Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tay hanyar fita Abdul-jabbar daya bita da kallo yace "alhaji zaki fadawa ba hajiya ba itace zata zauna min dake nike da damar zabar matar aure na".


Bata tsaya sauraron saba ta fice.


Dan murmushi Amfal yay cikin tsokana yace bros marakisiyya ce ta dace dakai ka manta lokacin da muka je garin kakanin ka kace kai baza ka auri karamar mace ba sai zundumemiya kaga zama yazo daidai da faduwa.


Harararsa Abdul-jabbar yay ina kake so nakai wannan girman nata ya wuce yadda nake so kalli a girman jiki ta fini a tsayi zamuyi kai daya so kake idan mun jera muna tafiya a rika zaton aunty nace".


Dariya Amfal yay ba wani auntyn ka ai kowa ya ganku yasan ka fita kana cikin matsala tunda ta raba gurin hajiya dama kullum zancen ta muyi aure sai kace itace zata zauna mana da matar.



Dan taje gurin hajiya ma ni abin ko dara ni baiyi ba dama gurin mami na tace zataje sai naji hankalina ya tashi amma hajiya buhun shiririta".


Bude baki Amfal yay hajiyan guda kake cewa buhun shiririta tana yabon ka sallah saika kasa alwala".


"Dan Allah Amfal ka isheni tashi kaje ba Ammy ce ke neman kaba ka tsaya gulma".


Mikewa Amfal yay oh i forgot thank you for reminding me dan wallahi da shirin baccin rana ma nake".


"You are not serious Amfal meke damun kane"?.

"Kana son yin wasa da tunanin Ammy".


Zama Amfal yay yana kallonsa yace but....

Katse shi Abdul-jabbar yay but what? let me advise you whatever you do in life you must use your time to get what you want musamman akan Ammy karka fada hallaka mahaifiyar kace ina fada maka".


Kai Amfal ya daga thank for your advise that's why i like you because you are a good brother nagode bari na dawo".


Fita yay yabar Abduljabbar shi kuma ya mike yana shiga bedroom yadan huta kafin ya dawo".


Part din Ammy Amfal ya shiga tana ganin sa ta saki murmushin farn ciki zama yay kusa da ita cikin ladabi yace" barka da hutawa Ammy na fatan kina lafiya".



Fuskarta wasai tace" lafiya kalau nake dan albarka saika ji kira ko".


Eh amma dama ko bata jeba inada shirin zuwa gaishe dake".


Mikewa Ammy tay ta shiga bedroom sai gata da kofi ta fito tana mika masa tace" ga abin sha Amfal karbi".


Kai ya girgiza batare da yayi magana ba.


Hade rai Ammy tay me kake nufi? Baza kasha ba kome wai Amfal zan cutar dakai ne kaifa dana ne taya kake tunanin zan baka abinda nasan me illa ne"?.


Kallonta Amfal yay Ammy ki fahimta ba ina nufin zaki cutar dani bane a'a kawai na koshi ne".


Ajiye kofin Ammy tay cikin komawa kalar tausayi tace" shikenan bazan maka dole ba saidai ka sani banji dadi ba bansan ranar da zaka yarda dani ba".


Sauke ajiyar zuciya yay to Ammy na kiyi hakuri bani zansha".


Da sauri ta suro kofin tana mika masa karba yay dan taji dadi ya soma sha yayin data rasa inda zata sa kanta ganin komai yazo karshe.


Da kuka sosai marakisiyya ta shiga gurin hajiya wanda tana ganin ta a haka ta soma tambayar ta".

"Ke yarnan lafiya meya faru kike kuka keda waye fada min".


Ji tay ance da nine hajiya kukan ta mara hujja ne karma ki bata lokacinki gurin tambayar ta wani abu".


Kara volume din kukan ta marakisiyya tay tana cewa" wallahi hajiya kuka na me dalili ne domin shine yasa ni meye laifi na meya rage ni da ban cancanti aso niba hajiya meye aibu na"?.


Babu fa yarnan wa zaice baki ba yarinya me kirki kamar ki irin ku ake nema a hada jini dasu".


