Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka dama to yata iya abinka da mara galihu.


Mikewa jakadiya tay tana kallon Safah tace tashi muje yarnan kinji.


Kai Safah ta girgiza tana matsawa kusa da Ammy ta zuba gwiwoyinta akasa tana hade hannuwanta guri daya cikin kuka tace.


"Dan Allah kimin rai karki sani cikin bayi wallahi niba baiwa bace ki barni natafi".


Dagowa Ammy tay tana kallonta tace ke harkin isa nafadi magana ki sauya min bakisan wace niba amma zaki sanI.

Mikewa Ammy tay zata bar gurin da sauri Safah ta rike mata kaya tana cewa dan Allah na roke ki kada ki mayar dani baiwa ki barni natafi.


Zaro ido jakadiya tay tana rufe baki ganin abinda Safan tay.


A fusace Ammy ta juyo tana wanke ta da mari abinda ba'a tabayi mata ba cikin tsawa tace jakadiya ki fitar min da wannan shashashar akuyar daga nan idan ba haka ba zan sauke duk wani fushina akan ki.


Jiki narawa jakadiya ta taso da gudun ta tana dago Safah tace ranki ya dade kiyi hakuri zanyi duk abinda kika umarce ni.


Cikin bacin rai Ammy tace wannan kuma ke kika sani matsalar kice ba tawa ba bace min da gani.


Rike hannun Safah jakadiya tay suna fita a part din suna tafe Safah na share hawayen damuwa da bakin ciki ada tana tunanin komawarta gida amma a yanzu ta cire rai karshen labarinta kenan tunda tazo wannan kaddararran gidan me tsaro kuma matsayin baiwa mara yanci babu ta yadda za'ai ta iya kubuta.

Ba wanda take jin tausayi idan ta tuno gida kamar baffanta da murtala batasan a wanne irin hali suke ba.


Har daki jakadiya ta kaita tana bata zani tace daura maza yata bari na baki ruwa ki wanka ki dawo cikin hayyacinki se muyi magana.

Kai Safah ta girgiza muryarta na fita dakyar tace bazan iya wanka ba abinci nake so yau banci komai ba.


Zaro ido jakadiya tay subahanallahi sannu kinji yarinya bari insa a kawo miki abinci.


Kwalla kira jakadiya ta fara da karfi Zarisha ina kika shiga ne ke Zarisha.


Da sauri wata budurwa ta budo kofa muryarta adan shagwabe tace wai umma kita kwalla kiran mutum dakyau bakiji yadda na tsorata ba.

Kallonta jakadiya tay Zarisha ba magana ba taimakon gaggawa zaki maza miko min abinci yarinyar nan taci.


Sai a lokacin Zarisha ta lura da Safah plate din roba ta dauka tana bude wata madaidaiciyar kula ta zubo kyakkyawar jalop din shinkafa me kifi tana mikowa jakadiya.


Karba jakadiya tay tana ajewa a gaban Safah tace ga abinci yata ci in Allah ya yarda baza ki wulakanta ba.


Ci Safah ta farayi a gaggauce wanda hakan ya tabbatar ta wuni bata ci komai din ba.

Zarisha dake kallonta baki bude tace" daga ina kika samota umma naga ban taba ganinta ba saifa yau"?.


Kai jakadiya tadaga" eh kwarai hakane Zarisha labarin duk dayane nima ban taba ganinta basai yau gimbiya Adama ce taban ita cewa gatanan asata cikin bayi bansan me hakan yake nufiba amma dole nabi umarnin ta".

Tsakin takaici Zarisha taja" Allah nagani na tsani matar nan gara daba ma a part dinta nake aiki ba shugaba daya kamata yaji tausayin mabiyansa amma ita ta kasance azzaluma muguwa me bakin hali".


Kallonta jakadiya tay cikin nuna gargadi dajan kunne tace" kul na haneki da furta irin wannan zararriyar maganar Adama nada munafikai cikin bayi masu yawa wadanda kekai mata rahoto bakisan su waye suba kamar yadda nima bansan suba dan haka karna sake jin kinyi wannan furucin mai hadari".

