Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naki" dawowa Safah tay tana karbar wayan tare da cewa" hello" dan janye wayar Abdul-jabbar yay yana kallon screen din kamar ita yake kallo dan lumshe ido yay tare da cewa subahanallah mene haka yake shirin faruwa dani"?.


Jin anyi shiru yasa Safah ta kalli wayar ganin ba katse kiran yaiba tace" ina yini"? murya 'kar'kar yace" ya kike"? Dan jinjina kai Safah tay wannan akwai jan aji cikin mazewa tace" kalau yaya dama nace bamu taba haduwa ba gashi muna matsayin yan uwa amma dai zaka zo bikina daga nan sai muga juna ko"?.


Cikin mamakin surutun ta Abdul-jabbar yace" eh zanzo saimu hadu" murmushi Safah tay wanda ya jishi tana cewa" to Allah ya kawoka yayana nagode sosai".


"Ok ba damuwa bari na gama wani abu zan kira saimu karasa maganar" to tace yayin da ya kashe kiran yana rufe littafin tare da dan rufe ido.



Ji yay Amfal na cewa" bros dawa kake waya ne naji muryar mace gashi naga ka shiga yanayi kodai aunty na samu you ban sani ba"? Bude ido Abdul-jabbar yay yana kallonsa yace" eh sai akai ya"? dariya Amfal yay" kai koda naji dama naga kwanakin nan kana yawan tunani ashe hubby ne ya shige ka lallai kace zamu sha bikin babban yaya".



Ko kula shi Abdul-jabbar baiyi ba Amfal yaci gaba" Allah bros har naji dadi kaga nima ya kamata na nemo muyi auren nan tare kuma ba zama honey moon ba kama kafar yaro amma wai a ina ka samu lady ban sani ba kuma da yaushe yar wanne garin ce"?.

Girgiza kai Abduljabbar yay yana kallon Amfal yace" oh kaga matsala ta dakai kenan please ka rabu dani karka dora min headache" dariya Amfal yay" ka huta sosai ango nikam na shiga wanka duk daren dadewa da kake boye min auntyn nawa zan ganta" wanka ya shiga yana cewa" wayyo Allah na dadi kashe hajiya bros zaiyi aure" Abdul-jabbar na jinsa bai tamka ba domin Amfal dan caza kaine ko ba nepa dole sai ana masa uziri.

MRS AL'AMEEN AHMAD💝.

TYPING📲
YUSRAH MUSA ABUBAKAR


💫ANNURI WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony



#YUSRAHMS#
NO.45 👉 46
Na Allah dake kallon Safah yace" to yaudai kun gaisa saura haduwa itace mai wuya" mikewa Safah tay tana cewa" bari nadan ari wayar nan nayi kira ina dawowa" cikin tsokana Hadiza tace" a'a fa kodai-kodai" fasa tafiya Safah tay ta juyo tace" kodai-kodai me"? Karfa ku fassara ni na Allah yace" kodai-kodai kin kyasa shine zaki mana dan waken zagaye ki kira shi"?.



Yatsina fuska tay" cafdi wa ya fada muku kunji ku da zargi to bashi zan kira ba nayi ya da murtalan"? na Allah yace" ba wani kedai fadi gaskiya karki yaudare mu muji labari ya canza" dariya Safah tay tana fita tace" yanzu zan dawo muku da salular ku".


Tana fita tafiya tay maidan nisa inda tasan ba mutane kuma bamai jinta takarda ta buda tana saka number ta kira bugu daya kuwa ta shiga kuma tay sa'a aka daga mata.


Dan daidaita murya tay tana cewa" hello hajiya ina yini ya gida ina Alawiyyah"? Daga can bangaren hajiya tace" lafiya dawa nake waya ban gane mai magana ba"? dariya Safah tay tana cewa" hajiya nice fa Safah dama kiran kinai mu gaisa a gurin baba maryam na karbi number".


