Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk daya ne Allah yasa ba'a riga niba"?zaro ido Amfal yay yana kallon ta yace"ni kuma ki rufa min asiri ban tashi yin aure ba ni yaro ne".


Kai Bilkisa ta girgiza "gaskiya kaiba yaro bane dan haka nayi kamu"cikin jin haushi Amfal yace "da yake farauta kika fito ba ni kuma nayi miki kama da zomo๐Ÿ‡ ko gafiya saiki kama kikai gidan ku"๐Ÿ˜.


Murmushi tay "abin baikai haka ba kawai nidai ka amince min ina sonka"banza Amfal ya mata zata sake mgn aka neme ta cewa ta fito filin taro ta fadi wacce amarya da rayuwar ta mikewa tay tana cewa"minti biyu bari na dawo".


Sauke ajiyan zuciya Amfal yay yana kallo Abdul-jabbar da shima shi yake kallo zayyi mgn ya mike yana cewa"malam na mamajo kana iya tasowa mu tafi kafin mayyar taka ta dawo "mikewa yai sunai wa ango alamar fatan akairi suka fita a wajen dan Abdul-jabbar ne dayaga abin Bilkisa bana, hankali ba yaiwa ango text cewa zasu tafi yayi kiran ta fili kafin ta farga su fece har dare yayi dan haka suna zuwa sallah sukai suka bi lafiyar gado.



Sosai abinda Safara'u tayi ya taba xuciyar murtala bai taba kawowa a ransa xata 'kishi tadau Adamu ba saida yaga hakan ya faru.



Saidai abin mmk da lallami ta hanya mafi sauki baba ya sauya akalar safah da addu'a sai son da takewa adamu ya koma kan murtala harma ana batun zuwa rokon arziki hankalin asabe ya tashi bata san safah ta samu inda zata huta tafi so koda yaushe ta kasance cikin wuya dan haka ta samu malam da shawara.



Malam abinda kai baka kyauta ba yarinyar nan Adamu take so amma shine ka mata asiri ta koma son murtala idan kai haka ka ha'ince ta kuma sai Allah ya tambaye ka me yasa ka aikata haka".


Malam dake sauraron ta yace"Asabe bansan shasanci barnan kafin ki tabo min bacin raina".


Mikewa Asabe tay Allah ya bada hakuri malam dan kawai na fada maka gaskiya da kasan yadda ake zagin ka a gari ance kayiwa Adamu kyautar zobe da ka hana murtala Safara'u ka bashi".


Sake cewa yai"nace kibar nan ko baki jini ba "kada kai, asabe tay cikin takaici tana cewa "ba laifin ka bane karatu ne ka dauka a gurin malamin ka malam Na Allah shine ya fara yi Saminun gidan kuka na san Fatima amma sbd kudi ya rude shi ya bawa sarki ita ya hana wanda yaiwa alkawari kaima hakan zakai kenan"?.


Ai na sani murtala nada manyan shanu da awakai ga gonaki kuma ga shago kaima shiyasa idon ka ya rufe sbd za'a rika kawo maka madara ohni Indo amma fa anji kunya".



Malam bai sake sauraron taba ya mike yana barin wurin Asabe data bishi da kallo tace"wallh malam indai ina raye safara'u bazata auri murtala ba idan kuwa ka taurare akan haka zansa kayi kukan bakin ciki da idon ka".


Yau ya kama juma'a dan haka tun wuri Asabe ta dafa abincin sayarwar ta saidai ta rasa inda Safah ta shiga karshe gudun kar ayi mata kwashe ta dau hijabin ta tana bi duk inda tasan tana zuwa amma kowa yace bai ganta ba.



Dole Asabe ta hakura tana dawowa gida tadau hayar wata yarinya a makotansu ta bata tallan abincin ta kuma dau kujera ta dake tana jiran komowar Safan.



Safah na gidan su Na Allah acan ta wuni sai bayan anyi sallah a masallaci tayi musu saida safe tayo hanyar gida tana shiga Asabe ta mike tana cewa"ke yar iska daga gidan ubanwa kike dan raini shine kikai tafiyar ki yawo baki zo kinmin tallar abinci ba ko yau saina ci ubanki".