Kai Zarisha ta daga cikin ladabi tace bazan sake ba umma kiyi hakuri.


Daidai Safah ta gama tasha ruwa kawai tana sauke ajiyar zuciya tadan dafe kanta da yake sarawa ta gefe daya.

Zuwa wani lokaci tadago tana kallon jakadiya kamar me kallon tv saiga hawaye a idonta.

Cikin muryar kuka tace nagode Allah ya saka da alkhairi taimakon da kika min na tabbata zan samu dan sassauci daga gareki".


Murmushi jakadiya tay a'a sam kada ki damu yata kisa a ranki keda Zarisha dayane a gurina kinji tashi mujeki wanka sai kizo ki huta.


Mikewa sukai suna fita yayin da Zarisha ta bisu da kallo cikin mamaki aranta tace to wannan kyakkyawar budurwar daga ina sam hakan baiyi ba data kasance cikin bayi.

πŸ‡ SAFREEYYAHπŸ‡


πŸ’«ANNURI WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«
🏑 Home of hospitality and harmony


😘 Mrs Al'ameen Ahmad ce.


#YUSRAHMS#
NO 59πŸ‘‰ 60
Da yake Safah ta kwana bata jin dadi tun dare zazzabi ke damuntaa sai ba inda taje tana daki a kwance ita kadai.


Jakadiya na part din amaryar sarki Fatima dake kallonta tace am Lantana inasan karin masu min aiki domin bayin da suke hidima a part dina sunyi karanta aikin ya musu yawa suna shan wahala kece babba ki zabo min wasu.


Jinjina kai jakadiya tay cikin girmamawa tace to ranki ya dade za'a samo miki in Allah ya yarda.

Yauwa Lantana a dubo min nagode.


Safah na kwance taji an banko kofa da karfi tay tunanin Zarisha ce amma tasan baza tay hakaba.

Bude idonta tay taga wasu yan mata biyu tsaye akanta suna kallonta.

Cikin muryar rashin lafiya tace suwaye ku me kuke nema?.

Cikin harara dayar tace jimin yar rainin hankali Zakiyya dama nasan jakadiya bata nan tana can cikin gida wato daga zuwanki harkin koyi fitsara irinta Zarisha ko wahala kuwa zakisha a gurin mu.

Safah data kasa dauke idonta akansu cikin mamakin kalamansu masu kama da wuta tace wai dan Allah meye haka kudin suwaye mena muku.


Babu abinda kikai mana banza kawai saboda jin dadi yasa muke miki haka muje Basira idan kinga dama gimbiya Adama na kiran ki.


Kamar walkiya ta nemesu ta rasa dakyar ta mike saboda jikinta babu karfi ta fita tana tafiya batasan inda take yiba.


Ko'ina mutane ne ke kaiwa da komowa harta fice daga shiyar bayi kallon yanayin gidan take tana mamakin girmansa gakyau harta shagala ga abinda ya kawota nan din.


Jitay ance mata ke wace wannan bakisan ba'a shiga nan din ba me zaki"?.

Cikin faduwar gaba Safah ta juyo inda akai maganar wani mejan kaya ta gani zaune kan kujerar roba da bulala a hannun shi.

Zaro ido tay jiki rawa tace dan Allah baba kayi hakuri bangaren gimbiya Adama nake nema.

Oh kinyi batan kai yarinya sai kace bakuwa baya zaki koma ki tambaya nan gurin dokuna ne.

Murmushin karfin hali Safah tay tana cewa nagode baba sannan ta juya.


Tayi tafiya medan nisa suka hadu da Zarisha da mamaki tace Safah ina zuwa keda baki da lafiya kuma bakisan ko'ina ba saikin bata.

Kallonta Safah tay yauwa Zarisha dan Allah ki nuna min part din gimbiya Adama.

"Amma me zaki mata?.

Nima ban saniba Zarisha har gurin wani me tsaron dokuna naje garin neman bangarenta na dade da fitowa.


Au kice har gurin babana kika je ai shine mahaifina muje na raka ki.

Wucewa sukai suna dan taba zance har suka shiga part din dagowar da Safah zatay suka hada ido da Ammy bugawa zuciyarta tay a ranta tace.