Murmushi hajiya tay" ayya Safah ashe kece ya gida fatan kun sauka lafiya yasu baffan ki? ki gaida min shi da kyau".

Kai Safah ta daga" to hajiya insha Allahu zaiji".


Shiru sukai na wajen minti biyu ba wanda yay magana sai daga baya hajiya tace" Safah ina fatan dai lafiya babu wata matsala naji kinyi shiru meya faru ne ko akwai wani abu"?.


Zama Safah tay kan wata sararriyar bishiya cikin tunanin yadda zata fadawa hajiya abinda ke ranta tace" am dama wata magana nake son fada miki amma na kasa tun muna nan saboda tsoron yadda zaki fahimce ni amma yanzu ya zama dole na fada miki gaskiyar komai danki dau mataki tun wuri".


"Ok Safah ina jinki fada min ko menene zan fahimce ki kar kiji komai ke tamkar 'yata haka na dauke ki".


Sauke ajiyar zuciya Safah tay cikin rashin jin dadin abinda hajiyan zata ji daga bakin ta tace" dama magana ne akan mk lokacin dana bata tsawon kwana uku ba kowa ne ya sace niba sai shi bayan na fito daga part dinku ya shaka min wani abu a hanci daga nan bansan komai ba sai ganina nayi a gidan sa akan gado kuma da nayi yunkurin gudowa ya tare ni a palon sa yace saina amince masa na bashi kaina zai barni na taho hakan shine burin sa kawai a gare ni".


Yayi iya juyin duniya da lallami naki amince masa a gaba na ya kira wata budurwa tazo gidan wai ta nuna min yadda ake wayewa" dan shiru tay sai kuma ta fashe da kuka tace hajiya kinsan abinda sukai a gaba na ya sadu da ita kuma yace wannan ba bakon abu bane a gurin sa yana da yan mata irin ta baza su kirgu ba da naga basa cikin hayyacin su shine na gudo daga gidan saiya biyo ni hanya ya dauko ni ya dawo dani gidan ku".



Shine washe gari da kika tambaye ni ina naje tsawon kwana uku kunya da nauyin ki yasa na boye gaskiya na kasa fada miki kuma yanzun ma dan Allah hajiya ki fahimce ni kiwa mk fada da nasiha kina masa addu'a Allah ya shirye shi amma kwarai yana da hali mara kyau a boye ki yafe min nasan za kiji babu dadi amma nima ba yadda na iyane ya zama dole na fada miki gaskiya".



Wani irin juyi kan hajiya yake jin abinda Safah ke fada mata wanda batai zato ba dakyar tace" na fahimce ki Safah kuma na gode da kika sanar dani wannan sirrin duk da bansan yawan shekarun da aka kwashe mk yana wannan abun ba ki gaishe min da kowa karki damu kuma kiyi hakuri abinda yay miki sai an jima".



Tun kafin Safah tay magana hajiya ta kashe kiran, numfashi Safah ta fitar cikin razani tare da dafe kai gaban ta yay wani irin yankewa lokaci guda bugun zuciyarta ya karu cikin tashin hankali ta fara maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un sai yanzu take jin dama bata fadawa hajiya ba mema yasa ta aikata hakan wanne hali hajiya zata shiga wanne mataki zata dauka akan mk tana tsoron fitina ta biyo baya.



Tunda suka gama waya hajiya ta kira mk cewa yazo yanzun nan tana neman sa kada ya kuskura ya bata mata lokaci gaba daya nutsuwa kaurace mata tayi zulumi bakin ciki sune tare da abinda mk yake aikatawa wanda bata sani ba su kawai take hangowa duk inda ta kalla mikewa tay ta soma zagaya falon ranta na mata suya akan halayyar mk wanda tana matsayin mahaifiya gareshi bata sani ba saidai taji daga wata majiyar amma tayi asara da bata fahimta tun farko ba ta sani cewa indai aka dauko yar aiki bata cin nisan wuta mk zaisa mata kahon zuka saiya kore ta amma bai taba nuna wani abu akan Safah ba saima yabon girkin ta da yake ta dauka gamon jini ne ashe akwai kullalliyar da yake kullawa a boye.




