Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciwon farfadiya.


Sannan SAFWAN DAUDA DA MATARSA ZARISHA UZAIRU MAGAJI akan sadaki naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba.


"Allah ya sanya alkhairi ya bada. zaman lafiya da zuriya dayyiba ya tsare sharrin mutane da fitina".


"Amin amiiin kawai kake ji ana ta fada duk gurin".


Kafin me martaba yay jawabi sosai da godiya ga duk jama'ar gurin da kuma nuna farin cikinsa ga wannan ranar sannan ya rufe da addu'a.


Daga Abdul-jabbar har Amfal ba wanda yake cikin hayyacinsa kallon suma ya koma wani iri waziri da ya fahimci yanayin su yasa dogarawa suka kare su saboda mutane suka shiga mota suka nufo gida.


Suna isowa gida ya rude da murna da bushe bushe da kirari da yabo duk gidan anyi masa kwalliya da furanni da kayan kyale kyale ko'ina ka duba photunan sune manne.


Suna fitowa a mota Abdul-jabbar ya yanke jiki zai fadi da sauri masu tsaron su suka tare shi suna daukar sa zuwa part dinsu domin ya suma".


Ammy dake cikin taro ganin dogarin da tasa ya kula mata da komai ya shigo yasa ta mike daga cikin yan uwanta tana komawa gefe tace.

"Ya ake ciki meye labari sun dawo an daura auren ne"?.


"Eh ranki ya dade an daura amma inaga yarima Abdul-jabbar ya suma domin naga an dauke shi an shiga dashi bangaren su".


Murmushi Ammy tay yayi kyau Abbas jeka ci gaba da kula min da komai".


"To ranki ya dade Abbas yace yana fita ita kuma ta juya cikin jin dadi tana cewa.

"suma daya kenan kai yanzu ka fara Allah yasa daga haka ma ace ka hadiyi zuciya ka mutu dazan fi kowa farin ciki".



Zarisha suna zaune tayi tagumi irin na amare cikin tsokana Safah tace yadai amaryar Safwan irin wannan tagumi haka kodai-kodai haaaa yau wata zata barnan ayyuri yuri gaskiya zarisha kinyi kyau matsalar tagumin nan ne ya bata ki".


Duka zarisha ta kawo mata Safah kinsan Allah ki rabu da ni.


"Jimin mace karfin amarci ko taya zan rabu dake bayan in an jima zaki barmu gobe war haka koda kudi bazaki ganni ba Allah sarki zarisha.


Ta fada cikin kalar tausayi tana sa hannunta tare da murtsuka idonta kamar me kuka.


Zarisha tace kiyi komai zan rama ne wata rana".


"Taya kenan madam din safwan"?.


"Ta yadda kika min zan rama idan kema kikai aure".


"Tab kina ruwa iya wuya waya fada miki zanyi aure ai yanzu nice autar umma muna tare iya rai da mutuwa ba me raba mu hehe wata kuwa yau zata fece gidan wani".


"Bari ma na miki waka me dadi kin zama kin zama kin zama kin zama dauko riga kin zama dauko wando kin zama dauko hul...


Bata karasa ba da gudu ta mike tana dariya daidai jakadiya ta shigo ita da hanne zama sukai cikin jimamin yadda Safah zata dau maganar da suke shirin fada mata.


Kallon jakadiya safah tay tana cewa umma kiga zarisha ko dan kawai nace da anjima zata ware tabar mu na zama autar ki shine take neman karya min kafa".


Murmushin yake jakadiya tay tana cewa zauna safah ki nutsu zamuyi magana ta fahimta".


Zama safah tay amma kawai sai taji hankalinta bai kwanta ba".


Cikin lallahi jakadiya ta rike hannun ta tana karbar kudin dake gurin hanne ta damkawa Safah a hannunta tace rike yata".


Rike wa safah tay cikin mamaki yayin da jakadiya ta soma magana cikin nutsuwa".


"Safah ke musulma ce ki yarda da kaddara me kyau ko mara kyau ki sani duk abinda ya faru dake dama bazai kuskure miki ba kuma duk abinda ya kuskure miki dama bazai same kiba".


