Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dade a min afuwa".


"Kece kika nad'a ta yayi kyau a Kira min ita ina son jin gaskiya".


"Dan Allah ranka ya dade kamin rai karka Kira ta nasan nayi kuskure amma zan gyara.


Kai Emir ya girgiza bai sake magana ba ya aika Kiran Hanne.


Wacce da kukanta ta shigo hannunta aka dama irin wannan ranar take tsoro ranar tonon asiri.


Tana zuwa ta kifa har Saida goshin ta ya tabo carpet saboda rawar da jikinta keyi kamar me jin tsananin sanyi.


"Kece Hanne sabuwar jakadiyar Adama wacce ta zaba"?.

Da sauri Hanne ta girgiza kai "a'a ranka ya dade ban karba ba".


"Meye hadin ki da ita har ta dangana hadarin da tai dake cewa laifin kine"?.

Shiru Hanne tai yace "fada min gaskiya ko yanzu na tura ki gidan yari ki karasa rayuwar ki acan".


Hanne da idonta kamar zasu fito waje jin abinda yace.


Tace "na shiga uku ranka ya dade ka gafarce ni wallahi zan fada".


"Ok yayi".

Goge gumin dake zuba mata Hanne tai tana cewa" na kasance tare da gimbiya Adama tun shekaru ashirin da uku da suka wuce.

Daga haka Hanne ta soma basu labari tun daga ranar data shigo part din Ammy sannan Abdul-jabbar yana shekara sha biyu ta tarar Ammy ta mare shi.


Da raka shi gurin hajiya datai har zuwa yaufa da Ammy taje ta kwankwatsa had'ari.


Sannan ta Dora da cewa ranka ya dade ni garkuwar sace ban taba cutar dashi ba haka ban Bari ko sau daya gimbiya Adama ta samu nasara a kansa ba.


Domin duk lokacin data aike ni gurin boka ina fita ne kawai daga masarautar nan Amma babu gurin wani boka da nake zuwa.

Dukiyar da take bani ma ban taba ci mata ko biyar ba tana can gurin kawata a wannan kauyen.


Ranka ya dade na biye mata ne domin ina jin tsoron karta samu wata su hada kai a cutar maka da danka.

Tun daga ranar Dana fahimci bata kaunar sa ni kuma na kasance inuwa gare shi nake gadinsa da kula da lafiyar sa ba tare da sanin kowa ba.

Amma ranka ya dade nasan nayi kuskure mai girma ina rokon ka da ka yafe min ba a son Raina bane na tuba".


Shiru kowa yai ya zubawa Ammy ido wacce ta sunkuyar dakai saboda tsananin kunyar abinda take boyewa yau ya bayyana harda abinda ta aikata ita kadai wasu taji Hanne ta fada ko da ya ta sani.

Kai Emir ya jinjina cikin mamaki wato wadannan abubuwan suna faruwa a masarautar sa bai taba sani ba shekaru ba daya ba ba biyu ba.

Ammy ya kalla yana cewa "Adama shin haka ne dukkan abinda ta fada gaskiya ne.


Dagowa Ammy tai tana kallon Emir dayai mugun hade rai zatai magana sai hawaye shar shar cikin tsananin jin kunya ta mayar da kanta kasa muryarta na rawa tace.


"Eh ranka ya dade gaskiya ne duk abinda ta fada na jahilci kaina gani nake kamar Abdul-jabbar ne ya raba ni da Amfal saidai yanzu na gane cewa laifi na ne".


"Na kasance kowacce Rana da kiyayyar sa nake kwana da ita nake tashi ban taba son saba saboda kishin da nai da mahaifiyar sa".


"Abdul-jabbar ya sha wuya a hannu na kafin ya mallaki hankalin kansa nabi hanyoyi da dama wajen ganin na kawar dashi amma hakan bata samu ba".

"Ko aura masa wannan yarinyar danai dan na kuntata masa ne nice nasa aka kashe masa dokin sa da salla sannan aka dora mata sharrin itace bayan bata San komai akan hakan ba".