Shigowar mk kenan ya nufi gurin hajiya dake ta zagaye palon tare da cewa" mum gani lafiya naji kin kira ni a waya muryarki wani iri meya ke faruwa"?.


Juyowa hajiya tay idon jawur dashi tana kallon mk a fusace wanda baiyi zato ba yaji saukar wani 'kwak'kwaran mari a fuskarsa kafin ya dago ta kara wanka masa wani cikin kuka ta soma magana" musaddiq ka wulakanta mu ka tozarta mu kayi watsi da tarbiyyar da muka baka ka nuna kaiba d'a nagari bane yanzu dabi'a ce mai kyau wannan ka dauka kamar kaidai kayi asara ace mazinaci ne mai lalata yaran mutane baka tsoron gaba ya naka yayan zasu taso kila ma sannan ba ranka mk me ka rasa tun yaushe nake binka kai aure ka'ki sai kace min da lokaci ashe kasan irin mummunan aikin da kake aikatawa tun kafin lokaci ya kure maka ka tuba ka koma ga Allah ka daina abinda kake idan kaki akwai ranar mutuwa kuma ita kayi shirinta koda yaushe ba'a sa mata rana ka tuba mk ina gargadin ka".


Jikin mk na rawa cikin tashin hankalin ya akai hajiya tasan yana harkar mata ya dago yana kallon ta yace" mum waye ya fada miki wannan maganar? bansan komai ba".


Hajiya da hawaye ke fita a idonta tace" baka san komai ba kana nufin karya akai maka ba halin ka bane mk duk abinda zakai kasa tsoron Allah a lamarinka maimaikon dana fada maka jikinka yay laushi ka tuba zuwa ga wanda ya halicce ka saika nemi karyatawa kana zamewa harda baka san komai ba"?.


Shiru mk yay cikin damuwa hajiya taci gaba" naji kaddara bakasan komai ba sharri akai maka amma Safah zatay maka karya ne baka aikata ba zata cemin kayi yanzun nan muka gama waya daita ta fada min duk abinda kai mata kaiko kunya baka jiba da kuma ace yarinyar bamai nisan hankali bace ta fadawa maryam me kake tunani kudin mu bashi zai ceto kaba da kuma itadin ta kasance mara kamun kai mai watsi da tarbiyyar iyayen ta kamarka saita biye maka kuyita aikata alfasha bamu sani ba harsai ranar tonon asiri randa cikin ya bayyana gareta kasa mu shiga uku".



Cikin sanyin jiki mk ya durkusa gaban hajiya yana cewa" kiyi hakuri mum na bata miki rai".

Cikin tsawa hajiya tace" ka yarda ka aikata kenan ka yarda halinka ne musaddiq bazan gaji da ce maka ka ji kunya ba kuma kayi asara shashashan yaro kawai kuma kada ka kuskura na ganka a palon nan idan na fito zamu neme ka sai dadyn ka ya dawo fita kaban guri karka sa na kama da wuta da zunubin ka".


Cikin jin kunan kalaman hajiya mk ya mike yana fita a palon zuwa harabar gidan ya shiga motarsa tare da kifa kai a sitiyari ya runtse idonsa saiji yay hawaye masu zafi suna diga masa cikin mamaki ya bude idonsa yana kallon mirron jikin motar ganin tabbas shawayen ne da gaske wani irin dukan glass din motar yay tare da furzar da iska mai tsananin zafi yana jijjiga kansa ko tsoron ya masa ciwo ba yay.