"Kiyi hakuri da abinda zai fito daga bakina Allah yasa bazan zama muguwar jakada gareki ba Safah ina me sheda miki cewa a yaune aka daura auren ki ke da yarima Abdul-jabbar akan wannan sadakin da kike gani a gaban ki naira dubu dari biyar".


"Bamu da tabbaci ko hakikanin me yasa gimbiya Adama ta zabe ki a cikin bayi saidai muna rokon ubangiji yasa haka shine mafi alkairi karki ji komai safah Allah yana tare dake".


"Kuma shine gatan ki shi zai tsare ki daga dukkanin sharri insha Allahu zaki farin ciki a gaba".


Wata iriyar zabura Safah tay cikin firgici da tsananin tashin hankali ta mike tsaye yayin da kudaden suka tarwatse farrr a dakin".


Muryarta na tsananin rawa tace" umma mafarki nake ko abinda nake ji gaske ne nice aka daurawa aure da dan sarki taya hakan ya faru dan Allah umma kice wasa kike min".


Cikin tausayawa jakadiya ta girgiza kai tana kama safah ta zaunar da ita tace.


'Yata kiyi hakuri idan kaddara tazo babu yadda za ai ba wasa cikin abinda na fada miki yanzu kedin surukar me martaba ce domin kin zama mata ga dansa Adama ce ta zabe ki".


Kuka safah ta fashe dashi tana dora hannunta aka tace" na shiga uku na lalace ni safah se kace me bakin iyaye rayuwa me nayi miki kike wahalar dani dama banzo wannan lokacin ba gara mutuwa akan naji wannan bakin labarin me tarwatsa farin ciki".


Hanne ce tace kai kai haba yarnan komai yay zafi maganinsa Allah ki daina kiran masifa a kanki ki godewa Allah a halin farin ciki ko tsanani zai zama garkuwa gareki".


Juya kai safah keyi cikin tarin damuwa ga wani ciwon kai daya kamata lokaci guda".


Tattara kudin jakadiya tay tana dauko wata jaka tasa a ciki sannan ta kalli Safah dake kuka wiwi tace".


Dan Allah yata idan har na isa dake to ki nuna min a aikace ina so kibar wannan kukan ki rungumi kaddara kinji".


Kai safah ta daga a bisa dole ta tsayar da kukan da take tana goge hawayen fuskarta kamar yadda jakadiyan ta umarce ta".


Tace shikenan umma na yarda da kaddarar data same ni Allah ya fitar dani daga tarkon da aka dana min wannan abin shiri ne amma ba komai mutum bashi da ikon aikata min wani abu sai Allah ya yarda".


"Yauwa yata alhamdulillah masha Allah ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai alkairi".


"Shikenan umma nagode Allah ya biya ki abinda kikai min kin rike ni tamkar yar da kika haifa baki taba nuna min wani bambanci da zarisha ba alhalin baki san ni wacce ba bakowa ne zaiyi abinda kikai ba ina alfahari dake a ko'ina zan bugi kirji na nuna ki matsayin mahaifiya ta".


Murmushin jin dadi jakadiya tay tana cewa karki damu kinji safah har abada kedin yata ce kisa a ranki bazan barki ba kina tare dani bari mu dawo".


Fita jakadiya tay ita da hanne yayin da safah ta juya tana kallon zarisha wacce ta zama tamkar gunki tana binsu da ido".


Ganin sun fita yasa ta sauke ajiyar zuciya tana cewa ke Safah wannan wanne irin abin mamaki ne haka kin gani ko nace wata rana zaki aure kince a'a bawa baida yancin kansa keda aure har abada gashi da Allah ya tashi baki mijin ma danya nuna miki ikon sa saiya baki me tsada wanda ya wuce ajin ki".


Kai safah ta girgiza tome zance zarisha kinsan ba a san raina hakan ta faru ba bani da burin aure wani a rayuwa kullum burina da addu'a ta shine na koma gida na auri murtala".



"Haka ne safah amma saiki hakuri tunda kaddara ta riga fata Allah yasa hakan ya zama silar farin cikin ki".


