Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kwana cikin shirin taryar sabuwar amaryar ki".



Kasa magana Ammy tay saboda bakin ciki sai kawai ta juya tana barin fadar tasa hankalinta inyai million ya tashi ko ganin gabanta batayi da yake bata cikin nutsuwar da zata iya magana a wannan lokacin kawai kwanciya tayi tare da kara fashewa da sabon kuka gaba daya ta rasa inda zata sa kanta hatta kwakwalwar kanta zafi take saboda daukar caji😢.


(Ayya Ammy sai hakuri fa mukan biki za musha mu gwangwaje💃💃).


Kome kuka ce?😝.


Wash😢 Allah fans typing akwai wuya😑 don haka gobe da jibi baza ku samu typing ba😝 zaku jini shiru zan huta sai ranar asabar in Allah ya bamu aron rai nagode yan whattpad ina yinku sosai ana tare👫💞.



Mrs Al'ameen Ahmad ce,👌.
👍 Taku har a kullum,
😘🙈We will meet again
🤗 Tnk for your support.


ONE☝ LOVE💝
YUSRAH MUSA ABUBAKAR CE..



BARKAN MU DA RANAR ASABAR YAN UWA FATAN KOWA YANA LAFIYA CIKIN FARIN CIKI DA KYAKKYAWAN YANAYI KAMAR YADDA NA MUKU ALKAWARI CEWA TYPING SAI RANAR ASABAR ALLAH YA KAWO MU SAI KU MATSO KUSA MU DORA INDA MUKA TSAYA DAN GANI NAZO KU FITO MU CASHE💃 YAU RANAR TAKU CE FANS WANNAN PAGE DIN NAKU NE MALLAKIN KUNE NA BADA SHI DUKA GARE KU KUN CANCANCI JINJINA👍 DA HANNU DUBU😝.



🌌💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION🌌💫
(🏡home of hospitality🤗 and harmony👌).



📝YUSRAH MUSA ABUBAKAR


DEDICATED TO
MY MOTHER I LOVE YOU MAY ALLAH ACCEPT YOUR DU'AS AMEEN MAMANA💞.



#YUSRAHMS#
NO.37👉 38
Hajiya Binta na zaune mk dake gefenta ta kalla tana cewa "bikin Salmah saura wata daya jiya dadin ku kafin ya tafi ya sameni akan na fada maka kafin lokacin bikin ka samo matar aure sai a hada ayi tare na isar da sakon sa yanzu ya rage naka kasan dai halinsa baisai na sake fada maka ba".


Cikin wani irin yanayi mk yace"haba mum aure kuma nida ban shirya yi a kwana kusa ba taya cikin wata zan nemo matar dazan aura please na roke ki idan ya dawo kice masa ba yanzu zanyi ba yadan karamin lokaci".

Wani kallo hajiya ta masa"Allah ko baba to baka isaba ni kaina na gaji da ganinka haka dandai ba yarda na iyane amma ga waraka tazo mk koba kaso dole ka nemo macen aure a wata dayan nan".

Hade rai yay"nidai dan Allah mum ku kara min lokaci zan samo ba yanzu ba".


"To ai ni kuma na dade da gano maka wacce ya kamata ka aura".


Mk da duk yaji hankalinsa ya tashi yace" wa kenan mum"? .

"Abidah mana mk ga mace a gida meye saika fita waje ka auro nice da kaina nayi tunanin hakan naga kuma ya dace mu hada zumunci mu kara karfafa shi".

A firgice mk yake kallon hajiya Binta muryarsa harta sauya yace"Abidah fa kika ce mum? wai Abidah dai dana sani ta gidan nan ko kuma wata ce dabam a wani wurin"?.
Dan harararsa hajiya tay"ji wani sokon banza Abidah tanan mana nake nufi 'yar gidan kawun ka 'Dayyabu zaka wani fuske kace wata ce dabam".

