana daidai jakadiya da hanne sun shigo".


Hanne tace yan mata ran gari ana ta shirin sallah Allah dai ya tashe mu lafiya wannan ba Rasheedan uwar soro bace"?.


Kai Rasheeda ta daga eh nice baba Hanne nazo gurin aunty na kawo mata kayan salla ne".

To yayi kyau Allah ya sanya albarka a kashe lafiya".


Mikewa Rasheeda tay tana cewa idan kun shirya zuwa jimawa zan dawo maganar lalle".


Suma mikewa sukai domin yi mata rakiya suna fita a dakin".


Jakadiya tace Hanne zauna mana kina ta tsaye zama Hanne tay tana cewa uhm na tsaya sababin kallon yaran zamani".


Dama zuwa nay akan maganar yadda goben komai zai tafi amma ya kike gani ko gurin Adama zamuje".


Kai jakadiya ta girgiza kinsan komai dacan ma gurin hajiya muke zuwa yanzun ma candin zamuje abune me girma daya shafi dukkan masarauta kuma tunda mahaifiyar sarki na raye dole gurin ta zamuje ba gurin matan saba".


To shikenan Lantana hakan yayi muje dama neman shawara ce shiyasa banyi da kaba".


Mikewa sukai suna fita lokacin su Zarisha sun dawo cikin zumudi Safah tace bari muga wanne kalar dinki ya dandako miki".


Bude ledar tay ta fito da zukekiyar atamfa tasha dinkin riga da skirt me kyau ga takalmi da gyale harda jakarta".


Uhm gaskiya zarisha gobe zaki fito sosai da sarki nada 'ya'ya mata da nace gobe kosu baza su fada miki wanka da kwalliya ba".


Dariya zarisha tay= kai Safah tsokanarki yawa gareta su da zasu yi ado da alkebba ta alfarma suna tafiya ana take musu baya har ki hada ni dasu".


Eh mana Allah ne me daukakawa yakan dauke ki yakai ki babban matsayin da baki tunani ba bari naga nawa dinki".


Duka iri daya ne itama riga da skirt din ne murmushi tay tana kallon zarisha tace kin gani ko alkhairi dango ne baya faduwa kasa banza".


"Na gani kam Safah lallai Safwan mutum ne daya kamata aso shi kinyi min gata da kika ganar dani na gode".


"A'a zarisha karki samu damuwa nice da godiya domin ni kuka fara yiwa alkhari kafin na muku ba wanda ya dube ni da idanun rahma saiku".


Kai zarisha ta jinjina tana tattare kayan tace shikenan Safah Allah ya kara barin mu tare yau tunda umma na ana zata kwana basai Rasheda ta mana lallen anan".



Washe gari tun asuba kowa ya soma shirin zuwa sallar idi d duk gida ya hargitse surutai sun yawaita dokuna kam sai shirin su ake kamar ba gobe.


"Safah dan Allah kiyi sauri kar lokaci ya kure mana sai safga kike ko baki da lafiya ne naga kinyi wani iri"?.

Zarisha ta fada tana dauko gyalen ta cikin yanayin matsuwa su tafi.


Sauke ajiyar zuciya Safah tay cikin mutuwar jiki tace.

"Wallahi Zarisha bansan meke damu naba jiya na kasance cikin farin ciki da zumudin wannan rana amma yau ina ta shi daga bacci naji duk jikina wani iri ga zuciya tana bugawa akai-akai".


Kallonta Zarisha tay kai Safah kema dai dan Allah manta muje kawai".


Mikewa tay tana karasa shiryawa suka fita gidan tsit kamar babu dan adam suna wucewa Basira dake boye da gudunta ta ruga bangaren Ammy.


Tana shiga ta durkusa kusa da Zakiyyah cikin haki tace" ranki ya dade sun fita yanzu tare da yar gidan jakadiya zasu tafi".


Kai Ammy ta jinjina ku tabbata kunyi taka tsantsan wajen yin aikin kada ku barI kowa ya ganku sannan dakun aiwatar kubar gurin kunji"?.


"To ranki ya dade muna godiya" suka fada tare da mikewa suna fita.

Waini Basira wanne irin aiki wannan matar zata samu ina tsoron takai mu hallaka".

Tsaki Basira tay ke dalla kin fiya tsoro babu abinda zai faru kisa tunanin ki guri daya".


"Na yarda dake shikenan muje" tafiya sukai suna tsara yadda zasuyi idan ta basu aikin.


Tsaye suke a filin hawa bayan an sako daga sallar idin cikin tsokana Safah tace" la Zarisha kalli can sahibin ki".