Kanta tayo zata fara dukan ta cikin tsawa taji ance"idan kika kuskura hannun ki ya sauka a jikin ta na datse igiyar auren ki duk ukun"da sauri ta janye hannunta tare da juyowa ganin malam tay tsaye rike da tasbaha yana ja.




Cikin bacin rai tace"yanzu malam a dakeni a hana ni kuka kawai gashi nan ta jawo min asara nayi kwashen abinci kudin mutane zai hau kaina wallh malam baka da adalci dan ba nice na haife ta ba shikenana ban isa da ita ba "ta karasa mgnr tana fashewa da kuka.




Karasowa malam yay yana cewa"wallh Asabe lokacin da ake rabon hankali bacci kike to bari kiji daga yau doka tace Safara'u ba zata sake tallar abinci ba kinji na fada miki".



Daki asabe ta wuce tana kuka yayin da malam ya kalli Safah dake tsaye yace"jeki kwanta"to tace tana shigewa daki shi kuma ya fita a gidan".




Ina godiya da nuna yabawar ki ga littafin nan my sister Zarah Musa dan Adam hakika bani da kamar ki a kullum roko na ki kasance cikin farin ciki mai dorewa.




Sauran yan uwa na nesa da kusa ina mika gaisuwa ta a gare ku tare da muku fatan alkhairin Allah a koda yaushe yakai muku inda kuke.

Maman Khaleel Zaria
Hajara Abla's Kano
Indo ce Kano
Rabi'at Bichi
Hajara birnin kudu
Zainab birnin kudu
Aishat birnin kudu
Ummi Salis kaduna
Ambaby kwalli kano
Walida kwalli kano
Batila Abdllh Dutse
Ruwaina Abdllh Dutse
Asiya Haladu Dutse
Badariyya Hassan Dutse
Aishat Abubakar Kebbi
Ameerah Hassan Dutse.

Dama wadanda ban fada ba kuma badan na manta ba duk ina gaida ku na gode kuma da yabon ku gare ni.



Bazan taba mantawa dake ba BASIRAH MUHAMMAD DUTSE INA MIKO TA'AZIYYAH TA GARE KI NA RASUWAR YARKI AISHATU BABY๐Ÿ˜ข KWANAN BAYA ALLAH YA MATA RAHMA YAKAI HASKE KABARIN TA MU KUMA IDAN TAMU TAZO UBANGIJI YA AMINTAR DAMU YA NUFE MU DA CIKAWA DA IMANI๐Ÿ‘๐Ÿ™. AMEEEEN.




YUSRAH MUSA ABUBAKAR SEE YOU NEXT TOMORROW BE WITH ME AT ALWAYS MY LOVERS๐Ÿค—๐Ÿ’˜.



Daga Alkalamin hamshakin group din nan mai cike da baiwa wanda kuka fi sani da taken๐Ÿ‘‰๐Ÿ‘‰๐Ÿ‘‰ ANNURI WRITER'S ASSOCIATION ๐ŸŒคHASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI YAYAN TAFIYAR MU BABU RAGO A CIKIN TA BABU YAUDARA KO HA'INCI TSANTSAN GASKIYA MUKE NUNAWAโ˜๐Ÿ‘๐Ÿ‘Œ.




๐Ÿ“–๐ŸŒซ๐Ÿ˜˜Mrs Al'ameen Ahmad ce.



๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜œLOVE FOR EVER๐Ÿ˜๐Ÿ˜




Typing๐Ÿ“ฒ
3:54pm monday February 2023



๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
SAFREEYYAH
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


๐Ÿ’ก๐Ÿ’ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ’ซ๐Ÿ‘Œ๐ŸŒŒ


๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€
๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€
๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€
๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€๐ŸŽ€
๐ŸŽ€๐ŸŽ€
๐ŸŽ€


๐Ÿ“–๐Ÿ–Š Yusrah M Abubakar


DEDICATED TO
MY MOTHER I LUV U AND I WILL BE WITH YOU ALWAYS YOU ARE THE BLOOD THAT IS SCULATED IN MY HEART.



WANNAN PAGE DIN NA MALLAKA MAKA SHI KAI DAYA MY BROS ABDALLAH MUSA ABUBAKAR .