Kai ya soma girgizawa"haba mum me zanyi da Abidah gaskiya batai min ba bata cikin tsarin kalar matan da nake son aura ki janye maganar nan mum hakan ba mai yiwuwa bane niba sa'anta bane".


"Bazan janye ba mk inji ubanwa kaiba sa'anta bane meka fita fada min naji kaga fa banson shashancin banza".

"Kiyi hakuri mum amma bana sonta dan Allah ki fahimta".
"Bazan fahimta ba ni Abidah nake so ka aura idan kanada ra'ayi ko gaba kaga wacce kake so saika aura ban hana kaba"tana fadin haka ta mike zata bar gurin cikin magiya mk yace"ki saurari hanzari na wacce nake so ita kadai ce bata da sa'a tafi karfin zama da kishiya kuma gidana na ita kadai ce maishi banyi don nasa mata biyu ba saboda gudun hayaniya".


Ba tare da hajiya Binta ta juyo ba tace" 'yar gidan uban waye ita data fi karfin zama da kishiya waye ubanta a ina take"? shiru mk yay ya kasa magana don yadda hajiya ta hauro kila idan tsautsayi yasa ya budi baki yace Safah ce may be ya jawo silar barin ta gidan shi kuma hakan ne baya so.

Tsaki hajiya taja jin yayi shiru tace"maganar banza ma kenan kaika sani saika fara shirye shirye tun yanzu kayo lefe basai lokaci ya kure ba"gaba tai ta barshi a gurin cikin wani kalar bacin rai.

Fitowa Abidah dake labe tayi tana dariya ta soma taka rawa a gaban sa tana cewa"gaskiya naji dadin wannan al'amari ya mk nan da wata na zama matarka kamar yadda nake mafarki kullum ashe dai tabarya zatai rana kai kuma ka zama turmi dama na fada maka bazan barka ka auri wata bani ba kuma dole ka koyi sona ka zauna dani iya raida mutuwa danna zame maka karfen kafa mai wuyar cirewa ni kujera ce dole ka zauna dani"ta karasa maganar tana sakin gud'a wacce ta sake tunzura mk a fusace ya mike ba tare data lura ba ta rike hanci tana faman 'kara kamar wata gyare😂.

Ji tayi ya damki hannunta ya soma tafiya da ita ko damuwa batai ba dan tasan koma me zaiyi mata dole shine mai auren ta har part dinsa sukaje sakar mata hannu yay yana shiga bedroom zuwa jumawa ya fito rike da bel damkar ta yay cikin son huce haushin sa ya soma shimfida mata a jikinta ihu ta kurma tana bashi hakuri yay banza da ita saida ya zaneta tas sannan ya bude kofa yana turo ta waje ya mayar ya rufe.


Cikin kuka ta daga murya tana kallon kofar tace" Allah ya isa azzalumi kuma hakan bazai hana na fadi abinda nay niyya ba dole kaso ni kuma ka aure ni bayan taimakon ka zanyi ganyar tsiya katon tuzuru kawai mai kwana rungume da filo"tana fadin haka da gudu tabar gurin saboda tsoron karya fito ya kama ta tasan saiya kusa kashe ta.



Zaune suke a daki ranar da maryama ta dawo daga yola cikin damuwa Safah ta kalle ta tana cewa" waini baba sai yaushe zan tafi gida ne? ina so naje naga baffana dasu malam da Hadiza Allah zaman nan din ya ishe ni".

Dariya baba maryam tay"kai Safah mene abin gajiya kuma dama nasan dole zaki kewar su wata biyar ba wasa ba amma ki kara hakuri so nake sai anyi bikin Salmah da Mk sai muje na raka ki kasuwa ki sayowa Baffanki d'an abin arziki ki kai masa dasu Hadizan kema kya sayi wasu yan abubuwan na aurenki da kudin aikin ki kamar kuloli da sauran su kinji ki 'kara hakuri saura yan kwanaki".


