Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saiki rungumi sorry kije kici gaba da zaman jinya garin kwadayi kin haifar da fitina tirrr.


Wani tsalle marwa tay a fusace zata shaki wuyan Seeya Samha ta tare ta tana riketa.

Cikin karaji marwa tace sakeni Samha wallhi yau ba wanda ya isa hanani cin uwar data haifi Seeya a gidan nan koda hajiya ce.


Kokarin kwacewa take da sauri Samha ta sake riketa tana cewa haba marwa kamar bake ba zakisa nakasa dake su raina ki wannan yarinyar tun washe gari hajiya tazo ta dauke ta babu wanda yasan inda take a yanzu ko gurin data kaita.


"Seeya kuma mahaukaciya ce ki daina biye mata ga alhaji can yana neman ki".


Jan ta Samha tay suka bar wajen tana sakarwa Seeya wata muguwar harara.

Tabe baki Seeya tay tana cewa kanki akeji ni nayi gaba na zama ciwon ido a gurinku nan gani nan bari abincin mayya.



Kamar yadda baffa yay alkawarin auren mariya anyi kuma yayi kokari wajen ganin cewa ya danne duk wata damuwar shi itama mariyan data fahimci hakan tana iya bakin kokarinta danta debe masa kewa.


Lokacin da Asabe taji baffa ya auri mariya hankalinta yay mugun tashi domin kawarta ce gashi auren harya mika wata biyu amma taga yayi burus da lamarinta ya manta da shafinta.

Bayan sallar ishsha hannunta aka ta bazama gidan malam na Allah da kukan ta suna zaune da Hadiza ta shiga tana durkusawa a gaban su.


Na Allah na ganinta yasan meya kawota amma saiya sake tuntubar ta yaji.

Subahanallahi Aishatu lafiya irin wannan kuka haka kamar anyi mutuwa meke damunki ko wani abune yake faruwa a bangaren naku"?.


Cikin kuka Asabe tace kaitona malam meye mabai faru ba magana ce akan malam Abubakar ka sake bashi hakuri dan inaga ya manta dani a rayuwarsa wallahi nayi nadama ko yanzu ya mayar dani na horu bayan auren kawata dayay dan Allah malam ka taimaka min kaine kadai zaka fada masa yaji Abubakar akwai saukin hali laifina ne.


Kai na Allah ya jinjina shikenan Aishatu zan masa magana kije kiyi shirin komawa gidansa yau muna litinin idan Allah ya nuna mana ranar juma'a za'a mayar da aurenku".


Cikin farin ciki Asabe tay godiya tana mikewa ta tafi koba komai zuwanta yayi amfani.


Zaune Zarisha da Safah suke karkashin wata bishiya me kyau gaske suna hira cikin nishadi sukaji ance.

Zarisha dama ke nake nema kidan ban lokacinki muyi magana ta fahimta dan Allah.


Duk juyawa sukai suna kallon gurin da akai maganar wani saurayi ne tsaye kusa dasu.

A fusace Zarisha ta mike zata bar gurin da sauri yasha gabanta ranta a bace tace" meye haka Safwan wai dan Allah na tambaye ka shin ana soyayya dole gaba daya kabi ka addabe ni ina zamana lafiya ka rabu dani kona hada ka da baban ku.


Dan murmushin so hana ganin laifi yay yana cewa shikenan Zarisha zan rabu dake amma dan Allah kice kina sona wallahi da gaske xuciyata kece take so".


Tsaki Zarisha tay tana wucewa tace har abada bazaka samu ba".


Binta yay da kallon tare da dafe kanshi cikin tarin damuwar kasa fahimtarsa da Zarisha tay lallai ya fada tsananin sonta me girma wanda yake jin tsoron abinda zai faru dashi nan gaba in bata amince masa ba gashi bashi kadai ke sonta ba yaji labari harda muzammil ga Sa'id.


Cikin tausayawa Safah dake kallonshi tace kayi hakuri zan taimake ka zanyi magana da ita zata fahimce ka".