"Duk wata damuwa da Abdul-jabbar zai shiga sila tace ko wannan hadarin danai na yau saboda nayi alkawarin bazai taba haihuwa a rayuwar saba kuma naga yara maza biyu ina tunanin 'ya'yan Amfal ne sakamakon har kurciya nasa a masa dan kar ya dawo".


"Sai Amfal yace ba 'ya'yansa bane yayan Abdul-jabbar ne shine hankali na yai mugun tashi bansan na dauki mota ba na tafi wannan kauyen gurin boka har nai hadari ba".

"Ranka ya dade alfarmarka nake nema nayi kuskure na aikata munanan abubuwan da basu dace ba na tsawon lokaci Amma Dan Allah kada kai fushi Dani wallahi na tuba zan gyara halaye na".


Banza me martaba yai da ita kamar ba dashi take ba ya dauke kai daga saitin ta cikin bacin rai da mamakin aiyukan data dade tana shukawa ba tare da sanin saba saboda ta mayar dashi biyo ta nan.


Ganin bata samu karbuwa a gurin saba ta juya gurin hajiya tana cewa "hajiya ki gafarce ni kuyi hakuri Dan Allah".

Mikewa hajiya tai tana cewa" a'a karki sako Dani babu abinda yai min zafi wannan tsakanin kune Allah ya shirye ki Adama" tana fadin haka tai waje.


Dole Ammy ta mayar da kallon ta kan me martaba daya tsime tace "ranka ya dade kayi hakuri kaban dama na karshe zan gyara kuskure na".

Mikewa Emir yai cikin fushi yace "ba damar haka komai yazo karshe" bude kofa yai ya fita domin bazai iya ce mata komai a yanzu ba zuciyar sa turiri take idan har ya tsaya yana kallonta baisan irin matakin daxai yanke mata ba.


Amfal daya fi kowa bacin rai akan wadannan abubuwan da Ammy ta aikata yace "gaskiya Ammy kinban mamaki keba uwa ta gari bace wacce za ai alfahari da ita nayi bakin cikin kasancewar ki mahaifiyar ta domin haka bai kare ni da komai ba sai damuwa Ammy ni ba d'anki babe domin kwata kwata baki dace dani ba bazan sake waiwayar kiba a cikin rayuwa ta".

Rike hannun Khairat yai zai fita da ita cikin damuwa Khairat ta riko shi tana cewa "dear kai hakuri Dan Allah karkai fushi Ammy mahaifiyar kace kasan duk lalacewar uwa uwace ka saurare ta yanzu ne ya kamata ku fahimci al'amarin uwa da d'a kai da it..............


Bata iya karasawa ba sakamakon tsawa daya daka mata sannan ya fige ta a tsiya ce kamar zata kifa yabar part din da ita.


Kuka Ammy ta fashe dashi na tarin nadama tana kallon Abdul-jabbar daya zuba mata ido tace.


"Na shiga uku na lalace ni Adama wacce irin rayuwa na tsinci kaina a ciki ranar tonon asiri tazo ina ma na mutu kafin zuwan wannan rana ta jin kunya da bakin ciki wayyo Allah na".

"Abdul-jabbar na hada ka da girman Allah ka yafe min abinda nai maka karka juya min baya kamar sauran nasan ka da kyakkyawar zuciya mai tausayi kayi hakuri".


Matsowa kusa da ita Abdul-jabbar yai yana kallon kafar data samu karayar yace.


"Ammy ki daina kukan haka shima wata cutar ne a gare ki".


"Kai ta girgiza"taya zan daina kuka bayan d'an Dana haifa ya kalli cikin idanuwa na yace ni ba uwarsa bace mai martaba yai fushi Dani hajiya tace babu hannunta nasan rayuwa tace tazo karshe".


"Ammy ki daina cewa haka ni na yafe ki ban taba rike kiba a zuciya ta kuma ban taba daina miki kallon uwa ba tunda nake ki dauka cewa babu abinda kikai min".


Ammy na kuka sosai tace "Abdul-jabbar ina matukar jin kunyar ka a yanzu na cutar dakai sosai".

"Babu komai Ammy karki damu ya wuce Abban mu da Amfal sunyi fushi ne idan suka huce zasu fahimce ki kuma zansa likita yazo ya duba ki".

Kukan Ammy ne ya karu jin abinda yace Wanda gashi Dan data haifa ya juya mata baya tace.