"Taya kenan zarisha bana tunanin zai karbe ni matsayin mata kamar yadda nima a raina bana jinsa matsayin miji".


Dan murmushi zarisha tay lallai Safah kin dauko da zafi kema kenan balle shi yanzu ya yake kitsawa".


"Koma menene zarisha ni bai dame niba kuma bazan bari a wulakanta ni ba dan na kasance baiwa".


"Tofa karfin hali barawo da sallama Safah bar cika baki a gabana karki shiga daka ciki muji ki lumui shiru tsit kamar an doke bakin tsanya da tabarya".


"Dawa badai da wannan din ba karki manta ba auren soyayya mukai ba auren tilastawa ne da biyu wannan matar Adama take kowa ta hada aure na dashi kuma saidai aniyarta ta bita".


Kallonta zarisha tay to kema kinyi magana idan ma danta cutar dake tay haka bazai samu ba saidai ta kwashi bakin ciki".


Safah zatay magana suka ga wasu bayi su goma sun shigo da sallama suna tambayar" wacce gimbiya Safara'u"?.


Kallon safah zarisha tay wacce ta ma'ke ta kame guri guda ga alamar firgici ya bayyana akan fuskarta".


Maida kallonta tay kansu tana cewa gata nan a zaune".


Wani kalar kyakkyawan mayafi me duhu suka fitar daga cikin wata hadaddiyar jaka suna cewa.


"Ranki ya dade daga part din amaryar sarki aka aiko mu cewa mu tafi dake".


Saurin kallon Zarisha Safah tay hawaye na neman tarar mata a ido".


Kai Zarisha ta girgiza mata alamar kar tayi kuka sannan ta mike tana zuwa kusa da ita ta mikar da ita tare da karbar mayafin da yake zuba uban kamshin turare ta yafa mata".


Daya daga cikin bayin ce tace an umarce mu cewa ta rufe fuskar ta ba'a bukatar wani ya sake ganinta".


Danjan mayafin zarisha tay tana karasa rufe mata fuskar sannan mutum daya ta tsaya a gabanta biyu a gefenta wasu biyun a daya gefen biyar suka take baya haka suka tafi da ita.

Wanda suna fita daga dakin zarisha ta fashe da kuka tana fadawa kan katifa dama dan karta sa Safan a damuwa ne yasa ta boye nata kukan amma tana matukar tausaya mata".


Da sauri jakadiya ta karaso dakin jin kukan zarisha ganin ita kadai yasa tace" lafiya Zarisha me akai miki"?.


Tashi zaune tay cikin shashshekar kuka tace umma sun tafi da ita shikenan sun raba mu wayyo Allah na Safah".


"Haba zarisha waya fada miki shikenan sun tafi da ita zata dawo fa ki kwantar da hankalin ki".


"Ina matukar tausaya mata umma wanda fa ya mata sharrin ta kashe masa doki shine fa aka aurawa ita Allah yasa kar yace zai mata wani abu ko yadau fansa".


"Ba wata fansa dazai dauka ai yaron nada hankali ki daina tausaya mata akwai nasara a gabanta saidai ki taya ta da addu'ar neman kariya daga sharrin mahassada da makiya".


"Shikenan umma zanyi abinda kika ce mu kuma haka tamu kaddarar take".



Har gaban fatima suka rakata sannan suka basu guri domin baza su kasa tattaunawa ba".


Cikin murmushi Fatima tace to suruka ta bude min fuskar taki na gani ko dan nawaya nada 'kashin arziki".


Jikin Safah a sanyaye ta bude mayafin batare data dago fuskarta ba".


Mamakine ya kama Fatima tace kamar Safah nake gani kawar yar gidan jakadiya ko".?


Kai Safah ta daga muryarta na fita dakyar tace nice ranki ya dade".


"Alhamdulillah tunda kece yazo gidan sauki dama tun kafin wannan ranar nake tunanin wace yarinyar da uwar gidan me martaba ta zabawa yarona ashe kece lallai ta iya zabe".