Goge hawayen fuskarta tay tace amma duk wannan yabon nawa da kikai ban yiwa jikan kiba baya sona yaki fahimta ta bansan meyasa ba dan Allah hajiya ki ganar dashi".



"Tofa Amfala ne me wannan aikin ko tunda kikace jikana nasan saidai shi tunda shine aljani kanin shedan".


Kai marakisiyya ta girgiza hajiya ba Amfal ba gashi nan kusa dake shine nake so hajuya ki taimaka min ya amince zai aure ni wallahi ina son sa".


Kallon Abdul-jabbar dayai mugun hade ransa hajiya tay tana cewa dama da kaine Abdullahi amma kayi girman kwabo na dauka da Amfala nema kai shiru kamar bakai a falon".


Kara daurewa yay to hajiya me zance bayan na fada mata bana ra'ayinta ko karya take so nayi bana yin duk abinda zai takura min".


Gyara zama hajiya tay yadda zata fuskance shi sosai tace to amma Abdullahi abune da ake neman sa yazo mana har gida kullum magana shine kuyi aure ga lokaci yazo kake neman zillewa".



Wanne lokacin ne yazo ai hajiya kiyi hakuri bance baza kiga aure naba amma gaskiya babu ranar yinsa ba shine a gaba naba".


"Gaskiya Abdullahi baka isa ba dole kai aure ko baka so tunda kuma anyi haka zansa ai min kiran baban naku shima Amfalan dole ya fito da wacce yake so idan ba haka akai muku ba inaga saikun tsufa kamar ni ba mace".



Mikewa Abdul-jabbar yai yana kallonta yace amma hajiya aure idan kaga zaka iya zama haka bai zama tilas basai idan kana tsoron fitina ko fadawa halaka sai kayi toni ba daya dan me zaki takura min".


"Saboda ni ina so naga jikanu na sunyi aure".


"Karki damu lokaci ne zamuyi ko ba yan ranki" yana fadin haka ya fice.


Da kallo hajiya ta bishi marakisiyya datai shiru tana sauraronsu jin yaki amincewa yasa taci gaba da kukanta tana cewa dan Allah hajiya ki taimake ni kada ciwon zuciya ya kama ni".


Dawo da kallonta kan marakisiyya tay wacce ta dage bil hakki tana kuka tace "karki damu yarnan ki kwantar da hankalin ki ki rabu dashi zan samu mahaifin sa".


Kai marakisiyya ta daga cikin jin dadi tace nagode hajiya Allah ya saka da alkhairi".


"Amin karki damu kinji komai yazo karshe".


Mikewa marakisiyya tai cikin murmushi taiwa hajiya sallama ta fita koba komai tasan yanzu tamkar ta aure shine haka take ji a ranta.


Fada hajiya ta kama in banda shashanci a nuna ana kaunarka kana zamewa kaida kake na miji ba kaine zaka rika bibiyarta tana ja maka aji ba sai kace a wasan kwaikwayo bari nasa amin kiran uban naku naji idan shine ma ya karanta muku kar kuyi auren saiya fada min naji".


Marakisiyya na shiga part din Ammy ta saki wata zazzafar guda me sauti sosai wanda saida Ammy ta toshe kunnen ta 🙉".


Cikin harara tace Ashiru kike zubawa wannan shedanin karar bani ba dan uban ki me ke damun kine yarinya kamar wacce aljanu sukaiwa gida aka".


Murmushi marakisiyya tai tana nufar hanyar bedroom tace" aiko da abba na ne a gurin sanda na shigo sai nayi gudar nan balle iya kece ki taya ni farin ciki na kusa zama amarya".


Cikin alamun tambaya da nuna kokin fara zarewa Ammy tace amaryar uban wa"?.


Dariya marakisiyya tai kai amaryar Abdul-jabbar man kisa ido zaki ga komai za kiji kira daga mahaifin su domin gurin hajiya naje nay kamun kafa".


A zabure Ammy tace wai kina da hankali kuwa kinsan me kike fada".


Fari da ido marakisiyya tai kwarai na sani mana kece dai kika kasa fahimta hankalina rass zaku sha biki".