On the authority of Anaass (RA)who say:
I heard the messenger of Allah(peace be upon him)said:
"Allah almighty has said:O son of Adam,as long you invoke me and ask of me,I shall forgive you for what you have done,and I shall not mind".
It was related by Attirmidhi,who said that it was a hasan hadith.


'YAN UWA WANNAN PAGE DIN NA SADAUKAR DASHI GA DUK WANDA YA KARANTA LITTAFIN NAN DOMIN PAGE DIN YA TARA DUNBIN ABIM MAMAKI๐Ÿ˜œ.


#YUSRAHMS#
NO.13๐Ÿ‘‰ 14
Cikin dare safah data kasance a dakin ta a kwance tana bacci kawai taji hayaniya a kanta ta dauka mafarki take saida taji abin bana 'kare bane ta bude idon ta Asabe ta gani tsaye a kanta gaa wasu samari biyu da bata san su waye su ba.


Zaune ta tashi cikin mamaki tana kallon Asabe kafin tayi wani yunkuri taji Asaben na cewa"gata nan kuyi yadda kuke so da ita kuma bance ku tausaya mata ba zan kuma biya ku kudi mai dubun yawa idan kuka keta mata mutuncin ta kuka wulakanta ta".



Jin abinda Asabe take cewa a matukar gigice Safah ta mike tsaye tare da nufar kofar fita tare ta garadan sukai suna finciko ta zuwa cikin dakin daya yace"ke dalla zonan gidan uban wa zaki fita"?ya fada yana fisge hijab din dake jikin ta kara ta saki tana fashewa da kuka ta soma kwalla kiran BAFFA BAFFA ka taimake ni zasu kashe ni.


Dariya Asabe tayi tana cewa"ai yarinya ki daina bata bakin ki domin kin makaro baffan ki yasha maganin bacci bazai san me yake faruwa ba kuma zan baki gargadi idan har gari ya waye kika ce nice nasa a miki haka wallh kashe ki zanyi idan kunne yaji to jiki zai tsira".



Saboda tsabar Safah bata cikin hankalin ta batasan me Asabe take cewa ba damuwar ta rikon da wannan katon ya mata burinta ta samu ta shammace su ta gudu juyawa Asabe tay tana fita a dakin".


Yayin da dukka su biyun suka rufu a kanta kowa da inda ya nufa kuka Safah keyi mai taba zuciyar mai sauraron ta ganin fa idan ta sake da gaske zasu keta mata mutuncin da Asabe tace gashi danne tan da sukai ko motsin arziki ta kasa.


Idon tane ya sauka akan kwalbar data dora maganin sauro akai baima daina ci ba hannunta ta mika da kyar ta samu ta dauko ta daidai dayan ya mike tsaye zai cire wandon sa wanda yake riken da ita ta saici goshin sa wajan saman kansa ta kuwa yi sa'a yayi aski malu ta sakar masa duka akai da wannan kwalbar sakin ta yayi ba arziki yana ihun neman agaji da kiran ta kashe ni.



Da sauri dayan yayo kansa yana cewa"mu gani mai tayi maka"? ganin shima dayan ya maida hankalin sa gurin waccan yasa a zabure Safah ta mike tana fita a dakin cikin masifar tsinka gudu yayin da dayan ya ankara shima yabi bayan ta cikin mugun kakkarfan taku.


Da yake kauyen baida girma nan da nan tayi nisa da shi ta shiga wani irin daji tana kuka gashi batasan inda take nufa ba tanajin yadda kafar ta ke taka 'kayoyi tana zafi amma haka ta daure taci gaba da shiga dajin.


Tuntube ta kwasa ta fadi a kasa daidai wanda ke binta ya karaso kafin tayi yunkurin tashi ya bita ya danne da karfin tsiya tana ihu da neman agaji amma saida ya mata fayde kana ya tafi ya barta a gurin a kwance kamar matacciya.



Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a gigice cikin burkicewa Baffa ya farka daga wannan mummunan mafarkin da yay bala'in tada hankalinsa wanda tunda ya farka a firgice da gudu ya fito daga dakin sa ya shiga cikin gida yana salati jiki na rawa ya shiga dakin Safara'u.