Allah ya baku zaman lafiya da farin ciki me dorewa a rayuwar auren ku kinji karki sa komai a ranki domin kinyi dacen miji na gari san kowa 'kin wanda ya rasa".


Safah kam bata iya magana ba kawai tay shiru tana sauraron ta ne har wasu manyan zababbun bayin data zaba wadanda zasu kula da komai suka shigo.


Kai tsaye ta basu umarni cewa gata nan ku shirya ta sosai yadda koni dakyar zan gane ta saboda kyau".


"To ranki ya dade za'ai duk yadda kika ce".


Safah data mike zasu shiga wani wuri da ita jitake kamar ta durkusa ta roki alfarmar cewa dan Allah Fatima tasa su rabu da ita amma saita kasa haka suka wuce tana gani"'.


Abdul-jabbar na zaune Amfal ya shigo shida marakisiyya gudun fitina domin batasan bada ita aka daura auren ba duk haukan ta yanzu ta zama matar Abdul-jabbar.


Zama tay kusa dashi tana cewa barka da hutawa angona gaskiya nayi dace dana sameka zan rike ka dakyau kada wata tamin kwacen ka zuwa jimawa zamu tare ko".


Kamar dutse takewa magana haka Abdul-jabbar ya bawa iska ajiyarta ji yake da ace itan cema da dama-dama.


Cikin shagwaba tace haba sweetheart magana fa nake ka share ni haka zamu rika zaman kurame gaskiya ka canza".


Fitowa Amfal yay daga bedroom da wata dankareriyar sarka a hannunsa yana mika mata yace ya kamata kije ki sake kwalliya domin tarar amaryata wacce ban santa ba bata sanni ba saita zo".


Mikewa marakisiyya tay tana cewa taya zan tari amaryarka bayan a lokacin nima ana cuku-cukun kawo ni dakin nawa mijin".


"Shikenan to naji jeki".


Juyawa tay zata fita tana kallon Abdul-jabbar daya zubawa screen din wayarsa ido tace.

"Sai anjima mijina ka huta lafiya" fita tay amma ko kadan bai dago ba balle yasan da wanzuwarta a gurin harta tafi.


Dariya Amfal yay kan bala'i amma fa akwai tashin hankali da rikici a gidan nan daga lokacin da marakisiyya ta gano cewa bada ita aka daura muku aure ba".


Dan shiru yay sai kuma yace" bros ya jikin naka wai me yasa ka suma ne dazu kaban tsoro wallahi".


"Idan abinda ya sani suma kake son sani tambayi kanka".


"Bros taya zan tambayi kaina idan ga miciji ai ba'a bin ja abinda yasa ka suman zaka fada min".


"Tambaya kake ko neman sani wai shin Amfal meyasa ka fiya takura ne kamar gidan haya"? Ka barni da abinda yake damu na daga baya ka tambaye ni".


"To shikenan bros nayi shiru ni kaina a damuwance nake amma ganin ka fini shiga matsalar yasa na boye tawa".


Kallonsa Abdul-jabbar yay a hakan"?.


"Kwarai bros Allah ka yarda dani".

"Ai dole na yarda dakai kodan abar maganar".


Dariya Amfal yay haka ne to bari nazo muyi salfie" dawowa kusa dashi Amfal yay yana daga wayarsa yadau photon su.


Sannan yace ina hajiya jarabu da kwai kullum maganarta aure gashi ta zuga abba ya mata saita zuba ruwa a kasa tasha".


"Malam karka soma daukar alhakin ta ba ruwanta cikin wannan al'amarin saidai idan akan ta zaka huce saboda abba ne ya maka kuma danta ne".


"Idan na huce akan sa dan danta ne ni kuma mahaifi nane kawai na hakura".


"Daya fi sauki" Abdul-jabbar ya fada tare da dan jingina bayansa jikin kujera ya fada duniyar tunani".


Safah kam taga duniya da yaji tun la'asar ake shirinta har bayan magriba duk ta gaji gabobinta na ciwo har suka gama sannan Fatima ta bada umarnin a mayar da ita gurin jakadiya kafin lokaci ya karasa".


