Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

GUDUN KADDARA Complete Hausa Novel Document by GUDUN KADDARA


GUDUN KADDARA

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 48413



GUDUN KADDARA

Reading Time: 4 Hours

Added On: 20, Jan 2025

Author: Safiyya Abdullahi Huguma ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Zafafa biyar

Author Phone : 09166221261

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 274.57 kb

File Type: txt

Views: 241+

Download: 235+

Last download: 4 days ago

Description/Story: *_Bismillahir rahmanir rahim_*

🏃🏽‍♀️ *_GUDUN ƘADDARA_*🏃🏽‍♀️

*H U G U M A*

PAGE 01


*_Da sunan Allah me rahama me jin qai,dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangijin talikai,tsira da aminci su tabbata ga shugaban halitta annabi muhammadu S A W_

_wannan karon labarin namu zai sauka ne a qasar nijer,duk inda akaga kuskure ko gyara sai ayi haquri,domin ni banigerian ce😂_


*_N I J E R maraɗi_*



Tun daga taku me nisan tazara tsakaninka da ainihin layin,amma kuma kana iya jin tashin sautin gangar kidan data karade kusan kowacce shiyya ta unguwar.

Lokacin da ka cimma nasarar isowa layin kuwa,taron dandazon samari ne da 'yammata 'yan bana bakwai,wadanda rayuwa da kuma duniya ke musu dadi suke cashewa,wasu cikin ainihin tsakiyar filin da aka bari domin bawa masu sha'awar taka rawar da kyau,wasu kuma daga bayan fage suke takawa suna kuma rausayawa. Kowannensu cikin shigar dake nuna zallar wayewa da kuma sukunin rayuwa yake. Kusan fiye da rabinsu kyawawan BUZAYE ne,wadanda aka fi sani da ABZINAWA,jefi jefi kuma kana iya hangen masu surkin launin fata,wanda wasunsu suka kasance barebarin nijer zabarmawa da sauran yarukan da qasar nijer din ta hada.

A hankali kyakkyawar motar fara qal qirar Yaris ke gangarowa. A kallon farko idan ka yiwa motar,yanayin yadda take gangarowa kadai zai iya sanyawa kayi zaton man fetur din dake taimakawa wajen motsawarta ne yake Shirin qarewa. Saidai kuma sam ba hakan bane.

Kyakkyawan farin matashin ba'abzinen dake zaune cikin motar ne ua zabi ya tuqa motar a haka,farin buzun saurayin da tashin farko kuma kai tsaye zaka kirashi da BALARABE zalla babu mix. Fuskarsa a dinke take tsaf,yana kuma wani irin tuqi kamar wanda jinin sarauta ke zagayawa a gangar jikinsa zuwa ruhinsa. Duka duka shekarun haihuwarsa ba zasu wuce ashirin da hudu zuwa da biyar ba. Amma wani irin lafiyayyen kwarjini dake shimfide akan fuskarsa zai sanya ka dauka wani babban mutum ne dake da wani muqami na mulki ko sarauta.

Tunda ya jiyo sautin kidan daga nesa ranshi ya soma baci,idan akwai abinda ya tsana cikin dabi'ar qasarsu yake da ikon da zai iya sauyawa to wannan tana daya daga ciki. Yaja tsaki har baisan adadinsa ba. Wannan hanyar itace hanya mafi sauqi a gareshi da zai isa unguwarsu,to amma yanayin yadda suka toshe layin yasan zaiyi wahala ya samu ya wuce cikin sauqi ko dadin rai.

Wani siririn tsakin ya sake ja,yadan cije jajayen lips dinsa na qasa yana cusa yatsunsa cikin lallausa kuma cikakkiyar sumarsa ta asalin buzaye,ya qara hannu daya kan guda dayan da yake tuqin akai,ya soma gangarawa da motar gefe don ya samu gurin parking.

Ya gwammace yabar motar a nan guraren,idan yaje ya karbo aiken daga wajen babbo din,sai ya dawo ya dauki motar ya wuce.

Kashe motar yayi,sannan ya zare key din,ya miqa hannunsa ya dauki wata baqar leda sannan ya buda motar ya zura qafafunsa dake sanye cikin boots din da wandon kakin sojin dake jikinsa shi kadai ya isa ya gaya maka waye shi?.

Tun tsaiwar motar taja hankalin mutane da yawa dake wajen,baisan me ya sanya ba,motar ba mallakinsa bace,amma a duk lokacin da ya shiga motar sai take qara masa kwarjini me yawa,abu daya da baiso yadda take sanyawa idanu ke yawa a kansa,wannan ya sanya ba kasafai ma ya fiya hawa din ba,saidai idan aiken gaggawa ne bobbo ko tati sukayi masa,kamar dai wannan aiken.