Kai Safah ta daga cikin jin dadin lissafin da baba maryam ta mata tace"to Allah yakai mu baba nagode" murmushi baba maryam tay"yauwa ko kefa kin kusa ganin Baffa kwantar da hankali".

* * *
«»«»«» »«»«»« «»«»«»

Kamar yadda Emir ya fadawa Ammy cewa zuwa sati amarya zata sauka hakan ne ya faru ankawo ta lafiya kuma part dinta yana kusa da part din Ammy a ranar dai Ammy ko iya runtsawa batayi ba tayi kuka tayi bakin ciki har bazai misaltu ba babban abinda yake daga mata hankali kuma yake bata tsoro taga amaryar ba wata babba bace dan batafi kanwarta ta biyu ba abin firgicin anan shine karfa nan da wani lokaci ta ganta da ciki ace itama zata haihu kila ba haihuwa daya bama yayanta suzo suyi yawa itama ya zama ta samu abin kirki a dukiyar sarki saidai ta dawo gefe ta zuba ido tay kallo wata banza tazo sama takai ta fita morewa ita data zauna dashi tsawon shekaru.



Ammy dake zaune idonta a rufe tana wannan maganar a zuciyarta a firgice ta bude idonta gani take kamar har hakan ta faru muryarta har wani sauti take bayarwa mai amo cikin takaici tace" inaaanh karya ne wallahi ni za'a wulakanta hakan bamai yiwuwa bane bazan taba barinki haihu ba saidai koni koke idan ba neman a tozartani a idanun bayi ba meye da girmana za'ai min kishiya bazan taba yarda da wannan ba".



Shiru tay tana huci daidai shigowar Hanne bayan ta gaishe da ita tun ba tace komai ba Ammy ta dube ta tana cewa"daga ina kike tun dazu ina jiranki"?.


Gyara zama Hanne tay tana cewa"ki hakuri ranki ya dade sako ne ya iske mu daga mai martaba cewa yana bukatar dani da jakadiya da Gambo sannan da bayi masu take baya muje mu raka masa amaryarsa fadarsa amma ki gafarce ni tuba nake".


Wani irin dafe kai Ammy tay jin hajijiya na diban ta da sauri ta nemi kujera ta zauna numfashinta na neman toshewa jin abinda Hanne ke cewa".


Ta dauki dogon lokaci a haka kafin daga baya ta sauke zazzafar ajiyar zuciya tana kallon Hanne tace"dole zama bai kama kiba idan na bari na zuba ido na saki baki inaji ina gani mai martaba zaimin nisa don haka ina so yanzu ki shirya kibar masarautar nan zama bai kama kiba ki tafi gurin malam ki masa bayani cewa ya raba sosayyar dake tsakanin sarki da wannan mayyar matar idan ta kama harda kisa ne yayi indai burina zai cika ban damu ba komai ma ayi zan baki kudade masu yawa don yaji dadin yimin aiki mai kyau tashi kije ki shirya saiki dawo".


"To ranki ya dade yanzu kuwa wannan abin bakin cikin har ina? barina dauko gyalena don babu wani shiri sai hankali yana kwance ake komai sauri zanyi na dauko" .

Fita Hanne tay tabar Ammy ta kasa zaune ta kasa tsaye tana cikin haka sanarwa tazo mata daga wata baiwa mai mata hidima cewa sarki na kiran ta.


cikin burkicewa bako shiri ta fita dama abinda take nema ne ya samu saboda saurin da take masu mata rakiya gudu gudu suke suna mamakin yau meya samu Ammyn ganin da sukai a hargitse take saidai baza'ace komai ba kishi yana saka mutum yayi fiye da hakama.



Kamar an jefata akai haka ta fada musu suna zaune suna zance Emir harda dariyarsa data dade bata gani yayi irinta ba cikin takaici take kallon duk su biyun ga wani kishi dake taso mata ji take zuciyarta na tunzurata ta fadawa amaryar nan da duka ta ru'kur'kusheta🙊😁 ko ciwon dake damunta zai kauce.