Kwance ya same ta tana shara bacci zama yay a gefen ta tare da zuba mata ido cikin tausayawa yana kuma share gumin daya jike masa fuska bai iya barin dakin ba dan gani yake kamar ba mafarki yay ba wadannan samarin zasu iya zuwa bai sake iya runtsawa ba sai salati da yake ta yi.



Bai bar dakin ba saida akai kiran sallar asuba sannan ya mike da kyar duk jikin sa ya mutu ya fita a dakin alwala yay masallaci ma kasa zuwa yay sai a daki yay sallar sannan ya dukufa wajan addu'ar neman kariya zuwa ga 'yar Allah ya tsare ta a duk inda ta tsinci kanta.



Saida gari ya waye sosai sannan ya shigo domin ya duba lafiyar ta a waje ya same ta tana karatu ganin sa yasa ta shafa fatiha tana cewa"Baffa ina kwana" lfy kalau safara'u fatan kin tashi lafiya ina fatan babu abinda ya sameki "?kaita daga yaci gaba da cewa"to kinji motsi ko kinga wani abu da daddare wanda ya tsorata ki ko kuma kinyi mafarki"? Nan ma kai ta girgiza masa"a'a Baffa banyi mafarkin komai ba kuma banji motsin kowa ba"sauke ajiyar zuciya yay yana hamdala zaiyi magana akai sallama.


Duka juyawa sukai suna kallon hanyar kofar gida da mmk baffa yace "maryama kece yau a garin namu"?murmushi matar tay tana karasowa tace "eh wallh abubakar nan na kwana da yake shigowar dare nayi a gidan kawu Hakilu na kwana".


Cikin fara'a baffa yace to sannu da zuwa maraba lale gaskiya naji dadi yaushe rabon da mu gana saiyau "



Maryam tace"wallh dai ka ganni adamawa ta boye ni ina can yanzun ma dakyar suka barni na taho ina Asabe ne".



Dan shiru Baffa yay tuna mafarkin da yayi kafi yace "tana daki kila ko wani abu take"safah ce ta gaishe da ita tana mikewa zata dau tsintsiya maryam tace"waini wannan ko itace yar taka ne ikon Allah abin ba wuya harta girma haka sai aure kenan".



Murmushi baffa yay yana cewa"wallh ai lokaci ma muke jira yar gida za'ai da murtala dan wajan kani na".



Maryam zatai mgn Asabe ta fito daga daki tana cewa sannu bakin sassafe "tun kafin maryam tay mgn asabe tace to nikam midille"zuwa ina kenan cewa baffa "tafiya Asabe ta fara tana cewa gidan mu"maryam ta tari numfashin baffa da cewa "haba Indo da wannan safiyar kamar me yaji"bata saurari maryam ba tay waje.




Kai maryam ta jinjina gaskiya lamarin asabe sai a hankali maida kallonta tayi akan baffa tana cewa"idan har haka take taya wannan yarinyar take rayuwa gaskiya Abubakar akwai gyara a gidan ka nifa sai naji hankali na bai kwanta ba ".


Sauke ajiyar zuciya baffa yay yana cewa"kullum ina kokari maryama bana so ace yata daya na kasa rike ta amma na sani cewa safara'u zaman wahala take a gidan nan babu wani jin dadi baba malam(Na Allah)ya nemi na bashi ita ta koma gurin sa da zama saidai inajin kunyar hakan mutane zasu ga kamar na kasa banfi karfin gida na ba ni kaina cikin damuwa nake".


Wani mafarki ma da nayi ya mugun daga min hankali ji nake kamar naje na samu dan uwana a daurawa safara'u da murtala aure a yau ko hankali na zai kwanta da abinda na gani cikin mafarki".


Kai maryam ta girgiza a'a Baffa idan bazaka damu ba zan tafi da safara'u adamawa domin nima nanda wata daya zan dawo kaga idan tabar nan din shikenan muna dawowa kawai sai ayi bikin ta ina ga hakan zaifi amma me kace ".


Shiru baffa yai na dan lokaci kafin yace"na amince maryam ku tafi domin na yarda dake Allah yasa haka shine mafi alkairi".