"Na gode na gode Abdul-jabbar Allah ya saka da alkhairi lallai nayi kuskure a rayuwa ta Dana kasa tsayawa na nutsu nasan cewa kai d'a ne na gari shashanci ya rufe min ido".


Mikewa Abdul-jabbar yai yana kallon Safah yace "princess muje".


Mikewa Safah Tai duk jikin ta yai wani iri Ammy data bita da kallo tace "kema ki yafe kinji Dan Allah karki duba abinda nai miki a baya.


"Babu komai Ammy Allah ya yafe mu gabadaya baki min komai ba na yafe miki".

Fita sukai suka bar Ammy na gurza kuka hannuwan ta biyu a kanta Marakisiyyah na gefe tari da bai kamata ba batai ba domin itama Tasha mamakin abinda Ammy din ta aikata Wanda batai tunani ba.


🍇 SAFREEYYAH 🍇

*If you don't know🤨 where you are going🤔 should know where you are coming from 😉.


#YUSRAHMS#
NO. 101 👉 102.
Tunda suka koma part dinsu komai Safah zatai a hankali kamar mara laka jawota kusa dashi Abdul-jabbar yai yana cewa" princess yadai"?.

Kamar zatai kuka tace" Allah Ammy ce taban tausayi duk jiki na yayi sanyi".


"Da gaske jikin ki yayi sanyi? Shiru tai yaci gaba "muje na dumama miki shi yanzun nan".


Jin abinda yace yasa da sauri ta mike zata gudu amma taji yai sama da ita yana cewa "haba my cutie jikin kine fa yai sanyi muje na baki dumi maybe twice dina su samu 'kani ko 'kanwa.


Zaro ido tai " 'kani kuma"?.


"Yes" shine abinda yace cikin dauke gira yana shiga bedroom da ita.

Nikam bazan bisu ba bacci nake ji😜 Bari na tsaya a palor.


Kullum sai likita yazo ya duba Ammy kamar yadda Abdul-jabbar ya fada sannan tsakanin me martaba da Amfal babu Wanda ya sake bi ta kanta.


Tayi kuka tayi roko tayi nadama mai tarin yawa da bakin ciki mara misalto amma kowa ya mata burus.


Haka rayuwa ta juya mata baya lokacin da ita kuma ta canza ta zubar da makaman yakin ta take so kowa ya fahimci ta zama ta kirki Amma babu hali.


Tun bata tafiya har tazo aka fara bata sanda guda biyu take dogarawa dasu tana dan zaga palon ta a hankali.


Samun me martaba Abdul-jabbar yai ganin watani sun wuce Amma har lokacin ya 'ki kula Ammy yaki bata lokaci suyi magana.

Suna zaune yace "Abba dan Allah alfarma nake nema a wajen ka".

"Ta me kenan babana"? Me martaba ya fada yana riko hannunsa.

Abdul-jabbar yace" dama magana ce akan Ammy Dan Allah kuyi mata hakuri kai da Amfal naga sauyi tare da nadama a tare da ita.


Kau dakai me martaba yai "babana bazan iya yafewa Adama ba cutar min kai da tayi ban sani ba har ta nemi karshe ka".


"Amma Abba Ammy tayi nadama ka saurare ta nasan tayi kuskure saidai kowanne Dan Adam ajizi ne"


"Nikam baba na gaskiya da harna yanke alaka tsakani na da ita dan bazan iya ci gaba da zama da ita ba ta ishe ni".

"Abba na roke ka kayi hakuri ka saurare ta karka sake ta tayi nadama Dan Allah kaje ka duba ta".


"Shikenan baba na zanje na duba ta saboda kai taci albarkacin ka".


Murmushi Abdul-jabbar yai "yauwa Abba har naji dadi da kace haka".

Rungume shi me martaba yai cikin tausayawa da kaunar sa yace "baba na kana da kyakkyawar zuciya Allah ya albarkaci rayuwar ka".

"Amin Abba na gode".


Ammy na zaune kamar mafarki taga Abdul-jabbar ya shigo bayan sa Amfal ne saidai ya hade rai fuskar sa ba walwala.