Kasa zama tay har saida Emir ya mata magana sannan ta zauna da 'kyar kamar me ciwon cinya sai cika take tana batsewa Emir yana lure da ita amma bai tanka mata ba yasan yanzu kishi ne yake ruda ta idan ta huce shikenan.


Ammy dake kallon matar tun dazu aranta tace" humm zaki bayani muje zuwa da kafafun ki saikin gudu daga gidan nan babu wacce ta isa a yanzu nay hadan miji da ita ki jira na baki wata daya a kinyi zama mai nisa a gidan nan domin lahira zatai bakuw,..............




Katse mata tunani Emir yayi ganin kallon kurullar yayi yawa yace"am Adama ga amaryata matata Fatima Zarah nasan jiya sunbi ta gurin ki da ita kuma sun baki amanar ta rokona don Allah ayi zaman lafiya da gaskiya dukkanin ku daya ne a gurina kowa auren ta nake bana jin cewa daya tafi daya ina son ku hade kanku kinga kece babba kada wata matsala ta taso daga gareki inayi muku fatan alkhari".




Ba zato Ammy tayi ta maimaita Fatima Fatima Fatima wanda da alama batasan tayi hakan ba sunan mahaifiyar Abdul-jabbar fa kenan a firgice ta kuma kallonta tana cewa"Fatima dai Fatima"?.


Kai Emir ya jinjina "kwarai Fatima sunan ta kinga ikon Allah ko? Ya dawo min da Fatima na dana rasa yanzu itace zata maye min gurbinta sannan kuma ta zama mahaifiya ga Abdul-jabbar ta rika debe masa kewa nayi matukar farin ciki sosai da samun ta kodan d'ana daya kasance cikin maraici baisan dadin uwa ba yanzu zaiji abinda kowanne mai uwa yake ji fatan kin gane"?.




Mai da kallon shi yayi kan amaryar yana cewa"Fatima ga mata ta Adama kuma mahaifiya a wajen d'ana Amfal".


Murmushi Fatima tay tana kallon Ammy tace"barka da kwana uwar gidan mai martaba fatan na sameki lafiya? jiya ban samu mun gaisa ba anata hayaniya".



Ammy datay wiki wiki ta daskare waje daya ta kasa magana saboda gani take kamar mahaifiyar Abdul-jabbar ce ta dawo da gaske,.

Dan saita nutsuwar ta tayi cikin ya'ke tace"lafiya ya kike"? da'kyar ta karasa maganar tana maida hawayenta.


Fatima da har lokacin fuskarta da annuri tace"Lafiya alhamdllh".



Ganin Emir na shirin magana ita kuma ta gaji da takaicin da take kwasa ta riga ta gama kulewa tazo wuya saitay saurin tarar numfashin sa da fadin" ranka ya dade bari naje ana jirana ka huta lafiya"tun baiyi magana ba kamar guguwa na diban ta tafice binta yay da kallo tare da girgiza kai duk yana hankalce da ita kawai basarwa yayi tunda ga bakuwa a gurin bai kamata yayi wata magana data danganci abinda ya shafi 'barakarsu ba kodan gudun jawo fitinar abinda zai faru a gaba".


Ammy na shiga part dinta ta tarar da Hanne zaune tana jiran ta dora hannuta tay aka🙆 ta zunduma wani uban ihu tana cewa" na shiga uku na lalace Hanne shikenan tawa tazo karshe Fatima ta dawo kodai dama rufe min akai ba mutuwa tay ba"?.


Hanne data gama firgita jin maganar da Ammy take wacce hankali bazai dauka ba tace" ranki ya dade kamarya ganin ta kikayi ko kuma fada miki akai naga dai wanda ya mutu ya tafi kenan taya ta dawo to"🤔?.


Ammy data rasa inda zata sa kanta tace" ni kaina bani da tabbacin hakan amma gashi nan mai martaba yana cewa shikenan Abdul-jabbar ya samu gurbin uwa shima saiya daina maraici kuma kice min Fatima bata dawo ba"?.