Da sauri Zarisha takai kallonta inda Safan ke nuna mata Safwan ta gano akan doki dan duka takai mata tana cewa

"Allah Safah kin ga ma raina ni zanyi maganin ki".


Yauwa Safah kalli wadancan masu kaya iri dayan to sune yayan sarkin dama kince baki taba ganin su ba".


Daga ido Safah tay ta hango su a fili suna tseran doki kamar zasu tashi sama🏇 dakyar kake ganin wulgin su tsabar gudu".


Zaro ido safah tay kai zarisha basa tsoron faduwa jifa yadda suke"?.


Dariya Zarisha tay ba wani faduwa bayan sun saba".


"Kai Safah ta daga zatay magana taji abinda bata taba jiba cikin tashin hankali ta kalli Zarisha wacce hankalinta kekan masu wucewa tawaga-tawaga.


Muryarta na rawa tace dan Allah Zarisha mubar nan meye haka yake tashi"?.


Murmushi Zarisha tay batare data kalli Safah ba tace ba wani abu bane bindigar sanarwa ce alamar sarki ya kusa karasowa".


Jin an sake harbawa ga harbin ba daya ba ba biyu ba yasa tace nidai muje kallon ya isheni haka ba dole bane".


"Kece fa kika ce saboda kiga sarki idan kuma muka tafi me akai kenan munzo a sadaka zamu koma a alakoro ".


Gaf da sarki ya karaso wata kankama Safah taiwa Zarisha tana rufe idonta alamar bazata gani ba.


Zuwan sarki yasa guri ya kara hargitsewa wanda yasa Safah taji kanta na juyawa da sauri ta saki Zarishan tabar gurin.


Cikin gida ta koma tana tafe tana waige-waige kamar mara gaskiya harta koma bangaren bayi zubewa tay akan katifar su tana sauke numfashi kamar wanda itace tay tseran.


A bangaren su Abdul-jabbar kam sunyi tsere sosai sun tsinka jinin jikin su saida mahaifin su ya shigo gida sannan suka rufo masa baya".


sauka Amfal yay yana kallon Abdul-jabbar yace kai amma fa na wahalar da kaina bros dama haka ka iya tsere ban sani ba na biye maka gashi yanzu duk gabobi na ciwo suke min".


Murmushi Abdul-jabbar yay yana shafa bayan dokin sa cikin jin dadi yaiwa dokin kiss yana kallon Amfal yace.


"Ina matukar son dokin nan saiya bani tausayi da naga yana hakin nan dama nasan dole zai wahala saboda ya dade ba'ai tseren dashi ba jifa yadda yake haki".


"To ai bros laifin kane kayi gudu sosai fa haka nake ganin ka kamar walkiya yanzu muje gurin hajiya ta bamu happy sallar mu".


Barin gurin sukai dai-dai nan su Basira suka fito da bokiti suna ajewa a gaban dokin ganin ya daina kai ya fara sha yasa da sauri suka sheka da gudu zuwa part din Ammy.


Tana ganin su ta mike tsaye tana cewa yane komai ya kammala"?.

Suna haki kamar ransu zai fita gashi sun gigice dakyar suke magana.

"Eh ranki ya dade abinda kika bamu mun saka masa kuma sanda muka taso yana sha".


"Yayi kyau ku zauna sai numfashin ku ya dawo normal kwa tafi".

Juyawa tay da wani irin murmushi a fuskarta ta wuce bedroom.


Safah na kwance ganin har lokacin Zarisha bata dawo ba yasa ta mike tana cewa barI naje naga. gurin aikina yau ban leka ba kar nayi laifi".


Har taje zata shiga part din kawai ta fasa tana juyawa ta koma inda ta fito".


Su Abdul-jabbar na shiga part din hajiya suka ga marakisiyyah a gurinta zaune sai zance take zuba mata gefe guda tana bare mata ayaba tana mika mata.


Tunda tazo basu hadu da Abdul-jabbar ba tay nacin harta gaji sai yanzu data ganshi.


Hankalinta inyai dubu ya tashi idota zaro cikin tsananin mamaki tace.

"Abdul-jabbar kai nake gani da gaske a gabana ko gizo kake min dama ba mutuwa kaiba" ta fada idonta na kawo hawaye.


Hade rai Abdul-jabbar yay baiko kalli inda take ba balle tasa rai zai mata magana.


Goge hawayen fuskarta tay tana mayar da hankalinta kan Amfal tace ashe dama bai mutu ba kasa ni kuka"?.


Zaro ido Amfal yay ke dawa kike ni zakiwa sharri da yaushe nace miki ya mutu"?.


"Wallahi Amfal kaji tsoron Allah kaifa kace min ya mutu ba sharri na maka ba".