Mikewa Ammy tai cikin bacin rai tace" marakisiyya shiga ki tattaro kayan ki baza ki sake kwana a masarautar nan ba tunda ke mitsiyaciya ce".


Dariya sosai marakisiyya take wanda Ammy tai tunanin koda gaske bata cikin han kalin ta tace.


Ni da masarautar nan mutu ka raba yanzu na sake samun sabon kusancin da yafi da bazan koma gida ba sai naga an tsayar da maganar aurena dashi dan haka ki kara hakuri".


Tana fadin haka ta bude kofa tana shiga tare da rufowa da karfi.


Dafe kai ammy tay na shiga uku na ni Adama sai yaushe hankalina zai kwanta a masarautar nan dana farajin dadi sai wani bala'in ya fito kai karya kike marakisiyya har abada bazan bari ki auri Abdul-jabbar ba koda zan tafi tsirara😱.


Yanzun kam alhamdulillah jikin Safah ya warware yadda basu yi tsammani ba domin tana iyayin komai da kanta kuma tana magana ba kamar da ba.



Kwata kwata Ammy ta kasa gane kan marakisiyya ta daina wuni a part dinta sai gurin hajiya ba dama tai mata magana sai tace aure shawara ta yankewa kanta kawai wacce taga ta dace.


Kallon hanne tay tana cewa dalilin da yasa na kira ki shine maza ki koma gurin boka a yau yau din nan basai gobe ba domin marakisiyya nason kashe ni".


Hanne tace to ranki ya dade amma me za'a ce masa"?.


Kudi me bala'in yawa Ammy ta nuna mata a cikin jaka tana cewa ki tafi masa da wannan idan kin fita ki tsaya kise kayan abinci masu yawa da rago kikai masa wannan aikin dazai min yafi na ko yaushe".


"Kice masa ina miko gaisuwa sannan kice inaso ya rufe min bakin me martaba da hajiya da bakin Fatima inaso zanyi wani abu idan na fada karsu tanka min kawai su amince".


Cikin zulumi da faduwar gaba Hanne tace to amma ranki ya dade komai yana bukatar shawara idan kuma kin gama yanke komai saina tafi".


"Kai Ammy ta jinjina hanne marakisiyya keson sani na shiga uku wai ta. rasa wanda take so sai Abdul-jabbar shine nake son na raba su ta hanyar yi masa aure".


A firgice hanne tace ranki ya dade kin samo matar da zaki aura masa ne"?.


Eh hanne saboda na wulakanta shi darajarsa tay kasa a cikin bayi zan zaba masa kedai ki tabbata aikin yayi dan wallahi bari kiji idan ma dungu kikai bakije ba kika dawo zan gane wannan lokacin so nake komai yazo karshe".


Jikin hanne na rawa ta mike tana cewa to ranki ya dade yadda kika ce haka za'ayi".


"Shikenan jeki ina sauraron ki nan da kwana biyu kada ki kuskure min".

"To zan kula zanyi duk abinda kika ce saina dawo" bayan fitar hanne murmushi Ammy tay tana cewa.


"Lokaci na yanzu zai fara Abdul-jabbar kai kuma yanzu naka sabon shafin damuwa da bakin cikin zai bude zaka gane ruwa ba sa'an kwando bane saina mayar dakai abin tausayi🙄.



Kamar yadda Ammy ta umarci hanne haka dole tay a wannan lokacin saboda gudun karta huce haushinta akanta boka kam yace aiki ya riga yaje sai biyan bukata daga baya.



Fitowar Ammy tana tafiya cikin isa yasa dukkan bayin da suke zirga-zirga dakatawa suna dukawa banda Safah da Zarisha wadanda suke shirin shiga part din Fatima.


Sawa tay akai mata kiran su taga wadanne isassun ne saida suka zo ta kare musu kallo tana cewa" .

dama nasan saike wannan fitsararriyar yarinyar kina matsayin baiwa amma duk wani abu da bayi keyi saiki rika nuna kinfi karfin yi ko".


Safah data riga tasan da ita take dagowa tay tana kallon cikin idonta batare da tay magana ba tasan idan tayi maganar ma wani laifin zata sake".