Murmushin karfin hali Safwan yay yana cewa sonta cuta ne a gare ni amma na yarda komai da lokacin sa zandau hakuri na gode sister".


Yana kaiwa nan yay gaba cikin mamaki Safah ta zuba masa ido domin yauce rana ta farko da wani ya budi baki ya kirata da yar uwar shi kuma sai taji dadin hakan.


Itama barin gurin tay domin taje ta samu Zarisha tana tafe fuskarta da dan annuri wanda rabon da taji farin ciki a zuciyarta harta manta.


A daki ta samu Zarisha tayi ta gumi tana kallon waje daya zama kusa da ita tay tana janye mata tagumin tace"

haba Zarisha kamar ba wayayyiya ba gaskiya ki canza meye laifin wannan gayen gashi yanzu kinsa shi a damuwa please ki tsaya ki fahimce shi ba kinsan iyayensa ba"?.


Sauke ajiyar zuciya Zarisha tay tana kallon Safah tace kema baki fahimci abinda yake cikin raina bako bana sonsa ne shiyasa bazan iya bashi lokaci na yaga kamar na yaudare shi".


To amma Zarisha kinsan dole baza kici gaba da zama haka ba zaki aure me yasa baza ki amince masa".


Kai Zarisha ta girgiza bana sonsa ne Safah ki daina min maganar sa kar hawan jini ya kama ni".


Dariya Safah tay Allah ya sauwake wata rana zakiji kina sonshi kuma nina fada miki wannan.


Cikin son abar maganar Zarisha tace na yarda dake hakan na iya faruwa amma yanzu muci abinci tukuna saimu dora a inda muka tsaya.


Cooler ta buda tana dauko musu tuwon shinkafa ga hadaddiyar miyar ganye ta saka musu a plate suka fara ci kafin jakadiya ta shigo dan tana can bangaren sarki yau yayi ba'ki tana musu hidima.

#Comment
#Safreeyyah


YUSRAH MUSA ABUBAKAR GIMBA
(Mrs Al'ameen Ahmad ce).


Monday's night: 08:30pm
5 ramadan (1444 hijri) we love our nabeey and peace be upon him Ameen.


#YUSRAHMS#
NO.65👉 66
Su Basira na goge goge Ammy ta fito daga bedroom zama tay bayan sun gaishe da ita ta kallesu tana cewa" ina wannan mara kunyar yarinyar take a wanne wajen take aiki .


Dan kallon juna sukai cikin tsoro sukace "ranki ya dade tana bangaren amaryar me martaba acan yanzu take aiki".


Wani irin zaro ido waje tay wanda yasa jikinsu ya fara rawa mikewa tay tana cewa meee? uban wa ya mayar da ita candin wake da wannan zarrar"?.


Jikinsu narawa muryarsu ma haka suka ce wallahi ranki ya dade bamu sani ba".


Fuuuu kamar iska na ingiza ta tafice sauke ajiyar zuciya Basira tay tana cewa tab yauda yaki a part din amaryar sarki dama inada iko da naje nayi kallo.


Dariya Zakiya tay yanzu ma wa ya hanaki zaki iya musu laben kofa.

Zaro ido Basira tay ke rufa min asiri kar ajimu kila muma an labe mana bamu saniba.

Kallon kofa sukai ganin arufe yasa Basira nufar gurin kayan marmarin dake aje gefe tana cewa Zakiya yau muna da shagali walahi saina debo mana kamar nasan haka zata faru nayo mana guzirin leda".


Dukawa tay ta kwashi san ranta sannan ta mike tana kallon Zakiyya tace muje ba jira kafin hamagon ta dawo ana can ana fama.


Fita sukai da sauri suna waige waige ko wani na ganinsu da suka ga ba kowa da gudu suka fita a bangaren.

TOFA AMMY TA SAMU BERAYE🐀🐁 A PART DINTA".


Fatima na zaune tana waya da gidansu ganin yadda Ammy ta shiga a hargitse yasa ta sauke wayar tana mata kallon mamaki da kuma yau me zatace ta mata.


