Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damu ba bayan rasuwar ta".


Cikin girmamawa Emir yace"Ai baba kunfi karfin haka a gurina badan ma yanayin da muke ciki na mulki ba da duk sati zan rika zuwa muku to amma babu hali".



Malam yace"karka damu hakan ma nayi matukar jin dadin ganin ku kuma ina fatan ba yau zaku koma ba"?.



Amsa Emir ya bashi"eh su ba yau zasu koma ba nine dai zan tafi domin zanyi baki da dare su daga baya zasu taho".
Dadi sosai malam yaji domin ko ba komai zasu saba da jikan su .



Lokacin da sarki ya tashi tafiya rakiya sukai masa kafin ya musu sallama da drivern sa suka wuce shi kuma malam suka dawo gida.




Hidima suka hau yi musu ta saukar baki wanda malam ya yanka rago guda ya kawai mahauta suka yo masa tsiren sa ga kuma hadaddan kindirmo wanda already tun kafin suzo yake a dafe".



Da dare bayan sunyo sallah malam ya raka su dakin da zasu kwana zaro ido waje Abdul-jabbar yayi yana kallon malam yace "haba dai katifar yayin shinkafa akai zamu kwana? Allah jiki na zaiyi ciwo ".



Malam dake kallon sa yace"to aiko dai akai zaka kwana domin mu bamu da katifa mai soso irin taku ta yan binni".



Gaskiya to ka nemo mana ko aro ce kafin gari ya waye wannan ai bazan iya bacci akai ba gashi ko filo babu Allah nan gaba idan zanzo da katifa zan rika zuwa".


Malam daya bude baki yana kallon shi yace"kaga dan binni harda wani filo to mu bamu dashi idan ba nine zan kwanta kai matashin kan dani ba"?kwanciya malam yay yana kallon shi yace "kwanta kawai ba matsala zan iya daukar nauyin ka har zuwa asuba".



Murmushi Abdul-jabbar yay yana dago shi yace"wanne kashi da ran jika fa kamar iska ta bushe dana dago ka idan kuma na kwanta a kanka ai gobe saidai mu kaika makabarta ".


Malam yace"aida ka kwanta kawai ba komai bakon ka annabin ka dan nayi maka haka yanaa hakkin bakunta ka farantawa bakon ka kayi masa hidima har na tsawon kwana uku".


"A'a to na yafe kawai zan kwanta a hakan saida safe"murmushi malam yay yana juyawa yace"Allah ya tashe mu lfy "daga haka ya fita zama Abdul-jabbar yay a gefen katifar yana kallon Amfal dake kallon sa tunda suka fara drama da malam yace"yadai zaka wani zuro min ido ko ban fadi gaskiya bane nasan yau har gari ya waye ba zamuyi baccin arziki ba".



Kai Amfal ya girgiza yana mikewa yace"Allah bros wani sa'in idan kana mgn kamar ba kaiba ji yadda ka takurawa tsohon nan da tsokanar ka ai wannan katifar tafi dadin kwanciya akan wacce kake kwana akai".



Inji uban wa ka taba ganin inda aka hada hanyar jirgi da mota"?Amfal yace"sosai ma kai baka taba gani ba kenan lallai ashe da sauran ka"rabuwa dashi Abdul-jabbar yay yana kwanciya.


"Subahanallah"abinda yace kenan jin kamar wanda ya kwanta akan dutsi dariya Amfal yay yana kallon sa yace"yadai akwai laushi ko matsa min na kwanta nifa sai naji ma kamar tafi tamu dadin kwanciya inaga idan zamu tafi zan sayi daya naje na dora akan gadon mu".


Da kuwa saidai ka kwana kai daya malam dan saimun raba dakin kwana".



Kallon fitilar dake dakin yay irin yar wayarin dinnan ce mai batir biyu yana cewa "badan dare yayi ba da nayi abubuwa da yawa amma Allah ya tashe mu lafiya" matsawa kadan yay inda Amfal zai kwanta tuni hannun sa ya soki wani dan yayi aikam ba arziki ya mike yana cewa shikenan yatsa na ya fice Amfal hasko min".



