Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muddin akace babu shi to nima bazan rayu ba".


Wani irin shako wuyan rigarsa Ammy tai tana mikar dashi tsaye idonta fal da hawayen bakin ciki tace" inji uban waye yace dan uwanka ne Amfal ka fara hauka ne ka bude idanunka dakyau ka fahimci masoyinka da makiyinka.


"Idan har shine ya samu dama irin taka kake a kwance bazai kiyin hawan ba amma da yake kai shashasha ne baka gane ba".


Banbare hannuwanta Amfal yai daga jikin rigarsa yana cewa wai Ammy meke damun kine me bros dina ya tare miki da bakya kaunarsa".


Cikin karaji tace ubanka ya tare min umarni nake baka ba shawara ba idan ka dauke ni matsayin uwa kaje ka samu me martaba kace zakai hawan zaka wakilce shi domin ko ka 'ki ko kaso kaine magajin shi Abdul-jabbar ba tashi zaiba".



Tana fadin haka tajuya fuuuu ta fice daga part din tana maimaita kalmar zata tsine masa idan bai amince ba".



Zama Amfal yai tare da dafe kansa/ da hannu biyu lallai baiyi farin cikin kasancewar Ammy matsayin mahaifiyarsa ba gara ace ya taso maraya zaifi samun walwala farin ciki da kwanciyar hankali.



Dafa kafadarsa Khairat tai cikin tausaya wa da kuma mamakin bakin hali irin na Ammy domin tana jin komai daga bedroom bata fito bane saida taji tafice.


Muryarta a sanyaye tace dan Allah kayi hakuri mahaifiyar kace kada kayi fushi zamu samu mafita daga abinda take so".


Dagowa Amfal yai cikin damuwa yace taya me kike tunani akan Ammy tana da wuyar sha'ani nayi matukar damuwa da dan uwana fiye da yadda kike zato".


"Na sani domin nima shaida ce hanya mafi sauki zamu bi wajen ganin komai ya koma daidai".


"Taya kenan wacce hanya ce"?.


Zama kusa dashi Khairai tay tana cewa zaka karbi hawan ne".


Kai ya girgiza ko kadan bazan/yi ba".



"Yauwa to hanya mafi sauki idan ka amince ranar hawan nida kai zamu sa mata maganin bacci shikenan kaga idan ta farka kace mata kayi zata ji dadin kabi umarnin ta".



Shiru Amfal yai yana kallonta cikin nazarin maganar data fada.


Gyara zatai tana cewa amma idan baka amince ba sai mu samu wata hanyar".



"Bawai ban amince bane a tunaninki Ammyce zata yarda ta amshi wani abu daga hannun mu tasha a wannan lokacin bazata taba yarda damu ba".


"Zata yarda kaidai kabar komai a hannu na".


"Shikenan Ummul na yarda dake" murmushi tai tana kallonshi ta dan jinjina kai.



Safah na zaune a palor ita kadai ta dafe kuncinta da hannu biyu cikin tsananin damuwa da rashin kwanciyar hankali ga wata rama datai kamar ba ita ba.


Jitai an sheke da dariya a saman kanta tare dacewa "a'a kaga matar gawa ana zaman jiran tsammanin ne gara kibar bata lokacin ki wajen tunani Abdul-jabbar ya mutu boye miki suke".



Murmushi Safah cikin halin ko in kula tace a haba da gaske labari me kyau taya kika sani"?.


"Dama aina fada miki kowa yaci tuwo dani miya yasha zaki dandana kudarki yanzu da bashi dawa zaki ta'kama"?.


"Dacan ma banyi takama dashi ba kece kike daukata a haka amma duhun jahilcin ki bazai barki ki gane hakan ba".



Wata dariyar marakisiyya ta kuma shekewa da ita tana nuna Safah tace "Yanzu zagaye nane lokacina ne tunda kika shiga tsakani na da abin kauna ta kema bazaki karajin dadin duniya ba wannan alkawari na ne".



"Mu zuba nida ke tunda har kina tunanin nida ke daya ne saboda kin auri jinin sarauta zan gwada miki wace ni".



"Saina mayar dake abar tausayi a masarautar nan kuma zaki gani".


"Oh da gaske? Kai amma dakin burge bari na fada miki wata magana ki adana duk wata kazamar kalmarki yanzu bani da isashshen lokacin haukan ki mijina ne a gaba na".