,Ganin Ammyn tay shiru gashi ta zuba mata ido kuma batay magana ba yasa tace" sannu da zuwa uwar gidan me martaba giwar mata bismillah zauna mana".


Dukkan girman idonta Ammy ta bude muryarta a kausashe tace" ke uwar shishshigi ina baiwa ta".


"Tofa wacce irin baiwa kuma kike tambaya kenan"?.


Bacin raine sosai a fuskar Ammy tace "au dan kin raina min hankali ma tambaya ta kike wacce ita kira bayin part dinki zan ganta indai tana nan".



Babu musu tay kiran kowa dukkan su suka taru daya bayan daya Ammy ke binsu da kallo acan karshe idonta ya sauka kan Safah dake zance kasa kasa da Zarisha.


Cikin tsawa tace" ke uban wa ya kawo ki part dinnan bada izni na ba yau saikin yabawa aya zakinta kafin na kirga uku ki bace min da gani a palon nan".


A firgice Safah ta mike domin tasan kaf cikin taron da ita take idonta harya kawo hawaye.


Kallon Ammy Fatima tay tana cewa" oh dama wannan yarinyar kike nufi aiko baki isaba yanzu kam ina tunanin ta fita daga sahun ki".


Wani irin kallo Ammy ta mata" kinsan da kudina na sayeta ba baiwar cikin gida bace balle kice dan haka dole ki bani ita ko bakya so".


Kai Fatima ta jinjina tace" shikenan na fahimceki nawa kika sayeta fada min saina fanshe ta".


Ammy data gama cika tace" bana bukatar wasu banzayen kudinki kawai ita nake bukata ba fatara ce ta kama niba".


Fatima da mamaki ya gama cikata jinwai sayenta tay tace" tunda bata sayarwa bace kinga ta zama baiwar gida dan haka zaki tashi baki da tsuntsu baki da tarko domiin wallahi duk abinda zaki bazan baki yarinyar nan ba ta riga ta fita daga hannunki kuma har abada kisa a ranki".


Tab kamar ta watsawa Ammy wuta tay kan dinning tana tarwatsa kayan gurin a hargitse tace" wallahi karya kike dole kiban yarinyar nan.


"Aiko baki isa ba tawa ce kuma zaki gani".


Hanya fita Ammy ta nufa tana cewa" zaki nadama saina mayar dake abar tausayi a masarautar nan".

Da kallo Fatima ta bita dariya na cinta tace" karyar banza mace kin girma amma har yanzu ba tunani zan gyara miki zama".


Sati biyu da komawar Asabe gidan baffa amma sakamakon yanzu labari ya sauya ba ita kadai bace tana da kishiya kuma gwanar sai duk zaman gidan baya mata dadi.


Zaune take kan kujera ta kalli gabas ta kalli yamma ta zuba uban tagumi gashi an kusa shan ruwa duk abin duniya ya dame ta.


Mariya ce ke kai komo a gindin murhu tana shirya kayan sayarwarta domin har sana'o'in da Asabe take yi mariya ta karbe guri.


Kwalla kira mariya keyi" Azima kina ina ne fito mana tunda yau ba azumi kike ba kar muyi kwashe".


Da sauri wata yar budurwa ta fito tana cewa to baba dakin kira almajiran sun kaimin kayan bana huta ba".


Mariya da hankalin ta ke kan dama kunun tsamiya tace kira su mana yanzu saina gama sannan zan kirasu haba Azima".


Fita Azima tay yayin da mariya ta mike tana kallon Asabe tace kawar arziki kawo kofin kunu da kwanan abinci ki kawo na masoyina ma tunda yau a dakin ki yake".


Cikin takaici Asabe ta mike jiki ba kwari tana shiga daki ta debo kwanukan takai mata.


Daidai baffa ya shigo da bakaken leda biyu a hannunsa maimakon Asabe ta tare shi da sauri mariya ta mike ta na nufar sa tace.


Allah sarki masoyina ina ka shiga ne tun dazu sai tunanin ka nake sannu da kokari kawo na rage maka kaya bana so kana wahala musamman a wannan lokacin na kishi ruwa".