Lokaci guda kuma ya tsaya da komai ya nutsu da wani kalar murmushi wanda bamai gane ma'anarsa sai shi yace" hummm Safah! Safah!! Safah!!! Nine kika tonawa asiri kamar yadda kike fada kika sa ni a tsaka mai wuya na rantse da Allah saina nemo ki duk inda kike zan binciko ki saina dau matakin da zaki dana sani baki da wani amfani yanzu a gareni mutuwar ki na hannuna baza ki sake jin dadin zaman duniya ba musaddiq bamai hada kafada dani ki jira zuwana gareki yau-yau din nan basai gobe ba bana tunanin za kiga wayewar gari domin idona idonki saina kashe ki muje zuwa".



Figar mota yay da mugun gudu ya fita a gidan yana tafiya wani gidan nasa da ban ba inda Abidah take ba waccan gidan sirrinsa ne ko iyayen sa basu san da gidan ba acan ya yada zango kafin ya gama shiri ya tafi neman ta.



Safah na zaune har wannan lokacin akan itacen duk jikin ta a mace ta kasa tashi ga hawaye da yaki tsayawa a idonta jin ana kiran sallar magriba yasa ta mike ta soma tafiya zata koma gidan su Hadiza takai musu waya.



Jitay ance" Safara'u daga ina dama ke nake nema tun safe na aiki Aisha gidan ku baffan ki yace kina gidan su na Allah".


A firgice Safah ta juya ganin murtala yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da kakalo murmushin dole tace" au ashe kaine daga ina haka"?.


Shima murmushin yay suna dan tafiya a hankali yace" na karbo mana ankon mune nida ke gashi naki kije dashi gida wannan ledar kuma cingam ne da zaki rabawa kawayen ki akwai kuma bakin lalle da ja yanzu dana sayo miki ki rangada min kunshi mai kyau sannan akwai kudi a ciki abinda kike bukata zaki iya fadawa Aisha saita sanar min sai anjima na wuce gida".



To nagode Allah ya kara arziki" kai ya daga yana wucewa ita kuma ta shiga gidan su malam na Allah domin tay sallah sai bayan isha ta tafi gida.


Misalin karfe goma na dare mk ya fito cikin shirin kaya bakake harda face mask yana saka wata hula wacce iya idonsa ne a waje zai fita kenan Abidah tace" wannan shigar kuma fa kamar wani shedan ina zaka je karfe goma na dare a haka"?.



Juyowa yay yana kallonta da muryar shi data riga ta canza sakamakon magana da baiyi ba tun la'asar yace" gidan ubanki zanje idan kina da sako shegiyar yarinya na sako dake cikin al'amari nane balle kimin shishshigi". Jada baya Abidah tay da sauri tana cewa" Allah ya baka hakuri" tsaki yaja kamar zai shako ta sai kuma ya fasa yana fita daga palon mota ya shiga kawai yabar gidan tare da zaro wata wuka cikin gidan ta sai sheki take dariya yay yana cewa" kwantar da hankalin ki wuka zaki sha jini nan da yan awanni Safah gani nan gareki".



Har kusan asuba mk na yawo amma babu wani haske akan abinda ya fito nema gashi baisan sunan garin ba balle ya tambaya ganin hasken rana ya fito yasa ya cire wannan bakaken kayan yasa riga da wando irin na mutane yaci gaba da tafiya har yazo wata bishiya ga yunwa na damunsa parking yay da motar yana fitowa ko zaiga wani mutum amma dai babu kowa tafiya ya farayi da kafa har yay nisa da motar jin ya gaji tunda bai saba ba ya tsaya a wata rijiya yana zama kan wani dan dutsi dake kusa da ita kafin ya samu wani yazo.



Yana nan zaune wani almajiri yazo shan ruwa mk na kallon sa saida yasha zaitafi yace" kai danzo na tambaye ka mana".