Ammy tasan Amfal mutum ne mai yawan fara'a zai wuya kaga fuskarsa ba annuri amma a yad lolda ta ganshi tasan sabida ita ne.


Hawaye ne taji ya cika mata ido gashi yaki kallon ma inda take kamar zuciyar ta zata soye saboda zafi tace.


"Amfal kayi hakuri abinda ya faru Dan Allah ka fahimce ni".

Kamar bazai magana ba sai kuma ya juyo yana kallon ta yace "Ammy me yasa baki hada ni kin cutar damu tare ba wai me bros dina ya miki ne a rayuwa ki fada min"?.


Jin abinda yace tuni Ammy ta soma zubda hawaye tace "Amfal babu abinda yai min kuskure da sharrin zuciya suka jawo na aikata masa Amma wallahi nayi alkawarin bazan sake ba kai dashi daya ne zan rike shi tamkar Dan Dana haifa".

Sauke ajiyar xuciya Amfal yai "Ammy idan har abinda kika fada haka ne naga canji bazan juri wannan abin ba".

"Wallahi Amfal gaskiya nake fada maka ka yarda dani na canza halaye na nabar hanyar boka".

"Shikenan" abinda Amfal yace bai sake magana ba.

Ammy tace" kenan baka yarda ba"?.

"No na yarda mana Ammy karki samu damuwa" durkusawa yai a gaban ta yana dafa kafafunta yace.

"Nima Ammy ki yafe min Dan Allah albarkar ki nake nema ke mahaifiya tace".

Kuka Ammy keyi tace "na yafe ka Amfal Allah ya maka albarka".

"Amin yace murmushi Abdul-jabbar yai yana cewa "na gyara wannan al'amarin".

Tun daga wannan rana Amfal ya sake mata kamar komai bai faru ba kullum suna part dintma ko basu zo ba zata aika ai mata Kiran su.


Sai dare kowa yake tafiya part dinsa a lokacin Khairat ta kusa haihuwa sosai suke kula da ita.

Zarisha kam takai wata uku da haihuwar yaronta namiji an saka masa sunan Abban Safwan.


Hanne tunda ta samu ta fita daga zargi babu ruwanta da shiga safgar kowa ta kame kanta.

Jakadiya ma tana nan kuma tayi farin cikin ganin irin son da Abdul-jabbar ke nunawa Safah tayi murna.


Twice sun girma har sun fara tafiya yara kyawawan kamar su daya sak ba'a iya banbance su sai idan suna ka Kira kaga mai sunan ya kalle ka Amma a haka baza kace ga Hassan ko ga Hussain ba.


Yan satika da basu wuce shida ba Khairat ma ta haihu itama dai baby boy murna kamar ba gobe gurin ahli ranar suna Amfal ya sanya masa sunan bros dinsa Abdul-jabbar.


Wanda kowa yayi farin cikin ganin irin shakuwar dake tsakanin su Abdul-jabbar shida Safah sunyi bajinta sosai sun bada mamaki.



Safah na zaune a palor taci kwalliya twice na gefen ta kowa rike da teddy suna wasa Abdul-jabbar daya shigo ya zauna kusa da ita.

Yana kallon ta yace "mumyn twice kina fama bari na Taya ki raino".

Murmushi tai zatai magana taji yace "am princess ki shirya gobe ina son zamuje garin mahaifiya ta ya kamata na kai ki domin su ganki".

Kai ta jinjina tana cewa "Allah ya kaimu".


Washe gari tayi mamakin ganin harda Ammy a tafiyar a lallai ta canza ga Fatima da me martaba dasu Amfal".


Tunda suka dauko hanya Safah ke bacci har suka shigo kauyen bata sani ba Saida akai parking Abdul-jabbar zai mata magana yaga ma ita baccin ta take shararawa.


'Dan shafa fuskar ta yai a hankali yana kissing lips dinta dake shinning sakamakon Jan baki me kyalkyalin data shafa.


A hankali ta bude idanunta tana kallon shi dan murmushi ya mata yana dora hannunshi a saman rigarta yadda breast dinta ya cika ya dago yace.


"Princess mun zo ki tashi" sai lokacin tadan kalli garin ta glass din motar zabura tai tana sake bude girman idonta muryar ta na rawa tace.