Ta fada tana karbar ledojin hannun nasa tabarmar da Asabe ta dauko zata shimfida da gudun mariya ta dauko ta na shimfida masa tana cewa" zauna malam bari a kawo maka abinci".


Abincin ta dauko da ruwa tana aje masa daga shi har Asaben sororo sukai suna binta da kallo.


Ledar daya ta ajiyewa Asabe ta hannunta kuma ta dauko karamin faranti juye abinda ke ciki tay kayan marmari ne an yanyanka ya sayo musu.


Zama tay tana bashi a baki domin an kira sallah baffa da mamaki ya gama cika shi yace" sannu mariya Allah ya miki albarka tashi kije kema kisha ruwan na gode da kulawa".


Murmushi mariya tay cikin jin dadi tace" ba komai masoyi ai dama abinda ya kawo ni danna kyautata maka na kuma debe ma kewa wannan hakki na ne".


Asabe ta kalla datay tsaye ta kasa cikata komai tace" haba ke kuwa an kira sallah fa amma kin tsaya a tsaye tserere kamar bishiya kodai azumin ba wuya ne"?'


Kallonta Asabe tay cikin tarin takaicin da take sata tunda ta dawo gidan zatay magana sai kuma ta fasa tana barin gurin.


Dan tabe baki mariya tay tana mikewa ta kalli baffa da murmushi tace" bari naje nima nasha ruwa nay sallah saina dawo yau hira zamuyi.

Kai baffa ya daga batare da yayi magana ba mariya kuma ta wuce.


Asabe kasa cin komai tay saboda bacin rai Allah-Allah take baffa ya dawo gida daga masallaci ayi wa tukar hanci dan tagaji da ganin takaicin da mariya ke kunsa mata ba dawowa tay dan hawan jini ya hauta ba".


Ba'a jima ba baffa ya shigo gidan lokacin mariya bata nan ta fita anguwa ko zama baiyi ba Asabe ta tare shi da magana.


"Malam ban dawo gidanka ba dan a dora min hawan jini ko ciwon zaman irin su ciwon zuciya gaskiya ka takawa mariya burki tun kafin ta kaini bango dan bazan yarda da wannan abin ba niba sakarya bace".


Cikin mamaki baffa yace" me kike nufi ban gane ba fito fili kimin bayani yadda zan fahimce ki".


Zama Asabe tay domin duk a tsaye take wannan maganar tace" ina nufin kaja mata kunne ta daina min shishshigi cikin lamurana ba ruwanta daduk abinda ya shafeni kamar dazu aiba a dakinta kake ba amma dan karuwanci tazo ta fitittike to wallahi ko kaska🐞 ce ita bata isa ta raba muba tayi kadan".


Baffa dake kallonta yace" to tunda zaki iya daukar mataki da kanki meye na fada min saidai inaso ki sani idan dama har ba zama ya kawo kiba fitina ce ta dawo dake ki kama kanki domin zaki koma gidan jiya".


Dafe kirji Asabe tay jin abinda yake cewa tace" yanzu kenan malam a dakeni a hanani kuka naga za'a cutar dani shikenan bazan fada ba".


Kai baffa ya girgiza" kinga Asabe da Allah banasan shashanci nan gaba inda kinsan maganar da zaki fada bata da mahimmanci ki daina bata min lokaci da dayanzu ba daya bane".


Kuka Asabe ta saki yayin da baffa ya juya yabar mata gidan.

Zama ta gyara tana share hawaye tace" shikenan ni Asabe na shiga uku na fito rana wannan wacce irin masifa ce ina zaune lafiya da a gidana da sana'a ta na jawo abinda ya sakeni gashi yanzu na dawo yar kallo" ta sake fashewa da kuka.



Yau da yake Safah sun gama aikin su da wuri a dakin jakadiya suna hira da Zarisha akan yadda zasu dau ado ranar sallah domin kowa free yake a ranar.