Cikin tsawa Ammy tace ke mayya ki daina kallona kina baiwa zaki dallara min ido nayi miki kama da gyatumar ki"?.


Takaici ne sosai ya kama Safah mikewa tay tana kallon Zarisha tace tashi muje kowa ma bawan ne".

Wani irin mari Ammy ta sauke mata kowa ma bawa kina nufin wato nida ke daya ne shiyasa ban isa ki duka min ba zaki gane kinyi kuskure".


Wasu bayi ta kalla cikin fushi tace ku kaimin ita part dina ku tsaya ku jire min ita harna dawo yau saikin gwammace mutuwa akan rayuwa".


Wucewa tay su kuma suka figeta kamar zasu yaga ta harda su Basira wadanda suka ji dadin abinda yake faruwa".


Kuka zarisha ta shiga part din fatima tana yi wacce take zaune tana shirya yaranta cikin mamaki tace" yar gidan jakadiya lafiya meye ya faru ko wannan yarinyar ce ta rasu"?.



Kai Zarisha ta girgiza cikin kuka tace ba rasuwa tay ba ta samu lafiya har tana yawo yanzu nan ta taho ta rako ni nayi aiki shine uwar gidan sarki tay kiran mu ta mare ta kuma tace a wuce mata da ita part dinta".


"Ok yanzu tana can part din nata"?.


"Eh tana can wasu bayi ne suka tafi da ita" mikewa Fatima tay tana fita.



Amfal na zaune yaga an shigo da mutum ana ja cikin bada umarni yace a sake ta sakin ta sukai sai sannan yaga ashe yariyar nan ce da bros dinsa ya mara.


Kallonsu yay me ta muku kuke janta"?.


Cikin hadin baki suka ce samu gimbiyar sarki tay tace mu kawo mata ita nan".


Ku sake ta tashi kije".


Godiya Safah tay tana fita daidai Fatima zata shiga suka hadu tace" kece ko me suka miki"?.


Kai Safah ta girgiza bata nan danta ne yace su sake ni".


Tsaki Fatima tay muje mutum ya girma amma ya kasa rike girman sa.


Har part dinta suka koma tace suje suyi aikin su wucewa sukai cikin jin dadi dan sunsan ko Ammy tazo saidai ta karaci hargowar ta.


Hanne ta cika burin Ammy don yadda ta umarce ta haka ta aikata kuma da alama aikin yaci tunda ta gwada kuma tay nasara".


Zaune suke gaban me martaba Ammy tay gyaran murya cikin son gwada sa'ar ta duk da tana shakku tace.


"Ranka ya dade baban Hassan da Husaini na Fatima ikon Allah dama wata shawara na kawo saidai bansan a yadda zaka dauki maganar ba".


"Kamar ya wacce irin shawara ce wannan"?.


Gyara zama Ammy tay tana dan soshe-soshe tace" dama ranka ya dade cewa nai kullum lokaci yana kure mana kwanaki saija suke gashi duniya na gudu amma bamuyi abinda ya dace akan yaran nan ba".


Me martaba da har lokacin bai fahimci inda ta dosa ba yace fito fili kimin bayani ban gane ba".



Dan shiru Ammy tay tana tunani a ranta ta fada ko karta fada zuwa can tace" dama akan auren yaran nan ne ya kamata ace kowa yana da iyalin sa amma naga ko maganar ba'ai.


Murmushi Emir yay kinyi gaskiya Adama dakyau amma ga mahaifiyarsa nan saiki tuntube ta idan ta amince shikenan".


Wiki-wiki Ammy tay cikin takaici tana kallon Fatima amma sakamakon so take burinta ya cika yasa ta kadar da zancen tace"


"To me kike gani umman sa".


"Yayi dama kullum burina kenan naga yarona ya girma kimarsa ta sake fitowa nagode da wannan shawara taki uwar gidan sarki".


Aran Ammy tace ahaf kimarsa ta fito kota dishashe ai bashi da sauran kima daga lokacin da liman yace fatiha tsakanin sa da wannan baiwar".