"Wannan ai kamar garin mu nake gani"?.


Kallonta Abdul-jabbar yai cikin mamaki yace "garin ku? Ke kuma me ya hada ki danan garin bafa a jihar kano muke ba".

Baki ta bude zatai magana ya hanata ta hanyar Dora nasa bakin akan nata jin ana kwankwasa glass yasa ya kalleta yana cewa muje.

Bude mata kofa yai ta fito sannan shima ya fito Amfal dake gefe ganin babu Jan bakin Safah a lips dinta kuma abinda yake zargi kenan cikin tsokana yai gyaran murya.


Yana cewa "bros yadai naga kayi wani iri"?.

Wani kallo Abdul-jabbar ya masa ganin yana dariya yace "mene damuwar ka me yasa ka fiya sa ido ne"?.

"Babu komai bros muje" wucewa sukai yayin da zuciyar Safah Tai bala'in tsinkewa jikinta yadau rawa sosai suna shiga taga abinda take zargi.

Cikin tashin hankali tace "malam Hadiza kune ko ido nane yake nuna min haka"?.


Dagowa na Allah yai ya zuba mata ido nadan lokaci cikin mamaki yace "kamar Safara'u nake gani dama kina raye 'yarnan ina kika shiga haka a duniya shekaru da yawa"?.

Durkusawa tai a gaban su tana fashewa da kuka tace "malam nice fatan kuna lafiya ina Baffa na yake"?.


"Baffan ki yana nan lafiya Safara'u kwantar da hankalin ki".

Hannu Safah ta rikewa malam tana kuka sosai tana kuma kallon su Dan gani take kamar gizo suke mata ba gaske sune a gaban taba.


Abdul-jabbar dayai suman tsaye zuciyar sa na bugawa cikin alamar tambaya yace "wai malam ka Santa ne"?.

Murmushi na Allah yai yana kamo hannunsa yace "ai Abdullahi itace 'kanwar taka yar uwar taka da nake fada maka ta 'bata".


Wata irin zabura yai yana kallon Safah da ita ma a razane ta dago tana kallon shi.

Muryarsa na rawa yace "wai kana nufin itace sister na data 'bata"?.

"Eh Abdullahi itace kaga ikon Allah ko ashe tana raye bamu sani ba".


"My cutie wai dama kece yar uwar tawa ban sani muna zaune tare ni ina neman ki ya akai kika je masarautar mu"?.

Numfashi Safah ta sauke me nauyin gaske tana cewa "tun rana da ana gobe daurin aure na Baffa ya Kira ni dakin sa yana min fada aka ce ana Kira na a waje.

Da naje nayi tunanin murtala ashe ba shi bane Musaddiq ne Wanda na zauna a gidan su lokacin da naje adamawa".

Malam ne ya katse ta "shine ya sace ki kome"?.

Kai Safah ta girgiza "a'a bashi bane shine dai silar Bari na gida kuma daga nan rayuwa ta juya min har zuwa yanzu".

"Wani abu ya miki"?.

Shiru Safah tai kamar baza ta fada ba sai kuma ta soma basu labarin tun daga zuwan ta gidan su mk komai bata boye da kuma dalilin zuwansa daukar fansa saboda ta tona masa asiri".


Malam da mamaki ya gama cika shi yace "to ya akai kika je kano har masarautar su Abdullahi kuma baki nemi dawowa gida ba"?.

Kuka Safah ta fara tuna irin bakar wuyar da tasha a hannun hajiya dasu marwa ga uwa uba Ammy nan ma ta musu bayanin da yadda taje masarautar da irin zaman datai har zuwa auren su da kuma yanzu.


"Wai kina nufin kedin matar aure ce kinyi aure kuma matar Abdullahi"? malam ya tambaye ta cikin tsananin mamaki.

Kai ta daga tana nuna masa twice dake kusa da Fatima tace "harda yara biyu muke dasu daya sunan mahaifin sa daya sunan Baffa na".


Kai malam ya jinjina yana kallon dukkan su biyun wannan karon ya kasa magana.

Kowa mamaki yake a gurin yana kuma girmama al'amarin kamar tatsuniya.