Hanne data fahimci ammy bata cikin nutsuwar ta ganin amaryar mai martaba da tay kwakwalwarta ta hargitse yasa tace" ranki ya dade kodai a rude kike kallon tsoro ki kaiwa amaryar mai martaba amma babu hadin hanyar mota data jirgi wannan Fatiman dabam haka wacce ta mutu ma dabam ki kwantar da hankalin ki mubi abin a sannu babu ko dangantaka tsakanin su".


Sauke ajiyar zuciya Ammy tay tana kallon Hanne tace"to yanzu yaya za'ai maganar zuwa gurin malamin ke nake saurara wacce hanya ya kamata mubi wanne mataki zan dauka"?.

Hanne a ranta tace" tabdijan ana wata ga wata wa zaki zura a rijiya gaba dubu naji kina cewa wacce hanya zamubi zaki bidai ni meye nawa a ciki meya kaini shiga cikin wannan cakwakiyar babu ruwan 'yar Idi da jefa kanta a fitina tazo ta kwabe dani ke matarsa ce zai iyayi miki afuwa idan yasan gaskiya kodan darajar aure da d'an dake tsakanin ku ni kuwa asuwa mai ido ba d'an ciki wannan fadan kune na cikin gida babu abinda yay min zafi zan tsoma kaina abinda bai shafe niba asiri ya tonu ki barni dajan ido".


Cikin tsawa Ammy tace" wannan wanne irin shashancin banza da wofi kika tsira Hanne kullum sai muna cikin magana ki kama wani sokon tunani ki rabu dani".


Jiki na rawa Hanne tace" kiyi hakuri dama shirun da kika ga nayi ina tunanin gurin malamin daya kamata naje ne".

"Ok yayi kyau to tuno ina sauraron ki".



Cikin salon da Ammy baza ta ramfo taba tace" ai ranki ya dade na gama tunani zanje wajen malamin da kawai zai kashe ta idan kina da bukatar hakan amma me kika ce ya shugaba ta".


Kai Ammy ta girgiza" a'a Hanne na fasa kasheta yanzu so nake ni da ita mu goga a haka batare da aikin malami ba da kissa ta zanyi amfani na 'kwace fada gurin mai martaba ya zama ni kadai yake gani a gaban sa".


Cikin sauri Hanne tace"eh ranki ya dade hakama za'ai wannan shawarar tayi hanya mafi sauki itace tabi wacce kuma zata bulle tanan kadai zaki mata zarra ki bata tazara ta gane kedin bata yau bace kin zarcewa tunanin ta kisa ta raina kanta a duk lokacin da kuke gabansa bazai kalle taba ke yake duba hankalinsa yana gare ki".

Cikin jin dan sassauci daga damuwar dake damunta ta dan ragu yasa ta kalli hanne tana cewa"Shikenan Hanne tashi kije zan jarraba wannan shawarar da kika bani saina sake neman ki idan naga tsarin dazan dauka akwai nasara da riba a cikin tafiyar".


Mikewa Hanne tay tana cewa" to ranki ya dade ki huta lafiya" tana fadin haka ta fice cikin jin dadin wata rana zata zame kanta daga jikin Ammy kafin komai ya baiyana.




MRS AL'AMEEN AHMAD CE👌.
()(*)() ()(*)() ()(*)()


GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GARE KI KANWATA SARATU YAKUBU FATAN RAHMAR ALLAH DA GAFARAR SA A GARE KI.


YUSRAH MS ABUBAKAR.
☝💝🍇🍉🍒🌹🍍🍑🌻🌼



TYPING📲
SATURDAY 08:03am 04/March/2023


🍇
🍇 SAFREEYYAH🍇
🍇




💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
(🏡home of hospitality🤗 & harmony✨)



STORY AND WRITTEN
📝Mrs Al'ameen Ahmad ce



WANNAN PAGE DIN NAKU NE 'YA'YA NA ALLAH YA RAYA MANA KU ABISA TAFARKIN MANZON ALLAH(S A W)🙏 AMEEN.
Aishat Mahraz
Auwal Mahraz
Hauwa Ahmad
Aishat Ahmad
Walida Abubakar
Jamil Ahmad
Muhammad Naseer
Fatima Sadauki
Adali Gali
Amatu Gali.