Cikin tsoro yaron yace" a'a malam ya hana mu yace indai mukaga bako ya kira mu ba dan garin nan ba kar muje" jin ya ambaci malam yasa mk yace" to naji basai kazo ba tsaya anan din nai maka tambayar waye babban malami a garin nan"?.


Kai tsaye almajiri dake sidin robarsa ta bara yace" sunan sa malam na Allah" kai mk ya jinjina" yana da wata 'ya ana ce mata Safara'u ko aurenta ma zaiyi"?.


Kai almajirin ya girgiza" a'a malam na Allah bashi da d'a ko daya saidai malamin mu shine yake da 'ya Safara'u ta dawo daga Adamawa ita da baba maryam gobe ma zaiyi aurenta a masallacin juma'a".


Cikin farin ciki mk jin ya samu almajirin mahaifin ta yace" to gaka ma da har ina kiran ka kana kin zuwa dama gidan sa nake nema ni daga birni nake kuma ni malamin tsafta ne muje ka nuna min gidan sa daga nesa zan baka irin kayan dana kawo masa ka gani biscuit da coculate muje maza ka kaini".


Da sauri almajirin ya wuce gaba mk ya bishi a baya da wani murmushin mugunta daga nesa da gidan suka tsaya almajirin yace" ga gidan can wancan malamin me rawani da yake zaune a tsakiya to shine baban ta gurinsa aka aiko ka" kai mk ya daga yana cewa" na gode kaji yaro toga caculate din taka" .



Karba almajirin yay yana tafiyarsa mk kuma ya zubawa baffa ido ko ba'a fada ba wannan mahaifin Safah ne ga dogon hancin ta nan ya gani juyawa yay yana komawa wajen motar sa bai karasa gurin baffan ba.


Mrs Al'ameen Ahmad ce,👍
Till we meet
Thank for your support🌹.


Typing
📝 Yusrah Musa Abubakar Gimba


Ayi hakuri da typing error🚨 banjin dadi😢 kwana biyu.


💫ANNURI 📝WRITER'S 👪ASSOCIATION💫
🏡Home of 🤗Hospitality and 💚Harmony


🍇SAFREEYYAH🍇


💞👉 Zarah Musa dan adam
💞👉 Naja'at Musa Abubakar
💞👉 Kubrah Sani Muhammad.



#YUSRAHMS#
NO.47 👉 48
Safah kam na can tana shan lalle a gidan wata mata wacce itama yarta ta dawo daga birni gurin yan uwan su ta koyo acan tazo tana yi.


Da gudu Aisha ta shigo gidan tana guda kamar hancinta zai cire cikin dariya tace" ahayye ayyuruyuri nanaye anayi muna jin dadi ana bari muna jin haushi ta yaya murtala ikon Allah bada kanki a sare kije gida kice ya fadi kai jama'a Safara'u irin wannan kyau haka lallai kice gobe ango zai shana jifa wani kamshi da kike kamar kin fada a rijiyar turare meye ne sirrin fada min naji kafin nawa yazo kinga na kware".


Harararta Safah tay" idan kin gama shashancin zaki iya bani sakon dana aike ki" dariya Aisha tay" beban komai ba yace bashi da kudi kiyi hakuri" wani kallo Safah tay mata tana cewa" me kika ce"? Cikin tsokana Aisha tace" yace bashi da ko kwandala duk kin cinye masa kudi"


Au haka ma yace dama in yana da kwandala ma me zatai mai sake min lallen nan Furera na dawo" jin haka yasa da sauri Aisha ta fito da dubu biyu tana mika mata tace" gashi nan ya bani kar kisa yanzu yazo ya zane ni da bulala kowa yana biki jikinsa a ware ni ina dingishi kamar gurguwa"


Ke kika sani can da yawar ki debo min ruwa ni nayi wanka mu tafi gida" bokiti Aisha ta dauka tana cewa" yanzu ma kuwa amaryar mu bayan yayana za'a burge naki debowa bani minti daya ina dawowa ta shagonsa zanbi ya sako kwalbar turare guda daya a ruwan" tana fadin haka ta fita dan daga murya Safah tay yadda zata jita tace" banda lokacin shashancin ki nidai burina ki kawo min ruwa malama".



