Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

24 yin

MOTAR KWADAYI Complete Hausa Novel Document by MOTAR KWADAYI


MOTAR KWADAYI

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 13918



MOTAR KWADAYI

Reading Time: 1 Hours

Added On: 20, Jun 2024

Author: Rasheeda A Kardam ,Khadeeja Candy ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : Unknown group

Author Phone : Not Inserted

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 75.6 kb

File Type: txt

Views: 585+

Download: 249+

Last download: 1 day ago

Description/Story: Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
MOTAR KWADAYI-
Page1-to-end
OCTOBER 20, 2016 | RASHIDATKARDAM | 2
COMMENTS
[8:13AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
Bismillahi rahmanu rahim.
Dukkan yabo, godia da tsarki, Mulki, sun
tabbata ga ubangijin Al’arshi maigirma.
Sauri2take tafiya, duk da saurin da
takeyi, hakan ba zai hana ka gane, cikin
nutsuwa ta ke tafiyar ba, sanye take da
hijab dinta har kasa, kalo daya zaka
mata ka gane yarinyar yar mutumci ne,
kuma tana da hankali.
Kalo na kai duba zuwa ga fuskan ta ba
laifi, tana da dogon hanci, gata da
yalwan gashin gira, wanda ko da batai ja
gira ba, hakan ba zai boye kyan da Allah
ya mata ba, tana da yar kamar baki, sai
manyan idonta masu fisgan mutum, tana
da haske dai2 gwargwado, ko dana kara
kalonta, tana da dan zayi san’nan ba
za’a kirata da guntuwa ba, ba kuma
za’ace mata doguwa can ba, tana da
jikin ta dan dai2, abun sai wanda ya
gani.
A hankali ta rinka tafiya, har ta iso
gurin masu sai da icce, sallama ta musu,
tace baba mai ice aban dami daya, nan
ta mika masa naira hamsin, ta zabi mai
kyau, wanda tasan zai yi ci, daukowa
tayi, ta nufo gida, sauri takeyi don yau
basu daura girki da wuri ba, kasan
cewan yau Umman ta ke da girki, sauri
take har ta iso dan ma dai2cin kofar
gidansu, sam bata lura da addah Safiya
tana zuwa ba, sai ji tayi sun karo da
mutum, ga iccen ya bugeta soaai wani
uwar ashar ta narko, Ayshat tuni ta san
kame agurin, cikinta ya soma dura ruwa,
don ta san yau ta jaza musu kwandon
bala’i, bakin ta na bari, tafara Adda dan
Allah kiyi hakuri bada sani…… Ai bata
karasa ba ta ji saukar dun’du, a bayarta,
Inna safiya ce, tace wato bakin halin ki
da na uwarki da kika gado, ya sauko kan
tilon yata, yar gwal ko don kunga ku
bakin jini ya muku yawa, kin rasa mai
tayawa shiyasa za’a sauke akan diyata,
to ahirr… Bazaku iya ba, tayi muku nisa,
nan takama hannun safiya suka nufi
cikin gd, safiya sai wani karai raya
takeyi, ita ala dole mai kyau, kallo na
tsaya kare mata, ba laifi tana da kyau
dai2 gwargwado kuma farace ainun
amma ta hada da man bleaching, san
nan ga duk wanda yasan kyau, Aisha tafi
Safiya kyau ita dai safiya farinta yayi
yawa, gashi ta hada da man bleaching.
Aisha ta dau iccenta, jiki ba kwari ta
nufi cikin gd, da sallamarta, tashiga
dakunsu, nan ta tarar da ummanta, ta
zabga uban ta gumi da sauri tayi gunta
idonta fal da hawaye, tace ummah
banson kina wan’nan yawan tunanin zai
iya jawo miki matsala, wataran sai lbr,
kuma duk abunda yayi farko zaiyi
karshe, sai da ta tabbatar hankalin
umma ya kwanta, ta nufi kitchen don ta
musu aikinsu, Aysha kenan yarinya mai
hankali da nutsuwa.
…………. Na…..
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:13AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
BY
Rash kardam
&
Khadeeja Candy
Bayan sallar i’sha aysha na zaune tsakar
gida ita da qawarta karima suna fira,
Safiya ta fito sanye da wani material
riga da saker kayan sunyi mugun kama
jikinta ga wani shegen Show ur back
daya fitar mata da rabin waya waje sai
wani munafikin gyale data dora a
kafada ringing wayarta tayi da sauri ta
dannan receive ta kara a kunne ” gani
zuwa yanzu ”
Ido aysha da karima suka bita dasu tana
kashe wayar ta watso musu harara ” to
kashedi dai wlh nan gani nan bari nafi
karfin mutum tsaye da kyau zaune da
kyau son kowa kin wadda ya rasa ” ta
karasa maganar tana ya mutsar fuskar
Ta nufi kofa tana wani yauki wai ita ala
dole ga mai farin jini
Ajiyar zuciya aysha ta sauke karima ta
kalle tace ” tayi abunta banga laifinta ba
tana da daraja dan shiyasa a
samarukanta baba talaka ” kallon tsoro
aysha ta mata ” haba karima ai darajar
macce kyau tarbiyarta da kula da kare
mutuncinta ba wai tara samari masu
kudiba ko saka suturar banza ba dan
kinsan duk namijin kirki bazai zo yace
yana sonki ba kuma duk wadda ya ganki
cikin wannan shigar bazai ga mutuncin
kiba ” karima tace ” kuma fa hakane dan
wani lokacin zakiga yan iskan ma matar
kwarai suke nema in suka tashi aure
Allah dai ya shirya mu ” aysha tace amin
wannan ai zubarda kimane ( hmmm ina
ma yan matanmu zasu gane wannan ba
wayeba bane )
Karima ta tashi tana fadin maganar kifa
haka take amman fa gamai hankali
nikan na tafi aysha saida safe to saida
safe karima na gode sai mun hadi
school,
…………NA……
Rash Kardam
&
Khadeeja Candy
[8:14AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
Safiya ko tana fita, na hango wata
katuwar mota dan nesa da gidansu,