Jitai Abdul-jabbar yace "bani address din gidan su wannan yaron".

Da sauri Safah tace "me zakai masa"?.

Kai tsaye ya bata amsa "hukunta shi zanyi mataki zan dauka a kansa me karfin gaske Wanda saiyayi nadamar zuwan sa duniya".

A rikice Safah tace "a'a ka rabu dashi karka masa komai ni na dade da yafe masa".

"Ni kuma ban yafe masa ba saiya gane kuren sa" Ya fada yana mikewa tsaye zai fita.

Da gudu Safah take ta rungume shi ta baya ba tare da jin kunyar kowa ba tana kwantar da kanta a bayan sa cikin kuka tace.

"Kaine kace idan mutum yai maka sharri ka bishi da alkhairi kaine kace Allah yana son masu yawan yafiya Dan haka ina rokon ka da ka yafe masa".

Juyowa yai yana goge mata hawayen yace "ok ya isa shikenan".


Suna cikin haka sai ganin Baffa sukai ya shigo a burkice yana kwalla Kira.

"Safara'u na kina ina da gaske kece kika dawo"?.

Jin muryar Baffa yasa ta dagowa daga jikin Abdul-jabbar ta tafi da sauri ta rungume baffan.


Maimakon ace itace zatai kuka saiga Baffa yana kuka sosai kamar yaro.

Yace "Safara'u dama kina raye dama zan sake ganin ki a ido na kafin na mutu ina kika shiga ne"?.

"Kayi hakuri Baffa nima bada Sona na barku ba kaddara ce ta gifta min dole sai nayi nisa da ku kuma hakan ya zama min babban alkhairi".


'yan gari kam sai tuttudowa suke suna zuwa kowa ya ganewa idonsa cewa da gaske ta dawo.


A guje murtala ya furtsimo cikin taro ya shigo yana haki kamar ransa zai fita yace.


"Safara'u dama kina raye ina kika shiga kika barni da ciwo da damuwa dama kullum ina fadawa Baffa kina nan zaki dawo baki mutu ba".

Cikin tausayawa Safah tace "Murtala kaine"?.

Farin ciki sosai murtala keyi yace "nine Safara'u ina nan ina ta jiran ki ashe zaki dawo"?.

Gaban tane ya fadi da sauri ta kallo Abdul-jabbar da ya zuba musu ido ganin tana kallon sa ya sake hade rai yana dauke kai daga saitin su.


Jikin tane yai sanyi ta kalli murtala da murmushin dole tace "na dawo murtala".

Zama malam yasa sukai ya bude taro da addu'a da nuna farin ciki da godewa Allah sannan ya nunawa Baffa twice matsayin jikanunsa da kuma labarin da Safan ta basu.


Kasa nutsuwa Baffa yai sai kallon Safah yake yana mamaki kuka suka ji Wanda kowa ya juya yaga waye.

Murtala ne ke nuna Safah idonsa jawur yace "da gaske Safara'u kinyi aure kin manta dani ni ina nan kullum ina tunanin ki ina damuwa dake na rike alkawarin dana dauka a zuciya ta.

Kowa tausaya masa yake hatta Abdul-jabbar da yaji kishi ya kama shi saida yaji mugun tausayin sa ganin irin son da yakewa Safah da jiran dawowar ta da yake.


Tashi yai yana kuka yabar gidan domin bazai iya jurar ganin taba kuma bayan ta haramta a gare shi ita matar aure ce yanzu.


Bayan komai ya wuce an nutsu sai sannan aka gaisa me martaba yace a ranar zasu wuce Adamawa masarautar su Fatima Amma malam ya hana su tafiya yace sai sun kwana sai washe gari suka tafi.

Amma Amfal da Khairat basu bisu ba Safah na gidan Baffan ta wanda tunda taje Asabe ke kuka tana neman gafarar ta.

Safah Kam ta nuna mata babu komai ta yafe mata dama ita bata rike taba".


Washe gari Abdul-jabbar da Amfal suna cikin zaga gari suka biyo ta lambu mai kyau Wanda kana gani saiya burge ka.

Amfal dake kallon kyan lambun yace "bros ya kamata mu shiga mu gano ciki".