Cikin jin dadi maryam tace"amin ngd baffa bari na koma gidan Hamza jibi zan tafi sai tayi shiri zuwa gobe to baffa yace yayin da maryama ta mike tana masa sai anjima.



Bayan tafiyar ta Baffa ya zaunar da safah yayi mata bayani kuma ta amince haka nan taji dadin barin garin da zatai bata san mene dalili ba ".


Baffa da kansa yaje gidan malam na Allah ya sanar dashi abinda ke faruwa kar kwana biyu su jita shiru zata dan bi wata kanwar sune zuwa adaamawa suma addau'a sukai sannan safah taje musu sallama suka mata nasiha".




Kamar yadda maryam tace bayan kwana biyu ranar da zata koma ta zo domin tafiya da safah nan fa bori ya hau Asabe tai ruwa tay tsaki ba inda safah zata je".


Maryama dake rike da hannun safa tace"saiki hana tunda yarki ce"asabe na jijjiga tace"wallh babu inda zata salon kije ki koyo mata iskanci malam kana gani kamar wanda ta asirce ka zata tafi maka da yarinya wata uwa duniya".


Ko sauraron ta baffa baiyi ba suka fita a gidan ya musu rakiya sannan ya sake bankwana da safah ya dawo gida"


Da bala'i kwando kwando asabe ta tare shi yana shiga ta mike"sannu da dawowa wanda ya rako maza duniya saki tumaki ballo jakuna wallh anyi asara kai kana nan ka bude hanci da baki yarka ta tafi binni ita kuma ana can ana koya mata yadda ake iskanc............


Cikin tsawa baffa yace"Asabe ya isheki bana son hauka shashashar banza shashashar wofi kawai wacce bata san ciwon kanta ba".yana fadin haka ya fice a gidan tsaki asabe tayi tare da cewa "Allah yasa a dirko mata ciki daga can ta dawo maka da abin kunya da zanfi kowa jin dadi ".




Sun sauka adamawa lfy a wani gida mai kyau inda anan maryam ke aiki ana biyan ta kudi mai tsoka wani bangare suka shiga a gidan har cikin dakin maryam tace ta huta kafin ta shiga cikin gidan ta dawo to tace mata.




Bayan fitar maryam zama safah tayi tana tunani Baffanta sai yanzun taji da bata biyo ta ba gara zama gaban babanta akan nan dukda bata ga komai anan dinba.


Tana cikin tunani maryam ta dawo da abinci a plate tana aje mata da pure water tace"Safara ga abinci kici saiki tashi kiyi wanka na fadawa hajiya tace na kaiki ta ganki kinsan me"?.



Kai safah ta daga maryam taci gaba "zance ta baki aiki kamar yan gyare gyaren kitchen da, goge goge kafin mu tafi zaki dan tara abin kanki tunda kinga aure za'ai miki dole akwai yar sayayyar da zakiyi ko"?.


Godiya safah tayi mata har taji yar damuwar ta taragu ta wannan hanyar tana bukatar wanda zai rika bata shawara haka amma batai dacen matar ubah ba.



Abdul-jabbar ne zaune gaban mahaifinsa suna mgn Emir ya dube shi cikin murmushi yana cewa"ya kamata kayi shiri kaje ka gano kakanun ka kila ma ka fara mantawa dasu laifi nane dana dade banje ba kuma ban kaika ba".


Dagowa Abdul-jabbar yay yana kallon shi yace"Abba ni kaina ina son maka tambaya akan haka domin ban manta suba kuma ina son naje na gansu".


Kai emir ya jinjina daidai Amfal ya shigo yace "hakan nada kyau yaushe zaka je"?kafin yay mgn Amfal yace "Abba gobe zamuje dan nima ina son zuwa".


To hakan nada kyau Allah ya tashe mu tafiya sai a fara shiri tun yanzu domin a tafi musu da abin arziki"Ammy dake labe ce ta shigo tana kallon Amfal tace "kaima naka kakanun zakaje ka gano yaushe rabon ka dacan harka manta amma yanzu kadau mazari da rawar kafa zakaje shishshigi".


Dan hade rai Amfal yay yana cewa"kaji Abba muna zancen mu "Emir dake kallon Ammy yace"dan bamu guri muna magana ne zuwa jimawa kya dawo".