wanda garun gidan ya tsufa wani gun
ma har ya zube, sai wani yauki takeyi
tana karairaya kamar bazata taka kasa
ba, bakin nan yaci wani uban janbaki
24hrs, gsky ba laifi safiya tana da kyau,
shi yasa yake rudinta take wan’nan
rayuwan,( yan mata ina kira gareku da
babban murya, kar kuga Allah ya hore
muku kyau, ya rudeku ya kaiku ga wata
rayuwan da bata da amfani, rayuwa mai
cike da nadama acikinta, kusani duk
wanda ya hau “MOTAR KWADAYI” zai
sauka, tashar wulakanci, Allah ya
kyauta, ya Allah kabamu ikon tsare
mutuncin mu da kimar mu, dana
iyayenmu, Ameen).
Ta isa gurin motar nan ta bude kofar ta
shiga,ko da na kali na cikin motar
matashine baki ne sosai, yana da dan
kauri, baya da tsayi sosai, bai wani
haduba, in ka kalle shi ka ganta kasan
kudinsa tabi, don basu dace ba, Safsey
yau kin so ki bata lokaci, cikin yanga da
karairaya tace, sorry Mubson na dan
tsaya wani abune, yace, kai ya kada don
ya san halinta yana cewa zai nuna fushi
zata fita a motar, motar ya ja suka bar
unguwan.
Malam Muhammadu da ke nesa yana
kallon yarsan, kai ya kada zuciyarsa cike
da bakinciki amma bai isa ya tanka ba
uwarta zata mishi ba dadi, kwalla ne ya
cika idonsa, “mun tausaya masa.
………….Na………
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:14AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
Suna fita ostrich suka nufa, nan suka sha
ice cream dinsu, bayan sun danyi hira
kafin ya mata sayya sosai a laida, safiya
abun nima ya samu don duk lokacin da
saurayi zai kashe mata kudi, to saken
fiskanta da ban ne, gari suka zaga sai
10:00pm ya ajiyeta a kofar
gidansu,hakan ma saida suka danyi hira,
kafin ta marairace ta kashe murya tace
my mubarak dina, daman akwai wasu
yan kudi nakeso kaban zanyi amfani da
su, sai da yayi jim kafin ya ciro 10k ya
bata, bata waniyi murna sosai ba, sai
dan kawai bata da kudi ta bude kofar
motar ta fita ko godia babu, tana fita ya
girgiza kai safiya kenan ko godia babu
kamar ita ta nemo su,(kira gareku mata
kisani duk kan kancin kyautar da
mijinki zai miki kizama mai yawan
godia kina masa adu’ah da fatan alkairi
hakan na kara soyayya, bawai sai matar
aure ba, harda yan mata kina yawan
yima saurayin ki fatan al’kairi, riba biyi
ga yin masa adu’ah, gashi kikara saye
zuciyarsa ta yanda zaiji sonki sosai,
kuma zaiji dadi).
Tana shiga gida, ta ga ummin aysha
tafito daga bayi da buta a hannunta,
wani kalo mata kafin ta saki shewa
hehehe wasu bakin jini ya musu yawa ko
mashin shini babu, haka za’a kare acin
towo miyar kuka, su da cin mai dadi sai
dai suga anayi, “kunu a wani gida”,
umma ko ta kanta bata bi ba tashiga
daki, mamanta ne ta foto tana mata
kirari sai ke yar albarka, kin gadoni ga
farin jini ga kyau yar halak, sai wani isa
take ita a dole tafi kowa kyau da farin
jini, suka nufi dakinsu cikin murna.
WAYE MALAM MUHAMMADU, DA
IYALANSA?
Malam muhammad Sabo asalin sunan sa
kenan, malam haifafen cikin garin
kaduna ne unguwar tudun wada layin
yan kosai, yataso cikin so da kauna gun
iyayensa duk da talakawa ne amma suna
iya bakin kokarinsi su kyautata masa.
……Na……..
Rash Kardam
&
Khadija Candy
[8:14AM, 10/23/2016] Rash Kardam:
MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
&
Khadija Candy
Haka suka dage masa gurin karatun
addini, ahaka har yayi saukansa na
Al’qur’ani mai girma, bayan shekara 8
da saukarsa Allah yayi ma babansa
malam sabo rasuwa, bayan ya rasu haka
zaije yayi aiki ya dan samo musu na
abinci, ana cikin haka Allah ya hada shi
da uwargidansa wato Amina soyayan su
sukeyi sosai dakd irama iyayenta ba
wasu masu kudi bane, cikin ikon Allah
bai samu wahala gurin aurenta ba, akayi
biki dai2na talaka a ka kai amarya.
Suna zaune cikin kwqnciyan hankali da
soda kaunar junansu, haka rayuwansu
yayi ta tafiya har suka kai 4 yrs da aure,
amma shiru ba wani lbr ko batan wata
bata taba yiba, ana haka mahaifiyar
malam muhammadu ta tashi da
matsanacin ciwon ciki tun kafin akaita
asibiti Allah ya karbi abunsa sunyi yan
koke, bayan rasuwarta da shekara 2
yan’uwan mahaifin shi suka daga masa
hankali wai sai ya kara aure, don
matarsa juya ce su kuma suna son ganin
jikan dan’uwansu, duk suka tsan gwami
amina bata isa tayi abuba su mata caaa
a kai, wataran tayi kuka ta koshi harsai
ta gode Allah, san’n kulum tanata rokon
Allah ya bata yaya na gari masu
Albarka.
Wasa-wasa yau anshafe shekara da yin
maganar aure bako alamar haihuwa,
nan suka hura ma muhammadu wuta
dole ya sa ya fara neman shawaran
Amina ganin ba sarki sai Allah yasa tace
ya kara aure kawai, tasan Allah na tare
da ita, ciki ba kwari ya fara binciken
wace zai aura wanda bazata takura ma
Aminarsa ba, ana haka har Allah ya
hada
Domin cigaba da karantawa sai ku downloading.
Yadda ake downloading na littafin: ku tabbata kunyi register da shafinmu sanna kunyi login, idan bakuyi register a kasa zakuga maballai guda biyu daya an rubuta LOGIN dayan kuma an rubuta REGISTER sai ku taba su kuyi register, daga nan sai ku yi subscription koda na naira 1000 ne, domin sai kunyi subs dinann ne kadai zaku iya dauko littatafanmu.