"Saboda me? Idan kuma masu lambun basa nan fa"?.

Amfal dake kokarin shiga yace "kalli kofar a bude take da alama akwai mutum Dan Allah muje".


Shiga sukai cikin sa'a suka hango wani dattijo a zaune cikin tsakiyar lambun inda ya kafa karamar rumfar hutu.


Da sallama suka karasa inda yake amsawa yai yana kallon su yace "samari daga ina"?.

Amfal daya ga kwandunan tumaturi da yawa gashi jawur d'aya ya dauka yana cewa "amma baba a shekara kwando nawa kake samu"🤔🙊?.


Dagowa dattijon yai yana kallon Amfal yace "kwando buhun uban ka nake samu🤣".

Baki Amfal ya bude yayin da Abdul-jabbar yai murmushi yana jinjina fitinar tsohon.


Yace "kayi hakuri baba".

Dattijo dake kallon Amfal yace "ka rabu dani yau nake ganin fitsararran yaro ya kuttun sayi kodai gwamnati ce ta turo ku kuji idan ina samu da yawa a sauke min haraji".


Abdul-jabbar yace "Dan Allah kayi hakuri baba bazai sake ba bamu da had'i da gwamnati".


Kallon tumaturin hannunsa Amfal yai yana sake kallon tsohon yace "kasan waye uba na kuwa"🙄?.

Mikewa dattijo yai yana dauko sanda yace "waye uban naka muje na ganshi🙈"?.

Da gudu Amfal ya fita daga lambun😜 hakuri Abdul-jabbar ya sake bawa tsohon sannan ya fito.

A bakin hanya ya samu Amfal sai haki yake kallonsa yai sai kawai yaji dariya ta kama shi.


Yace "wato garin tsokanar ka yau ka gamu da Wanda ya fika fitina".

Share gumi Amfal yai yana kallon lambun yace "kai wannan tsoho akwai masifa daga tambaya harda wani dauko sanda zai rad'e kamar Wanda yaga 'bera😂.

"To da me ya gani ina kayansa ka dauka masa daya rade kama ko sannu bazan maka ba".

"Kuma ni saina tsaya ya rade kamar ba matashi ba".

Kallonsa Abdul-jabbar yai "a haba sannu matashi ina fuka fukan tashin suke tunda naji kana neman mayar da kanka tsuntsu".

Dariya Amfal yai "bros muje kawai kada wannan dattijon ya biyo bayan mu".

"Oh ba kana da kafar gudu ba"?

"A'a nidai muje ko hanyar nan bazan sake biyowa ba" wucewa sukai suna yin kasuwar garin.


Bayan kwana biyu me martaba suka dawo shida su Fatima suka sake kwana daya sannan suka wuce kano harda su Amfal aka bar iya Safah da Abdul-jabbar.


Safah nason zuwa Adamawa gidan su mk amma sam tayi bi tayi lallashi Abdul-jabbar ya hana ta dakyar da kukanta ya barta taje.


Hajiya tayi murna tayi mamakin ganin ta lokacin da batai tunani ba balle kuma baba Maryam .

Har gidan Salmah Saida Safah taje Alawiyyah ma tai aure itama taje gidanta Amma bataje gidan Abidah ba.

Mk daya ganta yazo gaishe da hajiya duk yabi ya susuce ya rasa inda zaisa kansa saboda kunyar tuna abinda yai mata.

Farko ya fuske ya tuna idan bai nemi yafiyar taba lallai alhakin ta bazai taba barinsa ba domin bayan abinda yaiwa Safah masifu sun biyo baya a kansa.

A gaban hajiya da baba Maryam ya roki gafarar ta sannan ya fada musu shine silar batan ta da abinda ya kai shi kauyen shekarun baya.

Kuka yasa hajiya ta kama yi tana baiwa Safah hakuri its kuma tace babu komai ta dade da yafe masa.


Sannan aka nuna mata wata yarinya dake gefen hajiya cewa yarsa ce kuma sunan ta Safah.


Godiya Safah ta masa na takwara dayai mata kwanan ta uku ta koma kauyen su da abin arziki sosai Wanda hajiya da mk suka hada mata.



WASH ALLAH

Please Login or Register in order to submit comment