Innalillahi wainna ilaihi raji'un dama wannan matar data sayeni ce gimbiya Adaman na shiga uku me kuma zatai min.


Cikin tsawa Ammy tace ke ubanki kike kallo haka tun dazu na tura kiranki sai yanzu kika amsa ko kin dauka nan ma gidan bariki ne.

Saurin sauke kai Safah tay cikin bacin ran zagar mata mahaifi da tay yasa taki bata hakuri.

Karo na farko Ammy datay magana aka shareta balle a bata hakuri.

Cikin mamakin Safah daya gama cikata na tsaurin idon kin bata hakurin datay balle ta risina mata zatay magana.

Basira da Zakiyya dake gefe suna dutin su dadi ya gama cika su suka ce ranki ya dade dama da mukaje kiranta cewa tay baza tazo ba.

Cikin takaicinsu Zarisha tace wallahi karya suke mata bata da lafiya kuma ta dade da tahowa bata san hanya ba shine ta bata.


Tsawataccen kallo Ammy kewa Zarisha tace ke mara kunya kece figeggiya ko ita bata da bakin magana ke zaki ari bakin ta kici mata albasa wato ke yar gidan jakadiya ce ko? Shashasha.

Ran Zarisha ya baci domin tasan Ammy bata kaunar mahaifiyarta amma haka ta daure muryarta na nunI da fushi tace kiyi hakuri ranki ya dade.

Da hannu Ammy ta nunawa Zarisha kofa juyawa tay tana fita cikin tausayawa Safah.

Dawo da kallonta kan Safah tay tana cewa ke kuma karbi naki hukuncin.


Tun kafin Safah ta fahimci abinda Ammy keson cewa taji saukar bulala a bayanta.

A zabure ta juya yayin da taga wani bakin mutum ransa a hade me fushi da fushin wani.

Sake sakar mata bulalar yay ihu ta kwalla cikin jin zafi tana bashi hakuri.

Zarisha dake tsaye a waje tana jin komai ranta duk a dagule bata farga ba taga an budo kofa anturo Safah waje da karfi.

Saboda zazzabin da take yasa cikin rashin karfin jiki tay taga-taga zata fadi da sauri Zarisha ta tare ta idon ta na cika da hawaye ta dago ta tana cewa.


Muje Safah karki damu akwai Allah shine gatan kowa wata rana zatay dana sanin wannan abubuwan da take aikatawa.

Wucewa sukai Safah najan kafa sakamakon lankwashewa da yatsan ta yay.


Suna zaune shiru a daki jakadiya ta shigo ganinsu haka yasa tace lafiya me yake faruwa naga kunyi wani iri.


Muryar Zarisha me tattare da damuwa tace umma Safah bata jin dadi tana kwance wannan Adaman ta kirata haka kawai tasa babangida me dorina ya daki Safah bakiga yadda bayan ta ya tashi ba.


Shiru jakadiya tay dan bata da bakin magana akan haka saidai tana matukar tausayawa Safan domin ta fuskanci Ammy ta sata a sahun mutanen data tsana.

Hakuri taci gaba da bawa Safah tana kuma nuna mata komai me wucewa ne.

Sannan in anjima zaki tafi dakin su Basira acan aka baki masaukin ki.

Hade rai Zarisha tay kai umma maimakon kisa a bata dakin mu gaskiya bazata gurin yan iskan yaran can ba.

Kai jakadiya ta girgiza hum Zarisha kenan ke yarinya ce bakisan komaiba bani da wannan ikon Adama ce ta umarce ni.
a hakan ma bakisan da yadda muka rabu ba saida tamin tsiyal sannan ta barni na taho me kikee tunani idan banyi abinda tace bazan fuskanci zunzurutun hukunci a wajenta dama ba kaunata take ba kekin san da haka.

Tsaki Zarisha tay wai sai yaushe zamu samu canjin rayuwa ne?.

Dariya jakadiya tay ba rana saidai muyita hakuri kamar yadda kakannin mu da iyayen mu sukai.


Kamar yadda jakadiya tace da dare ta rakata dakin su Basira ta nuna mata inda zata rika kwanciya sannan ta fita.