Bayan sallar isha dukkan nin kawayen Safah sun hadu zasu taya ta cin tsire suna zaune a karkashin bishiyar zaitun din cikin gidan su sun taru yan kamun amarya su Asabe sai juyi ake ana gadara ansha sabon dinkin da Safah tayo mata a Adamawa gefe guda tukunya ce babba akan wuta ana dafa abincin yan kamu.



Safah suna zaune a daki itada baffa cikin nasiha baffa yace" Safara'u tun yau base gobe ba zan fara miki nasiha ki rike darajar auren ki murtala yarone me hankali kuma kinga ke marainiya ce baki da uwa baki da me baki shawarra saini din dai dan Allah Safara'u idan Allah ya tashe mu lafiya gobe za'a daura miki aure kije dakin mijinki ki zama me hakuri da juriya ki rike Allah ki roke shi zai amsa miki ki tsaya a kofarsa zai karbeki ki nufe sa zai cire ki daga cikin kunci da damuwa ki dogara dashi ya isar miki ki kula sosai ke kadaice 'yata ina son ki amma dole aure shine zai raba mu inai miki fatan alkhari Allah yayi miki albarka ya tsare ki a duk inda kika tsinci kanki".



Safah da hawaye ke zarya a kuncin ta da 'kyar muryarta na rawa tace" amin baffa nagode lallai kai ubah ne nagari wanda kowacce d'iya zatai alfahari da kai".



Kai baffa ya jinjina zaiyi magana suka ji anyi sallama a kofar dakin wani yaro na cewa" wai ance Safara'u tazo a waje".


Kallon juna sukai itada baffa kafin tace" kaje kace wai inji waye"? Dakatar da yaron baffa yay yana cewa" baki sani ba ko murtala ne kije ki gano mana amma karki dade kinga kin bar kawayen ki kuma na ji kina cewa a gurin maryama zaku kwana dasu" eh baffa acan zamu kwana bari na dawo" fita tay yayin da sukai karo da Aisha.


Dan dafe goshi Aisha tay tan acewa" wash saurin me kike haka zaki lagarta ni"? tura ta gefe Safah tay tana cewa" ke matsa mana kin wani tare min hanya murtala ne yake kira na" dariya Aisha tay" oh wannan shine angon zumudi inace gobe iyanzu an raka ki amma yaudin ma bazai barki ki huta ba" kallonta Safah tay" kinga ban hanya kar yaga na dade" matsawa Aisha tay" inye cankadi kaga masu miji gaskiya kar yaga kin dade duk da komai kikai burgeshi yake ke amarya ce bakya lefi ko kin cinnawa shagon angon ki wuta zaice kuskure ne ki karbo kudin tsiren tare dani dan Allah" banza Safah ta mata tana fita a gidan.


Ganin bata ga murtalan inda ya saba tsayawa ba idan yazo gurinta yasa ta cewa yaron" kai yana ina ne ban ganshi ba" dan tafiya sukai yaron yace mata" yana waccan bishiyar yace ki same shi" to tace yaron kuma ya juya abin sa.



Cikin mamaki Safah ta nufi bishiyar domin ta gano shi a zaune amma me yasa yau sai nan bayan koda wasa bai taba yin hakan ba ita kadai take tunani a zuciyarta harta karasa gurin da sallama tace" haba murtala yau kuma shirar harnan bayan layin mu me yasa baza ka karasa ba"?.