Safah ta kalle ta tana cewa" to amma Zarisha dame zamuyi kwalliya ba kayan sawa koda wannan uniform din gadon zamuci sallar"?


Dariya Zarisha tay tana kallonta tace" a'a za'a bamu kayan sallah masu aji ma kuwa ranar bakiga an gwada mu a part din amaryar me martaba ba"?.


Kai Safah ta daga" eh na ganii amma ban dau abinda muhimmanci ba na dauka ko wani sabon fi'ilin bautar ne haka".


Murmushi Zarisha tay zaki fara ko? Shikenan saboda mu bayine saimu kare a wahala babu jin dadi ba haka bane muma da ranar mu".


Safah tace" to maganar kayan kwalliya fa ko haka da bakin ido fuska a furje ake cin sallar"?.


Kai jama'a Safah kina da caza kai umma ce ke raba kayan kwalliya dan haka saiki baccinki da munshari ke ko baki ado ba zaki shiga ko'ina kyan fuskarki ma ya ishe ki".


Safah dake kallonta tace" tab wa ya fada miki ai kogi baiki yayyafi ba kuma ba'a kin kari koda na duka ne💪.


Jinjina kai tay" a'a wallahi indai kari na duka ne ina 'ki domin ba jikin karfe gare niba".


Dariya Safah ta mata jin abinda take cewa zatai magana Zarisha ta katse ta"


kinga Safah tunda azumin yau ba wahala muje mu sake rage ayyukan mu naji ma ana cewa samarin gidan sun kusa dawowa saura yan kwanaki".


Mikewa sukai cikin mamaki Safah tace wadanne samarin kike magana akai"?.


Daidai sun fara tafiya Zarisha tace" au baki da labari akan hakan sarki nada zaratan samari har biyu kusan kansu daya kuma duk sojoji ne amma basa kasar naji ana cewa sun kusa dawowa".


Kai Safah ta daga batare datay magana ba haka nan taji gaban ta ya fadi zuciyarta na bugawa da karfi.



#MRS AL'AMEEN AHMAD CE

WE WILL MEET AGAIN.😜



[03/29/23] +234 905 527 3614



🍇SAFREEYYAH🍇


#YUSRAHMS#
NO.67👉 68
Mk ne zaune cikin tsananin kunya a gaban mahaifan sa hankalin sa tashe musamman yadda mum nashi ke kuka akan abinda yake aikatawa.


Cikin nasiha daddy yace" Musaddiq mu suwaye a gurin ka"?.

Muryar mk na fita dakyar yace" kune mahaifa na daddy bani da wadanda suka fiku kuma kome na zama baza ku guje niba dan Allah ku gafarce ni na aikata kuskure abaya amma yanzu zan gyara zan zama na kirki".


Daddy daya zuba masa ido yace" to ai baka bari kaji abinda zance maka ba".


Kneel down mk yai yana girgiza kai yace" daddy nasani tambaya taza kai ni mizinaci ne? Eh amma ada yanzu na tuba na koma ga Allah dan Allah daddy ku yafe min".


"Musaddiq yan mata nawa ka lalatawa rayuwa"?.

Mk da jikinsa ke bari yace" baza su kirgu ba daddy ba'a iya jihar mu ko jahohin Nigeria ba har lokacin da naje karatu kasar waje".


Dafe kai daddy yay yana kallon mk cikin wani irin yanayin damuwa yace dama can kanayi ko a'a yaushe ka koya"?.


Sunkuyar dakai mk yay domin bazai iya fuskantar mahaifin nasa ba muryar shi na rawa yace.


Silar komai daddy wata baturiya ce muka hadu da ita karatu ya kaita Qatar yar America ce tunda muka hadu shikenan ta makale mun tace tana so nay girl friend da ita.

Na amince ganin mace ce ban taba kawo komai a raina ba wata rana da dare sosai ina zaune a masauki na naji ana buga min kofa da karfi kamar za'a balla dana tambayi waye.


Cikin muryar kuka tace itace wasu ne suka je har dakinta zasuyi mata rashin da'a.