Tana nan zaune suka shigo suna dariya da alama sun hada wata muguntar ne.

Zama sukai suna duba ledar hannunsu cikin tafi Zakiyya tace kan uba gaskiya Basira kiji tsoron Allah kina zaluntar gayen nan dama duk wannan nauyin balangu ne ba sonshi kike ba amma kitasa yana asarar kudinsa.


Tabe baki basira tay dama amfada miki nice nake cewa ya sayo min duk abinda kika ga ya bani ba nice na roke shiba ra'ayinsa ne dan haka manta kawai dashi muci nama Allah yasa gobe ya kawo kaza.

Dariya Zakiyya tay tana daukar naman tace shikenan bamu da bakin magana tunda muna kwasar gara.

Dagowa da zatay taga dan dishi-dishin Safah dake zaune a zabure tace haska fitila Basira meye waccan.

Da sauri suka haska fitilar dakin ganin safah yasa suka ce kan bala'i ana wata ga wata ke ubanwa ya kawo ki dakin mu sata kika zo mana ko.

Batare data kallesu ba tace sai kuje ku tambayi Adama da tace nanne masaukina bani da lokacin shirmen ku.

Shiru sukai suna kallonta basu sake tanka mata ba kawai da ido sukai zance suna maida kansu kan naman su.

Addu'ar bacci Safah tay tana tunanin zata samu jakadiya tace ta sauya mata daki bazata iya rayuwa da wadannan tantiran daki daya ba zasu dora mata hawan jini tunda bata san ranar barinta gidan ba kila har abada.


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
SAFREEYYAH
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


#Team Safah
#Team Abdul-jabbar


#YUSRAHMS#
NO 61πŸ‘‰ 62
Malam na Allah ne zaune baffa yana kusa dashi da alama magana suke me muhimmanci saboda yadda baffa ya nutsu kuma ya sunkuyar dakai irin ana gaban surukin nan.


Malam yace Abubakar watanni sunja amma babu wani labari akan batan Safara'u ni harna fitar darai gashi kun samu sabani da iyalinka abinda nake so dakai shine zama haka zai sanya ka cikin damuwa ba kowa a kusa dakai kayi hakuri ka mayar da Asabe dakinta.

Shine ma dalilin da yasa nakira ka jiya shine zuwanta na uku gurina akan nakira ka na baka hakuri tana son komawa dakinta.


Baffa dake sauraron malam cikin takaicin bazai iya musa masa ba matsayinsa na babba malaminsa kuma surukinsa ya isa dashi ta ko'ina.


Dole ya hakura ya sallama kai ya daga yana cewa to zanyi yadda kace amma bazan iya cigaba da zama da ita kadai ba zan auri Mariya dama harmun gama daidaitawa zuwa zan na fada maka kwanaki suka rage.

Murmushi na Allah yay eh hakan ma nada kyau Abubakar aiba haramun bane Allah ya nuna mana yasa ayi a sa'a ya sanya alkhairi da zaman lafiya.

Cikin jin dadin addu'ar malam na Allah baffa yace amin malam na gode.


Washe gari Safah nayin sallar asuba tabar musu dakin dama zarisha ta nuna mata dakin da suke kwana nanta shiga ganin zarisha nakan sallaya ga katifa empty yasa ta fahimci tatace kwanciya tay tadan sake matsewa kafin gari ya waye.

Karfe bakwai da rabi zarisha ta tasheta suka shiga gurin jakadiya bayan sun gaisheta ta basu abin karyawa takwas na cika ta debe su sukai.


part din Fatima domin dama acan zarisha ke aiki tay farin cikin ganin Safah ma can za'a kaita shikenan ta tsallakewa tarkon Ammy indai a part din Fatima kake aiki zewiya ta canza ka saidai in baka da hali.

Kana da dabi'u irin na beraπŸ–πŸme zare-zare barawo kenan to bazaku zauna inuwa daya da ita ba.

Zaune suka sameta a palor tana ganin jakadiya ta saki murmushi tana cewa barka da kwana Lantana fatan an samu?.