Har dakin jakadiya suka mayar da ita sai zuba kamshin daddan turare take ga wani uban tsaro da aka zuba a kofar dakin kamar wanda me martaba ne da kansa a dakin.



Kallonta zarisha tay daidai angama mata kwalliya itama tadau shiri cikin kyakkyawan less tace.

"Kan uba Safah kinga yadda kika koma kuwa princess sak hakan ma sai an tona samun irinki inama da waya na miki photo kisha mamakin kanki".


"Humm zarisha kenan karki manta wace ni baiwa ce ba auren soyayya nay kamar kiba balle nayi farin ciki nasani yau kwanan kunci da damuwa zanyi".


"Waya fada miki safah matsala ta dake maimaita abu wallahi kinji na rantse ko ki kara hakuri Safah akwai nasara a gabanki".



Ido kawai Safah ta zuba mata batare da tai magana ba domin bata da abin cewa ita yanzu tamkar yarinyar goye take sai abinda akace mata.


Basu fi mintuna biyar zuwa shida ba sukaji jakadiya ta shigo bayan ta wasu bayi ne anyi musu dinki iri daya sunsha kwalliya kowaccen su rike da fure me kyau a hannunta.


Cikin boye damuwarta jakadiya tace" yata taso muje lokaci yayi karki damu zanzo gurinki gobe yau ba damar nace miki wani abu".


Sunkuyar dakai Safah tay jikinta a sanyaye yayin da jakadiya ta rike hannunta zuwa waje.


Mamaki ne ya kama ta ganin yadda aka haskaka farfajiyar da fitilu an kawata ko'ina ga gurin yay matukar cika".


Doki aka kawo har gabanta yasha ado sosai kamar sarki ne zai hau wani irin juyawa kan Safah keyi tana kallon jakadiya tace.


"Umma me kuma za'ai da doki anan"?.


Dan murmusawa jakadiya tai batare data iya kallonta ba tace" kece zaki hau a miki rakiya zuwa sashin mijinki saboda ke aka kawo shi".


Zaro ido Safah tai dai-dai an saki busa ana kirari wani kalar kukan tashin hankali ne yazo mata.


Ta juya zata rungume Zarisha da sauri aka shiga tsakiyarsu wacce tafi kowacce baiwa kwalliya tace.


"Ki gafarce ni ranki ya dade yanzu kinfi karfin hada jiki da kowa matsayin ki ya wuce nan".


Tana ji tana gani saidai ta kalli Zarisha da ido har gaban dokin jakadiya ta kaita aka rike mata shi abisa dole badan tana soba ta taka tahau.


Amma dukkan jikinta rawa yake sakamakon bata taba hawa ba saiyau wanda yake rike da dokin aka budawa hanya ya soma tafiya.


Sannan sauran tawaga suka rufa musu baya da kirari da busa wanda ganin da gaske barin zarisha zatay yasa wasu zafafan bakaken hawaye suka fara zarya a fuskarta.



Ana fita da ita Zarisha dake tsaye ta 'kame guri guda ta yanke jiki ta fadi a gurin sumammiya.


Da gudu Rasheeda ta karaso gurin tana kiran sunanta a rikice ta kalli Fa'iza dake tsaye tace" sauri ki kira yaya Safwan dan Allah kice yazo muna nan aunty ce ta suma".


"To Fa'iza tace tana juyawa yayin da Rasheda ta dago zarishan dake kwance a kasa.


Wani bangare aka kai Safah wanda kamar ma ba'a masarautar yake ba shiru saidai haske darau ta kowacce kusurwa ga sanyi.


Tun da ga bakin kofar palon har zuwa cikun bedroom carpet ne shimfide anyi masa kwalliya ga kuma bayi tsaye gefe da gefen sa tun daga farko har karshe sauka Safah tay tana daga kafarta ta fara tafiya akan carpet din.


duk inda ta taka tana dauke kafarta za'a sa fure a gurin har kofar bedroom din sannan ta tsaya tare da karanta addu'a tai bismillah jakadiya na rike da ita suka.