#YUSRAHMS#
NO.39👉 40
Kwanaki nata tafiya har bikin su mk yazo anyi abubuwan kece raini sosai hajiya ta barnatar da kudi naban mamaki domin ba karya naira akwaita kamar kasa.

Abidah kuwa tun ranar da mk ya daketa tsoron zagin datai masa yasa washe gari tana jin yadau mota ya fita agurguje tai wanka ta shirya ta gudu gida bata dawo ba sai ana gobe dinner taji haushi ganin har lokacin Safah na gidan batay tunanin zata dawo ta sameta ba ta dauka ta ware 'kauyen su amma bari a gama bikin nan saita fadawa hajiya ita mk yake so akan ta yake wulakanta ta.


Washe gari tun safe ake shirin dinner har lokaci yay amma babu mk babu alamarsa Abidah ta kira wayarsa sakamakon angon Salmah yazo tun dazu suka wuce cikin damuwa harta soma bata kwalliyarta taje gurin hajiya.


Cikin kuka tace" mum kinga mk har yanzu baizo mun tafi ba Salmah nasan sun dade da zuwa nakira wayarsa yaki daga min dan Allah ki gwada kozan samu ya daga idan yaga kece".

Cikin bacin rai hajiya tace"kaji min iskancin banza to gidan uban wa ya tafi tun safe? Mk yana bata min rai da rashin jin maganar sa kinga daina bata kwalliyar ki bari na kira shi yanzu zaizo ku tafi".


Ta karasa maganar tana danna masa kira ta shiga amma bai daga ba harta katse kara sa masa wani kiran tay.

Mk na gidan sa rungume da seeker sunata aikata barna yana jin kiran yaki ko kallon wayar Seeker ce ta gaji tace" darling ana ta kiran ka please ka daga mana bakasan waye ba koda wata matsala ne".


Basar da ita yay kamar baiji ba har wayar ta katse saida aka sake kira kamar baya so duk da yaga me kiran kuma yasan akan me ta kirashi.

Yana dagawa maganar hajiya ce ta doki kunnen shi" kwarai mk yayi maka kyau ka tozartani ka nuna ban isa dakai ba a idon duniya yanzu dan ka wulakanta Abidah kowa yasan matar cushe ce kai haka? to amma ka sani ba ita ka wulakanta ba ni mahaifiyarka ka kunyata amma babu damuwa kayi duk abinda kaga dama lokacin kane"katse kiran tay tabar mk rike da waya yana kallo ya kasa magana.


Murmushi Seeker tay tana dafa shi tace" sorry dear muje na shirya ka kada lokaci ya kure ni ina nan kaje ka dawo" mikewa mk yay tare da kiran Abidah muryar sa da fushi yace" ke wacce irin dabba ce wato ni zaki hada da mum dina ko? zaki gane kuren ki zan cire duk wani gigi da yake damun ki kuma bazan biyo tanan ba idan kinga dama mu hadu acan" cilli yay da wayar ko kashewa baiyi ba ya wuce toilet yayin da seeker tabi bayan shi.


'Yan dinner kam da basu san wainar da ake toyawa ba ganin kowa daban yazo sai mamaki ya kama su ko yanzu haka salon ya koma amarya tazo da kawayen ta ango ma yazo da abokanan sa babu wani nishadi😝.


Tunda mk ya zauna hankalinsa kekan Safah wacce tasha kwalliya kamar ba ita ba tana zaune tare da Alawiyyah sai dariya suke suna tafawa.

Kasa dauke idanunshi yay akan ta aranshi kuma fadi yake" haba big girl taya mazan barki ki auri wani bayan sonki ya zame min ciwo bazan iya rayuwa ba idan babu ke kece macen da kika dace da tsari na kuma nake sonki da dukkan zuciyata".