Ba shiri Safah ta zubawa Fatima ido cikin mamaki jin tana matar sarkin masarautar guda maimakon ta bari a gaishe da ita amma itace ke fara gaida mutane.


Zama sukai cikin jinjinawa rashin girman kanta jakadiya na cewa ranki ya dade ga daya me hankali na samo miki zan sake dubawa na binkito miki wasu..


"To Lantana lallai kwarai babu shakka zatay hankali ko ba'a gwada ba ana sanin na hakika ido ba mudu bane amma yasan kima nagode haka ma kinyi min kokari.

Dadi sosai jakadiya taji shiyasa bata gajiya da zama tare da Fatima saboda tasan daraja da kimar dan adam.


Mikewa jakadiya tay cikin nuna godiya ta fita domin zata shiga bangaren hajiya ne.


Kallon su tay bayan fitar jakadiya tana cewa ke yarta ceko sunanki Zuhriyyah wannan bakuwar kuma mene sunan ta"?.


Dan sunkuyar dakai Zarisha tay murya a nutse tace sunana Zarisha wannan kuma kawa ta ce sunanta Safah.


"Ok yayi kyau Zarisha gurin da kike aiki kuje tare kema kya samu sassauci.


Kai Zarisha ta daga to ranki ya dade mun gode Allah ya kara girma.

Kallon Safah tay cikin nuna farin cikin ganin tunda tazo nan ta kubuta daga hannun Ammy tace tashi muje mikewa Safah tay tana godiya suka shiga wata kofa.



Watan ramadan ya kama dan haka aka ragewa bayi ayyukan su domin suma su samu sassauci a cikin azumin su musamman na bangaren Fatima sunfi kowa jin dadi da hutawa gashi kullum saita raba musu abun shan ruwa kala kala wani ma basu taba ganinsa ba balle suci.



Hanne na zaune Ammy ta fito ganinta yasa cikin mamaki da dan hanzarin son jin meye labari ta karaso ba kamar kullum ba fuskarta a sake ta zauna tana kallon Hanne.

Tace uhum ina jinki yau kuma da wanne kalar shirmen labarin kika zo"?.


Gyara zama Hanne tay tana dage kai sama alamun tunani.


Taje wani kauye can cikin surkukin daji tare da taimakon wata kawarta yar duniya kuma ta samu boka a wannan dajin kamar yadda Ammy keso.


Saida ya gama yan surkullen sa sannan ya bawa su Hanne damar zama jikin hanne rawa yake sosai da bata saba ba sai yanzu take dana sanin zuwanta sabanin kawarta data riga ta zama kwastomar wannan bokan nasan abin duniya.


Da boka ya bukaci tay bayanin abinda ya kawota kanta tsaye tace kasuwanci da daukar fansa suna ya kawo ni.


Boka dake ta gyada kai kamar kadangare yace bayani muka nema ba magana a dunkule ba.


Dan saita nutsuwar ta Hanne tay tana cewa boka aiki uwar dakina ce take son kashe kishiyarta kuma ta raba danta da dan uwansa sannan ta mallake mijinta sai abinda take so za'ayi.


Dariya boka ya kama ba kakkautawa har saida Hanne ta tsorata kuma tay dana sanin zuwan ta gurin.

Shiru yay tare da rufe idonsa yayin da wata bakar tsuntsuwa tazo ta sauka a kafadarsa tana wani irin kuka me firgitarwa zuwa dan lokacin da baifi sakan uku ba ta bace bat.


Bude ido boka yay yana cewa shikenan za'ai mata duk abinda take so aikin zaiyi nasara zamu tura wa samarin bakaken aljanun da zasu hanasu zaman lafiya kamar yadda take so zasu raba kansu su dawo makiyan juna.


Sannan game da kishiyarta wannan shiyafi sauki yau yau dinnan bazata kwana a duniya ba zamu tura mata mugun aljani me wuta da bakin takobi ya aikata.


Da sauri Hanne tace a'a boka ba wannan ya kawo niba ina son ka saba lamba kada ka aikata abu ko daya cikin wanda ka fada.


Zan hada hannu dakai domin yin kasuwanci kada ka tura a kashe kishiyarta kamar yadda take so ka kyale su fafata domin kuwa itace daidai da ita wacce take gyara mata zama.