Dawowa tay daga zancen zucin da take jin me martaba yace" ke Adama kece zaki wuce gaba domin wannan yarinya yar kanin kice hajiya ta same ni tun kwanan baya cewa tana son babana ya auri wannan yarinyar marakisiyya me kike gani shi kuma Amfal sai a nemo masa auren khairat yar gidan aboki na
".


Wani irin yankewa gaban Ammy yay ya fadi zuciyarta ta sauya bugu numfashinta na fita da sauri tace".


"Ayya ai ranka ya dade wannan an yi mata miji lokaci kawai ake jira a daura mata aure".


"Kash banji dadi ba yanzu ya za'ai to dan gaskiya bazai yiwu yana babba ace Amfal ya riga shi aure ba".


Ammy tace ranka ya dade naji kace khairat wacce suka taba kawo mana ziyara ita da maman ta yar abokin ka masarautar katsina ita kake nufi"?.


"Eh ita nake nufi yanzu damuwa ta babana shine matsalar".


Cikin farin cikin jin Amfal yar sarki zai aura dama sanda suka zo saida ta raya ina ma Amfal dinta ne zai auri wannan yarinyar ashe hakan zata faru".


Kallon me martaba tay alamar tunani yake tace" ranka ya dade da zaka amince kuma ka yarda dana fada maka wacce ya dace ya aura domin yarinya ce me hankali nutsatstsiya ba ruwanta da hayaniya ga ladabi".


"Wacece ita a ina take tunda harkin yaba da hankalin ta".


Gaban Ammy na faduwa cikin shakkar yadda zai dau maganar tace" a cikin kamilallun bayin masarautar nan take ranka ya dade ka yarda dani wallahi yadda kasan sarauniya haka take da cikar kyaun siffa ta dace dashi ta ko'ina".


Kallonta sosai me martaba keyi wanda saida taji dama bata fadi maganar ba can ta tsinkayi muryarsa yace.


"Shikenan tunda kince kin yaba da ita Allah yasa haka shine mafificin alkairi kuma yasa shine silar farin cikinsa yasa yarinyar ta zama garkuwa a gare shi".


"Amin abban mazaje nima na amince da haka da bawa da sarki duk daya ne sai wanda yafi wani tsoron Allah" Fatima ta fada.


Yayin da Ammy ta rasa inda zata sa kanta saboda murna ganin tarkon ta ya kama kurciya lallai ta yarda da aikin wannan bokan zata sake zage dantse.


Tsoma baki tay kuma kaga ranka ya dade bayi zasu sake ganin kimarka domin zasuyi tunanin suma suna da daraja".


"Gaskiya ne Adama kinyi kokari sannunki kin cancanti jinjina".


Cikin fara'a Ammy tace ai ranka ya dade ba komai yiwa kaine dashi da Amfal duk daya ne".


"Shikenan babu damuwa zan samu hajiya duk abinda mukai da ita zan kira ku".


Tab kamar ya yayyafawa Ammy ruwan kankara haka take jin sanyi na ratsa ta sai hura hanci take tasan komai yazo karshe yanzu zata fara juyinta a gaban Emir.



Gidan bariki misalin karfe tara da rabi na dare zage-zage Seeyah keyi tana hura usur kamar. zata tashi gidan wanda ba arziki kowa ya fito daga daki yaga meke faruwa".


Cikin masifa Samha ta kwace usur din tana cewa" ke dalla jaka uban me akai miki zaki wani damu mutane da hura wannan banzan abin"?.


Cikin bacin rai Seeya tace wallahi bazan yarda ba yan gidan nan na gaji da rainin wayon da ake min a kitchen idan na dora abinci kafin nagama sai an sata min dan bala'i yau kuma aka biyo ni har daki na gama yiwa saurayina farfesu kafin naje sayo juice na dawo na samu wata shegiyar ta shiga ta kwashe min rabin naman".


Tsaki marwa tay jimin shashasha shine zaki damu mutane uban me zamuyi da nama saidai mu baki keya dama waya sani ma ko kece kika cinye saurayin naki yazo shine kikewa mutane borin kunya".