"Ke nice zaki cewa na adana kazamar kalma ta me kika dau kan ki"?.



"Wannan tambayar keya dace ayiwa ita domin karamar kwakwalwarki na bukatar service".



"Kenan mahaukaciya kika mayar dani "marakisiyya ta fada cikin takaici".


"Baki Safah ta tabe tare da mata wani kallo daya kusa kwareta tace" kusan haka n auke da a tunaninki kanki daya sorry madam ki koma asibiti".


Cikin tsawa marakisiyya tace ya isheki kada ki nemi fada min bakar magana".



"Abu na karshe dazan fada miki dan nasan zaiyi matukar yi miki amfani shine nice silar kwanciyarsa jinya kuma boka na ya fada min cewa bazai taba tashi ba kuma duk da kinsan komai bazaki iyayin komai ina matukar tausaya miki matar gawa aci gaba da jiran tsammani".



Juyawa tai tafice cikin gadara tana karkada jiki Safah data bita da kallo aranta tace kenan tana nufin asiri ta masa taya zan ceto rayuwarsa".



Ganin Fatima tashigo yasa cikin ladabi ta sauka daga kan kujera tana durkusawa ta gaishe daita.


Dan murmushi tai tana dagota tareda maida ita kan kujera tace" ya jikin naki kin samu sauki"?.


Sunkuyar dakai Safah tai idanunta nakawo hawayen damuwa taya zata fara fada mata yadda sukai da marakisiyya a daina shan wahalar asibiti adawo gida a nemi maganin gargajiya".


Ganin tayi shiru yasa taci gaba kinga yata idan har baki warke ba ki fada min idan munje asibiti a sake duba ki"?.


Kai Safah ta girgiza tana dagowa ta kalleta zatai magana ta kasa sai kuka data ji yazo mata.


Rike hannunta Fatima tai tana cewa kinga saurara ki daina kukan nan haka karki karawa kanki wata matsalar".



Cikin kuka Safah tace taya hankalina zai kwanta bayan na kasa gane gaskiya".


"Wacce gaskiya"? Fatima tafada cikin yanayin mamakin maganar Safan.



Kukan Safah karuwa yai muryarta narawa tace mami ya mutu boye min kuke meyasa baza ku fada min ba"?.



Dan zaro ido Fatima tai ke kuma waya fada miki".


Safah tace "Dan Allah mami naroke ki idan harda gaske ya mutu ki daina boye min".


Murmushi Fatima tai tana cewa ko daya bai mutu ba kibar tunanin haka albishin ki yau kwanansa biyu da farkawa kawai ba a bayyana bane kuma kema dana fada miki karki fadawa kowa".


Tsayawa Safah tai cak da kukan tana goge fuskarta kamar wani zai rigata tace ya farka"? To amma zai iya tashi zaune ko tafiya"?.



"A'a bana tunani domin ko ajiya me martaba da mukaje ya mika masa hannu ya tashi kaiya girgiza kuma ya'ki yin magana".



Zaro ido Safah tai bazai iya tashi ba kenan".



"Bani da tabbacin hakan".


"To mami muje na ganshi tunda ya farka ina son ganinsa".


"Karki damu zaki ganshi amma me martaba bai bukaci hakan ba ki kara hakuri".


"To mami zanyi abinda kikace idan kunje kice inai masa sannu".


"Yauwa yata Allah ya albarkace ki kisa ranki a inuwa bari naje nabaro su husaini su kadai kada sumin barna sun fara rashin ji".


Mikewa tai tana fita yayin da Safah tashiga bedroom da gudu tana fadawa gado ta rungume filo ita kadai ta kama dariya cikin farin ciki".



Washe gari da wuri suka tafi asibiti wanda dama basu sanarwa Ammy ba duk da bawai sun fahimci tana farin ciki akan jinyar tasa bane domin ita a zatonta asirin boka ne.



Yana nan kwance kamar yadda yake tun ranar daya farka me martaba na zaune kusa dashi fuskarsa fal da damuwa.


Shigowar Fatima ganin me martaba ahaka yasa ta fahimci ya'ki yin maganar ne.


Cikin tausayawa ta kalleshi tana cewa baiyi maka maganar ba har yanzu ko".