Yara kuma karka rabasu idan san samu nema kayi wani abu dazai sake hade kansu da kaunar junan su fiye da yanzu boka idan kaimin haka ni kuma zan baka duk abinda kake so.


Boka dake zare ido yana surutai yace shikenan za'ai hakan amma yanzu dole kin sawa aljanu kwadayin shan jini domin sunyi haramar tafiya kasheta ma nine na dakatar dasu saikin kawo musu nama.


Kai Hanne ta daga to boka amma taya naman zai same ka.

Dan tabo ta kawarta tay ba gani ba ki damka komai a hannuna ni kuma zan kawo masa.

Ran boka ya dade mu zamu tafi duk abinda ta bayar zan kawo maka.


Mikewa sukai suna fita bayan sunyi tafiya me nisa sun fita daga dajin domin suna hango dan kauyen dake gefe tsayawa sukai jummale dake kallon Hanne tace.


Amma kawata meyasa kika canza abinda ta aiko ki bakya jin tsoron ta gane gaskiya ya zaki idan ta tarfa ki.


Dariya Hanne tay haba jummala nifa ba sokuwa ce irinta ba babu yadda za'ai ta gane.


Sannan bazan taba bari a cutar da Fatima ba domin mace ce wacce tasan abinda take zuwanta ta gyara mana masarautar nan ta kankaro darajar bayi ko nima ta taimake ni idan nabari aka cutar da ita kuma da hadin bakina na zama butulu.


Abduljabbar ya kasance maraya taba shi ze iya jamin masifa balle yaron ina kaunarsa tun baisan waye shiba nake bashi kariya irin sharrika da tarko kala kala da Adama taso jefa shi ban bari domin a lokacin da mahaifiyarsa ke raye ta taimake ni.

Bazan so ganin wani mummunan abu ya faru da danta ba kuma ace da hadin gwiwata wannan abun kunya ne a waje na.


Dariya jummale tay haka ne kawata kema kinyi gaskiya kuma kin riki kwakkwaran sheda yanzu muje ki karasa gidana kici abinci ki huta zuwa gobe da sassafe na miki rakiya ki tafi tunda kinga azumine ga magriba ta taho.

Wucewa sukai Hanne nacewa kamar kinsan yunwa nakeji azzalumar bata barni nayi suhur ka ba ta koro ni.

Cikin tsokana jummale tace ahayye nanaye damarki ta samu kawata shiyasa take juya ki kamar yadda ake juya moda a randa yayin debar ruwa.

Hanne tace eh damata ta gama samu yanzu lokacina ne ba nata ba muje ni kema duk kin dameni.


Murmushi tay lokacin data dawo daga tunanin ta dan kalli Ammy ganin yadda ta zuba mata ido yasa tay kasda kanta tana ce wa .


ranki ya dade ki farin ciki naje wani kauye can me nisa cikin daji kuma na samu ganawa da wani ri'kek'ken boka wanda ya iya kyakkyawan aiki na masa bayanin komai.


Yace aljanu na bukatar jini akai musu dabba sannan su bada damar ayi duk abinda kike so".


Cikin farin ciki Ammy tace dakyau Hanne yau bazan iya bacci ba saboda murna kuma nayi miki alkawarin kyauta me tsoka shima bokan haka yanzu yaushe yace ki koma,?.


Hanne nadan susa kamar sabuwar kamu tace ko gobe ma ranki ya dade beba da ranar komawa ba.

Ok zan hada miki kaya masu yawa wanda zaki kai masa dan yaji dadin yin aikin akan lokaci.

Mikewa hanne tay tana cewa to duk yadda kika ce bari na karasa bangaren mu sai goben.


Bayan fitar hanne murmushi ta saki tana cewa Fatima ki shirya kin kusa tafiya lahira sannan Abduljabbar zaka wulakanta rayuwa zatai maka tsanani dana Amfal kuma zai dawo gareni ta ruwan sanyi.

#MRS AL'AMEEN AHMAD CE.


#YUSRAHMS#
NO.63πŸ‘‰ 64
Safah na zaune tay tagumi ga robar abincin data karbo gabanta ko loma daya batay ba kawai ta fada kogin tunani.