Mikewa Amfal yay hankali tashe yana kunna hasken waya sai ganin dan yayin sukai makale zare masa Amfal yay yana cewa "sannu ashe ma dan wannan abinne kamar ba soja ba"hade rai Abdul-jabbar yay yana kallon saa yace"idan soja ne dan abu ya cutar dani bazan fada ba sbd gamai jikin karfe ko".



Dariya amfal yay "wallh harka tuna min da hajiya mai ran karfe Allah sarki masoyiya ta tana can kila ma ta dade dayin bacci ".



Abdul-jabbar bai sake mgn ba shima Amfal haka kawai dai sun kwanta tare da kashe wutar dakin".


Typing๐Ÿ“ฒ



๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡
SAFREEYYAH
๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡๐Ÿ‡



๐Ÿ’ซ๐ŸŒŒ๐Ÿ’กANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ’ซ๐ŸŒŒ๐Ÿ’ก



@YUSRAH MUSA ABUBAKAR



^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
^^^^^^^^^^^^^^^^^^
^^^^^^^^^^^^
^^^^^^^
^^^^
^^
^


MANXON ALLAH S A W
Ya wanda halin sane tayar da mai rauni dabi'ar kace taimako ya nasiruddini a kujerar ka awwalun ne kai marar sani ya wanda bai taba hanawa masu nema ba".


"Aminci ga miftahul jannatun na'ima
Aminci ga 'kiblar bayi a ran kiyama
Aminci ga mai shiryarwa cikin salama
Aminci ga duk mai matsayi dakai ya samu
Aminci ga duk mai girmaran dakai, ya samu
Aminci ga duk mai daraja dakai ya samu
Aminci ga fatuhul akbar aya imamu yusrah musa ce tare dani da gaisuwa ta".



#YUSRAHMS#
NO.17๐Ÿ‘‰ 18
Babu wanda yayi bacci a cikin su har gari ya waye dakyar kuwa sukaje masallaci sbd ciwon jiki.



Karfe 12:00 suka dawo gidan daga masallacin dan a cewar Abdul-jabbar ya danfi akan gidan a kofar dakin suka zauna kan babbar tabarmar dake shinfide lokacin malam ya dawo daga kasuwa shima ya zauna bayan sun gaisa Hadiza ta kawo musu kayan karyawa hadaddan kunu da kyakkyawar waina mai kuli gefe guda kuma ga kwanan tuwo".


Kallon ta Abdul-jabbar yayi"gaskiya nifa bazan ciba a nemo min abinci kawai naci dan yunwa nake ji"baki bude Hadiza tace"kuma bayan ga abinci nan har yafi kayan dadin da kake sha".




Shiru yay yaa kallonta sugar ta zuba cikin kunun tasa ludayi ta gauraya sosai sannan ta dau kofi karami ta zuba tana bashi tace"akwai dadi kwada sha kaji"kai ya girgiza dan haka Hadiza ta mikawa Amfal tana cewa karbi jika na dan Allah rabu da wannan kai ci abinka".




Karba Amfal yayi yana sha ya dago yana kallon Abdul-jabbar da shima shi yake kallo baiyi mgn ba yaci gaba da shan kunu sai gashi ya dire kofi yana cewa"kai gaskiya yayi sosai bari na kara"dariya Hadiza tayi wallh kara gashi nan kuma dan ma baka hada da wainar bane da sai kayi santi".




Duk yadda Abdul-jabbar yaso mazewa saida ya tambayi Amfal"wai da dadi ne"aje kofin Amfal yay yana cewa"to maganar gaskiya nidai ba nace ba sbd a tare dani akwai koshi saidai kaida kake jin yunwa ka gwadaa kar nace da dadi kasha bai maka ba kace nayi karya".




Harararsa Abdul-jabbar yay yana daukar kofin shima ya deba ya soma sha daga farko idan ka kalle shi zakai tunanin madaci yake sha sai daga baya suka ga ya dire kofi ya kuma deba dariya sukai amma ko kula su baiyi ba saida yasha kofi uku hatta wainar saida taki jiki".


Malam yace"wato dan binni ya akai ne? naga ka ware sai shan kunu kake da alama ya burge ka da mu zakaiwa bagu waikai sai andoni da kwai".