'Dan rufe ido yai cikin wani yanayi na shauki kamar kuma an tsikare shi ya bude idnosa maimakon ya sauke idon akan ta saiya sauke kan wani dake zaune kusa da kujerar ta da alama magana yake mata ita kuma tana shareshi mk jiyay jikinsa ya fara jijjiga kishin sa ya matso kusa mikewa yay yana nufar inda suke.


Daidai ya karasa Safah da bata ma lura dashi ba ta mike zata sauya guri shi kuma mutumin ya rike mata gefen maya fi wohoho! Ai kamar an watsawa mk ruwan zafi a jikinsa haka ya zabura yana daka wani tsalle sai gashi ya dira a gun ba wata wata ko jira ayi magana ya fidda hannu ya dauke mutumin da mari kafin ya dago ya kara masa a daya 'barin fuskar.


Cikin tsawa yace" sa'arka ce? ko tayi maka kama da irin yan iskan matan nan da zaka ja mata gyale dan uban waye kai? me ka taka saika fada min yau nace dan uban waye kai" ya karasa maganar yana damko wuyan rigar mutumin kowa a gurin rufe baki yay yana kallonsu yayin da Abidah ta lelayo ashar mai ruwa ta saki ganin akan wacce mk yake fadan.



Da gudu Salmah ta karaso tana cewa" haba ya musaddiq ba girman ka bane kaifa abokin mijina ne amma ka shake masa wuya haka kayi hakuri abinda yay mata bai kyauta ba kuskure ne".


"kuskuren uwar wa? dan yana abokin mijinki sai yazo yana ja mata mayafi shi dan iskan ina ne? baisan darajar mace ba sai uwars...


Rufe masa baki Salmah tay cikin jin kunya tace" ya musaddiq ka bari mana dan Allah".


Tsaki mk yaja mai karfi wanda yasa Salmah matsawa baya da sauri kafin ya juya yana fita a hall din a fusace Salmah batay tunanin don mk nason Safah ne yay haka ba ta dauka kawai ya kare mata mutunci ne sabanin Abidah da tasan komai kuka kawai ta kama ganin ya tafi babu abinda akai ga cake data sa akai musu da sunan su a jiki ta kashe kudi sosai kuma gashi ya tashi a banza wanda tay domin sa ko gani baiyi ba.



Har suka dawo gida Abidah na kuka cewa tay saita fadawa hajiya komai Salmah ce ta hana ta.


Washe gari aka daura aure wanda mk yaji tamkar da gaske igiya akasa aka daure shi saboda takaici dare nayi kuwa kowacce amarya akai hanyar gidan mijinta da ita babu wanda yakai Abidah zumudi yau zata kwana gidan mk matsayin matar sa.



A gaijye Safah ta shigo bangaren su bayan sun dawo daga rakiyar Salmah ganin baba maryam zaune tana shirya kaya tana gyara su yasa Safah tay tunanin ko shirin tafiya take musu.


Cikin farin ciki ta zauna tana cewa"baba maryam naga kina ta shirya kaya ko gobe zamu tafi nima na kwana a shirye? don sassafe zamu daga basai rana tayi ba don muje dawuri".

Dariya baba maryam tay tana kallonta tace" in banda abinki Safah mene na gaggawa kawai daga kare biki yau ko ba'ki basu tafi munyi gyare gyaren gida ba saimu tafi? Idan kikai hakuri bazaki sake sati a gidan nan ba bayan idan kin tafi ma ba dawowa zaki ba".


'Dan yatsina fuska tay"umh mezai dawo dani kam gara aure na ya fiye min Allah yasa murtalan ma yanzu ya kara tsayi wani gajere daf da kasa ma dashi wallhi ni nafi son dogon namiji ba irin sa ba kamar tuntube".


Rike baki

Please Login or Register in order to submit comment