Shigowa dakin su Zakiyya sukai suna zama cikin jan tsaki Basira tace wallahi lamarin goggo naban haushi yanzu wannan abincin ne zai ishe mu saikace wasu yayayyu.


Dan tabe baki zakiyya tay toya muka iya tunda iyayen mu ba sune masu gurin girki ba amma kalli na jikin jakadiya masu ido da kwalli an dibo haram ta fada tana nuna inda Safah ke zaune.


Kallon gurin basira tay tana mikewa tsaye kuturun uba inna yarda shegiya nake jifa abincinta yakai na mu na mutum biyu.


Cikin zuga zakiyya tace dauko mana shi kawai mu kara tunda naga yau tunani ne abincin ta.


Zuwa Basira tay ta suro kwanan tana afawa akan tasu ta zauna suka fara ci daidai Zarisha ta leko zataiwa Safah magana.


Ganin abinda ya faru afusace ta shigo dakin tana zuwa gaban su ba wani saurare tay bol da kwanan abincin ya tarwatse.


Mikewa sukai cikin huci Basira tace kan uban can Zarisha meye hakan ubanwa yace kizo ki barar mana da abinci?.


Cikin bacin rai Zarisha ta damko basira tana matse ta dakyau jikin bango tace uban kine wato saboda kunga bata kula ku shine kuke uzurar mata ko.


Ta fada tana kallon zakiyya danja da baya tay cikin shakka tace wallahi Zarisha bani bace Basira ce.

Hankada basira gefe tay tana cewa koma dai waye ubanku zakuci a gurina nibai dame niba fallallun daki kawai.


Safah ta kalla tana cewa muje kici acan mikewa Safah tay suna fita.

Dariya Zakiyya tay tana kallon Basira tace yi hakuri kyale zamu kamata ne saimun faffasa mata ido.


Tsakin takaici Basira taja tana nufar kofar fita tace dalla can banza rufe min baki matsoraciya da kika kasa yin komai a gabanta sai yanzu kike wani ihu bayan hari.


Dariya zakiyya ta sake shekewa da ita tana daukar sauran abincin dake kwanon tace kafin ki dawo bari na cinye wannan din.


Jakadiya na daki taga sun shiga ran Zarisha abace cikin alamar tambaya tace lafiya naga kina ta fushi?.


Zama sukai zarisha na debo musu abinci tace ina fa lafiya wadannan yan iskan su Basira sai takurawa Safah suke yanzu shiga ta sun dauke abincinta sun hade da nasu zasu cinye wa yasan iyakacin abinda suke mata tunda ba fada take ba dan Allah tunda yanzu a bangaren mu take aiki a raba ta da dakin umma.


Kai jakadiya ta daga shikenan Zarisha in anjuma kuje ta dauko katifar ta ki maida dakin ku.

Cikin farin ciki Zarisha tace yauwa yanzu naji magana.

Da gudu Marwa ta sheko daga harabar gidan tana shiga kitchen ta dauko muciya bata zame ko'ina basai kofar dakin da Safah ta zauna tana zuwa ta daga muciyar ta doka cike da masifa tace.


Ke munafika fito naci uwarki babu me hanani cin ubanki yau kema saidai ki kwanan asibiti kuma ki biya duk kudin da muka kashe miki nida Samha ko mu mayar dake tsohuwar dole mu zubar miki da hakora.

Ta karasa maganar tana sake dukan kofar da karfi saiga muciya ta balle gida biyu.

Dariya Seeya ke shekawa cikin tsokana tace lallai marwa kina jin dadinki wato muciyar da kike tukawa alhajin naki tuwon shinkafa ko semovita kika balla aikam bamu baki aro saidai ki sayo.


Cikin bacin rai marwa ta juya tana huci tace ke kuma akuya wa yasa ko dake maza ki saitawa kanki hanya kafin na miki mugun rashin mutunci.

Dan rike kugu Seeya tay oh da gaske baki da wannan kwarin gwiwar nidai gaskiya zan fada miki wannan yarinyar tay miki nisa

Please Login or Register in order to submit comment