Dariya Amfal yay yana kallon yadda Abdul-jabbar ya tsume yace" ba andoni ake cewa ba indomie take acan dinma koko da kosai yake karyawa dasu kawai yaga ku tsofi ne shine yake son yi muku burga ".


Malam yace "ai kuma saidai ya burge kansa gashinan ya dawo dai dai shine yake hade rai kar muce ya yaba da kunun da yasha kowa dai ya ganka yasan kai jinin fulani ne jauro".




Hadiza tace"nima na gani kuma na shaida ta tafar sauke Abdul-jabbar baice ba saima mikewa da yay yana cewa a sama masa ruwan wanka tashi Hadiza tayi dan ta dafaa masa da yake ana dan yin sanyi ne .




Tsaye Safah take tana gyara kayan abincin dake dinning a jere mk saurayin gidan shine babba ya shigo gano ta da yayi saiya fasa wuce wa ya karasa inda take yana kallon yadda kayan dake jikin ta sukai matukar yi mata kyau.




Ba zato taji an dafa ta a razane ta dago ganin wanda ke tsaye yasa jikinta na rawa taja da baya kara matsowa yay yana murmushi yace"first lady ya kike"? Muryar ta na rawa tace"lafiya".



Kai ya jinjina yana cewa"hakan nada kyau dama amm nace ba kinga lady ina jin yunwa please ki shiga kitchen ki samar min wani abu dazan ci kafin nayi wanka na fito"yana kaiwa nan yay gaba da kallo Safah ta bishi maganar Allah tunda saurayin nan ya dawo ta tsani gidan nan kuma zata samu baba maryam kawai tace ta mayar da ita gida hankalin ta zaifi kwanciya dan ta fuskanci mk kamar yana harkar mata.




Sauke ajiyar zuciya tayi bayan wucewar sa kafin ta koma bangaren da suke ta dauko hijab tana fitowa ji tayi ance "Safah ina zuwa"? a gicece ta juya dan saboda firgici bata iya bambance cewa muryar mace bace.


Ganin Alawiyah kanwar Salmah yasa ta sauke ajiyar zuciya tana cewa"wallh kitchen zan shiga wannan yayan naku ne yace na sama masa abinda zaici".




Kara kallon ta Alawiyah tay"humm ai yaya nada takura balle wannan karon da yayi sa'a kina gidan yana son mace wacce ta iya girki shi yasa yake damun ki da abincin ki baya burge shi zuwan sa da Yanzu yasa an dauko wata saidai kita hakuri kafin ya gama kwanakin sa ya koma".



Murmushin karfin hali safah tay batare da tayi mgn ba zata wuce Alawiyah tace"kinga raka ni anguwa har ma dawo dan wankan sa yakan ci lokaci" cikin jin dadi safah ta bita suka tafi dan dama fargabar komawa cikin gidan take tunda tasan hajiya bata nan taje gurin biki baba maryam kuma taje cikin yola ne dama iya itace a gidan suma yan matan duk suna makaranta batai tunanin Alawiyahn ta dawo ba".


Kuyi hakuri๐Ÿ™‡ typing yau baida yawa ina da uzurirrika ne๐Ÿ˜œ.


Mrs Al'ameen Ahmad ce ta kowa.



ONE LOVE๐Ÿ’•



Typing๐Ÿ“ฒ




๐Ÿ‡SAFREEYYAH๐Ÿ‡


ANNURI WRITER'S ASSOCIATION
BY Y M A TA AL'AMEEN.



๐Ÿ’ซ๐Ÿ’กANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐ŸŒŒ๐Ÿ’ก



๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ
๐Ÿ“ฟIt is FRIDAY DON'T FORGET TO RECITE SURATUL AL-KHAF,MAY ALLAH (S W T) OPEN THE DOOR OF SUCCESS AND HAPPINESS FOR ALL OF YOU (MUSLIM) AMEEEEEEN.๐Ÿ™


ALLAHUMMA SALLI WA SALLIM ALA SAYYIDIINA MUHAMMADIN SAYYIDIL MURSALINA.



๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ
๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ
๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ
๐ŸŽˆ๐ŸŽˆ
๐ŸŽˆ


#YUSRAHMS#
NO.19๐Ÿ‘‰20
Kamar yadda Ammy ta umarci Hanne haka ne ya faru bayan taje wani kauye tayi tambayar waye babban malamin da yake cire aljanu aka fada mata batai kasa a gwiwa ba taje gurin sa ta masa bayanin komai na cewa tana son maganin raba tsakani .