"Bana jin zai iya maganar abin yana bani tsoro babana bazai share niba tunda nazo nake masa magana amma saidai ya kalleni da ido".


Kallon Abdul-jabbar Fatima tai zata masa magana bazato suka ji yace" ina take"?.


Dukka zabura sukai cikin mamaki me martaba yace" ina take wa kenan wa yake nufi"? Ya fada yana kallon Fatima.


Murmushi tai tana cewa matarsa yake nufi tunda kaji yace ina take".



Gasa'ke me martaba yai yana kallon dan nasa cikin tsananin mamaki wato itace aransa yau kwana uku suna binsa yayi musu magana yaki lallai kam ikon Allah sai kallo.


Mikewa yai yana cewa muje daga waje Fatima ki turo masa ita ko zamu dace ya karasa warewa" .



Suna fita da kamar minti goma tashigo jiki asanyaye ta tsaya a bakin gadon kallonta yake sosai kamar yadda itama take kallonsa.


Yana daga kwancen ya miko mata hannu alamar ta daga shi matsawa tai kusa dashi sosai tana sa dukkan hannuwanta biyun ta dagoshi tayi tunanin zata jishi kamar kullum amma sai tajishi ko rabin nauyin da baiyi ba.



Zama tai a bakin gadon kawai ta zuba masa ido babu ko kiftawa ahankali taji yace" yau kwana na nawa a asibiti"?.


Sauke ajiyar zuciya tai daidai ya rike hannunta alamar jiran amsa kuka takama wanda batasan dalilin yinsa ba tana cewa.



"Ranar dakai tafiyar labari zuwa min yai baka raye nayi kuka na shiga damuwa da bakin ciki marar misaltuwa dana tuna cewa babynka zai taso maraya baisan mahaifin saba kamar yadda baka san mahaifiyar kaba".



Cikin rashin fahimtar zancenta yace" me kike nufi wanne irin baby kuma"?.


Dan sauke kai tai cikin jin kunya tace" babyn ka".


"Baby na kamar ya"?.


Shiru tai daga haka ta kasa bashi amsa tunani ya shiga yi akan maganarta zuwa wani lokaci ya kalleta yana cewa" kina nufin ciki ne dake๐Ÿ™Š"?.


Kara kasa tai da kanta ta kasa bashi amsa dago da fuskarta yai tai saurin rufe ido".


"Ciki ne dake" ya tambayeta a karo na biyu.


"Kaita daga tana dan kawar da fuskarta zaro ido yai cikin wani irin yanayi ciki dai na haihuwa take nufi kenan ya kusa zama dadyn baby a rika kiransa baba".



Numfashi ya sauke yana daga kansa sama yace alhamdulillhi bi ni'imatihi .


Juyo da fuskarta yai saitin inda yake yana kallon cikin idanuwanta fuskarsa da annuri yace" thank you my wife no one but you".


Dora nata hannun tai akan nasa da ke rike da fuskarta zatai magana sai kuma takasa ta saki murmushi".


Gira ya dage cikin alamar tambaya murmushin me take kaita girgiza tana cewa" kaine ya kamata a godewa".


"Meyasa za'a gode min ni kadai batare dake ba".


Shiru tai ya cigaba" kodan nine nai cikin๐Ÿ™ˆ"?.


Da sauri ta kifa kanta a jikinsa cikin kunyar abinda yafada.


"Ki bani amsa amma ance love me love my dog ko (maso uwa๐Ÿ‘ต yaso d'anta๐Ÿ‘ถ) duk wanda ya soni bai soki ba bai cika ba kuma ba masoyina bane saboda ke mata ta ce mother of my children".


Cikin tsananin jin dadi da farin ciki Safah ke kallonshi ko baice yana sonta ba tunda bai nuna mata kiyayya ba babu kamarsa".


Dan kasa yai da murya yana kallonta yace kada kowa ya san cewa kina da ciki ki rike sirrin a zuciyarki daga ni saike".


Ji sukai ance" sai kuma ni babu wanda zan fadawa".


Kallon kofar shigowa sukai cikin mamaki Abdul-jabbar yace Amfal amma tun yaushe ka shigo"?.


Zama Amfal yai a kujerar dake gefen gadon yana kallonsu shima da mamakin maganar da yaji sunayi wanda bai taba kawowa aransa Abdul-jabbar ya taba kwana daki daya da Safah ba duk abinda yake a tsokana yake daukarsa".