Mikewa tsaye mk yay yana cewa" wannan hamsim ne ba murtalan da kika sani bane barka da zuwa big girl nasan kinyi mamakin gani na amma ina tunanin kinsan abinda kika aikata min jiya kodan ba lallai ki tuna ba tunda karamar kwakwalwa gareki me kike tunani a kaina dama saboda rashin hankali da kike cemin wata rana zaki,tona min asiri gurin mahaifana da gaske kike? yayi kyau saidai karki manta abinda nace miki a waccan lokacin cewa idan tsautsayi yasa kika tona min asirina zan kashe ki kuma ban fasa ba yanzu ma abinda ya kawo ni kenan fatan kin shirya amsar hukuncinki big girl idan harkin shirya to nima a shirye nake".



Duk jikin Safah rawa yake saboda tsoro dan ja da baya tay tana kallon sa tace" ban fadawa hajiya don tayi maka wani abuba nafada mata ne tayi maka fada kuma ka shiryu ka gane cewa abinda kake bashi dakyau amma tunda kaidin batacce ne sai ince Allah ya shiryar dakai kuma kayi hakuri abinda ya faru na roke ka mk ba wata alaka tsakani na dakai ka rabu dani nayi rayuwa gobe ne daurin aurena karka bata min shiri bani da wani hadi dakai ka dauka ban sanka ba ka manta da komai ka gyara halin ka kanemi yafiya a gurin wanda ya halicceka ka daina saba masa kai mutum ne baudadde mara kyan hali kayi kokarin gyara halinka tun lokaci bai kure maka ba".


Kara bude idanuwan sa yay akanta jin abinda tace yana jijjiga kai yace" humm big girl kina ban dariya kuma kina bata lokacinki amfada miki wa'azi nazo kimin idai haka kike tunani to kinci kai babu abinda ya kawo ni wannan jakin sokon kauyen naku sai daukar fansa akan ki baki gane bane amma yanzu zan ganar dake ".



Cikin dakewa Safah tace" me kake nufi"?.



Fito da wuka yay yana kallonta yace "ga abinda zanyi kasheki zanyi na shafe tarihin ki a rayuwa shine babban burina".


Matsawa Safah tay tana kallonshi tace" karya ne wallhi nafi karfin ka wulakanta ni kaidin banza".


Jin abinda take cewa a fusace ya zare wukar daga cikin gidan ta ya nufo tada iya karfinsa ganin da gaske yake kashe ta zaiyi yasa a guje ta juya zuwa gida amma tayi rashin sa'a yasha gaban ta yana huci yace" ina kuma za kije ashe dai ina da zarra ki tsaya mana tunda kince kinfi karfina".



Ganin ya sake tahowa gurin ta gadan-gadan yasa da mugun gudu ta juya yayin da yabi bayan ta da iya karfinsa suka kasa sosai sukai nisa da garin suka shiga jeji mai, duhun gaske amma bai daina binta ba yayi mamakin gudun ta baiyi tunanin zata tsere masa ba.


Gajiya baffa yay da rashin dawowar Safan gashi ana ta jiranta dare na kara ja fitowa yay yana kiran Aisha gefe yace" Aishatu ina yar uwar taki tay ne jeki dubo ta kice tazo ku tafi gidan su maryaman mana lokaci na kurewa".


To baffa bari na dubo ta" cewar Aisha tana fita a gidan amma ga mamakinta layi babu kowa kuma iya dubanta da kwalla kira a banza tunani tay kodai Safan na shagon murtala da sauri ta nufi anguwarsu amma saita cire sabaninta iya murtala ne da abokanansa karasawa har gurin tay tana cewa" yayan mu wai tun dazu Safara'u ta taho gurin ka har yanzu bata koma ba muna ta jiranta baffa yace nazo na kirata mu tafi".



Mikewa murtala yay yana cewa" ni ayau bamu hadu da Safara'u ko sau dayaba" abokanansa ya kalla yana cewa" ku tashi muje" dukkanin su mikewa sukai suna nufar gidan baffa mamaki ne ya kama kowa jin ance

Please Login or Register in order to submit comment