Banza ya mata yana kallon hajiya yace hajiya ta nazo yawan salla a bani kudi ko nama".


Hajiya data aje sauran ayabar da take ci ta kalleshi tana cewa" babu abinda zaka samu maza tashi kaban guri".


Tofa dan kinyi sa'a ma nazo taya ki cin naman dokin da nasa aka yanka miki maimakon ki gode min".


Afirgice hajiya tace naman doki wato Amfala dama da kake cewa zaka sa a yanka min doki saida bakin hali yasa kasa aka yanka min din naci".


"Wayyo Allah na ina ganin kaddarorin ka yaron nan" ta fada hawaye na zuba".


Mazewa Amfal yay kamar gaske yace" koma me zaki ce nidai nasa an yanka miki kuma ba yadda zaki dani".


Cikin bori hajiya ta mike tana cewa i "idan ni ban isa dakai ba ai ubanka ya isa dakai bari naje na fada masa yadau matakin tunda kana neman kashe masa uwa ya kwata min yanci na".


Ganin da gaske fita take shirin yi yace dakata hajiya na miki tambaya irin wannan rudewa da kikai idan ma kinje zaice kin fara gigin tsufa ne gara ki hakura".

"Sannan gashi kina ta min asarar hawayen ki shin cin dokin harramun ne naga shima nama ne kamar ragon da aka yanka miki".


"Amfala nace ka tashi ka fice min daga nan ko saina sa an fitar dakai da karfi".


Dan zaro ido yay haba hajiya ni zaki sa a fidda ni da karfi kamar nazo office dinki neman taimako".

"To ki amsa min tambaya tasainatafi nace cin dokin haramun ne musamman a gurin ku tsofaffi yana kara lafiya da nisan kwana koba haka bane".


Hajiya data gama cika da haushi tace ban sani ba dan uban ka jeka tambayi Adama wato nice karamar dangar ka me dadin hallaka shiyasa duk wata bolar ka idan ka debo a kaina zaka juye ta".


Mikewa Abdul-jabbar yay ganin abin nasu bana kare bane gashi sun cika masa kai da hayaniya hanyar fita ya nufa yana cewa"


"hajiya ina miki barka da salla dan Allah ki rika gane halin Amfal dinki tunda ya saba kinsan ko baki da gata baza'a yanka miki doki ba naman rago kika ci ki kwantar da hankalin ki basai kin kai kara gurin Abba ba ".


Caraf Amfal ya cafe zancen da cewa bros me yasa ka tona min asiri daka barta ta kaini ramin gyare karewar kara kinsan shine ko bacci baya yi".


Hajiya tace bazan sake biye maka ba tunda ba tausayin tsufa na kake jiba kana sani kuka fita a nan karka sake zuwa guri na".


Mikewa Amfal yay yana cewa an gama hajiya ta gara nabi dan uwana dama duk fadin masarautar nan shi na sani ".


Da kallo hajiya ta bishi to ai da dadi tunda baka san da zaman Muhammadu da Adama ba suda suka haife ka balle mu yan gayyar sodi kakanni jeka can ka karata".


Ganin sun fita yasa da sauri Marakisiyya ta tashi zata bisu hajiya ta dakatar da ita" wa kike sunan naki ina kuma zaki je kina dan taya ni hira koma ki zaman ki ".


Cikin rashin jin dadi marakisiyya ta koma tana zama bata so haka ba itafa yanzu da babbar damara tazo masarautar nan ko ta halin kaka saita samu soyayyar Abdul-jabbar zata koma gida.


Amma zata gwada kamun kafa da hajiya ko zata dace.


Part din Ammy suka fara shiga yi mata barka da salla amma ko zama basuyi ba Amfal yace" Ammy cin doki haramun ne hajiya tace na tambaye ki"?.


Girgiza kai Abdul-jabbar yay yana wa Amfal kallon Allah ya shirye ka yasan a nan din ma soko zai mata sai kawai yace bari ya dawo ya fice daga part din".


Ammy tace waye ya tambaye ka"?.


"No ba kowa kawai yaune naga dokuna lutsa-lutsa shine na tambaye ki"?.


Sauke ajiyar zuciya Ammy tay Amfal meyasa kake gudu na baka zuwa inda nake nifa mahaifiyar kace baka da wacce ta fini duk duniya".


Kai Amfal ya jinjina kiyi hakuri Ammy yau ba gani nazo ba zanyita zuwa kullum daga yau zanyita miki naci har saikin gaji dani".


Murmushin farin ciki Ammy tay jin abinda yace tace" wallahi bazan taba

Please Login or Register in order to submit comment