Bayan malam ya gama sauraron ta yace"to alhamdllh naji dukkan bayanan ki kuma na fahimta bani sunan su "kara dukawa hanne tay tace Abdul-jabbar da Amfal shine sunan samarin".



Kai malam ya daga bayyi magana ya soma zana kasa yana gogewa yayi yafi sau ashirin, amma baiga komai ba wani irin farin abu ya tare abinda yake son gani dagowa yayi yana kallon Hanne yace "wannan aikin bazai yiwu ba banga komai ba saidai zanyi miki istihara na gani in yaso saiki dawo zuwa jibi na fada miki abinda na gani game da wadannan samari".


Godiya Hanne tay tana ajewa malam kudi mai shegen yawa wanda kafin ta mike malam yace"a'a dauke kudin ki bani bukatar ko sisi"jiki na rawa Hanne ta dauki kudin da ta aje masa tayi waje tana mamakin zuhudin malamin batai tunanin zaiki karba ba.



Batun su Abdul-jabbar kam shida Amfal cikin Adamawa suka shiga suka yo sayayya ta ban mamaki wanda da suka dawo saida malam yace sai sun mayar dakyar Abdul-jabbar ya lallame shi ya kyale suka shiga da kayan.




Katifu ne da kayan abinci da generator ya kuma yowa Malam da Hadiza dinkuna da abubuwan ban sha'awa na zamani yan gari harda zuwa kallo ranar da aka tayar da generaton wai gidan malam ya zama gidan yan gayu .



Mk bai kwana gida ba tun fitowar da yayi yaga ba Safah babu alamar ta ya duba ko'ina shiru yabar gidan domin wani program zaije .

Ita kanta safah da taji cewa baya nan tayi matukar farin ciki kuma hankalin ta ya kwana tana fatan har ta tafi gida karya dawo".



Hanne ce zaune tazo jin sakamako malam ya dube ta yana cewa"to kamar yadda na fada miki nayi istihara kuma abinda na gani shine baza su taba rabuwa ba kuma wani asiri ko magani da za ayi dan raba su bazai ci ba duk malamin daya karbi kudin ki da sunan zaiyi miki aiki a kansu to yaudarar ki kawai zaiyi danya ci kudin ki soyayya ce da shakuwa mai karfi tsakanin su shawarar dazan baki ki hakura ki kyale su suyi rayuwar su kema kya huta idan kinji amma idan baki yarda da abinda na fada miki ba zaki iya zuwa ki tambayi wani malamin da kike tunanin ya fini sani ki sake gwada sa'arki saidai ina da tabbacin ba zaki nasara ba zaki iya tafiya".


Jiki a sanyaye tace "malam to bazai yiwu ko wani abu da zaisa su'ki juna? ba wallh idan na koma uwar gida na zatai fushi dajin wannan labarin".




Shiru malam yay yana kallon ta yace"na fada miki babu wani abu daya isa raba su babu shi sai mutuwa kuma na gani duk wanda yay yinkurin cutar da dayan su to zaiga sakamakon da zai biyo baya ina sake jaddada miki da ki sanar da ita wacce ta aiko ki cewa injini malam nace ta zubar da makaman yaki ta kyale su suci gaba da rayuwa karta debowa kanta abinda yafi karfin ta domin akwai tsari sosai a jikin dukkan su biyun wanda mahaifiyar baban su ta yi musu tun suna kanana kuma har yanzu bata daina ba domin tana son su sosai".




Gwiwoyin Hanne duk a sace tayiwa malam sallama ta tafi da zulumin yadda zata fara yiwa Ammy bayanin abinda malamin nan yace amma zata san yadda zatai idan ta koma".



Sosai zaman kauyen malam na Allah ke yiwa Abdul-jabbar dadi dan har baya so su koma can gida duk da yana kewar Abban su.


Dawowar su kenan daga zaga gari suka iske malam a waje kan wani itace wanda kana gani kasan ya dade a gurin zama sukai suna sashi a tsakiya domin suji dadin hirar,.