"Dan bamu guri Ammy ta maimaita "eh haka nace yanzu lokacin ganawa da yaya nane naki lokacin sai anjima"juyawa Ammy tay tana fita cikin wani irin bacin rai ta koma part dinta".



Cikin tsawa tace da bayin dake ayyuka su fice su bata guri bata bukatar ganin kowa jiki na rawa suka fita idan da sabo sun saba ko ba'a bata mata raiba idan tay ra'ayi haka take musu balle yau da aka tabo ta.



Shigowar Hanne yasa ta mike tare da goya hannun ta a baya tana kaiwa da komowa dukawa hanne tay tana cewa"ran uwar gidana ya dade fatan ba wata matsala kamar naga kinadan cikin damuwa ".



Dakatawa da zaga palon tayi tana komawa kan cushion din ta zauna muryar ta da fushi tace"ba kama bane lallai hanne ciwon xuciya na neman kama nI sbd rashi kauna da Amfal ke nuna min hakan yana mugun daga min hankali ace dan da na haifa baisan gani na balle yazo inda nake dole zan tashi tsaye zama bai kama ni ba yanzu ba lokacin kwanciyar hankali bane meye mafita"?mema zanyi wacce hanya zanbi ta ina zan fara ya za'ai na kwato dana".


Kasa da murya hanne tayi tana cewa"ranki ya dade kar aji mu ya kamata mubi a huce zanje gida a cikin satin nan daga can zansan abinyi kafin na dawo zan taho miki da abinda zaki alfahari dani sai kinyi min kyauta mai tsoka tajin dadi".


Zama ammy ta gyara "kamar ya ban gane ba me kike nufi".


Hanne tace"ina nufin zanje gurin wani babban Malami ya yi mana duba akan mene dalilin da yasa danki bai damu dake ba kuma ya mana taimako yadda za'a raba kansu suji basa kaunar juna".



Sauke ajiyar zuciya Ammy tay "shin kin tabbata aikin zaiyi nasara "?.


Kwarai ranki ya dade ina da tabbaci aikin sa tamkar yankan wuka yake kuma yana ci sosai".


To lallai ina son haka idan kin tashi tafiya zan baki kudi masu yawa wanda zasu isa ayi komai tashi kije"mikewa hanne tay tana gdy ta fita".



Ammy taji matukar dadi gani take kamar ta faru ta kare bata son alakar shakuwar dake tsakanin Abdul-jabbar da Amfal ko kadan kuma ta daura niyya wannan karon sai tayi nasara .



๐ŸŽ€Mrs Al'ameen Ahmad ce,๐ŸŽ€


Mu kasance a koda yaushe one love kawaye da masoya.


YUSRAH CE MAI TAMBARIN Y M A ๐Ÿ‘Œ.




Typing๐Ÿ“ฒ


๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
SAFREEYYAH
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
ยปยซยปยซยปยซ ยซยปยซยปยซยป ยซยปยซยปยซยป ยปยซยปยซยปยซ


๐Ÿ“–๐Ÿ–Šยฅu$ยฎah Musa
###==###
#####
###
##
#.

Banga abin ambata ga dukka wanin daha ba shi daya xa a so guda bawai gaibu ba,kafi kowa kyauta sannu gwarzo na Khadija kai muke wakewa we ๐Ÿ’ž u manxon Allah peace be upon you.



#Team Safreeyyah}
#Team Abdul-jabbar}.
#Nima nasa kaina team Yusrah ๐Ÿ˜

Ku matso kusa ranar muce masoya ina gaisuwa da nuna kulawar ku gare ni na jina kwana biyu shiru da kukai kuma kuna ta aiko da text cewa, lafiya wallh kalau yan uwa jiya da shekaran jiya muna hidimar biki ne shi yasa kuka jini, shiru amma sakamakon nema na da kuke xan daure yau nayi page daya ko baida yawa ne na gode da kauna๐Ÿ’•.


To nima sai nayi nasara๐Ÿ˜  Ammy muje zuwa maman khaleel tahau lilo ๐Ÿ˜œwayyo dadi๐Ÿ™† .