"Amfal nace yaushe ka shigo tunanin me kake"?..


Murmushi Amfal yai yana cewa wayyo bros na kusa zama small dad ka taya ni da murna ashe aunty na ta kusa bamu baby"๐Ÿ˜?.


Tsimewa Abdul-jabbar yai yana kallonsa yace ba wannan na tambaye kaba yaushe ka shigo nace"?.


"Me kike nufi wanne irin babyn kuma tun lokacin daka fadi haka na shigo".


"Am dan Allah Amfal kada naji maganar nan a bakin kowa sirrice kamin alkawari".

"Allah bros nai maka alkawari babu wanda zaiji".


"Yayi ina abban mu"?.


"Yana can ya shiga damuwar rashin maganarka da kin tashin ka ashe kai kana nan kana soyewa".


"A'a ka manta konewa nake jeka kira min shi".


Mikewa Amfal yai cikin tsokana yace ka fadi gaskiya bros domin konewar kuke irin wannan kallo haka" sai kuma yasa dariya yana fita".


Shigowar su me martaba yasa Safah mikewa da sauri zata bar gurin riketa yai tareda girgiza kai.



Kallon me martaba yai yana cewa" Abba".


"Na'am babana yaya jikin naka"? Ya fada cikin mamakin ganinsa a zaune".


"Na samu lafiya abba mu tafi gida".


"Mu tafi gida kuma ka bari saika sake warwarewa".

"Allah abba zaman asibitin ya isheni".


"Tofa babana yaushe ka farka kasan kana asibitin dahar ya isheka"?.


"Tsaya ma na tambayi likita yace baka da ciwon hawan jini amma meyasa kake yawan suma da salla ma ankawo min labarin ka fadi waime ke damun kane".


Dan shiru yai taya zai fada musu akan batan sistern sane sauya zancen yai da cewa abba zan fada maka amma saimu biyu".


"To amma babana abar maganar sallamar nan yau".

"Allah abba ka fahimce ni bazan iya sake kwana anan ba".


"Shikenan bari naje gurin doctor da dare zan turo a dauke ka domin yanzu idan mun koma hayaniya zata dameka".


Kallon Safah Fatima tai taso mu tafi".


Ba kunya Abdul-jabbar yace mami abarta anan zamu taho tare".


Fatima bata sake magana ba dan dama tsokanarsa take haka suka tafi suka barsu su biyu.


"Cikin tsokana Amfal ya leko yana cewa bros ko na zauna nima mu tafi atare"?.


"Ban gayyace kaba jeka".


"Ohni Amfal muhammad wato bros aure dadi ko tona fece" ya fada yana rufe musu kofa.


Kamar yadda me martaba ya fada cikin sirri da dare aka zo aka daukesu wanda babu wanda ya sani acikin enemies dinsu.


#Comment
#Vote
#Follow.


#YUSRAHMS#
NO.93๐Ÿ‘‰ 94
Ammy kam ba kunya ko nuna damuwarta akan rashin lafiyar Abdul-jabbar da batasan ya dawo gida ba taje gurin me martaba tana kas dakai.


"Tace ranka ya dade dama akan maganar hawan da kukai da Amfal ne naji shiru gashi gobe ne shine nazo na sake shaida maka cewa mun zauna dashi yace zai wakilce ka".



Murmushi me martaba yai domin daga ji yasan shirin tane yace to dakyau saidai ma na hutar dashi".


"Meyasa ranka ya dade shi ya kamata ya wakilce ka domin shine jininka magajinka".


"Nasan da haka amma yanzu babu maganar wakilci da kaina zanyi hawana".


Cikin rudewa Ammy tace ranka ya dade zakai abin kunya kuma mutane zasu zageka danka yana can rai a hannun Allah kace zakai hawa ka tuna fa a icu yake kuma jinjiyar motsinsa bata harbawa amma zakai shagalin salla".


"Kwarai Adama nine ya kamata nayi abina da kaina domin kama da wane bata wane".


Wani abune ya tokare wuyan Ammy garin yin gyaran murya ya kwareta ta soma tari me martaba na kallonta tayi ta gama muryarta a shake tace".


"Ranka ya dade shawara nake baka kada bakin mutane ya kamaka ka bawa Amfal hawan nan saboda larurar danka".