Da kyau ya hade fuskarsa ba yana ci gaba da ratsa taron,wanda kusan maza sunfi yawa a ciki,zuciyarsa na baci a duk sanda yaga wata mace a cikinsu. Wannan wacce irin lalacewa ce?,qarfi da yaji suna daukan kansu kamar suna france?,baisan wacce irin dabi'ar banza ce wannan da har yau suka kasa dainata ba.

Sake kame jikinsa yayi da kyau lokacin da yake niyyar ratsawa ta sararin da aka bawa masu sha'awar raqashewa da kyau. Duk yadda yaso ya dauke idanuwansa daga kan yarinyar dake tsaye tsakiyar filin tana taka rawa cikin wani irin salo na qwarewa da kuma gwaninta,karya jiki tako ina,kama daga qugunta har zuwa qirjinta da ko irga dangi bata farayi ba,amma tabbas tana kan hanya. Qafafunta da take kadawa tayi gaba ta dawo tayi baya kamar wadda ake matsawa remote control.

Wata mummunar faduwa gabansa yayi,tun daga cikin qwaqwalwarsa zuwa kunnuwansa yaji wani irin sauti kamar an qwala masa farantin silver

"SULTANA!" ya kirayi sunanta cikin wani irin zallar fushi da ya cukuda da tsananin mamaki.

Ko kadan bata fahimci da tsaiwarsa a wajen bama bare ta jiyo kiran da yayi matan. A hankali daya cikin 'yammatan dake tsaye daga gefe,wanda tun ratsowarsa gurin yayi matuqar tafiya da hankalinsu ta matsa daura da ita kadan tana tabota. Sai data daddaki bayanta kusan sau uku sannan ta waiwayo,saidai maimakon idanunta su sauka akan wadda ke tabata din,basu zame ko ina ba sai cikin idanunsa.

Iyakar razana da firgita ta jita har tsakiyar hantarta,to amma ita din nuna tsoro ko razani saman fuskarta ba al'adarta bace,wannan ya sanya ta juya abinta,saidai kuma ta fara lissafin ta yadda zata zame tabar wajen tun kafin ya yarfata.

Ta karanto tunaninsa kuwa a dai dai,sanda yake taku cikin tsananin zafi don ya cimmata tayi amfani da wannan damar ta kurda ta cikin mutane ta fice. Sama ko qasa sultana tayi masa batan dabo. Cikin zafi yaja da baya ya kutsa ta gefen mutanen cikin sassarfa yana fita daga taron,burinsa shine kawai ya cimmata. WAI YAUSHE TA KOMA HAKA?,YA AKAYI TA SAUYA GABA DAYA?,DABI'UNTA SUKE KOMAWA MASU BAN TSORO?. Wannan tambayar itace ta dinga masa rakiya tana kuma ingizashi da sassarfa,har zuwa lokacin da ya dangane da katafaren gate din gidan nasu.

Cikin wani irin zafi ya tura qaramar qofar dake maqale da gate din gidan,a take ta bude ta kuma hadu da bango ta bada sautin BUM!. Farar buzuwar dake tsaye cikin parking space na gidan ta waiwayo wadda shekarunta ba zasu haura arba'in da hudu zuwa arba'in da biyar ba.

Idanu ta kafeshi dashi sosai sanda yake takowa cikin gidan,ba ita kadai ba,hatta baaba leko me gadin qofar gidan shi da hamidan dake da alhakin gyara da baiwa tsirran da suka qawata harabar gidan ruwa suma binsa sukayi da kallo. Dukkaninsu ya dauki hankulansu,saboda sanin da sukayi masa. Mutum ne da fushinsa bai fiya zuwa da sauqi ba,hakanan yana da wata irin zuciya wadda a duk sanda ta motsa sai kowa cikik gidan yaji a jikinsa. Duk da cewa ba kasafai yake irin wannan fushin ba,amma abu ne da kusan kowa na cikin gidan baya da burin gani a tattare da shi.

Har ta bude baki zatayi magana sai ta fasa,taja wani dogon tsaki tana dauke kanta daga gareshi. Ko ba'a gaya mata ba tasan shi da waye,yanzun nan ta wuce ta gabanta da wani mugun gudun data tabbatar ba lafiya ba.

"A kirawoshi ne hajiya?" Driver hamidou ya fada yana karya murya,saboda ya sani,ita daya ce tal a gidan zatayi furuci qwaya daya da zai dakatar dashi,duk kuwa irin girman fushin da ua debo. Yanayin fushin da ya shigo dashi din kuma ya bayyana muraran ba me sauqi bane,yasan kuma sahun wace ya biyo,ba zaiso kuma a taba lafiyarta ba,don akwai jituwa me yawa a tsakaninsu.

Harara ta watsa masa da fararen idanunta kamar zata cinyeshi danye

"Ban sakaka ba sarkin kankanba"

"Allah ya huci zuciyarki" ya fada yana bude mata motar. Fararen qafafunta ta zura ta shige abinta,cikin ranta tana addu'ar

"Allah yasa ya kakkaryata kowa ya huta" ta fada tana
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download GUDUN KADDARA

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album