Koma dai me zaku ce min dole in fada bazai yiwu a dake ni a hanani kuka ba saina fada duk bankadaddiyar data san ta shiga ta dauka min wallahi tayi gaggawar dawowa dashi kafin taci kaniyar ta".


Dariya Samha tay tofa kunji yan gidan nan wanda ya dauki jagwalgwalon farfesun ta ya dawo mata dashi kafin taci kaniyar sa".


Shewa suka saki gaba dayansu wanda yasa seeyah tsalle ta damko wuyan Samha nan suka fara dambe yayin da wasu ke musu kida wasu na waka an rasa me raba su".


Hannun rigar Samha Seeyah ta fincike tana jefar shi a kasa wanda hakan ya sake tunzura Samha jin an kaure da dariya.


Yasa ta riko wuyan rigar Seeya taja da dukkar karfinta sai gashi ta yaga rigar daga diri-diri saurin rufe kirjinta Seeya tai da hannunta cikin takaicin abinda Samha din ta mata".


Ihu gurin ya dauka yeeeeh ahayye nanaye ayyuriri ana yi muna jin dadi ana bari muna jin haushi yau munyi kallo a bati ina gayun gidan nan kuzo ku kalli tv".


Jin abin yaki karewa yasa saurayin seeyah fitowa ganin ta tsakiyar taro gashi ba riga yasa ya furmutsa ya shiga ciki yana riko hannunta suka fito.


Samha data raka seeyah da harara tace yanzu na nuna miki makomar ki banza kawai an fada miki kowa irin kine".


Juyowa seeyah tay ba hakura nai ba ki jira gamuwar mu saikin yabawa aya zakin ta zaki gane fankam fankam bata kilishi".


Kowa watsewa yay yayin dasu marwa suka wuce daki cikin mamaki suka ga Abaseey sai dariya take harda kyakyatawa tana rike ciki.


"Ke kuma lafiya wannan haukan na meye haka".


Tsayawa da dariyar Abaseey tay tana dauko wani babban plate tace ga abinda nake wa dariyar nan".


Zaro ido sukai a tare dama kece kika sace mata kajin"?.


Gira Abaseey ta daga a gaba na ta gama farfesun ga kamshi da yake zubawa saici take ni kuma yawu na yana tsinkewa shiyasa bayan fitarta sayo juice din nabi har daki na kwaso rabo na ku zauna mu debi gara aini ko a sama kake girki dan taken rowa idan naga dama sai naci".


Zama sukai kowa na yagar inda yake so suka fara ci marwa tace shegiya ashe dai ta iya girkin na dauka kafar baya ce".


Samha tace da muna shiri da ita gobe idan kalos zaizo ita zan bawa tayi masa amma in nai haka na aje abin fada gara na burbura da kaina".



Abaseey dake santi tace ki bari goben ma idan farfesun zatai saita gama zamuyi mata musanye dama baza mu sa maggi a ciki ba haka zamu dafa kamar abincin mayu kome kuka ce".


Dariya sukai kwarai Abaseey kin iya kawo shawara haka za'ai gaskiya ke tantiriya ce bari gobe tayi muga wanne irin hauka zatai idan mukai mata musanyen".




SAFREEYYAH



💫ANNURI WRITERS📝 HOME🏡 OF HOSPITALITY🤗 AND HARMONY🕊.




#YUSRAHMS#
NO.81👉 82
Yau take juma'at babbar rana Su Amfal na zaune a palon su suna dan hira ta yan uwa shida Abdul-jabbar wani bawa yay sallama yana dukawa cikin ladabi yace.


"Barkar ku da wannan lokaci fatan kuna lafiya sako daga me martaba yace a kawo muku wannan kayan ku saka su idan lokacin masallaci ya karaso ku same shi a fadarsa".


"Yayi jeka" mikewa bawan yay yana fita yayin da Amfal ya bude kayan yana cewa.


"Wanne irin kayan ne wannan"?.


Fitowa dasu yay dakakkiyar shadda ce shakwara da jamfa tasha aiki ga sabin takalma da huluna duk iri daya masu mugun kyau sai kyalkyali suke".


Kallon juna sukai yayin da Amfal ya zaro ido waje Abba ne ya dinka mana kayan nan kace yau wankan namu ne ko baka gani bane bros"?.