"Wai waye ya fada miki yana asibitine an bashi sallama yana cikin masarautar nan".


Wata zabura tai a razane tace me? ya warke dama ya farka ya tashi ne yana yin tafiya ko a'a".


"Yana yin komai da kansa cikin walwala kamar da".


Kukan bakin ciki Ammy ta fashe dashi harda dora hannu a kanta tace wayyo Allah".


Cikin mamakinta me martaba yace wayyo me kuma kukan na meye".


Dan daidaita nutsuwarta tai ga wani 'kululin bakin ciki daya rufeta najin ya tashi kenan aikin boka baiyi ba kome".


Ganin irin kallon tuhumar da me martaba ke mata yasa ta share hawaye duk da sunki tsayawa tana gogewa wasu na zubowa tace".


"Ranka ya dade kukan farin cikine kullum da tunanin halin da yaron nan yake ciki nake kwana nake tashi ba dare ba rana inata addu'a Allah ya amsa rokona ya tashi kafadunsa".


"Shakka babu ya warke Adama sannunki da kokari ya fada cikin basarwa danya san karya take abinda ta fada wayancewa tai".



Mikewa Ammy tai tana goge fuska tace 'shikenan ranka ya dade sai anjima".

Kafin Emir yai magana tuni tai waje ba kunya a hanya tana tafe tana kuka hannunta a ka๐Ÿ™†.



Washe gari ranar sallah ce kowa sai farin ciki yake gashi tazo da juma'a babbar Rana Abdul-jabbar bai fita ko ina ba yana part dinshi tare da matar shi.


Suna zaune a palor ba zato ko jin sallama sai ji sukai an sheke da dariya ana cewa.


"A'a mijin baiwa yadai ana fama dama na fada maka saina kaskantar dakai na mayar dakai abin tausayi na hana ka jin dadi kuma buri na ya cika".


Dagowa sukai ganin Ammy tsaye kuma itace ke maganar yasa Abdul-jabbar yace.

"Sannu Ammy fatan kinyi salla lafiya ina Amfal bros dina"?.


Hade rai tai "ban sani ba, ba wannan ya kawo niba".

"Ok yayi kinzo duba ni ne"?.


Ammy tace "Allah ya sauwake a matsayin ka nawa"?.


"A matsayina na d'anki ko ban dauka daidai ba"?.


Wani kallon barazana Ammy ta masa tana cewa "d'ana? Tabdijan lallai sai yau ka sake tabbatar min da cewa jinyar dakai ka fita daga hayyacin ka na tsawon wata guda ya fara taba maka kwakwalwa.


Koda kuskure kada ka sake min kallon uwa a wajenka ni Amfal ne dana kaidai ka nemi taka kodan ta sheka ni ban taba sonka ba kuma bazan soka ba har abada.


Bari kaji wata magana na aura maka baiwa ne dan na wulakanta ka na nunawa bayi matsayinka baka da wata kima a idanuwansu.


Kasan ya akai na kamo lagon ka na kuma aura maka wannan yarinyar saboda kace duk duniya babu Wanda kaji ka tsana sama da ita.


Ni kuma sai nayi amfani da wannan damar wajen kuntata maka tare da tilasta ka aure ta domin nayi alkawarin hana maka farin ciki a rayuwarka to ya kaji irin salon nawa"?.


Sosai Abdul-jabbar ke kallonta kuma baiyi mamakin furucinta ba.


Murmushi ya mata cikin rashin nuna damuwar abinda ta fada yace.

"Haka ne? To dakyau gaskiya kinyi kokari ya kamata a jinjina miki kuma na gode da abinda kikai min domin kinyi min zaben mace ta gari wannan yarinyar ta daban ce ta bambanta da saura yanzu dukkan mata a banza nake kallonsu domin ina da beauty na".


Cikin jin haushi Ammy tace "nasan kace haka ne Dan Raina ya baci Amma nasan komai baka kaunar wannan yarinyar.


"Waye ya fada miki bana kaunar mata ta?.


Shiru Ammy tai ta zuba masa ido yaci gaba "duk duniya a yanzu babu Wanda ya kaini son yarinyar nan kaunar ta a cikin ruhina take yawo sonta a jini na yake idan babu ita to babu ni".


"Ka fada ne Dan naji haushi"? Ammy ta tambaye shi.