Da naji haka saina tashi na bude mata kofa tana shigowa ta rungume ni ba yadda banyi ba akan ta sake ni addini na bai amince ba taki saida na nuna mata bacin raina na samu ta rabu dani.


Tace min tsoro ne yasa tamin haka nayi hakuri na dauka da gaske take bayan wani lokaci ta tashi daga inda take ta dawo kusa dani ta matse ni.


Ina yunkurin tashi ta rike min riga muryarta a sauye tace wai tana tsoron komawa hotel dinta karsu dawo su wulakanta ta zata kwana tare danI.


Na nuna mata ban amince ba saita fito fili tace min to ta amince min nayi disvirgin dinta akan wadancan su sameta ta bani kyautar kanta.


Mamaki da tsoro ne suka kama ni nace mata bazan iya sabawa ubangijina ba haramun ne abinda take so nayi a addini na.

Saita fashe min da kuka tana zuba gwiwoyinta akasa tare da rokona na taimake ta dukda haka batay nasara akaina ba dana ga zata matsa min lamba nace ta fice min daga daki.


Sai tace min zata tafi amma yanzun tana jin yunwa ne nadan hada mata coffee zata sha banyi musu ba na dauka da gaske take ashe tarko ta hada min.


Kitchen na wuce na hado mata coffee din nima na hado nawa dana zo na bata saita min godiya ta amsa kurbarta daya ta aje cup din tace nadan soya mata kwai ko biyu ne wannan bazai dauke ta zuwa safiya ba.


Mikewa nay na sake shiga kitchen saitai amfani da wannan damar ta zuba min kwaya cikin coffee na ban sani ba dana kawo mata waina kwan saina dau coffee din na kama sha sabanin ita data zuba min ido ko kiftawa batai.


Tana hankalce da duk motsina zuwa wani lokaci na fara ganin hajijiya na diba na naga sanda ta taso ta dawo kusa dani da kuma lokacin data zuge min zip din wando na.

Typingh amma daga nan ban sake sanin komai ba saida gari ya waye na ganni kwance kan gado tana gefena kuma idonta biyu gashi babu kaya a jikina.


Raina a bace na tambaye ta meta min kanta tsaye tace fayde tamin domin tana sha'awa ta kuma taga bazan bata hadin kai ba.


Yunkurawa nai zan tashi amma sai naji ko hannu na bazan iya dagawa ba kamar ba jini a jikina.


Dariya tay tana kallona tace ai ko gobe zakaje ahaka idan ba nice naga dama ba bazaka iya tashi ba domin anyi maka muguwar allura me matukar kashe jiki.


Kuma kana tambayar menay maka nasan tunda baka cikin hankalinka zaka shiga shakkun taya ina mace zan maka fayde bari yanzu na gwada maka.


Kaina ta fada dama babu kaya a jikinta ina ji ina gani maimakon ace namiji ne yakewa mace ta karfi amma mace ce meyin abin mamaki.


Da gaske take fayde tamin domin a yadda aka sani itace zatay kuka ko ihu amma nine meyi ko a mafarki ban taba kawowa araina mace zata iya saduwa dani ba saida na gani ido.



Bazan iya iyakance kwanakin data deba tana azabtar dani ba wasu lokutan harda kawayenta take gayyatowa suzo su farmin ba yadda na iya har nazo na saba abun ya zame min jiki.


Wata rana tazo da wani likita ya cire min wasu abubuwa daure a bayana shikenan naji dukkan karfina ya dawo a matukar fusace na tashi zan shako wuyanta amma ta fice aguje daga dakin.


Shikenan rabona da ita ban sake ganinta ba dana tambaya akace min ta gama karatun ta ne gida ta tafI dama kafin nazo ma shekararta uku.


Tun daga sannan hankalina yaki kwanciya na gaza yin karatu har asibiti naje akan likita ya duba min lafiyata saboda ciwon mara dake damuna sai yace min sparm ne yake taruwa min a mara sosai aure ya kamata nayi domin magani bazai min amfani ba.