"Nagani Amfal Allah ya sanya alkhairi gaskiya ne Abba ya fito damu".


Ya karasa maganar a hankali ga yaji duk jikinsa yayi sanyi lokaci guda dan lumshe idonsa yay ya soma karanta addu'a.


Bros bari naje na shirya da wuri dan kada lokaci ya kure ya kamata kaima ka tashi ka shirya muje domin lokacin ya karaso".


Bude ido Abdul-jabbar yay yana kallonsa kafin ya kalli agogon dake daure a hannunsa ganin lokacin kadan ya rage yasa ya sauke ajiyar zuciya yana mikewa suka shiga bedroom batare da yayi magana ba".


Emir na zaune shima yaci uban kwalliya yana jiran suyaji ana musu kirari alamar sun shigo daidai ya mike tsaye sukai sallama.


Da kyakkyawan murmushin sa ya tare su yana bude hannuwan shi alamar su taho gare shi rungume shi sukai cikin jin dadi ya fara jero musu addu'a suna amsawa sannan yace su tafi masallaci kada lokacin sallah yya gabato suna gida.


Fita sukai suna shiga mota daya da abban su gashi abinda ya bada mamaki sunga bakin fuskoki ga tarin jama'a makil ga motoci ta ko'ina abin ba magana.


Anan zuciyar Abdul-jabbar ta sake tsinkewa sabanin Amfal daya kalleshi cikin tsokana yace" Allah bros dan baka ga kanka a mirror bane bakaga yadda kayan nan sukai matukar yi maka kyauba kamar ango".


Kai Abdul-jabbar yagirgiza humyim yaro baka da hankaline zan tanka maka amma bari mu dawo daga masallaci idan har babu abinda ya faru saina biye maka".


"Lallai bros mezai faru ka kwantar da hankalinka sallah zamu je".


"Naji to rufe min baki".


Murmushi me martaba yay yana kallonsu cikin burgewa wato koda kwana daya mutum ya fika toya fika Amfal bai ankara ba amma da yake Abdul-jabbar ya girmeshi shi yasha jinin jikinsa amma Amfal na warkajabe walle dinsa.


Bayan anyi sallah juma'a mutane na kara taruwa kamar anyi busa wanda ya kasa fahimtar hakan maimakon anyi sallah a watse sai a kuma taruwa tome za'ai.


Bai nutsu ba saida yaji 'kishin-'kishin din ana tambayar baban Zarisha wazai mata wali ya sunan babanta sannan yaji jikinsa ya fara rawa.


Mahaifin Zarisha shi yace zai karbi wali sannan ya fadi sunan mahaifinta kamar yadda ya tambayi matarsa jakadiya ita kuma da lallami ta tambayeta ta fada mata.


Anja lokaci sosai anayin abu daya wanda har hakan ya basu mamaki.


Dan tsaki Amfal yay nifa bros rigar nan ta ishe ni gaskiya gashi Abba yaki tasowa mu tafi kome suke ina ganin fakar ido zanyi na fece gid.....


Bai karasa maganar ba ya tsaya tsam tare da kamewa guri daya jin abinda ake shela.


"Eh masha Allah alhamdulillah Allah yayi an daura auren babban yaron sarki ABDUL-JABBAR MUHAMMAD ABDUL-JABBAR DA MATARSA SAFARA'U ABUBAKAR akan sadaki naira dubu dari biyar lakadan ba ajalan ba".


Wani irin juyawa kan Abdul-jabbar keyi ga uban gumi da yake tsatstsafo masa ta ko'ina a jikinsa lokaci guda ya nemi dukkan nutsuwar sa ya rasa".


Amfal zaiyi magana yaji ance sannan an daura auren kanin sa AMFAL MUHAMMAD ABDUL-JABBAR DA MATARSA UMMUL-KHAIRI ABDUL-HAMID akan sadaki naira dubu dari biyar lakadan ba ajalan ba.


Dafe kirji Amfal yay tare da zaro ido sai kuma jikinsa yadau rawa kaf kaf kaf kamar me

Please Login or Register in order to submit comment