Kallon su yake cikin murmushi yace"Abdullahi da rabon dai baza ku ga juna ba kaida yar kanwar taka domin sun tafi Adamawa ita da maryama tun watan jiya kuma bana tunanin zasu dawo kwana kusa bansan ranar da zaku hadu ba lokacin da kuka zo kaida Muhammadu a sanda zaku tafi aikin soja batai wayon da za'a ce mata kai din yayan ta bane shine ya hana haduwar ku amma ina rokon Allah yasa ku hadu a kwana kusa".



Abdul-jabbar dake sauraron sa yace"naji kace kanwa ta a ina muka hadu wace ita"?.


Kai Malam ya jinjina kwarai ita din yar uwar kace Abdullahi domin ta kasance yar gidan kanwar mahaifiyar ka Zainabu wanda ita ma Fatima bayan ta rasu da yan shekaru ta bita to yar data bari ce ita kadai ce kuka hada kakanni da ita domin ni dama Fatima da Zainab ne kawai na haifa a duniya su kuma suka haife ku hakika ina sonku ina alfahari da ku".



Sosai Abdul-jabbar ke kallon shi yana juya maganar a ranshi lallai yana son ya ganta ita kadai ce jinin sa dazaiyi alfahari da ita a matsayin dangin sa na uwa bai daina duban Malam ba yace"me taje yi a Adamawa kuma yaushe zata dawo"?.



"Bani da tabbaci Abdullahi domin ba muyi zancen da ita ba kawai dai tazo yI mana sallama ne da yake gidan mahaifin ta yana gaba da mu ne sosai idan ma dai baku hadu yanzu ba tunda idan ta dawo mahaifin nata yace zaiyi mata aure da yaron kanin sa inaga ma kun wuce ta majalisar su san wani shago in kazo bikin sai kuga juna".



Cikin saurin da ba shiri Abdul-jabbar yace"aure kuma ?yanzu har tayi girman da za'ai mata aure? kodai irin auren kauyen da kuka saba za'ayi mata kodan ba nace ba bansani ba koda kadan na fita".



Dariya na Allah yayi yana cewa"sannu dan binni aikam dai baza a kira ta da yarinya ba tunda a 'kalla zatai 18 nake tunani idan ba mantawa nayi ba saidai tana da tsayin kafa idan ka ganta zakai tunanin ta haura shekarun nata"'.



"Ahhh kaji irin abin da nake fada tana tsayin kafa shiyasa za'ai auren taa lokacin ta baiyi ba tana yar karamar ta tafara tara yara duk subi su dora mata hawan jini wanda keda 18 ni a gurina yarinya sharaf wacce bata sansan ciwon kanta ba".



Kallon sa Amfal yay"Allah malam gyabbo uban yan son girma kace za musha kallo idan ka tashi zaben macen aure sa'ar shekarun ka zaka dauka don na ramfo manufar ka tuntuni na fahimci inda ka dosa nan kusa".



Aiko tukuicin harara ya samu cikin dakewa da tsokana Amfal yace"karya nayi maganar gaskiya malam bana son borin kunya kawai ka fito kace shirgegiyar mace kake so wanda ta kaika ba karamar yarinya ba kome kace mgn ta nakan daidai "?.


"Ban sani ba domin ban sako dakai ba uban yan shishshigi" .


Dariya Amfal yay "ni kuma nasa kaina wallh idan mutum ya zauna bros yadda kake da burga tsaf zaka sakaltar dashi dan kawai na fadi gaskiya".


"Ka fadi gaskiya ko ka shararawa mutane karya malam dama idan baka fada ba ni a tsari na babu auren yarinya mai karamin shekaru sabod.......bai karasa ba Amfal yamai rada a kunne dan kada na Allah yaji.


Yace cikin kasa da murya sosai"saboda idan ka auri karamar yarinya balla ta zakai baza ta iyaa da bukatunka ba tayi maka kadan a gado ko "?kallon sa Abdul-jabbar yay cikin xaro ido zaiyi mgn .