Ya ya akeyin Subscription namu : Bayan kun yi Login ko register daga kasa zaku ga wani jan maballi (button) an rubuta SUBSCRIBE sai ku taba shi zai kaiku inda zaku zabi package wato tsarin subs na ku da mu. akwai na wata guda, watanni biyar da shekara guda. da zarar kun zaba zai kaiku inda zaku biya kudin, wanda daga nan sai ku cigaba da downloading kawai abunku

ABUN LURA : duk wani littafi da kuka gani a shafinnan kyauta ne, wannan tsari mun zo da shine don mu samu hanyar da zamu iya rike shafin muna managing na shi, izan ku kayi subs na mu tamkar DONATION ne ku ka yi mana, ku ka bamu kwarin guiwa don mu ciagaba da kawo muku sabbin littatafai, amma duk wanda ya ga bazai iya ba toh zai iya karanta littafin kyauta a cikin shafinnan namu batare da ya downloading ba, kawai ya yi kasa zai ga Koren maballi (button an rubuta) START READING sai ya taba zai kaishi inda zai karanta littafin.

Sannan duk wanda yaga kamn wannan process din zai bashi wahala kai tsaye zai iya min magana ta whatssApp +2348140419490, ya tura min kudin ni kuma zan dora mai subs din akan account na shi

NB: iya ta haka ne zaku iya karanta wannan littafi a shafinmu babu wata hanyar. DAN ALLAH KU DAINA MANA MAGANA AKAN MU TURA MUKU LITTAFI TA WHATSAPP, BAMA TURAWA HANYA GUDA MUKE TURA LITTATAFANMU SHINE WEBSITE NA MU https://taskarnovels.com.ng DUK MAI BUKATAR LITTAFINMU YA JE CAN YA KYAUTA NE, AMMA DOWNLOADING KUWA BA KYAUTA BANE SAI YAYI SUBSCRIPTION NA WEBSITE NAM
This is not the real Download Button


Read / Download MOTAR KWADAYI

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

This is not the real Download Button
Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album