#YUSRAHMS#
NO.15๐Ÿ‘‰ 16
Maryam ta samarwa Safah aiki a gidan kuma nan ba laifi mutane ne masu karamci domin babu wani kyama ko tsangwama da suke nuna mata domin yan matan gidan basuyi zaton aiki tazo ba duk zaton su ko yar wani mai kudin ce dan Safah ba baya ba kyan fulani farin fulani jinin fulani gaba da baya jawur take"'



Tsaye take a kitchen tana wanke wanke Salmah ta shigo da jaka a hannunta alamar fita zatai kallon Safah tayi tana cewa"Na Allah(haka suke ce mata tunda tazo suka ji sunan kauyen su sai suke tsokanar ta) please kafin na dawo a school kimin crispy onion rings da irin lemon da ki kaiwa aunty Abida ranar da saurayin ta yazo nima anjima zanyi bako".



Murmushi safah tay"anya salmah ban iya hadawa ba amma bari na tambayi umma maryam saita nuna min"ok dan Allah to dan Allah karki manta ki tsara min sosai"amsawa safah tayi yayi da salmah ta fice bayan ta gama wanke komai ta fita a kitchen a palor suka hadu da maryam fada mata abinda salmah keso tay dan haka kitchen din suka koma a hankali take nunawa safah yadda ake hadawa har suka gama kuma dukkan wani girki da zasuyi safah na kokari wajan ganin cewa ta haddace komai".



Washe gari sosai Emir yasa akai shiri suka kama hanyar kauyan malam na Allah sosai Abdul-jabbar ke farin cikin zaiga ahlin mahaifiyar sa har jin dadin sa bai boyu ba.



Alhmdllh sun sauka lfy yayin da suke kallon komai da kowa ba Abdul-jabbar daya dade baizo ba kuma ya manta garin hatta Emir da kansa mmk yake garin yayi mugun sauya masa kuma ya kara cika ba kamar da ba domin a da idan ka samu gida anan sai, kayi tafiya mai nisa ka samu wani yanzu kuwa garin a cike yake harda karamar kasuwa suke da ita.



Sosai malam na Allah ya sauke su hannu biyu da farin cikin sa wanda bazai misaltu ba yana kuma kallon wadannan kyawawan samarin da a ransa yana ayyana akwai jikan sa a cikin su dan gidan yarsa Fatima.





Shima Abdul-jabbar a nasa bangaren cewa yake wadannan suna suka haifi mahaifiya ta hakika ina matukar son su ina kuma burin kasancewa da su.



Emir dake murmushi ya kalle malam na Allah yana cewa"Baba ayi min afuwa na rashin zuwa akan lokaci da banyi ba bawai na manta daku bane sai yanayin mulki da yake da takura amma ina mai baku hakuri gani yau nazo na kawo muku jikanku ku ganshi shima ya ganku kamar yadda baku manta dashi ba shima haka yace min bai manta daku ba saidai baisan hanyar zuwa garin ba gashinan kusa dakai wannan kuma dan uwansa ne kanin sa Amfal".


Na Allah da tunda Emir ya fara mgn yake zubar da hawayen tuna yarsa ya zubawa Abdul-jabbar ido ya kasa mgn har saida Abdul-jabbar ya rike masa hannu sai kawai ya karasa fashewa da kuka .



Yana cewa "Allah sarki Fatima Allah ya jikan ki Da rahma yakai haske makwancin ki Sannu yaro kaji Allah ya baka hakurin rashin mahaifiyar ka hakika ina sonka kamar yadda nake son mahaifiyar ka fatan kaima haka".


Allah sarki rungume shi Abdul-jabbar yay ba tare da yayi mgn ba Hadiza ma na gefe tana sharar hawaye shi kanshi Emir jikin sa yayi sanyi sosai ganin yadda malam yake kuka da tsufan sa.



Basu iya hana malam kuka ba saida yayi sosai sannan ya share hawaye da murmushi akan fuskar sa ya kalli Emir yana cewa"ngd sosai muhammadu Allah yayi maka albarka kwarai naji dadi sosai kuma na sani koda ace Fatima baku hada jini da ita ba baza ka manta

Please Login or Register in order to submit comment