Amfal yace"karka wani wayance nasan haka zaka ce shiyasa na riga fada"ya karasa maganar yana dage gira ga dariya fal cikin sa ganin yadda Abdul-jabbar din ke binsa da kallon ya kasa maida masa martani"



"Nace ko nayi karya ne baa haka Kake nufi ba naga kana ta kallo na kodai ka shigaa shauki ne ban sani ba"?jin har lokacin bai tanka masa ba yace"gashi na hasbo jirgin ka lallai bros idan Kai aure zamu sha kallo saidai mu rufe kunnen mu da idanuwan mu dan kada mu makanc.........tashi yay da gudu ba tare daya karasa ba ganin Abdul-jabbar na shirin rike shi ya koma gefe yana dariya dan sarai dama so yake Abdul-jabbar din ya magantu.


Na Allah na kallon su cikin jin dadin ganin yadda kansu yake a hade yayi farin cikin hakan kuma ya godewa Allah idan ba ka sani ba baza ka taba cewa uban su daya ba idan kuma aka fada maka sai kayi mmk,.


Dawowa Amfal yay yana kallon sa yace"haba my bros ya muna mgnr arziki kuma ka wani kore ni dan Allah kaka malam jiye mana wannan maganar dan kawai na fadi......tarar numfashin sa Abdul-jabbar yay da fadin kasan Allah Amfal ni da kaine idan bakai shiru ba".



Rufe baki Amfal yay cikin zolaya yace"na rufe ruf๐Ÿ™Š kar muje bacci ka mulmule min wuya sorry bros dina I am so sorry don't disturbing me ba da kai nake ba misali nayi ".


"Kai ka sani I shall not mind"



Rike baki malam yay "to naji kun fara sako turanci ni kuma bana ji abar maganar ku tashi na raka ku gidan mahaifin ta"mikewa sukai suna sashi a tsakiya yayin da duk inda suka gifta kallon su ake mutane na mamakin wai wannan yayan sarkin kano ne kuma babban dan gidan Fatima ne jikan malam na Allah".



Mrs A Ahmad ce.



We will meet again
Thanks for loving me.


Nafila bayan sallar magriba๐Ÿ‘‡
Raka.a biyu ce
Bayan ka idar da sallar magriba saika ta kayi niyyar nafila a raka.ar farko zaka karanta fatiha da 'kulya daya raka'a ta biyu kuma fatiha da 'kulhuwa daya kayi zaman tahiya kai sallama,idan kai haka Allah zai fidda kai a zunubin ka kamar yadda miciji yake fita daga cikin sa'bar sa.


Allah ya bamu ikon yi Amin.


"(Azeemu domin muntahal mukami
(A kara hau dani makurar mukami
(A karfafa mini a dade ni kaimi
(Na bayyanar da sirri na zuciya ta).


Ina godiya Safiyyah Aliyu Zaria (maman khaleel khairi da kuma khaleepha)ina matukar jin dadi da nuna kulawar kI gare ni Allah ya kara barin mu a tare may Allah help and bless you and your household anywhere you are.


๐Ÿ’• Mrs A Ahmad gnrl๐Ÿ’•.



Typing๐Ÿ“ฒ


๐Ÿ‡SAFREEYYAH๐Ÿ‡




๐ŸŒŒ๐Ÿ’ก๐Ÿ’ซANNURI WRITER'S ASSOCIATION๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ก๐ŸŒŒ
Gidan haske da samar da farin ciki da karbar bakin ta ANNURI tana maraba marhabun
lale lale da kowa ba cuta kuma babu cutarwa.


18@Yusin Al'ameen Ahmad ยปยซยปยซยปยซ ยซยป ยปยซยปยซยปยซ [email protected]



Whattpad.
Mrs Al'ameen Ahmad ce.


ADDU'AR NEMAN SAMUN SHIRIYA A WAJEN ALLAH (S W T) KAI DA IYALAN KA DA AL-UMMAR MUSULMI BAKI DAYA.๐Ÿ‘‡
=====Rabbana waja'alna musullmaini laka wamin zurriyati na ummatan muslimatal laka wa'arina manasikana watub alaina innaka antat tauwabur raheem=====.


ยปยซ ยปยซ ยซยปยซยป ยปยซ ยปยซ
๐Ÿ‘ Rabbana waba'asfihim rasulan minhum yatlu alaihim ayatika wa yu'allimuhumul kitaba walhikimata wa yuzakkihim innaka antal azizul hakim.


Allahuma antas salam wa minkas salam tabarika ya zuljalalu wal ikram.