Cire mata kyakkyawan takalmin kafarta jakadiya tay tana aje shi gefe ta rike mata kayan jikinta yadda zata ji dadin hawa gadon kayan sun mata nauyi saboda bata saba da irinsu ba.


Jan hular alkyabbar jakadiya tay tana rufe mata fuska batare da tace mata komai ba saboda bata da abinda zata ce mata yanzun sai kawai ta juya tana fita daga dakin tabar ta ita kadai.


"Yanzu umma shikenan na rabu daku kiga wani guri da aka kawo ni me tsaro taya idan na bukaci ganin ki zan samu".


Safah ta fada kamar me tsoron magana jin shiru yasa ta bude fuskarta ganin ba jakadiya gashi taji shiru kamar ba halitta me rai tsit yasa ta fahimci ta tafi ba kowa kenan.


Wani irin tsamm tai tana fadawa duniyar tunani wato matar mutum kabarinsa ba kalar kalatar da mk baiyi ta amince ta aure shiba taki.


Ga murtala sun goga da Adamu yayi nasara ana gobe daurin aure kaddara taratsa mk ya tarwatsa mata farin ciki ta shigo hannun kandas.


Ta zama kadara hajiya ta sayeta ta kaita gidan bariki da nufin ta rika samar mata kudi.


Tsautsayin zata bar gidan yasa marwa ta tura mata kwarto yaji rauni'.



Daga nan ta kawo ta wannan gida na sarauta matsayin a maida ta baiwa a bata wahala a mata azaba ta gamu da kalubalen Adama.


Ba shakka ko tantama batai wannan hadin auren Adaman ce wato ta tsaneta shiyasa ta aura mata wanda yake zargin ta kashe masa doki.


"Kodai shine Abdul-jabbar din da take cewa ta tsana wanda ba danta ba"?.


Wata zuciyar tace kwarai haka ne Safah kinyi gaskiya ba makawa shine makiyanta ta hada guri daya".


Sauke ajiyar zuciya tay daidai ta dawo daga tunanin tace ba wani bawa da yake da ikon cutar da dan uwansa sai Allah yaso dan haka duk mugun nufinki zai koma kanki".


"To amma shi yasan bata san sa ta tsane shi ko a'a bai sani b.....


Shiru tay jin kamar motsi ta kasa kunne tafiya taji kamar an nufo dakin da take da sauri ta mike tsaye tare da dirowa daga kan gadon.


Kara tasa tare da rike kafar saiga hawaye dama kadan take jira bude kofar dakin akai ana shigowa tuni ta manta da zafin da karfata ke mata.


Tana kallon kofar shine ya shigo domin shike da damar hakan duk gidan ba namijin daya isa shigowa sai shi din.


Tuni dukkan ilahirin jikinta yadau wata irin tsumar rawa ga tsoro daya mamaye ta tuna marin daya sharara mata ranar sallah sai kawai kuka ya kwace mata.


Durkusawa tai a gurin tana sunkuyar da kanta tace" dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri kamin afuwa wallahi ba laifi na bane bansan komai ba".


Ko kallon inda take baiyi ba saboda takaici shi damuwarsa a yanzu ya samu sauki daga ciwon kan dake damun sa wuceta yai kamar baiga mutum ba.


Dakyar ya karasa gadon wata hajijiya na diban sa idonsa duhu baya ganin komai sai jinsa yay ya fada saman gadon idansa a rufe so yake ya mata magana akan ta dame shi da hayaniya amma ko bakin ya kasa budawa.

tun yana jin kukanta sama-sama har baccin wahala ya dauke shi kan bai daina masa ciwon ba.


Safah kam zulumi da rashin kwanciyar hankali bai barta ta iya koda gyangyadi ba idonta tar ta kwana har gari ya waye bata iya runtsawa ba.


Ganin lokacin sallar asuba na neman kurewa gari yayi sha yasa ta mike dakyar saboda kafarta datai tsami ga ciwon da gabobinta ke mata".


Kofar da take kusa da ita ta nufa a hankali ta murda saitai sa'a kofar ta bude shiga tay tana addu'ar Allah yasa toilet ne.