"Ko daya Ammy ba haka bane gaskiya ce nake fada miki akan abinda baki sani ba ina matukar son mata ta".


Cikin bacin ran abinda yake fada tace "wallahi Abdul-jabbar kayi da yar halak zan nuna maka karshen ka saina wulakanta ka Wanda Fatima da zata dawo saita yi kuka da idanuwanta kuma zaka gani muje zuwa koni ko kai".


Juyawa tai ta fice ya bita da kallon mamaki yana tunanin yaushe Ammy zata gyara halayyarta ne.


Kukan da Safah keyi ne ya dawo dashi daga duniyar tunani yana kallon yadda kyakkyawar fuskarta ta baci da hawaye.


Cikin alamun tambaya yace "kukan me kike"?.


Wani sabon kukan ne ya sake zuwa mata har tana rike hannunshi cikin tausayawa tace.


"Kayi hakuri komai yai zafi maganin sa Allah me kaiwa Ammy ne haka me yasa baza ta barka ka huta ba rashin uwa shine yake jawowa haka Amma ni rashin uwar bai kaini wannan matakin ba ta hada ni aure dakai saboda wata manufarta akan haka ina sake baka hakuri.


Matso da ita yai kusa dashi da murmushi a fuskarsa batare da yai magana ba yana rungume ta a jikin shi.


Kuka take sosai yana shafa bayan ta cikin nutsuwa a hankali cikin kunnen ta yace "is ok karki damu kukan ya isa haka".


Saida ta gaji domin ta kasa daina tsayawa bacci ne ya dauketa gyara mata kwanciya yai a jikinsa yana goge mata fuskar ta.


Bai kaita bedroom ba ya barta tayi baccin kusan awa biyu sannan ta farka cikin mamaki take kalloshi kenan bai fita ko ina ba.


Zatai magana taji yace "I LOVE U".


Zaro ido tai muryarta na rawa tace "kana Sona"?.

Baiyi magana ba sai kallonta da yake ci gaba Safah tai "Amma kafi karfi na kaiba sa'ana bane".


"Waye ya fada miki kece kika dace da tsarin rayuwa ta ina sonki da dukkan zuciya ta ina so babyn mu ya taso cikin soyayya ni naki ne kema tawa ce bana hada sonki da kowa fatan zaki bani hadin kai zaki amince"?.


Ya fada yana bude mata hannun shi ๐Ÿคฒ alamar mubaya'ar ta yake jira.


Cikin farin ciki Safah ta kifa fuskarta akan tafin hannun nasa tana murmushi a hankali tace.

"Na gode nima ina sonka kuma zanci gaba da sonka har karshen rayuwa ta bazan manta da alkairin ka ba duk matsayin ka da mukamin ka baka kyamace niba bayan ni baiwa ce".


"Kowa ma bawa ne babu sarki sai Allah" karki damu I love you".


Kallonsa take cikin girmamawa da kima ya sake samun matsayi a zuciyarta.


Cikin ba zata taji yace "gobe zamuyi tafiya muje ina so mu gaisa da mahaifan ki kiyi musu sallama".


Shiru tai cikin tunani to yanzu ita ya zatai wa zata nuna dabara ce ta fado mata ta kalleshi jiki a sanyaye tace.


"Bani dasu".

"Baki dasu kamar ya"?.


"Sun rasu" Safah ta fada hawaye na neman zubo mata.


Kai ya jinjina 'Allah ya musu rahma ya haskaka kabarin su".


"Ameen" Safah tace.


Mikar da ita yai yana rike hannunta suka fito daga part dinsu suka wuce ziyara gurin hajiya.


Kamar yadda ya fada mata washe gari tun asuba suka bar masarautar suka tafi Jordan harda Amfal da Khairat.


Ammy bata San 'kasa daya zasuje ba har tana murnar yanzu tunda kowa yana da mata shikenan sun rabu shakuwan dake tsakanin su zata ragu daga haka kowa ya kama gabansa.


Ammy na zaune bayan kamar tafiyarsu da sati daya ta kalli Hanne fuskarta wasai da murna tace.


"Na gode Hanne kinyi min komai kin taimaka nakai makiyi na kasa bazan taba mantawa dake ba kuma nayi miki alkawarin kyauta me girma".