#Astagfirillahal azimul lazi la'ilaha illah huwal hayyum 'kayyum wa'atubi ilaihi๐Ÿ‘‰ idan ka fadi haka sau uku 3x bayan kowacce sallar farillah Allah zai gafarta maka zunubin ka na shekara dari hudu.



YUSRAHMS ABUBAKAR
๐Ÿ™‹Nifa I have no girman kai๐Ÿ™†๐Ÿ˜ if you are fushi๐Ÿ˜ ๐Ÿ˜Ž๐Ÿ™„ dani to wallh you are just batawa kan k lokaci๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜๐Ÿ˜ƒ .




#YUSRAHMS#
NO.21๐Ÿ‘‰ 22
Yau mk ya dawo gari safara'u bata sani ba saida sukai abincin breakfast ita da baba maryam taje serving dinsu ta ganshi gaban ta ne yay mugun faduwa nan tahau maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un.


Suna hada ido ya daga mata gira "alamar yadai"?saurin dauke kai tayi daga saitin inda yake da kyar hannun ta na rawa ta gama serving dinsu Allah Allah take tabar gurin sbd shi zata tafi kenan hajiya Binta data fahimci kamar safan bata cikin hankalin ta tace"meke damun kine Safara'u ko baki da lfy ne baki fada ba".



Shiru tay har saida hajiya Binta ta sake tambayar ta dakyar jikin ta duk a sanyaye tace "eh hajiya bana jin dadi ne".



"Ok kuma shine baza ki fada ba in banda abinki ai jinya ta koru komai jeki kwanta zansa a kira doctor ya duba ki"to safah tace zata tafi kenan taji mk na cewa"kawai mum bari na kaita a duba ta basai yazo ba" ba damuwa kadai hajiya binta tace"shi kuma ya mike cikin murmushi yana kallon safah da itama shi ta zubawa ido cikin tashin hankalin jin abinda yace tasan akwai wani kullalliyar da yake shiryawa.


Har inda take ya tako cikin kasa da murya yace"big girl ina jiran ki a mota na zaki ganta black idan kin gama shiryawa kuma ki tabbata kinsa turare Mai matukar karfi da dadi saboda ina son haka".



Yana fadin haka ya tafi ya barta a gurin ta daskare kamar Wata gunki cikin tarin kunar rai da fargaba salmah data lura da tsaiwar taa tace"safah kije mana ki dauko hijab dinki yaya baya son African time".


Daga kafa safara'u tayi cikin tarin damuwa ta soma tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki har ta fita a part din ta shiga bangaren su kwanciya tayi akan katifa hawaye na zuba a idon ta lallai bata kaunar zaman Gidan nan sbd mk bari baba maryam ta shigo tace mata tana son taje taa gano baffan ta daga nan idan ta tafi baza taa sake dawowa ba har abada lamarin mk yana bata tsoro bargo taja tana lulluba kamar meyin bacci taci gaba da tunani kafin shigowar baba maryam din.



Ba zato taji an yaye bargon data rufa kan tayi wani yunkuri ta sake jin ana jan zip din rigar ta a burkice ta wuntsula tana sauka daga kan katifar ta diro kasa wanda babu shiri ta saki kara sakamakon tankwashewar da kafar ta tayi durkusawa tay a gurin cikin azaba tana cewason "wash Allah kafa ta".


Kanta mk ya nufo yana cewa sorry muga kafan mi tayi"ganin yayo kanta zai rike kafar yasa taa mike tana ja baya da sauri kara matso ta yayi.


Cikin kuka tace"dan Allah ka bari bana so karka ka taba ni"dakatawa yay yana kallon ta yace"humyimm village girl wai ke me yasa bazaki waye ba ne gaki a haka beauty amma sai duhun kai look madam I love you ina sonki ne ki fahimta mana ki saki jikin ki dani zaki huta zan baki duk abinda kike so idan naji kina da dadin harka ma maybe na aure ki ladyna ko me kika ce ni da ke mun zama abokan harkalla".



Zaro ido safah tay cikin tashin hankali tace"nidai dan Allah kayi hakuri ina da wanda zan aura"kallon sama da kasa ya mata yana cewa"yayi kyau Amma da alama

Please Login or Register in order to submit comment