Na shiga damuwa sosai a wannan lokacin domin nasan kona fada muku baza ku fahimce niba ga halaka da ciwon keson kaini dole na samawa kaina mafita ta hanyar biyewa yan mata daga nan na saba shiyasa ko maganar aure bana so dalilin kenan.


Ku gafarce ni ina me neman afuwarku nayi watsi da tarbiyyar da kuka bani amma kar kuyi fushi dani nayi alkawari bazan sake aikatawa yar kowa rashin da'a ba zan gyara kuskure na natuba zuwa ga Allah ya yafe min kurakurai na.



Kasa magana daddy yay sai kaida yake girgizawa cikin dagulewar yanayi.


Cikin kuka hajiya Binta tace kaji ko alhaji na shiga uku na lalace yanzu da wanne idon zamu kalli jama'a ka gama wulakanta mu ka zubar mana da mutunci a gari.


Riko hannunta mk zaiyi a tsawace tace karka taba ni da wannan hannun tashi ka bawa mutane guri.


Cikin damuwa mk ya kalli daddy dake kallon mum yace daddy ku fahimce ni wallahi natuba bazan sake ba.


Hajiya Binta zatai magana daddy ya daga mata hannu✋ alamar ya isa haka baison jin komai yace.


Me faruwa ta riga ta faru saidai Allah ya tsare gaba ya muka iya da kaddara.

Cikin bacin rai hajiya Binta tace oh abinda zaka ce kenan kamar wanda yasabo goyon baya daga gare ka.


Hade rai daddy yai bai kulata ba ya maida hankalinsa kan mk yana cewa" lallai musaddiq ka aikata munanan ayyuka a baya ba tare da sanin kowa ba sai mahaliccin ka.


Ina so kaji tsoron sa ka duba girmansa karka sake aikata zina dan Allah musaddiq".


Muryar mk na rawa sosai yace wallh daddy nayi alkawarin bazan sake aikata zina ba har karshen rayuwata zan gyara mu'amala ta da halayya ta bazan sake yin wani abu daya kauce hanya ba.


Mum ya kalla yana cewa kiyi hakuri mum dan Allah ki yafe min na tuba.


Batay magana ba daddy ne yaci gaba da masa nasiha karshe yace ya tashi yaje gida yay nafila ya kuma roki gafarar Allah.


Sannan yace ya tashi ya tafi sosai mk yaji dadin ganin cewa dadin nasa ya fahimce shi yasan a hankali mum ma zata fahimta.



Guda ce da shewa sosai ke tashi a karkashin bishiyar zaitun din gidan su Safah mariya ce ke bubbuda kaya tana cewa kai madallah masoyina Allah ya kara budi irin wannan cakare mu da kayan sallah atamfa mekyau haka kamar muna gidan gwamna.


"Asabe 'kawalli da romo kina ina ne fito mana kiyi kallon abin arziki yanzun nan Bara'atu yar gidan mero me dinki ta kawo mana dinkunan mu".


Fitowa Asabe tay daga daki tana cika da batsewa tace aikin banza mutane na bacci kinbi kin dame su wannan ihun naki atamfa kuma bana bukata ke kike fatarar zani saiki hada ki daura".


Rike baki mariya tay tana dariya tace ikon Allah daga magana sai cibi ya zama 'kari kada Allah ya saki bukata keda ba'ai miki gwaninta gaskiya da masoyina yayi hakuri da halinki".


Tsaki Asabe tay wannan kuma ke kika sani mace sai karuwanci".


Cikin harara mariya tace na isane karuwancin ma iyawa ne in fitsari banza ne kaza ma tayi.


Juyawa Asabe tay tana tafiya tace humm mariya ci gaba da kaini bango zan kama kine zaki bayani.


Mikewa mariya tay tana cewa bari nazo yanzu ma ki kama ni dama azumin yau ko a jikina gashi ba kowa a gidan saimu dambu mu juya mu fidda rainin dake tsakanin mu zaki bayani idan jikin ki ya fada miki.



Ganin mariyan tabi bayanta kuma sarai tasan tafi karfinta

Please Login or Register in order to submit comment