Hanne dake Duke gaban Ammy tana sauraronta tace "ranki ya dade yanzu me ya rage me kike bukata"?.

Kad'a kai Ammy tai tana cewa "komai yazo karshe Hanne domin burina ya cika daga wannan abin".


"Mene shi ranki ya dade"?.

Mikewa Ammy tai tana zagaya cushions din dake palor tace "ina so kije gurin boka kice masa yaiwa Abdul-jabbar kurciya ya mantar dashi gida ya juya masa kwakwalwa ta yadda zai manta da gida ya daina tunanin dawowa har abada bana bukatar sake ganinsa".


Kallonta Hanne tai wato matar nan kwai hamshakiyar muguwa wato batar da Abdul-jabbar ne aniyart............

"Tunanin me kike"?.

"A'a babu komai yadda zanyi Shirin tafiyarsu nake tsarawa".

"Ok yayi kyau ya kasance anyi aiki cikin nasara idan abinda nake fata ya samu zan daukeki na kai ki babban matsayi".

Shiru Hanne tai tana tunanin da fargabar abinda zai biyo baya babu abinda take tsoro kamar ranar tonon asiri.


A firgice ta dago jin Ammy na cewa "tare ya kamata muje domin cikin sauri ya kamata a aikin".


Kai Hanne ta gurgiza cikin tsoro tace "ranki ya dade ni kadai ma zan iya aiwatar da komai basai kinje ba karki damu zanji da komai wannan hakki na ne".


"Hakan yayi kuma naji dadi a bisa taimakon ki Hanne kiyi shiri a yau kije".

Mikewa Hanne tai tana cewa "to ranki ya dade ki huta lafiya" daga haka ta fice tabar Ammy ranta fesss.

Mrs Al'ameen Ahmad ce.

[23/06/11 06:06pm] Typing ๐Ÿ“ฒ

๐Ÿ‡SAFREEYYAH๐Ÿ‡

YUSRAHMS ABUBAKAR


#YUSRAHMS#
No. 95 ๐Ÿ‘‰ 96
Jordan misalin karfe goma na dare Safah na tsaye jikin window ta daga labule tana kallon waje cikin yanayin jin dadi da debe kewa.


Jin kamar dumin Abu a bayanta yasa da sauri ta juya ba zato taji ta fada cikin kirjinsa rungume ta yai yana dago fuskarta ya mata ๐Ÿ˜˜ kiss cikin nuna kulawa yace.


"Me kike kallo my cutie tun dazu kina tsaye anan"?.

Kankame shi tai tana murmushi tace "kawai ina kallon kasar ne banyi tunanin zanga Koda airport neba a rayuwa ta balle har nahau jirgi nazo wata kasar".


Daukarta yai Saida ya kaita kan kujera sannan ya zauna yana zaunar da ita akan kafafun shi cikin nuna kauna ya Dora hannun shi akan marar ta yana shafawa yace.

"Hello my little prince how are u"?.


"Taya zai jika har ya amsa"? Safah ta tambaye shi da fara'a a fuskarta.


Dagowa yai ya zuba mata kyawawan idanuwansu shi zuwa wani lokaci yace.

"Me zai hana ya ji ni karki manta dad din shi ne fa".


Safah tace "Duk da haka yaron dake ciki baisan komai ba".

"Wa ya fada miki zuba ido ki gani Bari na dawo zaki Sha mamaki idan kika ji yace "good night my sweet dad".

"Ni kuma nace masa "sleep well my baby my little one I luv u.

"Kiji yace me too dad".


Dariyar da bata shirya ba daidai ya Mike yana fita a palon sauke ajiyar zuciya tai tana mikewa ta shiga bedroom.


Wanda tayo tana gyara jikinta da gashinta Saida ta gama tadau kayan bacci zata saka tana juyowa suka hada ido dashi yana tsaye ya harde hannuwan shi a kirji kawai yana kallon ta.


Dan murmushi tai tana karasowa inda yake zatai magana ya ware hannun shi ya dauketa yana dorata akan gado tare da kallon rigar baccin da take kokarin sawa.


Yace "me zaki da wannan"?.

Shiru tai tana kallonsa ganin ta'ki daina kallon yaci gaba "madam yadai nace me zaki da wannan"?.


Sai sannan ta samu damar bashi amsa "sakawa zanyi domin

Please Login or Register in order to submit comment