Fatan ta ya samu dan ganin babban bandaki tay bata tsaya kalle kalle ba tai maza tayi alwala tana fita.


Akwai sallaya ta dauka tay sallah sai a lokacin taji bacci ya fara kamata amma ko lumshe ido ta kasa.


Abin har tsoro ya bata ganin har wajen sha biyu bai farka ba gashi so take ta fice daga dakin amma dalilin dan tafiyar datai tsamin kafar ya dame ta.


Gani tai yayi juyi cikin salati ya tashi zaune ya dafe kansa da hannu biyu ya dade a haka daga baya ya sauka a gadon.


Baima. lura da ita ba ya wuce toilet ganin lokaci ya kure yasa cikin gaggawa yayo wanka da alwala ya fito.


Sauke kai safah tay saboda towel ya dauro kuma iya kugu jikinta ne yadau kakkarwa tunda take bata taba ganin namiji a haka ba".


Gashi yana da yalwataccen gashi a kirjinsa baki wulik me shekin gyara ga kyan kirar jiki ai safah saita rude.


Jallabiya ya saka yana sanya turare me masifar kamshi ya tada sallah.


Kai kamshin turaren nan yayi wanda saida ya samar da nutsuwa a zuciyar safah har dan lumshe ido take tana budewa.


Saida ya idar yay addu'o'in sa da komai ya shafa ya mike yana juyowa abisa akasi suka hada ido wanda Safah da sauri ta janye nata.


Shikam cikin tsananin mamaki ya kara bude idonsa sosai akan ta zuciyarsa na fada masa cewa wannan yarinyar data kashe maka doki ce.


Kenan itace matar tawa ita Abba ya aura min baisan na tsane taba innalillahi wa inna ilaihi raji'un lallai da akwai matsala.


Safah taji a jikinta har lokacin idonsa na kanta wanda hakan yake neman dauke mata numfashi ba zato taji zazzakar muryarsa yace.


"Ke dago min fuskar ki".


Ba shiri ta shiga taitayin ta tare da shan jinin jikinta ta dago amma bata iya kallonsa.


Dukkan girman idonsa ya bude akanta cikin tambayar zuciyarsa yace.

"Mene ya samu idanunta suka kumbura haka kuma sukai ja"?.


Shiru yay yana tunanin meya kawo mata hakan can wani bangaren yace masa.

"Ba lallai idan jiya ta samu bacci ba shiya jawo mata hakan.


Bai sake ce mata komai ba ya bude kofa ya fice sauke ajiyar zuciya tay tunda har bai mata komai ba kila ya hakura.


Yana fita bai tsaya ko'ina basai tsohon part dinsu cikin mamaki yaga Amfal zaune yana breakfast zama yai yana kallon shi yace".


"Amfal badai anan ka kwana ba kar kace baka je kaga yarinyar mutane ba.



Kai Amfal ya girgiza yana cewa" barka da kwana bros ba anan na kwana ba tun karfe tara dai nazo ina jiranka sai naji shiru shine nace kila ko kana can kana shan dumi domin da kiran ka zanyi a waya na fasa tuna da dayanzu ba daya bane.


Wani kallo Abdul-jabbar ya masa jin abinda yake cewa.


Yace a'a ka manta ba dumi nake can nake sha ba kuna nake sha wato zaka fara ko ka samu abinyi kuma kenan".


Dariya Amfal yay "Ba haka bane bros kawai dai na fada ne toya auntyn nawa fatan tana lafiya"?.


"Ok naji kana da number Zainab"?.


"Eh baka zanyi"?.


"No kirata kawai kace ina neman ta yanzu tazo".


"Shikenan an gama babban yaya" Amfal ya fada yana tura kira bayan ta daga ya fada mata saida ya katse ya kalli Abdul-jabbar tare da mika masa tea yana cewa.


"Amma bros me zakaiwa Zaina ita likitan hajiya ce namiji ya kamata ka kirawo idan duba ka za'ai".


"No Amfal bafa ni zata duba ba wannan yarinyar ce.


"Oh ashe aunty nace babu lafiya

Please Login or Register in order to submit comment